Risalatul Al-Huƙuƙ
![]() | |
Maudu'i | Bayanin haƙƙoƙi Da wazifofi da suke wuyan mutum dangane da sauran mutane |
---|---|
Ya Fito Daga | Imam Sajjad (A.S) |
Madogaran Shi'a | Tuhaful Uƙul, Alkhisal, Man La yahduruhul Faƙihu |
Hadis Silsilatuz Zahab • Hadis Saƙlaini • Maƙbulatu Umar Bin Hanzala • Hadis Ƙurbu Nawafil • Hadis Mi'iraj • Hadis Wilaya • Hadis Wisaya • Hadis Junud Aƙli Wa Jahal • Hadis Shajara |
Risaltul Al-Huƙuƙ (Larabci: رسالة الحقوق) wani hadisi ne daga Imam Sajjad (A.S) dangane da haƙƙoƙi guda hamsin da suke kan wuyan mutum; misalin haƙƙin Allah, haƙƙin Shugabanni, haƙƙin gaɓoɓi, haƙƙin, dangi da ayyuka misalin sallah, azumi, Hajji, layya da sadaka. Mafi tsufan litattafan da aka naƙalto wannan hadisi su ne Tuhaful Uƙul, talifin Ibn Shu'uba Harrani wanda ya rasu shekara ta 381 h ƙamari, da sauran litattafai guda uku na Shaik Saduƙ wanda ya rasu shekara ta 381 h ƙamari, daga littafansa Man La yahduruhul Faƙihu ɗaya daga cikin Kutubul Arba'a, da kuma Al-Khisal da Al-Amali.
Masu nazari kan hadisi sun tafi kan ingancinsa sakamakon ingancin marawaitansa da kuma litattafan da aka rawaito shi, wannan Risala an tarjamata zuwa harsuna daban-daban daga harshen Ingilishi, Faransanci, Urdu da Hindu, kuma an yi sharhi daban-daban a kansa.
Taƙaitacciyar Gabatarwa.
Risalatul Al-Huƙuƙ, wani hadisi ne daga Imam Sajjad (A.S) ya ƙunshi bayanin adadin wasu haƙƙoƙi da suke kan wuyan mutum, misalin haƙƙin Allah, haƙƙin Shugabanni, haƙƙin dangi da haƙƙin gaɓoɓin jiki.[1] Kan asasin naƙalin Shaik Saduƙ a cikin littafin Al-Khisal, Imam Sajjad (A.S) ya rubuta wannan hadisi da surar wasiƙa zuwa ga ɗaya daga cikin Sahabbansa.[2]
Ingancin Hadisin Da Litattafan Da Suka Naƙalto Shi
Masu Nazarin hadisi tare da la'akari da zuwan silsilar Sanadin hadisin cikin ingantattun litattafai sun yi hukunci kan ingancin wannan hadisi,[3] Abu Hamza Sumali ya naƙalto wannan hadisi daga Imam Sajjad (A.S) Malaman ilimin Rijal na Shi'a suna ƙidaya Abu Hamza cikin zaɓaɓɓun ƴan Shi'a, sannan kuma amintacce mutum abin da dogara da riwayarsa.[4]
Mafi daɗewar litattafan hadisi da suka naƙalto wannan riwaya sun naƙaltota cikakkiya ba tawaya, waɗannan litattafai su ne: Tuhaful Al-Uƙul na Ibn Shu'uba Harrani,[5] wanda ya rasu shekara ta 381 h ƙamari, Alkhisal,[6] Man La Yahduruhu Faƙihu.[7] da Al-Amali duka waɗannan litattafai guda uku talifin sun kasance rubutun Shaik Saduƙ, wanda ya rasu shekara ta 381 h ƙamari.[8]
A cewar Muhaddis Nuri cikin littafin Mustadrakul Wasa'il, Sayyid Ibn Ɗawus wanda ya rayu tsakanin shekaru 589-664 shima ya kawo wannan hadisi cikin littafinsa mai suna Falahul Al-Sa'il ya kuma ce ya samo shi ne daga littafin Rasa'ilul Al-A'imma, rubutun Kulaini.[9] na'am babu wannan Magana cikin kwafin Falahus Sa'il da aka buga a wannan zamani, amma masu nazari da gyare-gyare kan littafin Al-Mstadrak suna cewa cikin kwafin rubutun kan Duwatsu akwai ita wannan maganar a jikinsu,[10] wani abin jan hankali na daban shi ne cewa ainahin littafin Rasa'ilul Al-A'imma da Kulaini ya rubuta ya ɓata ɓat babu shi.[11]
Bambance-bambance Masadir
