Jump to content

Fatahi Shaƙaƙi

Daga wikishia
Fatahi Shaƙaƙi
Wanda ya kafa Harikatu Jihadul Islam Falasɗinu kuma babban sakatare
Cikakken SunaFatahi Ibrahim Abdul-Aziz Shaƙaƙ
Tarihin Haihuwa4 Janairu 1951
Wurin HaihuwaFalasɗinu
Tarihin Shahada26 Oktoba 1995m
Wurin ShahadaWalta a ƙasar Malta
ƘabariMaƙabartar shahidai a sansanin `yan gudun hijira na Al-Yarmuk a Damishƙi
AddiniMuslunci
AikiLikita
MuƙamaiBabban sakataren Jihadul Islam Falasɗinu


Fatahi Ibrahim Abdul-Aziz Shaƙaƙi, ( rayuwa tsakanin 1951-1995, shi ne wanda ya kafa ƙungiyar jihadul Islam Falasɗinu, kuma ya kasance cikin fitattun ƴan gwagwarmayar neman ƴancin Falasɗinu daga mamayar gwamnatin Sahayoniyya. Bayan ya samu canjin tunani da ya samo asali daga shan kayen da ƙasashen Larabawa suka yi lokacin yaƙin 1967m da kuma tasirantuwa da ya yi da tunanin Sayyid Ƙuɗub da juyin juya halin Muslunci na Iran, sai ya assasa nazariyyar gwagwarmayar Muslunci.

Shaƙaƙi ta hanyar rubuta littafi mai suna "Khomaini hanyoyin samun mafita da mayi" ya gabatar da juyin juya halin Muslunci Tare da ƙarfafa hanyoyi guda uku na asali "Muslunci, Falasɗinu da Jihadi", ya nesanta kansa da shiga harkokin siyasa, ya fifita zaɓar hanyar gwagwarmaya ɗauke da makami.

A shekarar 1995 miladiyya, bisa umarnin firaministan Isra'ila na lokacin, kuma ta hannun hukumar leƙen asiri ta Isra'ila wace ake kira da "Mossad" ne suka kai farmaki kan Shaƙaƙi tare da hallaka shi, da wannan ne ya rabuta da samun shahada, an binne Shaƙaƙi a Damishƙi ƙasar Siriya, kashe shi da Isra'ila ta yi ya fuskanci martani da ƙungiyoyi da ƙasashen Muslunci, daga jumlarsu Ayatullahi Khamna'i, jagoran Iran ya fitar da saƙon ta'aziyya kan shahadarsa.

Muhimmanci Da Matsayi

Fatahi Shaƙaƙi yana daga cikin sanannun ƴan gwagwarmayar Falasɗinu, kuma ya kasance babban sakataren ƙungiyar jihadul Islam Falasɗinu tsakanin shekarun (1979-1995m).[1] Bayan zurfafa karatu a fanni lissafi da likitanci, sai ya shagaltu da ayyukan yaƙar Isra'ila ta ɓangaren al'adu da soja. Shaƙaƙi tare da wallafa littafin "Khomaini hanyoyin samun mafiya da mayi" ya gabatar da juyin juya halin Muslunci na Iran matsayin abin kwaikwayo cikin farkawar Muslunci, sannan ya fara gaggauta kafa ƙungiyar jihadul Islami. Ya yi imani da asalai guda uku, Muslunci, Falasɗinu da Jihadi, waɗannan abubuwa uku sune suke samar da gwagwarmaya ta gaskiya, kuma ya yi watsi da duk wani kira na sulhu da Sahayoniyya.[2]Ya na ganin ranar ƙudus ta duniya a matsayin ranar raya Muslunci da raya jihadi kan Sahayoniyya, kuma rana ce abar girmamawa.[3]

