Sayyid Hassan Nasrullah

Daga wikishia
Sayyid Hassan Nasrallah

Sayyid Hassan Nasrullah (Larabci: السيد حسن نصرالله) "Rayuwa: 13 ogusta 1960-27 satumba 2024" malamin addini kuma ɗan siyasa ɗan shi'a mutumin ƙasar labanun, mutum na uku cikin jerin Manyan Sakatarorin ƙungiyar gwagwarmaya ta hizbullahi lubnan, Sayyid Hassan Nasrullah ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da suka kafa ƙungiyar hizbullahi lubnan, a zamanin shugabancinsa ƙungiyar hizbullah ta zama wani ƙarfi na soji da siyasa a yankin gabas ta tsakiya.

ƴanto kudancin labanun daga hannun ƴan mamaya na isra'ila da cin nasarar a yaƙin kwanaki 33 da ya faru tsakanin dakarun hizbullahi da sojojin haramtacciyar ƙasar isra'ila a shekarar 2006 duka sun faru lokacin jagorancinsa. Da wannan dalili ne aka sama suna Sayyidul muƙawama (Shugaban gwagwarmaya), haka nan sakamakon cin nasara a lokuta daban-daban kan sojojin haramtacciyar ƙasar isra'ila an gabatar da shi matsayin mutum mafi farin jini ko kuma jagoran duniyar larabawa da gabas ta tsakiya.

Nasrullah ya yi karatu a hauzar ilimi ta birnin najaf da take ƙasar Iraƙi, da hauzar Imamul Al-muntazar da take Ba'alabak labanun, ya kassance cikin almajiran Sayyid Abbas Musawi, haka nan cikin wani taƙaitacen lokaci ya halarci darasussukan malamai misalin Sayyid Mahmud Hashimi, Sayyid Kazim Ha'iri da Muhammad Fazil Lankarani a birnin ƙum na ƙasar Iran.

Sayyid Hassan Nasrullah a shekara ta 1975-1982, ya kasance memba a ƙungiyar Janbeshe Amal, wata ƙungiya ce ta siyasa ta `yan shi'a a ƙasar Labanon. Amma a shekara ta 1982 tare da gungun malamai masu fafutuka suka ɓalle daga wannan yunƙuri na ƙungiyar Amal, sannan suka kafa kungiyar Hizbullah a ƙasar Labanon.

Bayan shahadar Sayyid Abbas Musawi a ranar 16 ga Fabrairu, 1992, an zabe shi a matsayin babban sakataren ƙungiyar Hizbullah, kuma yana kan wannan matsayi har zuwa shahadarsa a shekarar 2024/1403. Sayyid Nasrallah, a lokacin da yake rike da muƙamin Sakatare-Janar ya yi tuntuɓar juna da kuma ganawa da jagororin gwagwarmaya.

Hassan Nasrullah, ranar juma'a 27 ga watan satumba shekara ta 2024 m, ya rabauta da samun shahada sakamakon harin jiragen sama da suka jefa masa bom da haramtacciyar ƙasar isra'ila ta kai kudancin labanun, martani daban-daban ya biyo bayan fitar labarin tabbatar da shahadantar da shi. Sayyid Ali Khamna'i, jagoran jamhuriyar muslunci ta Iran, maraji'an taƙlidi misalin Sayyid Ali Sistani, Nasir Makarim Shirazi, Husaini Nuri Hamdani. Subhani, Shubairi Zanjani, Jawadi Amoli, Bashir Najafi da shuwagabanni da kuma ƙasashe daban-daban da ƙungiyoyin gwagwarmaya misalin ƙungiyar hamas, ƙungiyar Jihad Islami Palasɗin, ƙungiyar Ansarullahi Yaman, ƙungiyar fatahu, ƙungiyar Asa'ibu Ahlil Haƙƙi, ƙungiyar Amal Lubnan, Tayyar Hikima Al-hikima Al-watani, Tayyar Sadar, dukkaninsu cikin fitar da bayani sun yi ta'aziyyar shahadar Sayyid Hassan Nasrullahi tare kuma da alawadai da harin ta'addanci isra'ila da ta yi kansa wanda ya yi sanadiyar shahadarsa. ƙasar Iran ta shelanta zaman makoki na kwanaki biyar sannan a ƙasashen labanun, siriya, Iraƙi da yaman an shelanta makokin kwanaki uku. Nasrullahi kafin shahadarsa a lokuta da daman gaske cikin shekarun 2004, 2006, 2011 sojojin haramtacciyar ƙasar isra'ila sun kai hare-hare kansa tare da yunƙurin hallaka shi amma cikin taimakon Allah ya tsallake rijiya da baya ya kuɓuta daga lafiya lau ba tare da taɓa lafiyarsa ba. ɗansa Sayyid Muhammad Hadi Nasrullahi a cikin shekarar 1997 bayan ɗauki ba daɗi da suka yi da dakarun haramtacciyar ƙasar isra'ila ya rabauta da shamun shahada.

Sayyidul Muƙawama Da Ɗauki Ba Daɗi Tare da Ƴan Mamaya

Sayyid Hassan sakamakon rawar da ya taka cikin kwato yankin kudancin labanun , [1] a shekarar 2000 bayan mamayar isra'ila ta yi da ya ɗauki tsawon shekaru 22 da kuma cin nasara da hizbullahi lubnan suka yi a yaƙin kwanaki 33 da ya faru a shekarar 2006m an masa laƙabi da taken Sayyidul muƙawama.[2]

Nasrullah sakamakon gwagwarmaya da kuma irin nasarori da hizbullahi suka dinga samu lokacin jagorancinsa ya zama mutum mafi farin jini a duniyar muslunci,[3] duniyar larabawa[4] kuma an gabatar da shi shugaba mafi farin jini da iko a ƙasashen larabawa na yankin gabas ta tsakiya.[5] Sayyid Nasrullahi mutum mai kaifin harshe da fasahar bayani wanda haka ya taimaka cikin ƙara ƙarfafar farin jini da tasirinsa cikin al'umma.[6] bisa naƙalin jaridar Euronews jaridar harshen turanci daga Associated Press, Sayyid Hassan Nasrullah mutum ne da ya samu ƙarɓuwa da girma wurin miliyoyin al'ummar larabawa da musulmi a faɗin duniya.[7] Euronews sun gabatar da Sayyid Nasrullah matsayin babban maƙiyin isra'ila da ƙasar Iran take ƙawance da shi..[8]

