Yahaya Sinwar
| Jagorancin Hamas da kuma yaƙi da Isra'ila | |
|---|---|
| Cikakken Suna | Yahaya Ibrahim Hassan As-sinwar |
| Laƙabi | Abu Ibrahim |
| Tarihin Haihuwa | 29 Oktoba 1962 miladiyya |
| Wurin Haihuwa | Khan Yunus Falasɗinu |
| Tarihin Shahada | 16 Oktoba 2024 miladiyya |
| Wurin Shahada | Rafa, kudancin Zirin Gaza |
| Ƴaƴa | Ibrahim da... |
| Addini | Muslunci |
| Mazhaba | Ahlus-Sunna |
| Muƙamai | Shugaban Hamas a Zirin Gaza/shugaban ofishin siyasa na Hamas, yana cikin mutanen da suka tsara Tufanul Al-Aksa |
| Bayan | Isma'il Haniyye |
Yahaya Sinwar, (Larabci: يحيى السنوار) rayuwa tsakanin 1962-2024 miladiyya, wanda ya kasance ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar gwagwarya ta Harkatu Hamas, wanda Isra'ila ta kashe shi a ranar 6 Oktoba 2024 miladiyya, an zaɓi Yahaya Sinwar matsayin shugaban sashen siyasa na Hamas bayan shahadar Isma'ila Haniyye[1] ya kasance kan wannan muƙami har zuwa lokacin shahadarsa. Yahaya Sinwar ya kasance cikin mutanen da suka tsara ofireshin ɗin Tufanul Al-Aksa (Wani ofireshin na musamman a cikin mamayayyar Falasɗinu).[2] Tun daga watan Fabrairu 2017 Sinwar ya kasance yana jogarantar Zirin Gaza.[3]] Sinwar ya kamanta yaƙin da Falasɗinawa suke yi da Isra'ila da yaƙin da sojojin Yazid suka yi da Imam Husaini (A.S) a shekara 61 hijira ƙamari, ya kuma ce: Wajibi ne mu ci gaba kan hanyoyin da muka fara, ko kuma dai mu bari a maimaita wata Karbala daban.[4]
Sinwar a ranar 16 Oktoba 2024 miladiyya, cikin wani rikici da ya kasance tare da sojojin Isra'ila a garin Rafa kudancin Zirin Gaza ne ya yi shahada. Sojojin Isra'ila sun ɗauki gawarsa sun tafi da ita mamayayyar Falasɗinu, labarin shahdarsa ya yi matuƙar yaɗuwa a kafafen watsa labarai.[5] Har ila yau, hallarar Yahaya Sinwar cikin yaƙoƙi daban-daban da kuma shahadarsa, lamari ne da ya ja hankalin tashoshin dandalin sada zumunta na yanar giza gizo.[6] Hotan gwagwarmayarsa a lokaci na ƙarshe a rayuwarsa a gaban Isra'ila, ya kasance hoto mafi tasiri a shekarar 2024 miladiyya, kan asasin ƙuri'un jin ra'ayi da tahsar rasad ta gudanar a ƙasar Misra.[7]
Ayatullahi Khamna'i, jagoran jamhuriyar Muslunci ta Iran cikin wani saƙo na ta'aziyya ya bayyana Yahaya Sinwar matsayin mujahidi jarumi da kuma fuska mai haske ga gwagwarmaya, wanda ya yi naushi mai nauyi da ba zai taɓa gyaruwa ba a ranar bakwai ga Oktoba (Ofireshin ɗin Tufanul Al-Aksa) wanda ya kasance rubutaccen tarihi da ba za a taɓa mantawa da shi ba a wannan yanki. Haka nan rashin wannan jarumi cikin gwagwarmaya lamari ne mai matuƙar raɗaɗi, sai dai kuma ya jaddada cewa shahadarsa da shahadar sauran kwamandojin gwagwarmayar Muslunci ba zai taɓa kawo cikas cikin ci gaban wannan yunƙuri ba..[8] Ƙungiyoyin gwagwarmaya misalin Hizbullahi Lubnan, Harkatu Jihadul Islami Falasɗin, Harkatu Nujaba Iraƙ, Harkatu Ansarullahi Yaman, Hizbullahi Iraƙ, cikin saƙo da ko wanensu ya fitar, sun yi ta'aziyya game da shahadar Yahaya Sinwar.[9] Bisa roƙon da Harkatu Hamas ta yi daga musulmin duk faɗin duniya game da yi wa Sinwar salatul ga'ib,[10]A ƙasase daban-daban na duniya Musulmi sun taru sun yi masa salatul ga'ib.[11] Cikin ƙuri'un jin ra'ayi da tashar Rasad Misra ta gudanar daga masu sauraronta daga Larabawa a ranar 30 Disamba 2024 miladiyya, an zaɓi Yahaya Sinwar a matsayin mutum mafi tasiri a duniyar Larabawa.[12] Har ila yau, a shekarar 2025 miladiyya ya kasance cikin jerin mutane hamsin masu matuƙar tasiri a duniyar Muslunci.[13]
An haifi Yahaya Sinwar a ranar 29 Oktoba 1962 a sansanin ƴan gudun hijira a yankin Khan Yunus da yake a kudancin Zirin Gaza. Babansa da babarsa sun fito daga garin Ishkilon, a shekarar 1948 miladiyya sakamakon yaƙin Isra'ila da kasashen Larabawa aka tilasta musu yin gudun hijira.[14] Yahaya Sinwar ya samu shaidar digiri na ɗaya daga Jami'ar Muslunci ta Gaza.[15] Sakamakon tuhumarsa da kashe sojojin Isra'ila guda biyu a shekarar 1988 miladiyya ne haramtacciyar ƙasar Isra'ila ta ɗaure shi a kurkuku ɗauri na dindin har ƙarshen rayuwa. Sai dai kuma bayan shekaru 23, a shekarar 2011m cikin wata musayar fursunoni da ta gudana tsakanin Isra'ila da Hamas ne ya shaƙi iskar ƴanci. A lokacin da Sinwar yake kurkukun Isra'ila ya koyi yaren Abraniyanci. Bayan sakinsa ya yi jawabi da harshen Abraniyanci zuwa ga Sahayoniyawa. Haka nan ya tarjama wasu rubuce-rubuce daga harshen Abraniyanci zuwa harshen Larabci.[16]
Bayanin kula
- ↑ «Hamas’s pick of Yahya Sinwar as leader makes a ceasefire less likely»، economist.
