Zahra (Laƙabi)

Daga wikishia
(an turo daga Zahara)

Zahra (Larabci: الزهرا) ɗaya ne daga cikin laƙubban Sayyida Faɗima (S)[1] da yake da ma'anar fari da mai haskakawa da bayyanarwa[2] kai kace misalin lu'ulu'u mai kyalkyali.[3] Allama Majlisi cikin fassarar wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) ya tafi kan cewa dalilin da ya sanya akewa Sayyida Faɗima (S) laƙabi da Zahra sakamakon kasancewarta tare da haske na ma'anawiyya.[4] kalmar Zahra ko faɗima Zahra suna daga sunaye da aka yi amfani da su cikin riwaya yayin magana game da Faɗima (S) haka nan Imaman Shi'a sun shahara da sunan ƴaƴan Faɗima Zahra.[5]

Cikin hadisai an ambaci adadin dalilai game da sanya mata wannan suna, daga jumlarsu akwai wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) da yake cewa an kirata da laƙabin Zahra sakamakon kasancewar fuskarta fuskar mai haske a wurin Imam Ali (A.S).[6]cikin wasu riwayoyin daban ya zo kamar haka: lokacin da Faɗima take tsayuwa da ibada haskenta na haskaka halittun sama; kamar yadda taurari suke haskaka halittun ƙasa.[7] haka nan an rawaito cewa Allah ya halicceta daga hasken girmamarsa, kuma lokacin da ya halicce ta sai ya haskaka sammai da ƙasa da haskenta, idanun mala'iku suka lumshe.[8] an naƙalto wata riwaya daga A'isha game da haskakar fuskar Sayyida Faɗima.[9]

Game da sunayen Sayyida Faɗima ya zo cikin riwayar Imam Sadiƙ cewa haƙiƙa Faɗima tana da sunaye da laƙubba guda tara a wurin Allah: Faɗima, Siddiƙa, Mubaraka ɗahira, Zakiyya, Radiya Mardiyya Muhaddasa da Zahra.[10] daidai da abin da ya zo a riwayoyi, ta samu waɗannan sunaye kan asasin falaolin da take da su.[11]

Cikin litattafan riwaya na shi'a an keɓance sashe-sashe da suka tattaro bayanin laƙubban Zahra; kamar dai yadda Shaik Saduƙ ya keɓance fasali guda cikin littafin Ilalul Ash-shara'i[12] da Allama Majlisi cikin littafinsa Biharul Al-anwar cikin mujalladi na 23. Kan asasin rahotonni game da adadin sunayen da aka yi rijistarsu a ofishin rijista sunaye da bayanai na ƙasar Iran, haƙiƙa sunan Zahra ya kasance sunan aka fi raɗawa yaran da aka haifa a ƙasar Iran, alal misali a shekarar 1392 hijira shamsi daidai da 2013 miladi wannan suna shi ne suna da ya zo matsayi na biyu cikin adadin sunayen mata a ƙasar Iran.[13]

Bayanin Kula

  1. Sheikh Saduq, Al-Amali, 1417 BC, shafi na 74; Kulayni, Al-Kafi, 1363 AH, juzu'i na 1, shafi na 240; Masoudi, Asrar al-Fatimiyyah, 1420 H., shafi 409.
  2. Ibn Atheer Al-Jazari, Al-Nihayah fi Gharib al-Hadith wa al-Athar, Dhayl Wajah Zuhr.
  3. Ibn Manzur, Lisan al-Arab, Dhayl Wajah Zuhr.
  4. Majlisi, Jala’ al-Uyun: Tarikh Chahardeh Masum, 1380 AH, shafi na 162. . ↑
  5. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 99, shafi na 180 da 297; Sashe na 98, shafi na 345.
  6. Sheikh Saduq, Illal al-Shara’i’, Al-Dawri Library, juzu’i na 1, shafi na 179-181.
  7. Sheikh Saduq, Ilal al-Shara’i’, Al-Dawri Library, juzu’i na 1, shafi na 181.
  8. Sheikh Saduq, Ilal al-Shara’i’, Al-Dawri Library, juzu’i na 1, shafi na 180.
  9. Al-Qarmani, Al-Akhbar Al-Dul wa Athar Al-Awwal fi Al-Tarikh, Beirut, juzu'i na 1, shafi na 256; Shushtari, Kafa Gaskiya da Rusa Ƙarya, 1409 AH, juzu'i na 19, shafi na 10.
  10. Sheikh Saduq, Al-Khisal, 1362H, juzu'i na 2, shafi na 414.
  11. Sheikh Saduq, Al-Amali, 1417 BC, shafi na 692; Kulayni, Al-Kafi, 1363 AH, juzu'i na 1, shafi na 240; Masoudi, Asrar al-Fatimiyyah, 1420 H., shafi 409. ↑
  12. Sheikh Saduq, Ilal al-Shara’i’, Al-Dawri Library, juzu’i na 1, babi na 143. ↑
  13. «ثبت بیش از ۱۲ میلیون از القاب حضرت زهرا(س) در ثبت احوال کشور...»، مندرج در سایت خبرگزاری مهر.

Nassoshi

  • Ibn Athir al-Jazari, Abu al-Saadat, Al-Nihaya fi Gharib al-Hadith waAl-Athar, binciken Tahir Ahmad Al-Zawi - Mahmoud Muhammad Al-Tanahi, Al-Maktab Al-Alamiya Publications, Beirut, 1979 .
  • Ibn Manzoor, Muhammad Ibn Makram, Lasan al-Arab, Nasher Dar Sadhir, Beirut, bugun farko, 1414H.
  • «ثبت بیش از ۱۲ میلیون از القاب حضرت زهرا(س) در ثبت احوال کشور...»، خبرگزاری مهر، تاریخ درج مطلب: ۳۱ فروردین ۱۳۹۳ش، تاریخ بازدید: ۳۰ اردیبهشت ۱۴۰۳ش.
  • Shushtri, Nurullah bin Sharif al-Din, Ihqaq al-Haq wa Izhaq Al-Batil, Library Public Library na Ayatullahi Ayatullahi Murashi Najafi (RA), Qom, 1409 AH.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, al-Khisal, bincike na Ali Akbar Ghafari, Kum Madrasin Society, Qom, 1362.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Dalilan Al-Sharia, Makarantar Al-Davari, Kum, Bita.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Al-AMali, Qum, Al-Baath Institute, 1417H.
  • Al-Qarmani, Ahmed bin Yusuf, Al-Akhbar Al-Dawwal da Atar al-Awwal fi al-Tarikh, binciken Dr. Fahmi Saad da Dr. Ahmed Hatit, malamin Al-Katb. Beirut, Beta.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, bincike na Ali Akbar Ghafari, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1363.
  • Majlesi, Mohammad Baqer, Jala Al-Ayoun Tarikh Chahardeh Masum, Seyyed Ali Imamian ya yi bincike, Qom, Sarwar, 1380.
  • Majlesi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1403H.
  • Masoudi, Mohammad Fazil, Israr al-Fatimiyah, bincike: Seyyed Adel Alavi, Al-Zaer Foundation, 1420 AH.