Jawabin Sayyid Hassan Nasrullah: Mun amsa kiranka ya Husaini

Babban Sakataren Ƙungiyar Hizbullahi Lubnan

Sayyid Hassan Nasrullah bayan shahadar Sayyid Abbas Musawi a ranar 16 ga watan fabrairu shekarar 1992 m, bayan taro da membobin ƙungiyar hizbullahi lubnan suka yi an naɗa shi matsayin babban sakataren ƙungiyar hizbullahi.[9] yayin karɓar wannan muƙami ya kasance yana da shekaru 32 a duniya.[10]

An ce a lokacin shugabancinsa ƙungiyar hizbullahi lubnan ta canja ta zama wani ƙarfi na siyasa da soji a yankin gabas ta tsakiya[11] hizbullahi sun samu nasarrori daban-daban mafi muhimmanci daga cikin su ita ce nasarar ƴanto yankin kudancin labanun daga mamayar haramtacciyar ƙasar isra'ila a shekarar 2000 m. da kuma cin nasara a yaƙin kwanaki 33 da suka yi da isra'ila a shekarar 2006, da fatattakar ƙungiyoyin ƴan ta'addan takfiriyya a shekarar 2017.[12] rawar da Nasrullahi ya taka cikin musayar fursunoni da aka yi tsakanin hizbullahi da kuma karɓo gawarwakin shahidan hizbullahi daga hannun isra'ila a shekarara 2004 ana ganin haka wani babban makulli da ya buɗe ƙofofin nasarori da aka samu daga bay.[13] Hizbullahi lokacin jagorancin Sayyid Hassan Nasrullahi sun kutsa fagen siyasa, ba'ari daga membobinta sun lashe zaɓen kujerun ƴan majalisu wanda hakan ya basu damar shiga majalisar dokokin labanun.[14] Hizbullah dai ta shiga harkokin siyasa ne a zamanin Sayyid Hassan, kuma wasu daga cikin mambobinta sun shiga majalisar dokokin ƙasar Labanon.[15]

Sayyid Hassan Nasrullah ya kasance mutumin da haramtacciya ƙasar isra'ila ta sanya shi cikin jerin mutane da take da shirin hallaka rayuwarsu, an ce tun daga shekarar 2006m[16] sakamakon tsanantar barazana kan hallaka shi hakan ya tilasta masa ɓuya da taƙaita bayyana cikin jama'a.[17] maimakon yin jawabi cikin taron jama'a sai ya koma amfani da kafar sadarwa cikin gabatar da jawabi ga al'umma.[18] Sayyid Hassan Nasrullah yana ganin hizbullahi matsayi wata ƙaya kan idanun amurka kuma ta kasance wata babbar katanga da ta hana isra'ila cimma burinta na mamaye ƙasar labanun.[19]

Jawabin Sayyid Hassan Nasrullah A Ranar Ashura Shekara 2012m
Da ruhinmu da ’ya’yanmu da dukiyoyinmu, sai mu ce wa Hussaini (A.S.): "Labaika Ya Husain". Ba za mu juya wa wannan yarjejeniya da gayyatar ba... Zuwa ga duk azzalumanku dawagitrai, masu keta alfarma, masu fasadi, masu neman dama da masu karya karfin zuciya, mun daura damara mun tsaya kyam, Ƙudurinmu da tsayawarmu a rufe suke. Muna cewa mu ’ya’yan wancan imamin ne, maza da mata, kuma `yan`uwan wadannan matasan da suka tsaya tare da Hussaini a ranar Ashura. Kuma sun maimaita wannan jumlar ta Hussaini tana magana ne akan tarihi "Haihata minnaz zilla"

[20]

Alaƙa Tare da Ƙungiyoyin Gwagwarmaya

Sayyid Hassan Nasrullah kodayaushe ya kasance yana da alaƙa ta kusa-kusa da mihwarin muƙawama. ya ba da haɗin kai tare da jagororin Iran da ƙungiyoyin gwagwarmayar kwaton ƴancin palasɗin misalin Hamas.[21] lokacin da isra'ila ta fara zafafa kai hare-haren kisan kiyashi a kan al'umma zirin gaza, bayan ofireshin ɗin ɗufanul al'aƙsa, ya samar da wasu dakaru da za su taimakawa al'ummar palasɗin cikin yaƙar isra'ila da taka mata burki daga ci gaba da kisan ƙare dangi har zuwa ƙarshen yaƙin gaza.[22] lokacin shugabancin Nasrullah sun samu kyakkyawar alaƙa da ƙungiyar Amal ta labanun.[23]

Sayyid Hassan Nasrallah (mutum na farko a hannun dama) da Sayyid Abbas Musawi (mutum na farko a hagu) sun gana da Ayatullah Khamenei (1370).