- ↑ «Hamas’s pick of Yahya Sinwar as leader makes a ceasefire less likely»، economist.
- ↑ «یحیی سنوار بار دیگر بهعنوان رئیس حماس در نوار غزه انتخاب شد»،Euro News
- ↑ «السنوار، نبرد غزه را به واقعه کربلا تشبیه میکند»،(Abna News Agency).
- ↑ «بازتاب شهادت یحیی سنوار در رسانههای خارجی»،Mashreq News.
- ↑ «"کرسی وکوفیة وعصا".. المشهد الأخیر للسنوار کما رآه مغردون»، Aljazira
- ↑ «بمشاركة 300 ألف شخص.. شبكة رصد تعلن نتائج استفتائها لعام 2024»، Tashar Rasad
- ↑ «پیام رهبر انقلاب اسلامی در پی شهادت مجاهد قهرمان، فرمانده «یحیی السنوار»»، Shafin yanar gizo na Ofishin Kula da Watsa Ayyukan Ayatollah Khamenei.
- ↑ «واکنشهای بینالمللی به شهادت یحیی سنوار»،Mashreq News
- ↑ «حماس تدعو لأداء صلاة الغائب علی الشهید القائد یحیی السنوار»Shafin yanar gizo na Harakar Ƙungiyar Ƙin Zalunci ta Musulunci Hamaas.
- ↑ Alal Misali ku duba «رفعوا صوره بالملاعب وأدوا صلاة الغائب.. المغاربة یتفاعلون مع استشهاد السنوار»، Aljazira.
- ↑ «بمشاركة 300 ألف شخص.. شبكة رصد تعلن نتائج استفتائها لعام 2024»، Tashar Rasad
- ↑ «Top 50-2025»، The Muslim 500.
- ↑ «یحیی السنوار أسیر محرر قاد حرکة حماس واستشهد فی مواجهة مع الاحتلال»، Aljazira.
- ↑ «یحیی السنوار أسیر محرر قاد حرکة حماس واستشهد فی مواجهة مع الاحتلال»، الجزیره.
- ↑ «یحیی السنوار أسیر محرر قاد حرکة حماس واستشهد فی مواجهة مع الاحتلال»، Aljazira.
Nassoshi
- «السنوار، نبرد غزه را به واقعه کربلا تشبیه میکند», Kamfanin Dillancin Labarai na Abna, labarin da aka buga: Yuni 13, 1403, ya ziyarci: Nuwamba 2, 1403.
- «بازتاب شهادت یحیی سنوار در رسانههای خارجی»،Labaran Mashareq, labarin da aka buga: Oktoba 17, 1403, an ziyarta: Oktoba 19, 1403.
- «پیام رهبر انقلاب اسلامی در پی شهادت مجاهد قهرمان، فرمانده «یحیی السنوار»», Yanar Gizo na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei, shigarwa: 18 ga Oktoba, 1403, ziyarci: 19 ga Oktoba, 1403.
- «حماس تدعو لأداء صلاة الغائب علی الشهید القائد یحیی السنوار», Gidan yanar gizon Hamas Islamic Resistance Movement, shigarwa: Oktoba 18, 2024, shigarwa: Oktoba 23, 2024.
- «رفعوا صوره بالملاعب وأدوا صلاة الغائب.. المغاربة یتفاعلون مع استشهاد السنوار», Al Jazeera, shigarwar labarin: Oktoba 19, 2024, Ziyara: Oktoba 23, 2024.
- «"کرسی وکوفیة وعصا".. المشهد الأخیر للسنوار کما رآه مغردون», Al Jazeera, Labari da aka buga: Oktoba 19, 2024, shiga: Oktoba 23, 2024.
- "واکنشهای بینالمللی به شهادت یحیی سنوار», Labaran Masreq, Ranar shigowa: 18 Oktoba 1403, Kwanan ziyarar: 3 Aban 1403.
- «یحیی السنوار أسیر محرر قاد حرکة حماس واستشهد فی مواجهة مع الاحتلال»،Al Jazeera, labarin da aka buga: Oktoba 18, 2024, shiga: Oktoba 21, 2024.
- «یحیی سنوار بار دیگر بهعنوان رئیس حماس در نوار غزه انتخاب شد»، یورونیوز.
- «بمشاركة 300 ألف شخص.. شبكة رصد تعلن نتائج استفتائها لعام 2024»، Tashar Rasad, kwanan shigarwa: Disamba 30, 2024, kwanan wata ziyara: Janairu 2, 2025.
- «Hamas’s pick of Yahya Sinwar as leader makes a ceasefire less likely»، economist.
- «Top 50-2025»، The Muslim 500, Accessed: 5 March 2025.