Falasɗinu A Mahangar Ayatullahi Khamna'i (Littafi)
| Fayil:فلسطین از منظر حضرت آیت الله خامنهای.jpeg | |
| Marubuci | Sayyid Ali Khamna'i |
|---|---|
| Maudu'i | Falasɗinu |
| Harshe | Farsi |
| Adadin Jildi | Jildi 1 |
| Mai bugawa | Intisharat Inƙilabe Islami |
| Tarihin bugawa | 2011 miladiyya |
Falasɗinu a mahangar Ayatullahi Khamna'i, (Larabci: فلسطين في مواقف آية الله العظمى الإمام الخامنئي) wani littafi ne cikin harshen Farsi da ya ƙunshi maganganun Sayyid Ali Khamna'i, jagoran juyin juya halin muslunci na Iran, game da Falasɗinu, ba'arin ra'yoyin Sayyid Ali Khamna'i da suka bayyana cikin wannan littafi sun kasance kamar haka: ingantacciyar hanyar samun warwara cikin mas'alar Falasɗinu tana cikin shirya jin ra'ayin al'umma tare da tarayyar baki ɗayan Falasɗinawa; Hanya kaɗai ta samu ƴancin Falasɗinu ita ce gwagwarmaya, sulhu da tattaunawa tare da Isra'ila babbar asara ce ga Falasɗinawa, goyan bayan Falasɗinu da al'ummar Falasɗinu wajibi ne a shari'ance.
Wannan littafi an buga shi cikin harshen Larabci, haka kuma an zaɓi wasu abubuwa daga cikinsa cikin harshen turanci, wannan littafi ya yi matuƙar tasiri da yaɗuwa cikin kafofin watsa labarai na Isra'ila.
Abin da Yake CIkin Littafin
Littafin “Falasɗinu a mahangar Ayatullahi Khamna'i jagoran juyin juya halin muslunci” wasu ra'ayoyi ne na Ayatullahi Khamna'i game da Falasɗinu, abin da wannan littafi ya tattaro shi ne nassin huɗubar juma'a ta ranar ƙudus, a ranar 8 Agusta 1980 miladiyya, cikin taken (Tunawa da ranar ƙudus ta biyu) kuma sashe takwas na asali da littafin ya ƙunsa ya haɗo da game garin batutuwa, faɗuwa da nasarori, manyan nauyi da yake kanmu, lefuka, hanyoyin samun mafita, Jaruman Falasɗinu, wayar da kai, gobe mai haske,[1] Sa'id Sulhu Mirzayi ne ya harhaɗa wannan maganganu zuwa littafi wanda ya kasance malami na Shi'a[2] Daɗi kan tattaro maganganu Ayatullahi Khamna'i ya haɗo da wasu batutuwan daban.[3]
Ba'arin Ra'yoyin Ayatullahi Khamna'i Cikin Wannan Littafi
- Hanyoyin warwara cikin mas'alolin Falasɗinu na cikin shirya jin ra'ayin kowa da kowa tare da tarayyar baki ɗayan Falasɗinawa daga musulmansu da Kiristoci da Yahudawa baki ɗaya da suke zaune a mamayayyar ƙasar Falasɗinu da wajenta.[4]
- Falasɗinu za ta ƴantu[5] kuma hanyar samun ƴantuwar ta yana ƙunshe cikin gwagwarmaya ba wai sulhu da tattaunawar kan teburi ba[6] Tattaunawa game da mas'alar Falasɗinu babban kuskure da ba za a yafe shi ba, kuma babu abin da za a samu daga gare shi sai asara mai girma ga Falasɗinawa, kuma zai jinkirta samun ƴancin Falasɗinu.[7] Har ila yau, a shekarar 201r miladiyya Ayatullahi Khamna'i ya yi hasashe nan da zuwa shekarar 2040 babu maganar wani abu wai shi gwamnatin Sahayoniyya a wannan duniyar.[8]
- Bisa koyarwar addinin Muslunci kari da goyan bayan al'ummar Falasɗinu wajibi kan duk wani musulmi.[9]
- Batun Falasɗinu yana cikin mafi muhimmancin batutuwa a duniyar Muslunci.[10]
- Mas'ala ce da ƴan adamtaka ba wai zallan Larabci da Muslunci ba.[11]
Gabatarwar Ali Akbar Wilayati
Ali Akbar Wilayati, ya rubuta wata gabatarwa kan wannan littafi, cikin wannan gabatarwa ya bayyana cewa mamaye Falasɗinu da ƙirƙirar daular Sahayoniyya wani makirci daga yammaci domin yaƙar duniyar Muslunci.[12]
Yaɗuwar Littafin A Kafafen Watsa Labarai Na Isra'ila Da Amurka
A shekarar 2015 miladiyya, lokaci ɗaya da fara tattaunawa kan makamashin nukiliya na gwamnatin jamhuriyar Muslunci ta Iran tare da ƙasashe biyar, wannan littafi ya yi matuƙar yaɗuwa da tasiri cikin jarudu da mujallun Amurka da Isra'ila da ma ƙasashen turai.[13] Benjamin Netanyaho firaministan Isra'ila na lokacin, a ranar 1 Oktoba 2015 miladiyya cikin taron majalisar ɗinkin duniya, a lokacin da yake gabatar da bayani ya nuna kwafin wannan littafi, tare da bayyana matsayar gwamnatin Iran da Ayatullahi Khamna'i game da Isra'ila a matsayin tsokana da nuna ƙarfi, jawabin Netanyaho ya yi tasiri cikin kafofin watsa labarai na cikin gida a Iran, kuma ya kwaɗaitar da mutane neman wannan littafi su karanta.[14]
Buga Wannan Littafi Da Tarjama
Littafin Falasɗinu a mahangar Ayatullahi Khamna'i an buga shi cikin harshen Farsi a shekarar 2011.[15] Bayan nan an sake buga shi a lokuta daban-daban[16] Kwafi na farko na wannan littafi ya ƙunshi maganganun Ayatullahi Khamna'I zuwa shekarar 2011, amma a bugun da akai daga baya, an ƙara da jawabansa har zuwa shekarar 2017, Bayan nan an sake buga shi a lokuta daban-daban[17] Wannan littafian tarjama shi zuwa harshen larabci tare kuma da taƙaice shi da harshen Ingilishi. Bayan nan an sake buga shi a lokuta daban-daban[18]
Bayanin kula
- ↑ Duba: Khamene’i, Falasɗinu, bugun shekara ta 1397 Hijira Shamsiyya (daidai da 2018 Miladiyya), Fihirisar Abubuwan Ciki, shafuka ز - ظ.