Alaƙarsa Tare da Iran

Sayyid Hassan Nasrullah yana kyakkyawar dangantaka da alaƙa da shuwagabannin ƙasar Iran,[24] Lokuta daban-daban ya yi tafiya zuwa Iran sannan ya gana da jagororin ƙasar, farkon zuwansa Iran ya kasance a shekara ta 1360[25] ko 1361shamsi [26] Ya gana da Imam Khumaini a Hosseinieh Jamaran. A shekara ta 1365 shamsi, ya kuma ya je ziyarar Imam tare da 'yan Hizbullah. Ganawarsa ta ƙarshe da Imam Khumaini ita ce ‘yan watanni kafin rasuwar Imam da kuma rikicin kungiyar Amal da Hizbullah..[27]

Kamar yadda ya zo a cikin tarihin rayuwar Sayyid Hassan Nasrallah, dangantakarsa da Ayatullah Khamna'i ta fara ne a shekara ta 1365 shamsi.[28] lokuta da dama ya gana da sojoji da jami'an ƙasar Iran misalin Ƙasim Sulaimani da Husaini Amir Abdullahiyan ministan harkonin ƙasar waje na wancan lokacin.[29]

Nasrullah yana ɗaukar Iran matsayin babbar masoyiya da take bai wa Hizbullahi kariya da goyan baya, kuma ita ma Hizbullahi a gefe guda tana kare Iran da maslahohinta..[30] daga jumlarsa goyan baya da hizbullahi tana nuna Iran ana iya ishara da matsayar da ta ɗauka bayan harin da Isra'ila ta kai kan ofishin jakadancin Iran da da yake dimashƙi ƙasar Siriya, Sayyid Hassan Nasrullahi ya fito ƙarara ya bayyana cewa haƙƙin Iran ta bada amsa kan harin ta'addanci da isra'ila ta kai mata.[31] kuma ya kasance yana alfahari da ƙawance da suke yi da ƙasar Iran.[32]

A watan Nuwamban shekarar 2009m, Hassan Nasrallah ya ba da sanarwar tare da gabatar da sabuwar takardar siyasa ta Hizbullah, wadda ake ganin daya daga cikin manufofin wannan kungiyar shi ne lazimtar wilayatul Faƙihi da kuma ɗaukarsa matsayin layin da za a tafi a kansa.[33] a cewar tashar Aljazira,[34] da Euronews,[35] ba'arin masana da kuma masu adawa da hizbullahi da jagoranta Sayyid Nasrullah matsayin suna ɗaukarsu matsayin yaran Iran da wakilanta da suke kare manufofi da maslahohin Iran a ƙasar labanun.[36]

Sayyid Hassan Nasrullah
Mun yi imani cewa Yazidu na wannan zamani wanda ya zama wajibi mu tunkare shi mu yaƙe shi kamar a filin karbala kamar misalin zainabawa ba kowa bane ba komai ba ne sai manufar amurka da sahayoniya, wata manufa ce da take barazana ga al'umma da wayewarta, addinan sama da abubuwa masu tsarki. mun kasance zainabawa husainawa gaban wannan ƙuduri da manufa da sahayoniya da amurka, tunƙarar wannan ƙuduri a wurin mu shi ne abu na farko da ya wajaba kan mu.[37]

Tarihi Da Karatu

Sayyid Hassan Nasrullah, ya kasance daga fitattun mutane masu farin jini a wurin al'ummar lubnan a ranar 31 ga watan oktoba shekarar 1960[38] ko 1962 m, [39] aka haifi Sayyid Hassan Nasrullah a wata unguwa ta talakawa da ake kira da suna karantina a gabashin bairut,[40] mahaifinsa Sayyid Abdul-karim da mahaifiyarsa Nahdiyya Safiyud-dini,[41] sun kasance mutanen ƙauyen baruziyya jihar Sur kudancin ƙasar labanun da suka yi hijira zuwa babban birnin kubnan.[42] a wasu madogarai an ce an haife shi ne a ƙauyen Al-baruziyya.[43] Sayyid Hassan Nasrullah yana da ƴan uwa maza guda uku da mata guda biyar..[44] lokacin samartakarsa ya kasance yana sayar da kayan marmari a wani shago tare da ɗan uwansa.[45]

Sayyid Nasrullah ya yi karatun firamare cikin makarantar Annaja a yankin tarbawiyya, bayan fara yaƙin basasa yaƙin cikin gida a shekarar 1975 ya shi da ɗan uwansa da danginsu sun koma ƙauyen al-baruziyya mahaifar babansa, ya ci gaba da karatun sakandire a jihar sur. [46]

Sayyid Hassan, a cewarsa, tun yana yaro ya kasance yana sha’awar makarantar hauza, amma iyayensa sun yi adawa da hakan[47] A shekarar shekarar 1976m sakamakon ƙarfafawa da kwaɗaitar da shi da Sayyid Muhammad Garawi limamin juma'a a garin Sur kuma ɗaya daga abokan Sayyid Muhammad Baƙir Sadar ya yi kan karatun addini, Sayyid Hassan Nasrullah ya yi hijira zuwa birnin najaf domin karatun addini, Sayyid Muhammad Garawi cikin wata wasiƙa da ya rubuta ya gabatar da Sayyid Nasrullah ga Sayyid Muhammad Baƙir Sadar, Sayyi Sadar ya sanya Sayyid Abbas Musawi matsayin wanda zai kula da karatun Nasrullah da sauran buƙatunsa na ɗalibta.[48] A shekarar 1978 m, Sayyid Hassan ya kammala marhalar darasussukan sharar fage a hauza ilimiyya, bayan shekaru biyu na zamansa a Najaf, sakamakon matsin lamba daga gwamnatin ƴan ba'as ta Iraƙi,[49] ya koma labanun, bayan kafa hauzar Imam Muntazar a garin ba'alabak a shekarar 1979 m, Sayyid Hassan Nasrullah ya ci gaba da karatunsa na hauza kuma yana koyarwa.[50] a shekarar 1989 [51] ko 1990m,[52] tsawon shekara ɗaya[53] ya je ƙum domin ci gaba da karatun addini., lokacin zamansa a ƙum ya halarci darasin Sayyid Mahmud Hashimi, Sayyid Kazim Ha'iri da Muhammad fadil Lankarani.[54] dalilin komawarsa gida wata jita-jita ce da ta yaɗu wai an samun tsanantuwar rigima tsakanin Hzibullahi da ƙungiyar Amal.[55]

Bayanin rayuwar Sayyid Hassan Nasrallah

Baya ga karatunsa, Nasrallah ya kuma kammala horon soji daban-daban da kwasa-kwasan dabarun tunkarar ƴan ta'adda[56]

