Masallacin Al-Aƙsa

Daga wikishia
Masallacin Al-Aksa

Masallacin Al-Aƙsa (Larabci: المسجد الأقصی) na ɗaya daga cikin masallatan garin Baitul-muƙaddas kuma alkiblar musulmi ta farko. A bisa hadisai Annabin mu Muhammad (SAWW) ya tafi mi'iraji daga nan. Alƙur'ani ya ambace shi lokacin da yake ambaton labarin Mi'iraji a cikin suratul- Isra'i. Masallacin Al-Aƙsa Yanada daraja da girma a gun musulmi , Yahudawa da Kirista , A cikin hadisai na Musulunci, ana ambatan masallacin ƙuds, kusa da Masallacin Haram da Masallacin Annabi , kuma an ce yin salla a cikinsa yana daidai da salla dubu a sauran masallatai.

Yahudawa sun yi imanin cewa ragowar Haikalin(jikin) Annabi Sulemanu yana ƙarƙashin Masallacin Al-Aƙsa. A cewar wasu Kiristoci, ruguza Masallacin Al-Aƙsa da gina saban ma'abar Sulemanu shine sharaɗin bayyanar Almasihu. Don haka wasu yahudawa suke ƙoƙarin ruguza masallacin da ƙoƙarin maido da Ma'abad Suleiman. Saboda haka ne sojojin Isra'ila suka hana musulmi shiga wannan masallaci. A shekara ta 1969 wani bayahude ya cinnawa masallacin wuta, don haka ne aka sanya ranar 31 ga watan Agusta ranar masallatan duniya a kalandar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Ginin da ake kira Masallacin Al-Aƙsa a yau an kafa shi ne a zamanin Abdulmalik bin Marwan a ƙarni na farko kuma an yi masa kwaskwarima da gyara shi a lokuta daban-daban.

Wuri Da Aka Sanya Masa Suna

Masallacin Al-Aƙsa a ma'ana yana nufin masallaci mafi nisa , wani masallaci ne a birnin ƙudus a ƙasar Falasɗinu, wanda ke kudu maso gabashin birnin,[1] Dangane da dalilin da ya sa aka sanya masa suna masallacin Al-Aƙsa, sun ce saboda nisan da yake dashi zuwa Makka da Masallacin Harami, wanda shine gurin rayuwar Annabi da Musulmai.[2] A cewar wasu masu bincike, masallacin Al-Aƙsa da yazo a cikin Alƙur'ani, wani yanki ne mai girma da ya haɗa da Masallacin Sakhra(wurin Mi'iraji), Riwwaƙ da sauransu[3]Don haka wasu malaman tafsirin Shi'a sun fassara masjidul-aƙsa da yazo a alƙur'ani a aya ta farko ta suratulIsra'i da Baitul-Maƙdis,[4] wanda Annabi Dawud da Sulaiman suka gina shi,[5] A wasu hadisai an ambaci Masallacin Al-Aƙsa da sunan Baitul-muƙaddas.[6]

Wasu sun ce lokacin da Annabi ya yi mi’iraji babu wani gini da ake kira masallacin Al-Aƙsa kuma kalmar masallaci a ayar Mi'iraji tana nufin wurin ibada.[7]

A yau, ginin rufin da aka gina a zamanin Abdulmalik bin Marwan a yankin masallacin mai tsarki shine ake kiransa da masallacin Al-Aƙsa , kuma daga wajen da aka gina wannan ginin ne aka yi wa laƙabi da masallacin Al-aƙsa. sai daga gefe akwai Masallacin Sakhra, sai Masallacin Umar, sai bango mai haske ... duka in aka haɗasu ana kiransa da masallacin Al-Aƙsa.[8]

سُبْحَانَ الَّذِی أَسْرَ‌یٰ بِعَبْدِهِ لَیلًا مِّنَ الْمَسْجِدِ الْحَرَ‌امِ إِلَی الْمَسْجِدِ الْأَقْصَی الَّذِی بَارَ‌کنَا حَوْلَهُ لِنُرِ‌یهُ مِنْ آیاتِنَا ۚ إِنَّهُ هُوَ السَّمِیعُ الْبَصِیرُ‌

Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar dare da bawansa daga masallaci mai alfarma zuwa Al'Aksa wanda muka sanya albarka a geffansa domin nuna masa wasu daga ayoyinmu lallai shi shi ne mai ji mai gani.