Cikin masadir na hadisi an naƙalto matanin Risalatul Al-Huƙuƙ tare da bambance-bambance, daga jumlarsu akwai litattafai guda biyu Tuhaful Uƙul da Al-Khisal, cikinsu an kawo hadisin filla-filla tare kuma da Muƙaddima da take takaice bayanin bahasin cikin hadisin,[12] wannan muƙaddima babu ita cikin litattafan Man Layahduruhul Al-Faƙihu da Al-Amali,[13] haka kuma cikin littafin Al-Amali ya fara ne da gaɓar bayanin kan haƙƙin mutum a kan kankin kansa;[14] saɓanin sauran litattafan guda uku waɗanda suka fara da gaɓar bayani kan haƙƙin Allah.[15]
Adadin Haƙƙoƙin
Adadin haƙƙoƙi da aka yi bayaninsu cikin Risalatul Al-Huƙuƙ kamar yadda ya zo a riwayar Tuhaful Al-Uƙul haƙƙoƙi ne guda hamsin, sannan a gaɓar ƙarshen wannan hadisi bayani ya zo kamar haka: (waɗannan haƙƙoƙi ne guda hamsin),[16] amma shima Shaik Saduƙ yana ganin adadinsu shi ne haƙƙoƙi hamsin,[17] saboda a cikin littafin Al-Khisal ya rubuta taken suna kan zaɓaɓɓen hadisi kamar haka: haƙƙoƙi guda hamsin na Ali bn Husaini da ya rubuta su zuwa ga Sahabbansa.[18]
Ba'arin marubuta da suka naƙalto matanin Risalatul Al-Huƙuƙ sun ambaci adadin hamsin da ɗaya.[19] hakan ta faru sakamakon littafin Tuhaful Al-Uƙul bai ambaci Hajji ba cikin jerin haƙƙoƙi, tun da Hajji ta zo a cikin riwayar da Saduƙ ya kawo.[20] sai ya zamana an bijiro da wannan mas'ala kamar yadda ɗaya daga masu warware bayani da ƙarin haske yake faɗa, sai aka sanya hajji cikin jerin haƙƙoƙi da suka zo a Tuhaful Al-Uƙul kaɗai dai mai littafin ya samu zamewar alƙalami ne ya manta bai rubutawa da ita; duk da cewa an gama tantace adadin waɗannan haƙƙoƙi amma an samu ba'arin wasu marubuta suna rubuta abin da ba haƙƙi ba a cikin jerin layin haƙƙoƙi.[21]
Abin da Yake Ciki
Haƙƙoƙi guda hamsin da suke cikin Risalatul Al-Huƙuƙ sun kasance cikin rukunai bakwai da za su zo a ƙasa:
- Haƙƙin Allah
- Haƙƙoƙin gaɓɓan sassan jiki: harshe, kunne, idanu, hannu, ƙafa, ciki, al'ura.
- Haƙƙoƙin Ayyuka: sallah, hajji, sadaƙa, layya.
- Haƙƙoƙin Shugabanni: Sarki, Malami, Haƙƙin mamallakin bawa kan bawa.
- Haƙƙoƙin waɗanda ake shugabanta: mutane (haƙƙin mutane kan Sarakunansu) Almajirai, Mata, bawa (haƙƙin bawa kan mai gidansa)
- Haƙƙoƙin Dangi na Nasaba: Mahaifiya, Mahaifi, ɗa, ɗan'uwa.
- Haƙƙoƙi wasu daban: shi ne wanda ya ƴantar da kai daga bauta, bawan da kuka ƴantar da shi, ma'abocin yin Ihsani, mai kiran sallah, limamin sallar jam'i, abokin zama, maƙoci, aboki, abokin tarayya, dukiya, wanda ake bi bashi, abokin mu'amala, mai da'awa, wanda aka yi da'awa kansa, abokin shawara da kai, mai karɓar shawararka,mai neman nasiha, mai yin nasiha, mafi girma, mafi ƙanƙanta, wanda yake da buƙata daga gareka, wanda kake da buƙatar daga gare shi, mai munana maka mai faranta maka, abokin addini, Ahlul zimma.[22]
Tarjamomi
An tarjama Risaltul Huƙuƙ zuwa harsuna masu yawan gaske daga jumlarsu akwai Farisanci, cikin Sanin Littafan Imam Sajjad (A.S) akwai jumlar tarjama guda talatin da aka yi cikin harshen Farisanci kan Risalatul Al-Huƙuƙ,[23] daga jumlarsu akwai:
- Tarjameh Risalatul Al-Huƙuƙ Imam Sajjad; rubutun Rida Bahatesh
- Tarjameh Risalatul Al-Huƙuƙ Imam Sajjad: Simaye Muminin, talifin Muhammad Sadiƙ ƙabadi.