Matarsa Da ƴaƴansa

A shekarar 1978 m, lokacin yana da shekara 18 a duniya ya auri Faɗima Yasin wace ta haifa masa ƴaƴa maza uku, su ne Muhammad Hadi, Muhammad Jawad da Muhammad Ali da kuma ƴa mace guda mai suna Zainab.[57]Sayyid Muhammad Hadi babban ɗan Sayyid Nasrullah a ranar 12 ga watan satumba shekarar 1997 ya yi shahada baya ɗauki ba daɗi da suka da sojojin isra'ila a kudancin labanun, gawarsa ta kasance hannun isra'ila, bayan shekara ɗaya sun bada gawarsa a wani musayen fursunoni tsakanin hizbullahi da isra'ila.[58]

Ayyukan Siyasa Da Zamantakewa

Sayyid Nasrullah a farko-farkon rayuwarsa ya fara da shiga fagen siyasa. Ba'arin ayyukansa a fagen siyasa su ne kamar haka:

Sayyid Hassan Nasrallah A Lokacin Samartaka
  • Sakamakon alaƙarsa da Sayyid Imam Musa Sadar, a shekarar 1975 m, bayan kammala karatun sakandire ya zama memba a ƙungiya amal tare da ɗan uwansa Sayyid Husaini, ya kuma kasance wakilin ƙungiyar amal da ƙauyen baruziyya.[59]
  • A shekarar 1982 ya kasance memba a kwamitin siyasa na ƙungiyar amal, kuma shi ne ke wakilcin wannan ƙungiyar a yanƙin baƙa'u.[60]
  • A shekarar 1982 m, bayan isra'ila ta mamaye labanun da kuma bijiro da ƙudurin yin sulhu tsakanin isra'ila da ƙasar labanun, Sayyid Hassan Nasrullah tare da wasu jama'a daga malamai misalin Sayyid Abbas Musawi da Subhi ɗufaili sun tattara inasu inasu sun fice daga ƙungiyar amal, su ne suka fara assasa tubali na farko cikin kafa ƙungiyar hizbullahi lubnan.[61]
  • A shekarar 1985m an naɗa shi wakilin hizbullahi lubnan a yankin baƙa'u.[62]
  • A shekarar 1987m ya zama shugaban kwamitin gudanarwa da kuma majalisar shura ta ƙungiyar hizbullahi.[63]
  • Daga shekarar 1989 zuwa 1990 Sayyid Hassan Kuma kasancewarsa a birnin ƙum shi ne wakilin kungiyar Hizbullah a Tehran kuma shi ne ke da alhakin bin diddigin ayyukan Hizbullah a Iran. [64]
  • Shekarar 1992 Har ila yau, tare da kashe Sayyid Abbas Mousaɓi, an zabe shi a matsayin babban sakataren kungiyar Hizbullah.[65]
  • A shekara ta 1360 shamsi, Sayyid Hassan ya samu izinin karbar haƙƙoƙin Shari'a da kuma samun iznin amfani da su cikin ayyukan hisba da shari'a. [66] har ila yau ya kasance wakilin Ayatullahi Khamna'i a garin Bairut da Jabal Amil. [67]

Shahada

Sakon ta'aziyyar Ayatullah Khamna'i Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran
Babban Mujahidi jagoran masu fafutuka a yanki. Fitaccen malamin addini kuma jagoran siyasa, Sayyid Hassan Nasrallah Rizwanullah alaihi, ya samu falalar shahada a cikin daren jiya a kasar Labanon inda ya tashi zuwa wurin mahaliccinsa. Sayyed Aziz mukawama ya samu ladan Jihadi na tsawon shekaru goma da sunan Allah da wahalhalun da ya fuskanta a lokacin gwagwarmaya mai tsarki... Falalar shahada ta kasance musullaminsa dama bayan kokari da yawa. Duniyar Musulunci, mutumci mai girma; Sannan kuma kungiyar gwagwarmaya ta yi rashin wani fitaccen mai rike da tuta, kuma Hizbullah ta yi rashin shugaba mara misaltuwa, amma albarkacin Jihadin da ya kwashe shekaru da dama ana yi ba zai taba rasa ba. Harsashin da ya kafa a Lebanon ya kuma ba da jagoranci ga sauran cibiyoyin juriya. Da rashinsa,gwagwarmaya bawai kawai ba za ta gushe ba, a'a, da albarkar jininsa da sauran shahidai, wannan lamari zai kara karfi. Hare-haren da 'yan adawar suka kai kan tsohuwar gwamnatin Sahayoniya da ta lalace kuma za ta fi daukar hankali. Mummunar dabi'ar gwamnatin Sahayoniya ba ta yi nasara ba a cikin wannan lamari. Jagoran juriya ba mutum ba ne, hanya ne kuma makaranta, kuma haka za a ci gaba. Jinin shahidi Sayyid Abbas Musawi bai tsaya a kasa ba, haka nan jinin shahidan Sayyid Hassan ba zai tsaya a kasa ba.[68]

Tushen ƙasida: Hallaka Hassan Nasrullah

A ranar juma'a 27 ga watan satumba shekarar 2024m bayan harin jiragen isra'ila a wani gini a kudancin labanun Sayyid Hassan Nasrullah ya rabauta da shahada, sojojin haramtacciyar ƙasar isra'ila sun yi da'awa cewa wannan wuri da suka kai hari cibiya ce ta jagororin ƙungiyar hizbullah da suke amfani da wurin domin shirya zama na sirri.[69] Sojojin Haramtacciyar gwamnatin sahayoniya sun yi ikirarin kai hari a cibiyar kwamandojin kungiyar Hizbullah da wurin taron[70] Bayan wannan harin sojojin Isra'ila sun sanar da mutuwar Sayyid Hasan Nasrallah da wasu kwamandoji irinsu Ali Karki.[71] ranar asabar 28 ga watan satumba shekarar 2024m ƙungiyar hizbullahi lubnan sun sanar da shahadar Sayyid Hassan Nasrullah.[72] haka nan a haramin Imam Rida (A.S)[73] an sanar da tabbatar da shahadarsa.[74]