Suratul Isra'i aya 1

Falala

Masallacin Al-aƙsa musulmai da kiristoci da yahudawa suna girmama shi. A cewar Yahudawa, ragowar Ma'abad sulaman yana ƙarƙashin masallacin Al-aƙsa.[9] Musulmai sun yi imani da cewa Annabin Musulunci yayi mi'iraji daga wannan wuri,[10] Kafin sauya alƙibla , a shekara ta biyu bayan hijira,[11] Don haka a zamanin ƙajar da Pahlawi wasu ‘yan Shi’ar Iran in sun je ziyarci wuraren ibada kamar makka da madina suna biyawa ta birnin Ƙudus dan ziyarar masallacin Al-aƙsa.[12] A cikin hadisai an sanya masallacin Al-aƙsa ɗaya daga cikin masallatai huɗu masu daraja, akwaimasallacin Harami, da masallacin Annabi da masallacin Kufa .[13] A wasu hadisain babu masallaci a Kufa. Al-aƙsa ɗaya ne daga cikin masallatai masu daraja guda uku, tare da masallacin Harami da masallacin Nabi,[14] Yin salla ɗaya a waɗannan masallatai uku daidai yake da salla dubu a sauran masallatai.[15] Tabbas akwai hadisai da suke nuni da fifikon masallacin Kufa akan masallacin Aƙsa a cikin ruwayoyin Shi'a.[16]

Tarihi

An ce a karon farko, Annabi Dauda ya fara gina Ma'abad a wurin masallacin Al-aƙsa sai Annabi Sulaiman ya kammala shi, wanda ake kira Ma'abad Sulaiman, ko maabad Jerusalem, ko Ma'abad na Iliya da buƙ'a ɗin Iliya.[17] A cewar Gustavo Bon, masanin tarihi na ƙarni na 19 da na 20, kafin mamaye birnin Ƙudus da musulmi suka yi, akwai wata maj'ma'a da ake kira cocin sayyada Maryam a harabar masallacin Al-aƙsa.[18] Yazo a takardun da suka rage tun daga ƙarni na farko, an gina ginin masallacin Al-aƙsa a zamanin Umayyawa da kuma a ƙarni na farko.[19] A cewar Ibn Kasir, masanin tarihi na ƙarni na takwas, An gina masallacin ne a shekara ta 66 bayan hijira bisa umarnin Abdulmalik bin Marwan, wanda aka fara a shekara ta 65-86 bayan hijira, kuma ya ƙare a shekara ta 73 bayan hijira.[20] na mulkin sa (86-96 AH).[21] Ibn Kasir ya rubuta cewa: Abdulmalik ya gina masallacin Aƙsa da gine-ginen da ke kewaye da shi da nufin hana ƴan ɓangaran Sham (Syria) zuwa aikin Hajji da tilasta musu ɗawafi a kewayensa, ya yi hakanne saboda Abdullahi bin zubair yana amfani da aikin hajji wajan kamfen da muzanta Abdulmalik[22] a idan masu aikin Hajji dan ya karɓi bai'a ya karɓe mulkin kuma hakan riba ce a gareshi.[23] a cikin hudubarsa. a ranar Arfah da ranekun Mina, ya ambato la’anar da Annabi ya yi wa Hakam ɗan Asi, kakan AbdulMalik da zuriyarsa, hakan ya taimaka wajan mutan sham suka karkata zuwa gare shi.[24]

Ƙayadaddun Bayanai Kan Ginin Masallacin

Ginin masallacin Al-aƙsa gini ne da akayi shi a Da'ira tsawon mita 80 da fadin mita 55. Musa Ghosheh, Tarikh Majmu'eh Masjid Al-Aqsa, 1390, shafi na 10. An gina ginin masallacin a kan ginshiƙan marmara 53 da Foundation 49.[25] Haka nan cikin sa yana da faɗi sosai ta yanda ƙubbar masallacin take a tsakiyarsa.[26] Nasir Khusro (394-468 AH), matafiyi mai yawan duniya na ƙarni na biyar, da ya ziyarci birnin Kudus a shekara ta 438 bayan hijira.[27] ya kawo bayanin masallacin Al-aƙsa a cikin littafin tafiyarsa kuma ya yi bayani kan samuwar masu hidima da kula da gurin tin a wancen lokacin.[28]

Gyara Da Sabunta Ginin

An gyara ginin masallacin Al-aƙsa tare da sabunta shi a lokuta daban-daban. Abbasiyawa da Fatimiyyawa da Ayyubiyawa da Daular Usmaniyya na daga cikin gwamnatocin da suka gyara shi kuma suka sake ginin shi.