- Tarjameh Risalatul Al-Huƙuƙ Imam Sajjad, rubutun Muhammad Jawad Maulawi Niya
- Tarjameh Risalatul Al-Huƙuƙ Imam Sajjad, Ali Shirawani.[24]
Ƙari kan haka, wannan hadisi yana cikin ba'arin litattafan da aka tarjama su, daga jumlarsu littafin Al-Khisal Na Saduƙ rubutun Muhammad Baƙir Kamrayi, Zindigani Ali Bn Husaini tare da Alƙalamin Jafar Shahidi, da kuma tarjamar littafin Tuhaful Uƙul ta hannun Ahmad Jannati.[25] Akwai tsammanin cewa Muhammad Baƙir Khatun Abadi wanda ya rasu shekara ta 1127 shi ne mutum na farko da ya fara tarjama Risalatul Al-Huƙuƙ.[26]
Haka zalika an tarjama zuwa wasu harsunan daban; daga jumlarsu Ingilishi, Faransanci, Girkanci, Urdu, Tajiki, Armeniyanci, Hindu, Malayi, Serbiyanci, Tagaluk (manil) da Amhari (Yaren ƙasae Etopiya). [27]
Sharhi
An yi sharhi masu yawan gaske kan Risalatul Al-Huƙuƙ ba'arinsu sun kasance:
- Huƙuƙ Az Didgahe Imam Sajjad (A.S) rubutun ƙuduratullahi Mashayiki.
- Risalatul Al-Huƙuƙ Imam Sajjad (A.S) rubutun Ali Muhammad Haidari Naraƙi.
- Tarjameh wa sharhu Risalatul Al-Huƙuƙ Imam Sajjad (A.S) Muhammad Sepahri.
- Huƙuƙ Islami; ya haɗo da wazifofin ɗaiɗaikun mutane da na zamantakewa kan asasin Risalatul Al-Huƙuƙ Imam Zainul-Abidin (A.S), rubutun Ali Akbar Nasiri.
- Ta'ammulat fi Risalatul Al-Huƙuƙ Lil Imam Ali Bn Husaini (A.S) talifin Muhammad Taƙi Al-Mudarrisi.
- Tafsilul Al-Huƙuƙ; Sharhu Riwa'i ala Risalatul Al-Huƙuƙ Lil Imam As-Sajjad (A.S) Muhammad Husaini Al-Ramzi Al-ɗabasi.
- Risalatul Al-Huƙuƙ; rubutun Sayyid Hassan ƙubanci.
- Al-Ma'idatul Al-Samawiyya fi Sharh Al-Risalatul As-Sajjadiyya; rubutun Ma'asum Bn Radiyyu Husaini ƙahastani.
- Sharhu Risalatul Al-Huƙuƙ Hazrat Sajjad; rubutun Musɗapa Mir Taƙiyyu
- Al-Nahjaini fi Sharhi Risalatul Al-Huƙuƙ lil Imam Ali Bn Husaini; rubutun Salihu Bn Mahadi Salihi.
- Risalatul Al-Huƙuƙ; talifin Ayatullahi Husaini Ali Muntazari.
Ku Duba
Bayanin kula
- ↑ Duba Ibn Shu'ba Harrani, Tohaf Al-Aqool, 1363, shafi na 272-55; Sadouq, Al-Khisal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 564-570; Sadouq, Man La yaihdara Al-Faqih, 1413 AH, Juzu'i na 2, shafi na 618-625; Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 368-375.
- ↑ Sadouq, Al-Khisal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 564.
- ↑ Hosseini Jalali, Jihad Imam Sajjad, 1382, shafi na 293.
- ↑ Najashi, Rijal Al-Najashi, 1365 AH, shafi na 115.
- ↑ Ibn Shuba Harrani, Tohaf al-Aqool, 1363/1404 AH, shafi na 255-272.
- ↑ Sadouq, Al-Khisal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 564-570.
