Shin Akwai Mai Taimako Da Zai Taimaka Mini

Daga wikishia
Zanen Allo na Ashura ta hannun Mahmud Farashiciyan

Shin akwai wani Mataimaki da zai taimaka mini? (Larabci هل من ناصر ينصرني) Shahararriyar jumla daga bakin Imam Husaini (A.S) a ƙarshen mintunan da suka rage masa a rayuwa a ranar Ashura, a cewar Jawad muhaddisi cikin al’adun Ashura wannan jumla da wannan ma’anar ba ta zo ba cikin litattafan tarihi, [1] sai dai cewa wasu masadir da suke da alaƙa da waƙi’ar Karbala sun kawo wata jumla kwatankwacinta. [2] Bisa naƙalin marubutan waƙi’o’in Ashura lokacin da Sahabban Imam Husaini (A.S) suka yi shahada sai ya zamana shi kaɗai ya rage a raye, sai ya furta wannan jumloli kan harshensa

«هَلْ مِنْ ذَابٍّ يَذُبُّ عَنْ حَرَمِ رَسُولِ اللَّهِ هَلْ مِنْ مُوَحِّدٍ يَخَافُ اللَّهَ فِينَا هَلْ مِنْ مُغِيثٍ يَرْجُو اللَّهَ بِإِغَاثَتِنَا هَلْ مِنْ مُعِينٍ يَرْجُو مَا عِنْدَاللَّهِ فِي إِعَانَتِنَا؛

Shin akwai wani mai bada kariya da zai baiwa haramin Manzon Allah? Kariya shin akwai wani mai kaɗaita Allah da yake jin tsoron Allah game da mu? shin akwai wani mai jin kuka da yake fata daga Allah cikin jin kukanmu ? shin akwai mai taimako da yake fatan daga abin da yake wurin Allah cikin taimakonmu? [3] Imam Husaini (A.S) lokacin da yake gidan Bani Muƙatil yayin da ya gayyaci Ubaidullahi Bn Hurri Ju’ufi ya zo ya taimaka masa sai Ubaidullahi ya nemi ya yi masa uzuri, sai Imam ya ce masa ya tashi ya fita daga wurin, saboda matuƙar ya ji sautin neman taimakon Imam sannan yaƙi amsawa to Allah ya halaka shi, [4] wasu ba’ari suna ganin taken “Labbaika Ya Husaini” matsayin amsa kiran tamaikonsa a ranar Ashura. [5] A cikin fim ɗin ranar Ashura wanda Shahram Asadi ya shirya wanda aka yi shi game da waƙi’ar Karbala, Jarumi na farko a cikin Fim ɗin ya kasance wani matashi sabon muslunta, ya bada labarin cewa ya ji wata murya cikin kunnensa tana ta maimaituwa “Wanene zai taimaka mini?” sai ya bibiyi sawun wannan murya har zuwa Karbala. [6]

Bayanin kula

  1. Muhaddi, Farhang Ashura, 1376, shafi na 471
  2. Sayyid Ibn Tawus, Allahouf, 1348, shafi na 116; Ibn Nama Hali, Muthir al-Ahzan, 1406H, shafi na 70.
  3. Sayyed bin Tawus, Allahouf, 1348, shafi na 116.
  4. Tabari, Tarikh Al-Umam wa Al-Muluk, 1387 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 407
  5. <a class="external text" href="https://www.mehrnews.com/news/5552800">«شعار «لبیک یا حسین» به معنای اجابت دعوت سیدالشهدا(ع) است»</a>خبرگزاری مهر.
  6. <a class="external text" href="https://hawzah.net/fa/Magazine/View/89/3367/15514">«نگاهی به فیلم روز واقعه»</a>پایگاه اطلاع‌رسانی حوزه.

Nassoshi