Ya zo cikin bayanin da hizbullahi suka fitar kamar haka: Sayyidul muƙawama, bawan Allah na gari Sayyid Hassan Nasrullah ya rabauta da samun shahada, ya kasance jagora jarumi kuma sadauki, mai hikima, mumini ma'abocin basira ya rabauta da shiga ayarin shahidan karbala ya amsa kiran Allah.[75] Bisa naƙalin da tashar Aljazira ta yi daga tashar isra'ila, haramtacciyar ƙasar isra'ila cikin wannan hari ta yi amfani da bom mai nauyin ton 85 kusan guda biyu irin bom da ake amfani da shi ake fasa manyan duwatsu, duk da cewa yarjejeniyar geneba ta haramta amfani da irin wannan bom ɗin.[76]

Martani

Shahadar Sayyid Hassan Nasrullah ta haifar da martani daban-daban, Sayyid Ali Khamna'i Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran,[77] da maraji'an taƙlidi misalin Sayyid Ali Sistani,[78] Nasir Makarim shirazi,[79] Husaini Nuri Hamdani,[80] Jafar Subhani,[81] Sayyid Musa Shubairi Zanjani,[82] Abdullahi Jawadi Amoli.[83] Bashir Najafi[84] da jami'atu mudarrisin hauze ilmiyya ƙum.[85] sun aiko da saƙwannin ta'aziyya.

Dauloli da shuwagabannin ƙasashe daban-daban misalin Iran, Rasha, Iraƙ, Yaman.[86] Cuba,[87] Benezuwala,[88] da ƙungiyoyin gwagwarmaya misalin ƙungiyar Hamas, ƙungiyar Jihad Islami Palasɗin, ƙungiyar Ansarullahi Yaman, ƙungiyar Fatahu, jama'atu asa'ibul haƙƙi, ƙungiyar amal lubnan, Sayyida Ammar HakimTayyar Alhikima waɗaniyya, Muƙtada Sadar jagoranTayyar Sadar[89] da Jama'atu Islam Pakistan[90] su ma cikin bayani da suka fitar sun yi ta'aziyyar shahadar Sayyid Nasrullah tare da alawadai da harin da isra'ila ta kai masa wanda ya yi sanadiyar kashe shi.

ƙasar Iran ta sanar da makokin kwanaki biyar[91] a ƙasashen labanun,[92] Siriya,[93] Iraƙi[94] da Yaman[95] a hukumance sun sanar da makokin kwanaki uku a ciki da wajen ƙasashen. Hauzozin ilimi a ƙasar Iran sun sanar dagatar da karatu a ranar lahadi sannan malamai da ɗalibai sun shirya taro da kuma jerin gwano domin alawadai da wannan ta'addanci.[96] a ƙasar an dagatar da bakiɗayan zaurukan wasanni da sinimomi domin nuna jimami da ta'aziyya.[97]

Al'ummar ƙasashe daban-daban misalin Iran,[98] Pakistan, Yaman, Jodan, Marokko, gaɓar kogin Jodan(Palasɗin), Bahraini da Iraƙi sun yi jerin gwano domin yin alawadai da kisan Sayyid Hassan Nasrullah.[99]

Mas'ud Fezeshkiyan Shugaban ƙasar Iran, cikin saƙon ta'aziyya da ya fitar ya bayyana cewa an bada umarnin wannan harin ta'addaci ne daga ƙasar Amurka, kuma ya yi bayani ƙarara cewa amurka ba za ta iya wanke kanta daga hannu cikin ayyukan ta'addancin sahayoniya ba..[100]

Yunƙuri Kashe Sayyid Hassan Nasrullah

A lokacin da yake jagorantar ƙungiyar hizbullahi, a lokuta daban-daban ya tsallake rijiya da baya, baya ga yunƙurin hallaka rayuwarsa da isra'ila ta yi, ga wasu adadin yunƙurin kashe shi da aka yi kamar haka:

  • A shekarar 2004m an yunƙurin kashe shi ta hanyar sanya masa guba a abinci
  • Harin bama-bamai kan gidansa a shekarar 2006m
  • Kama wasu ƴan ta'adda da suke yunƙurin kai hari kan motarsa a shekarar 2006m
  • Jiragen isra'ila sun tarwatsa wani gida da ake tsammanin yana ciki a shekarar 2011m

A shekarun baya bayan nan sakamakon barazanar hallaka rayuwarsa Sayyid Hassan Nasrullah ya takaita bayyana cikin taron jama'a, sannan an samar wasu jami'an tsaro na musammam domin kula da lafiyarsa..[101] Abu Ali Jawad sirikin Sayyid Hassan Nasrullah shi ne ya kasance yana jagorantar masu tsaron lafiyarsa.[102]

Rubuce-rubuce Da Aka Yi Game da Nasrullah

An yi rubuce-rubuce daban-daban game da Sayyid Hassan Nasrullah ciki har da littafi, fim da documentary kai har ma da waƙoƙi. Ba'arin waɗannan ayyuka su ne kamar haka:

Jawabin Sayyid Hassan Nasrallah a ranar Ashura 1434H
Da ruhinmu da ’ya’yanmu da dukiyoyinmu, sai mu ce wa Hussaini (A.S): “Labbaika Ya Hussain”. Ba za mu juya wa wannan yarjejeniya da goron gayyata ba... Ga dukkan azzalumai da Dawagitai da masu cin hanci da rashawa da masu cin riba da kuma masbarnata wajen karya muradinmu da azama da tsayuwa, muna cewa mu 'ya'yan wancan Imami ne, wadancan. maza da waɗancan matan da ’yan’uwan waɗannan matasa sun tsaya tare da Hussaini a ranar Ashura suna faɗin maganar Husaini. "Haihata minna zilla"[103]

Litattafai

  • Sayyid Aziz (Tarihin rayuwarsa daga bakinsa) Hamid Dawud Abadi ya rubuta sannan Ayatullahi cikin tsokaci kan wannan littafi yana cewa duk wani abu da zai kasance sanadin sanin Sayyid Nasrullahi da girmama shi abu ne mai kyau da nake buƙatarsa.
  • Sayyid Hassan Nasrullahi: Iƙilabi, talifin Rif'at Sayyid Ahmad, Asma'u Khawaja Zade ta tarjama shi, kamfanin Nashar Ma'arif suka buga shi a shekarar 1394 hijira shamsi.
  • Azadtarin Marde Jahan; talifin Rashid Jafar pur.
  • Nasrullah: wata tataunawa ce ta musamman da Rida Za'iri ya yi tare da Sayyid Hassan Nasrullah.
  • Rahbari Inƙilabi Sayyid Hassan Nasrullah; talifin Azita Bidaƙi ƙurbag.