- ↑ Sadouq, Man Layihdara Al-Faqih, 1413 AH, Juzu'i na 2, shafi na 618-625.
- ↑ Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 368-375.
- ↑ Muhaddith Nouri, Mustadrak Al-wasa'l, 1408H, juzu'i na 11, shafi na 169.
- ↑ Duba Muhadith Nouri, Mostadrak Al-Wasa'il, 1408H, juzu'i na 11, shafi na 169.
- ↑ Hosseini Jalali, Jihad Imam Sajjad, 2002, shafi na 289.
- ↑ Duba Ibn Shu'ba Harrani, Tohaf al-Aqool, 1363/1404H.
- ↑ Duba Sadouq, Man Layihdara al-Faqih, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi: 618; Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 368.
- ↑ Duba Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 368.
- ↑ Duba Ibn Shu'ba Harrani, Tohf al-Aqool, 1363/1404 AH, shafi na 255; Sadouq, Al-Khasal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 564; Man Layihzara al-Faqih, 1413 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 618.
- ↑ Duba Ibn Shu'ba Harrani, Tohf al-Aqool, 1363/1404 AH, shafi na 272.
- ↑ Sadouq, Al-Khisal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 570; Sadouq, Man Layihdara Al-Faqih, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 625; Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 375.
- ↑ Duba Sadouq, Al-Khisal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 564.
- ↑ Hosseini Jalali, Jihad Imam Sajjad, 1382, shafi na 294.
- ↑ Hosseini Jalali, Jihad Imam Sajjad, 1382, shafi na 294.
- ↑ Hosseini Jalali, Jihad Imam Sajjad, 1382, shafi na 294-297
- ↑ Hosseini Jalali, Jihad Imam Sajjad, 1382, shafi na 305-307.
- ↑ Habibi da Shamsud-dini Mutlaq, 1394, shafi na 321-328.
- ↑ Habibi da Shamsud-dini Mutlaq, 1394, shafi na 321-328. Kitabeshainsi Imam Sajjad, 1394, shafi na 321-324
- ↑ Sepehri, Tarjameh wa Sharh Risalatul AL-Hukuk Imam Sajjad na , 2004, shafi na 29 da 30.
- ↑ Hosseini Jalali, "Rasalah al-Haqq", shafi na 707.
- ↑ Habibi wa Shamsuid-dini Mutlaq, 1394, shafi na 329-332.
Nassoshi
- Habibi, Salman wa Mukhtar Shamsud-din Motlaq, KItabe Shinasi Imam Sajjad, Sahifah Sajjadiyeh wa risaleh Hukuk, Tehran, Majalisar Ahlul-Baiti ta Duniya, bugu na farko, 1394.
- Hosseini Jalali, Seyyed Mohammad Reza, Jihad Imam Sajjad, Musa Danesh, Mashhad, Islamic Research Foundation, bugun farko, 1382 ya fassara.
- Ibn Shu'ba Harrani, Hasan bin Ali, Tohf al-Aqool an Alil -Rasoul, bincike na Ali Akbar Ghafari, Kum, Jamia Madrasin, bugu na biyu, 1363/1404 AH.
- Muhaddith Nouri, Hossein bin Muhammad Taqi, Mustadrak Al-Wasail wa Mustanbat Al-Masa'il, Cibiyar Al-Baiti, bugu na 1, 1408H.
- Najashi, Ahmed bin Ali, Rijal al-Najashi, Qom, Jamia Madrasin, bugu na 6, 1365.
- Sadouq, Mohammad Bin Ali, Al-Amali, Tehran, Kitabchi, bugu na 6, 1376.
- Sadouq, Muhammad bin Ali, Man Layihzara al-Faqih, bincike na Ali Akbar Ghafari, Qum, Jamia Modaresin, bugu na biyu, 1413 AH.
- Sadouq, Muhammad bin Ali, al-Khasal, bincike na Ali Akbar Ghafari, Qom, Jamia Modaresin, bugun farko, 1362.
- Sepehari, Muhammad, tarjama wa Sharh Risale hukuk Imam Sajjad (a.s) Qum, Darul Alam, bugu na 8, 2004.
- Hoseini Jalali, Sayyid Mohammad Reza، «رسالة الحقوق»،"Encyclopedia of the World of Islam (Juzu'i na 19), Tehran, Gidauniyar Dairetul Ma'arifa ta Musulunci, Bugu na Farko, 1393 H."