Tarihin Rayuwa

An haifi Fatahi Shaƙaƙi a ranar 4 Janairu 1951m, a sansancin na Rafa a Gaza..[4] Mahaifinsa ya kasance lebura ɗan ƙwadago kuma limamin ƙauyen Zanuƙa.[5] Ya yi karatun firamare da sakandire a makarantun hukumar jin ƙai ta (UNRWA) a sansanin ƴan gudun hijira na Rafa, bayan sai ya shiga jami'ar Birzeit Uniɓersity da take kusa da garin Ramallah a gaɓar jogin Jodan, bayan nan a ƙoƙarinsa na ci gaba da karatu a fannin likitanci sai ya shiga jami'ar Zaƙariƙ ta Misra.[6]

Bayan dawowa daga Misra, da farko ya fara aiki a asibitin Biktoriya a Baitul Muƙaddas bayan nan sai aka zaɓe shi a matsayin likitan ƙananan yara a Zirin Gaza.[7]

Kisan Gilla Da Kuma Shahada

A ranar 26 Oktoba 1995 miladiyya, a Walta babban birnin ƙasar Malta ne ma'akatan ƙungiyar leƙen asiri ta Mossad suka hallaka Fatahi Shaƙaƙi.[8] Is'haƙ Rabin, firaministan Isra'ila na lokaci shi ne da kansa ya bada umarni wannan ta'addanci.[9]

ƙungiyoyin, da ɗaiɗaikun fitattun mutane da ma ƙasashen Muslunci sun yi martani kan shaharSa.[10] A ƙasar Iran, Ayatullahi Khamna'i, jagoran juyin juya halin Muslunci bayan Imam Khomaini, cikin saƙon ta'aziyya da ya fitar, ya bayyana Fatahi Shaƙaƙi a matsayin mujahidin, jarumi kuma muklisi, ya kuma jaddada cewa Fatahi ya kasance cikin haskakan fuskokin gwagwarmayar Muslunci da al'ummar Falasɗinu ta samar.[11] Bisa la'akari da tasirantuwar Fatahi da shi'anci[12] an ce gabanin shahadarsa ya zama ɗan shi'a.[13]

Am binne Fatahi Shaƙaƙi a maƙabartar shahidai da take sansanin ƴan gudun hijira da yake Yarmuk Damishƙi babban birnin ƙasar Siriya.[14]

Tunaninnikan Siyasa Da Ayyukan Gwagwarmaya

Bayan shan kaye da Larabawa suka yi a yaƙin 1967 miladiyya, Fatahi Shaƙaƙi ya samu sauyin tunani, ta yadda ya tasirantu da tunanin Sayyid Ƙuɗub da juyin juya halin Muslunci na Iran.[15] Ya yi imani da cewa "Muslunci, Falasɗinu da Jihadi" su ne runai uku na asalin gwagwarmaya, kuma duk wani yunƙurin sulhu da gwamnatin Sahayoniyya, abin watsi ne..[16]Har zuwa ƙarshen kwanakin rayuwarsa ya ci gaba da tafiye-tafiye tsakanin manyan biranen ƙasashen Larabawa da Musulmi domin ba da kariya ga manufofin Falasɗinu, da goyan bayan mahangarsa game da gwagwarmaya ɗauke da makami..[17]

Shaƙaƙi a cikin littafin “Al-Imam Khomaini Al-Hallul Islami Wal-Badil” a shekarar 1979m, littafi na farko cikin harshen Larabci da aka rubuta game da juyin juya halin Muslunci na Iran wanda aka sanya shi maye gurbin tunanin gabashin duniya da yammaci.[18] Yaɗa wannan littafi ya jawo hukumar Misra ta kama shi tare da tsare shi.[19]Shaƙaƙi ya ƙarfafa haɗin kan Musulmi kai hatta kiristoci Falasɗinawa cikin yaƙar mamayar Isra'ila, yana la'akari da jihadi na Muslunci matsayin wata ƙungiya ta yunƙurin juyin juya halin Muslunci wace bai kamata ta kutsa kanta ba cikin fagagen siyasa ba.[20]