Fimafimai Da Documentary

  • Musatanad “Negahi Be Zindagi Sayyid Hassan Nasrullah” an nuna wannan fim a tashar khabar ta ƙasar Iran.
  • Mustanad “Munadiyan Azadi (ƙismat Sayyid Hassan Nasrullah) an nuna shi a tashar khabar iran.
  • Mustanad “Nasrullah Dar Ceshme Dushman” fim mai nisan minti hamsin da tashar Al-mayadin ta nuna shi, laccoci me nasa da aka mayar da su fim tare da fashin baƙi daga masana siyasar haramtacciyar ƙasar isra'ila.

Bayanin Kula

  1. Nuri, Shi'aya Lebanon, 2009, shafi na 172.
  2. «حسن نصر الله.. قائد جعل من حزب الله قوة إقليمية»، شبکه الجزیرة.
  3. «روزنامه آلمانی: سید حسن نصرالله محبوب‌ترین شخصیت جهان عرب و اسلام است»، خبرگزاری جمهوری اسلامی.
  4. «نصرالله محبوب‌ترین رهبر جهان عرب»، خبرگزاری جام‌جم آنلاین.
  5. «محافل صهیونیست: نصرالله با شهامت‌ترین رهبر جهان عرب است»، خبرگزاری جمهوری اسلامی.
  6. «حسن نصر الله.. قائد جعل من حزب الله قوة إقليمية»، شبکه الجزیرة.
  7. «حسن نصرالله نزدیک‌ترین متحد ایران و دشمن سرسخت اسرائیل که بود؟»، یورونیوز.
  8. «حسن نصرالله نزدیک‌ترین متحد ایران و دشمن سرسخت اسرائیل که بود؟»، یورونیوز.
  9. «الأمین العام لحزب الله السید حسن نصرالله»، وبگاه الخنادق؛«سید حسن نصرالله: سمبل مقاومت»، وبگاه دیپلماسی ایرانی؛ «حسن نصر الله.. قائد جعل من حزب الله قوة إقليمية»، شبکه الجزیرة.
  10. «سید حسن نصرالله: سمبل مقاومت»، وبگاه دیپلماسی ایرانی.
  11. نگاه کنید به: «سید حسن نصرالله به شهادت رسید»،‌ خبرگزاری ایسنا؛ «حسن نصرالله نزدیک‌ترین متحد ایران و دشمن سرسخت اسرائیل که بود؟»، یورونیوز.
  12. «حسن نصر الله.. قائد جعل من حزب الله قوة إقليمية»، شبکه الجزیرة.
  13. «حسن نصر الله.. قائد جعل من حزب الله قوة إقليمية»، شبکه الجزیرة.
  14. خامه‌یار، «حزب الله و سید حسن از جنگ‌های داخلی تا جنگ ۳۳ روزه»، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امام موسی صدر.
  15. خامه‌یار، «حزب الله و سید حسن از جنگ‌های داخلی تا جنگ ۳۳ روزه»، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امام موسی صدر.
  16. «"معاریف" تکشف فی تقریر حول وحدة حمایة نصرالله تفاصیل محاولات اغتیاله»، وبگاه النشرة.
  17. نگاه کنید به:‌ «سید حسن نصرالله: من سخنگوی ایران نیستم»، خبرگزاری انتخاب؛ «حسن نصرالله نزدیک‌ترین متحد ایران و دشمن سرسخت اسرائیل که بود؟»، یورونیوز.
  18. «نگاهی به سه دهه سکانداری نصرالله در حزب‌الله/ سید حسن؛ چریک معمم»، خبرگزاری خبرآنلاین.
  19. «سید حسن نصرالله: من سخنگوی ایران نیستم»، خبرگزاری انتخاب.
  20. «سخنرانی سید حسن نصرالله، دبیر کل حزب الله لبنان، در روز عاشورا ۱۴۳۴» ؛ سایت مقاومت اسلامی لبنان.
  21. «حسن نصرالله نزدیک‌ترین متحد ایران و دشمن سرسخت اسرائیل که بود؟»، یورونیوز.
  22. «حسن نصر الله.. قائد جعل من حزب الله قوة إقليمية»، شبکه الجزیرة.
  23. «سید حسن نصرالله: من سخنگوی ایران نیستم»، خبرگزاری انتخاب.
  24. نگاه کنید به:‌ «حسن نصرالله نزدیک‌ترین متحد ایران و دشمن سرسخت اسرائیل که بود؟»، یورونیوز.
  25. «سید حسن نصرالله»، وبگاه فرهیختگان تمدن شیعه.
  26. Davodabadi, Seyyed Aziz, 2013, shafi na 41.
  27. داودآبادی، سید عزیز، ۱۳۹۱ش، ص۴۱و۴۲.
  28. Davodabadi, Seyyed Aziz, 2013, shafi na 44.
  29. «حسن نصرالله نزدیک‌ترین متحد ایران و دشمن سرسخت اسرائیل که بود؟»، یورونیوز.
  30. «سید حسن نصرالله: من سخنگوی ایران نیستم»، خبرگزاری انتخاب.
  31. «حسن نصرالله نزدیک‌ترین متحد ایران و دشمن سرسخت اسرائیل که بود؟»، یورونیوز.
  32. «سید حسن نصرالله: من سخنگوی ایران نیستم»، خبرگزاری انتخاب.
  33. «حسن نصر الله.. قائد جعل من حزب الله قوة إقليمية»، شبکه الجزیرة.
  34. «حسن نصر الله.. قائد جعل من حزب الله قوة إقليمية»، شبکه الجزیرة.
  35. «حسن نصرالله نزدیک‌ترین متحد ایران و دشمن سرسخت اسرائیل که بود؟»، یورونیوز.
  36. «حسن نصرالله نزدیک‌ترین متحد ایران و دشمن سرسخت اسرائیل که بود؟»، یورونیوز.