Mansur Dawaniƙi (mulki: 136-158 AH).[29] da Mahdi Abbasi (126-169 AH), ɗaya daga cikin khalifofin Abbasiyawa ne da suka gyara tare da sake ginin masallacin Al-aƙsa wanda girgizar ƙasa ta ruguje shi.[30] Har ila yau, bisa ga wani rubutu da aka samu , ance akan Umarnin al-Zahir La'izaz Dinulllah, ɗaya daga cikin khalifofin Fatimiyya, an gina ƙubba a kan masallacin Al-aƙsa a shekara ta 426 bayan hijira.[31] da kuma umarnin Al-Mustansir li Dinullah a shekara ta 458 bayan hijira, aka sake gina barandar arewacin masallacin.[32] A shekara ta 1099miladiyya, daidai da shekara ta 583 hijira ,‘yan Salibiyya (kiristoci ) sun ƙwace birnin Ƙudus, suka gina coci a wani bangare na masallacin, a wani ɓangaran suka mayar da shi wurin hutawa da rumbun ajiyar kaya,[33] A shekara ta 589 hijiri Salahuddin ayyubi ya shine ya karɓe shi daga hannun su, ya sake gina mihrabin masallacin, ya maida ƙubbar sa, sannan ya sanya minbari na katako a cikinsa,[34] Sauran sarakuna da daular Usmaniyya ma sun sake ginin masallacin a lokuta daban-daban.[35]

Ayyukan Da Yahudawa Suke yi

1Yahudawa sun yi imanin cewa ragowar Haikalin(jikin) Annabi Sulemanu yana ƙarƙashin Masallacin Al-Aƙsa.[36] Don haka ne wasu daga cikinsu suke kokarin ruguza masallacin da farfaɗo da ɗakin ibadar Sulaiman.[37] a cewar masana, tonon da gwamnatin Sahayoniya ta keyi a ƙarƙashin masallacin ana ɗaukarsa a matsayin barazana ga wannan ginin. ya haifar da manyan tsage-tsage a jikin bangwayen masallacin.[38] An ce wasu Kiristoci sun yi imanin cewa rugujewar Masallacin Al-Aƙsa da gina Ma'abadu Sulemanu na uku a wurin sharaɗi ne na bayyanar Almasihu.[39] Saboda haka sojojin Isra'ila suna hana musulmai shiga masallacin.[40] Masallacin Al-Aƙsa alama ce ta Musulunci a garin baitul-maƙdis.[41] A ranar 21 ga Agusta, 1969miladiyya wani Bayahude mai suna Dennis Michael William Rohan ya ƙona Masallacin Al-Aƙsa, wanda ya lalata wasu sassan masallacin tare da ruguje rufin masallacin. Haka nan kuma ya ƙona tsohon mimbarin masallacin na shekara ta 583 bayan hijira.[42] A cikin kalandar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, An sanya ranar tunawa da ƙona masallacin Al-aƙsa ranar 31 ga watan Agusta, ana kiransa da ranar Masallaci ta Duniya.[43]

Bayanin kula

  1. Hamidi, Tarikh Urushalima, 1381, shafi na 183.
  2. Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 12, shafi na 7; Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 6, shafi na 612.
  3. Musa Ghosheh, Tarikh Majmu'eh Masjid Al-Aqsa, 1390, shafi na 7.
  4. Tabarsi, Majma Al-Bayan, 1372, juzu'i na 6, shafi na 612.
  5. Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 13, shafi na 6.
  6. Misali, duba tafsirin Imam Hasan Askari, 1409H, shafi na 661.
  7. Hamidi, Tarikh Urushalima, 1381, shafi 183-184.
  8. Musa Ghosheh, Tarikh Majmu'eh Masjid Al-Aqsa, 1390, shafi na 7.
  9. Tawfighi, Ashnayi ba Adyan Buzurg , 2005, shafi na 88.
  10. Suratul Isra, aya ta 1.
  11. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 331.
  12. Misali, duba Jafarian, Panjoh Safarnameh Hajji Qajar 50, 2009, shafi na 230.
  13. Sheikh Sadouq, Man Laihzara al-Faqih, 1413 AH, Mujalladi na 1, shafi na 29.
  14. Bukhari, Sahihul Bukhari, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi na 398.
  15. Tafsirin Imam Hasan Askari, 1409H, shafi na 661.
  16. Ayashi, Tafsir al-Ayashi, 1380 AH, juzu'i na 2, shafi na 279; Muhaddith Nouri, Mustadrak Wasal al-Shi'ah, 1408H, juzu'i na 3, shafi na 409.
  17. https://www.masjed.ir/fa/article/2835
  18. Gustavo Bon, Tamadduni Islam be Nakle az Hamidi, , Tarikh Urshalim, 2008, shafi na 183.
  19. Duba Musa Ghosheh, Tarikh Majmu'eh Masjid Al-Aqsa, 1390, shafi na 10.
  20. Ibn Kathir, al-Bidaiya wa al-Nihaya, 1407H, juzu'i na 8, shafi na 280.
  21. Musa Ghosheh, Tarikh Majmu'eh Masjid Al-Aqsa, 1390, shafi na 10.
  22. Ibn Kathir, al-Bidaiya wa al-Nihaya, 1407H, juzu'i na 8, shafi na 280.
  23. Yaqoubi, Tarikh Al-Yaqoubi, Dar Sadir, juzu'i na 2, shafi na 261.
  24. Ibn Kathir, al-Bdaya wa al-Nihaya, 1407H, juzu'i na 8, shafi na 280.
  25. Hamidi, Tarikh Urushalima, 1381, shafi na 183.
  26. Musa Ghosheh, Tarikh Majmu'eh Masjid Al-Aqsa, 1390, shafi na 10.
  27. Nasser Khosro, Safarnameh 1368, shafi na 26.
  28. Nasser Khosro, Safarnameh 1368, shafi na 32.
  29. Hamidi, Tarikh Urushalima, 1381, shafi na 183.
  30. Musa Ghosheh, Tarikh Majmu'eh Masjid Al-Aqsa, 1390, shafi na 11.
  31. Musa Ghosheh, Tarikh Majmu'eh Masjid Al-Aqsa, 1390, shafi na 11.
  32. Musa Ghosheh, Tarikh Majmu'eh Masjid Al-Aqsa, 1390, shafi na 11.
  33. Hamidi, Tarikh Urushalima, 1381, shafi na 183.
  34. Hamidi, Tarikh Urushalima, 1381, shafi na 183.
  35. Musa Ghosheh, Tarikh Majmu'eh Masjid Al-Aqsa, 1390, shafi na 13-15.
  36. Tawfighi, Shnayi na Adyan Buzrg, shafi na 88.
  37. Barghoti, "Israeli excavations threaten Al-Aqsa Mosque: Experts".
  38. «الحفريات الإسرائيلية أسفل القدس والأقصى
  39. «آتش زدن مسجدالاقصی اقدامی برای سنجش غیرت دینی مسلمانان بود»،
  40. «گزارش: اسرائیل آمادۀ تخریب مسجدالاقصی و ساخت «سومین معبد» می‌شود»
  41. «پشت پرده توطئه های جدید علیه مسجد الاقصی/تحلیل»
  42. Musa Ghosheh, Tarikh Majmueh Masjid Al-Aqsa, 1390, shafi na 16
  43. «علت نامگذاری روز جهانی مساجد چیست؟»، خبرگزاری صداوسیما