- ↑ A matsayin misali, duba: Khamene’i, Jihād Tabyīn, bugun shekara ta 1400 Hijira Shamsiyya (daidai da 2021 Miladiyya), shaidar littafi (shinasnāme-ye ketāb).
- ↑ Khamene’i, Falasɗinu, bugun shekara ta 1397 Hijira Shamsiyya (daidai da 2018 Miladiyya), shafi na 506.
- ↑ Khamene’i, Falasɗinu, bugun shekara ta 1397 Hijira Shamsiyya (daidai da 2018 Miladiyya), shafi na 599.
- ↑ Khamene’i, Falasɗinu, bugun shekara ta 1397 Hijira Shamsiyya (daidai da 2018 Miladiyya), shafi na 599
- ↑ Khamene’i, Falasɗinu Az Manzare Ayatollah Khamene’i, bugun shekara ta 1397 Hijira Shamsiyya (daidai da 2018 Miladiyya), shafuka 487 zuwa 490.
- ↑ Khamene’i, Falasɗinu, bugun shekara ta 1397 Hijira Shamsiyya (daidai da 2018 Miladiyya), shafi na 500
- ↑ Khamene’i, Falasɗinu, bugun shekara ta 1397 Hijira Shamsiyya (daidai da 2018 Miladiyya), shafi na 603
- ↑ Khamene’i, Falasɗinu, bugun shekara ta 1397 Hijira Shamsiyya (daidai da 2018 Miladiyya), shafi na 29
- ↑ Khamene’i, Falasɗinu, bugun shekara ta 1397 Hijira Shamsiyya (daidai da 2018 Miladiyya), shafi na 538-39
- ↑ Khamene’i, Falasɗinu, bugun shekara ta 1397 Hijira Shamsiyya (daidai da 2018 Miladiyya), muqaddimehshafi na 29
- ↑ Khamene’i, Falasɗinu, bugun shekara ta 1397 Hijira Shamsiyya (daidai da 2018 Miladiyya), shafi na 3-4
- ↑ Khamene’i, Falasɗinu, bugun shekara ta 1397 Hijira Shamsiyya (daidai da 2018 Miladiyya), gabatarwa (Fishguftar), *shafi na “و” (shafi na 6 ko kusa da farko a tsari na Farisi).
- ↑ گفتوگوی مشرق با نویسنده کتابی که نتانیاهو را برآشفت، Shafin labarai na Masreq
- ↑ Khamene’i, Falasɗinu, bugun shekara ta 1397 Hijira Shamsiyya (daidai da 2018 Miladiyya), gabatarwa (Fishguftar), *shafi na “و” (shafi na 5 ko kusa da farko a tsari na Farisi).
- ↑ Khamenei, Falasdinu, 2018, Fishguftar, shafi na 5
- ↑ Khamenei, Falasdinu, 2018, Fishguftar, shafi na 5
- ↑ Khamenei, Falasdinu, 2018, Fishguftar, shafi na 5
Nassoshi
- Khamene’i, Sayyid Ali, Jihād Tabyīn Dar Andishe Ayatollah Khamene’i, an shirya ta Saʿīd Ṣulḥ Mīrzāyī, birnin Tehran, Ma’aikatar Bugawa ta Inqilābin Islāmi, shekara ta 1400 Hijira Shamsiyya (daidai da 2021 Miladiyya).
- Khamene’i, Sayyid Ali, FalasɗinuAz Manzare Ayatollah Sayyid Ali Khamene’i (Allah ya tsawaita zamaninsa), Shugaban Juyin Juya Hali na Islama, an shirya ta Saʿīd Ṣulḥ Mīrzāyī, birnin Tehran, Ma’aikatar Bugawa ta Inqilābin Islāmi, shekara ta 1397 Hijira Shamsiyya (daidai da 2018 Miladiyya).
- گفتوگوی مشرق با نویسنده کتابی که نتانیاهو را برآشفت،kafar labaran Mashregh News ta ba da ruwaya game da wallafar littafin “Falasɗinu daga Mahangar Ayatollah Khamene’i” a ranar 13 Mehr 1394 Shamsiyya (daidai da Oktoba 5, 2015