  37. سخنرانی سید حسن نصرالله، دبیر کل حزب الله لبنان، در روز عاشورا 1434 ؛ سایت مقاومت اسلامی لبنان.
  38. «حسن نصر الله.. قائد جعل من حزب الله قوة إقليمية»، شبکه الجزیرة؛ خامه‌یار، «حزب الله و سید حسن از جنگ‌های داخلی تا جنگ ۳۳ روزه»، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امام موسی صدر.
  39. Davodabadi, Seyed Aziz, 1391, shafi na 11.
  40. «حسن نصر الله.. قائد جعل من حزب الله قوة إقليمية»، شبکه الجزیرة.
  41. «سید حسن نصرالله»، وبگاه فرهیختگان تمدن شیعه؛ «سید حسن نصرالله رهبر و الگوی جهان عرب»، خبرگزاری جمهوری اسلامی.
  42. «حسن نصر الله.. قائد جعل من حزب الله قوة إقليمية»، شبکه الجزیرة؛ «سید حسن نصرالله: سمبل مقاومت»،‌ وبگاه دیپلماسی ایرانی.
  43. «حسن نصر الله.. قائد جعل من حزب الله قوة إقليمية»، شبکه الجزیرة.
  44. داودآبادی، سید عزیز، ۱۳۹۱ش، ص۱۲؛ «زندگینامه: سید حسن نصرالله»، وبگاه همشهری آنلاین.
  45. خامه‌یار، «حزب الله و سید حسن از جنگ‌های داخلی تا جنگ ۳۳ روزه»، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امام موسی صدر.
  46. Davodabadi, Seyyed Aziz, 2013, shafi 19-14.
  47. خامه‌یار، «حزب الله و سید حسن از جنگ‌های داخلی تا جنگ ۳۳ روزه»، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امام موسی صدر.
  48. خامه‌یار، «حزب الله و سید حسن از جنگ‌های داخلی تا جنگ ۳۳ روزه»، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امام موسی صدر.
  49. «سید حسن نصرالله»، وبگاه فرهیختگان تمدن شیعه؛ «زندگینامه: سید حسن نصرالله»، وبگاه همشهری آنلاین.
  50. خامه‌یار، «حزب الله و سید حسن از جنگ‌های داخلی تا جنگ ۳۳ روزه»، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امام موسی صدر.
  51. Davodabadi, Seyed Aziz, 2013, shafi na 19-14.
  52. خامه‌یار، «حزب الله و سید حسن از جنگ‌های داخلی تا جنگ ۳۳ روزه»، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امام موسی صدر.
  53. خامه‌یار، «حزب الله و سید حسن از جنگ‌های داخلی تا جنگ ۳۳ روزه»، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امام موسی صدر.
  54. «سید حسن نصرالله»، وبگاه فرهیختگان تمدن شیعه؛ «زندگینامه: سید حسن نصرالله»، وبگاه همشهری آنلاین.
  55. خامه‌یار، «حزب الله و سید حسن از جنگ‌های داخلی تا جنگ ۳۳ روزه»، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امام موسی صدر.
  56. «زندگینامه سراسر مبارزه و مجاهدت شهید سید حسن نصرالله»، خبرگزاری العالم.
  57. داودآبادی، سید عزیز، ۱۳۹۱ش، ص۳۰؛ «سید حسن نصرالله»، وبگاه فرهیختگان تمدن شیعه.
  58. «سید هادی نصرالله که بود؟»،‌ خبرگزاری بین‌المللی قدس.
  59. خامه‌یار، «حزب الله و سید حسن از جنگ‌های داخلی تا جنگ ۳۳ روزه»، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امام موسی صدر؛ «سید حسن نصرالله»، وبگاه فرهیختگان تمدن شیعه.
  60. خامه‌یار، «حزب الله و سید حسن از جنگ‌های داخلی تا جنگ ۳۳ روزه»، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امام موسی صدر؛ «سید حسن نصرالله»، وبگاه فرهیختگان تمدن شیعه.
  61. خامه‌یار، «حزب الله و سید حسن از جنگ‌های داخلی تا جنگ ۳۳ روزه»، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امام موسی صدر.
  62. خامه‌یار، «حزب الله و سید حسن از جنگ‌های داخلی تا جنگ ۳۳ روزه»، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امام موسی صدر.
  63. «سید حسن نصرالله رهبر و الگوی جهان عرب»، خبرگزاری جمهوری اسلامی.
  64. Davodabadi, Seyyed Aziz, 2013, shafi na 34.
  65. «سید حسن نصرالله رهبر و الگوی جهان عرب»، خبرگزاری جمهوری اسلامی.
  66. Khomeini, Sahifa Imam, 1389, juzu'i na 15, shafi na 338.
  67. Davodabadi, Seyyed Aziz, 2013, shafi na 34.
  68. «پیام تسلیت به مناسبت شهادت جناب سید حسن نصرالله رضوان الله علیه دبیر کل شهید حزب‌الله لبنان»، دفتر حفظ و نشر آثار حضرت آیت‌الله خامنه‌ای.
  69. «حسن نصر الله.. قائد جعل من حزب الله قوة إقليمية»، شبکه الجزیرة.