Nassoshi

  • Allameh Tabatabai, Sayyid Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci na kungiyar Seminary Society, 1417H.
  • Ayashi, Muhammad Bin Mas'ud, Tafsir Al-Ayashi, Seyyed Hashem Rasouli Mahalati, Tehran, Al-Matabah Al-Alamiya, 1380H.
  • Bukhari, Muhammad bin Ismail, Sahihul Bukhari, Mustafa Dib al-Bagha, Beirut, Dar Ibn Kathir, Al-Imamah, 1407 H.
  • Hamidi, Sayyid Jafar, Tarikh Kudus (Beit al-Maqdis), Tehran, Amir Kabir, 2001.
  • Ibn Kathir, Ismail Ibn Umar, Al-Bidayah wa Al-Nihayah, Beirut, Darul Fikr, 1407H/1986 Miladiyya.
  • Jafarian, Rasul, Littattafan tafiya Hajji hamsin, littafin Alam, Tehran, 2009.
  • Muhaddith Nouri, Hossein bin Muhammad Taqi, Mustadrak al-Wasail da Mustanbat al-Masal, Qum, Cibiyar Al-Bait, 1408H.
  • Musa Ghosheh, Mohammad Hashem, Tarikh Majmu'eh Masjid Al-Aqsa, wanda Seyyed Shahram Farhanian da Hodsa Atefi suka fassara, Qum, Edian Publishing House, 1390.
  • Nasser Khosro Qabadiani, Safarnameh, Mohammad Selahshor art studio, 1368.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Man La yahdara Al-Faqih, Ali Akbar Ghafari, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta Qum, 1413 AH.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh al'umam wa Al-Muluk, wanda Muhammad Abulfazl Ibrahim ya yi bincike a Beirut, Darul Trath, 1967 miladiyya/1387H.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Gabatarwa na Mohammad Javad Balaghi, Tehran, Nasser Khosrow Publications, 1372.
  • Tafsirin Imam Hasan Askari, Qum, Madrasa Al-Imam Al-Mahdi, Farja Al-Sharif, 1409H.
  • Tawfighi, Hossein,Ashnayi ba Adyan Buzurg, Tehran, Kungiyar Nazari da Harhada Littattafan Dan Adam na Jami'a, Qum, Cibiyar Al'adu ta Taha da Cibiyar Kimiyyar Musulunci ta Duniya, bugu na 8, 2005.
  • Yaqoubi, Ahmed bin Abi Yaqoob, Tarihin Eli Yaqoubi, Beirut, Dar Sadir, Bita.