Kafa ƙungiyar Jihadul Islami Falasɗinu

Fatahi Saƙaƙia ƙarshe-ƙarshen shekarar 1970 miladiyya, tare da wasu jama'a daga ɗaliban jami'a Falasɗinawa a Misra, suka kafa ƙungiyar Jihadul Islam Falasɗinu, daga jumlar membobi da suka assasa wannan ƙungiya, akwai Ramadan Shala, Abdullahi Asshami da Abdul-Aziz Auda..[21] An ce, wannan ƙungiya tare da jaddada aniyarta kan gwagwarmaya ɗauke da makamai da kuma nisantar harkokin siyasa, kuma tafi samun ƙarfafa alaƙa tsakaninta da Iran fiye da Hamas.[22]


Zaman Kurkuku Da Kuma Kora

A shekarar 1983 miladiyya, gwamnatin Sahayoniya suka kama Fatahi Shaƙaƙi tare da ɗaure shi har tsawon shekaru 11 a kurkuku. Har ila yau, a shekarar 1986m, nan ma bisa tuhumar kai makamai Zirin Gaza, an ɗaure shekaru huɗu, a shekarar 1988m nan ma an kore shi zuwa ƙasar Labanun.[23] A lokacin korarsa sai ya ci gaba da ayyukan siyasa da soja, ya kuma kasance mai shiga Tsakani nu kusa-kusa tare da jamhuriyar Muslunci ta Iran da Hizbullahi Lubnan.[24]

Bayanin kula

  1. Royvaran, Inqilabe Islami Iran Az Negahe Shahid Fatahi Sahaqaqi, shafi na gaba. 45.
  2. شقاقی - فتحی ابراهیم، Daneshnameh Falasdin.
  3. Ruzeshomare Tarikh, 2011, shafi na 2980
  4. فتحي الشقاقي، Aljazira.
  5. مؤسس "الجهاد" فتحي الشقاقي، Almayadeen.
  6. Hazrati, Khorshid Dar Sayeh, 2018, shafi na 287
  7. فتحي الشقاقي، Aljazira.
  8. Ruzeshomare Tarikh, 2011, shafi na 2981
  9. ترور رهبران مقاومت،Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
  10. شقاقی - فتحی ابراهیم،Daneshmaneh Falastin.
  11. پیام تسلیت در پی شهادت دکتر فتحی شقاقی رهبر جهاد اسلامی فلسطین،Ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei.
  12. Shahadah, al-Masua al-Shalimeh, 2010, juzu'i na 3, shafi na 202.
  13. مزار شهید «فتحی شقاقی» قبل از تخریب، Kamfanin dillancin labarai na Abna..
  14. مزار شهید «فتحی شقاقی» قبل از تخریب،Kamfanin dillancin labarai na Abna..
  15. شقاقی - فتحی ابراهیم، Daneshnameh Falastin؛ زندگینامه دکتر فتحی شقاقی، Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr.
  16. شقاقی - فتحی ابراهیم، ، Daneshnameh Falastin.
  17. فتحي الشقاقي، Aljazira.
  18. Khamenei, Tawahhum Sulte, 2013, shafi na. 482.
  19. فتحي الشقاقي، Aljazira.
  20. دیدگاه‌ رهبران فلسطینی درباره دوگانه سازش و مقاومت،Khabar Online.
  21. مؤسس "الجهاد" فتحي الشقاقي، Almayaden.
  22. دیدگاه‌ رهبران فلسطینی درباره دوگانه سازش و مقاومت، Khabar Online.
  23. فتحي الشقاقي، Aljazira.
  24. دکتر فتحی شقاقی؛ بنیانگذار جنبش جهاد اسلامی فلسطین، Kwalejin Uriha.

Nassoshi

زندگینامه دکتر فتحی شقاقی، خبرگزاری مهر، تاریخ انتشار مطلب: ۷ آبان ۱۳۸۴ش.