  70. «انفجارهای مهیب در بیروت؛ اسرائیل: مقر فرماندهی مرکزی حزب‌الله را هدف گرفتیم»،‌ خبرگزاری یورونیوز؛ «بمباران شدید و پیاپی بیروت/ارتش اسرائیل: هدف، مرکز فرماندهی اصلی حزب الله بود»، خبرگزاری جمهوری اسلامی.
  71. «الحرب على غزة مباشر.. الجیش الإسرائیلی یعلن مقتل نصر الله وقادة بحزب الله»، شبکه الجزیرة.
  72. «شهادة الأمين العام لحزب الله سماحة السيد حسن نصرالله»، سایت المنار.
  73. «لحظه اعلام خبر شهادت سید حسن نصرالله در حرم مطهر رضوی»، خبرگزاری مهر.
  74. «لحظه اعلام شهادت شهید نصرالله در حرم امام علی(ع)»، خبرگزاری خبرآنلاین.
  75. «شهادة الأمين العام لحزب الله سماحة السيد حسن نصرالله»، سایت المنار.
  76. «A closer look at type of weaponry believed to have been used in Beirut attack»، Al Jazeera Media Network؛ «استفاده از ۸۵ تن بمب برای ترور نصرالله»،‌ خبرگزاری مشرق نیوز.
  77. «پیام تسلیت به مناسبت شهادت جناب سید حسن نصرالله رضوان الله علیه دبیر کل شهید حزب‌الله لبنان»، دفتر حفظ و نشر آثار حضرت آیت‌الله خامنه‌ای.
  78. «واکنش‌های منطقه‌ای و بین‌المللی به شهادت دبیرکل حزب‌الله لبنان»، خبرگزاری مهر.
  79. «آیت‌الله مکارم شیرازی: امت اسلامی مجاهدت‌های شهید سید حسن نصرالله را فراموش نمی‌کند»، خبرگزاری جمهوری اسلامی.
  80. «پیام آیت‌الله نوری همدانی در پی شهادت سید حسن نصرالله»، خبرگزاری جمهوری اسلامی.
  81. «آیت‌الله سبحانی شهادت سید مقاومت را تسلیت گفت»، خبرگزاری ایسنا.
  82. «پیام تسلیت آیت‌الله العظمی شبیری زنجانی در پی شهادت سید حسن نصرالله»، خبرگزاری رسمی حوزه.
  83. «آیت الله جوادی آملی شهادت سید حسن نصرالله را تسلیت گفت»، خبرگزاری جمهوری اسلامی.
  84. «آیت‌الله العظمی بشیر نجفی: آزادگان جهان بدانند که خون این سید مجاهد به هدر نخواهد رفت»، خبرگزاری رسمی حوزه.
  85. «جامعه مدرسین حوزه علمیه قم درپی شهادت سید حسن نصرالله: جهان جز با نابودی اسرائیل و آمریکا روی صلح و آسایش را نخواهد دید»، خبرگزاری شفقنا.
  86. «واکنش‌های منطقه‌ای و بین‌المللی به شهادت دبیرکل حزب‌الله لبنان»، خبرگزاری مهر.
  87. «کوبا: ترور ناجوانمردانه دبیرکل حزب‌الله را به شدت محکوم می‌کنیم»، خبرگزاری العالم.
  88. «ادامه محکومیت جهانی ترور شهید سید حسن نصرالله (۱)»، خبرگزاری صداوسیما.
  89. «واکنش مقاومت به شهادت سید حسن نصرالله»، باشگاه خبرنگاران جوان.
  90. «محکومیت جهانی ترور شهید سید حسن نصرالله»، خبرگزاری صداوسیما.
  91. «پیام تسلیت به مناسبت شهادت جناب سید حسن نصرالله رضوان الله علیه دبیر کل شهید حزب‌الله لبنان»، دفتر حفظ و نشر آثار حضرت آیت‌الله خامنه‌ای.
  92. «اعلام ۳ روز عزای عمومی در لبنان»، خبرگزاری العالم.
  93. «واکنش‌های منطقه‌ای و بین‌المللی به شهادت دبیرکل حزب‌الله لبنان»، خبرگزاری مهر.
  94. «واکنش مقاومت به شهادت سید حسن نصرالله»، باشگاه خبرنگاران جوان.
  95. «واکنش مقاومت به شهادت سید حسن نصرالله»، باشگاه خبرنگاران جوان.
  96. «راهپیمایی و خروش حوزویان و ملت داغدار قم در روز یکشنبه»، خبرگزاری رسمی حوزه.
  97. «سینماها و تئاترها تا اطلاع ثانوی تعطیل شدند»، خبرگزاری ایسنا.
  98. «مردم شهرهای مختلف در سوگ شهید راه قدس/ ایران یک صدا در حمایت از لبنان و فلسطین»، خبرگزاری مشرق نیوز.
  99. نگاه کنید به:‌ «ادامه محکومیت جهانی ترور شهید سید حسن نصرالله (۱)»، خبرگزاری صداوسیما؛ «ادامه محکومیت جهانی ترور شهید سید حسن نصرالله (۲)»، خبرگزاری صداوسیما؛ «تظاهرات مردم رام‌الله، عمان و مغرب در محکومیت ترور سید مقاومت لبنان»، خبرگزاری العالم.
  100. name=":0">«پیام دکتر پزشکیان در پی شهادت سید حسن نصرالله»، پایگاه اطلاع رسانی ریاست جمهوری اسلامی ایران.
  101. «ترورهای نافرجام سید»،‌ وبگاه همشهری آنلاین.
  102. نگاه کنید به:‌ «ترورهای نافرجام سید»،‌ وبگاه همشهری آنلاین؛ «"معاریف" تکشف فی تقریر حول وحدة حمایة نصرالله تفاصیل محاولات اغتیاله»، وبگاه النشرة.
  103. «سخنرانی سید حسن نصرالله، دبیر کل حزب الله لبنان، در روز عاشورا ۱۴۳۴» ؛ سایت مقاومت اسلامی لبنان.

Nassoshi

Template:چپ‌چین