Muzaharar Arba'in, (Larabci مسيرة الأربعين) ko Tattakin Arba'in, aƙida ce ta 'yan Shi'a da ake yi a ranekun ƙarshen safar kusa da 20 ga watan(Arbain Hussaini). Ana gudanar da wannan tattaki ne daga sassa daban-daban na ƙasar Iraƙi da wasu garuruwan Iran zuwa Karbala da nufin gudanar ziyarar Arbaeen. Yawancin masu ziyarar suna zuwa garin Karbala ne daga garin Najaf. A kan hanyoyin ziyarar akwai wuraren tarbar maziyarta, waɗanda ake kira da maukibi.

Hotan Tattakin Arba'in na shekarar 1970 miladiyya

A lokacin mulkin Saddam Hussein, an sanya takunkumi kan gudanar da wannan tattaki, amma bayan rugujewar hizbi ba'as ta Iraƙi a shekara ta 2003, aka sake farfaɗo da wannan tattaki kuma a duk shekara, bayan 'yan Shi'ar Iraƙi, 'yan Shi'ar wasu ƙasashe, musamman Iran. suna zuwa muzaharar Arbain. Rahotanni sun ce baya ga ‘yan Shi’a, kungiyoyin ‘yan Sunna, Kiristoci, Yazdi da sauran addinai su ma suna halartar muzaharar ta Arbaeen.

A cikin 'yan shekarun nan, miliyoyin mutane ne ke halartar wannan tattakin; Ta yadda aka san wannan taron a matsayin babban taron addini na shekara-shekara a duniya. Game da adadin waɗanda suke halartar wannan tattakin, an bayyana al-ƙaluma tsakanin mutane miliyan goma sha biyu zuwa miliyan ashirin.

Asalin Samuwar Tattakin Arba'in

Imam Hassan Askari (A.S): Alamomin mumini guda biyar ne:

• Sallar raka'a 51 raka 17 na farali raka 34 nafilfilin dare da rana.
• Ziyarar Arba'in.
• Sanya zobe a hannun dama.
• Dora goshi kan kasa yayin sujjada.
• Bayyanar da karatun bismilla

Shaik Tusi Tahzeeb Ahkam.bugun shekara 1407, juzu'i na 6, shafi na 52

A bisa wani hadisi daga Imam Hasan Askari (A.S) ya bayyana tattakin Arba'in a matsayin ɗaya daga cikin alamomin Mumini [1] wasu malamai sun bayyana wannan hadisi a matsayin ɗaya daga hujjojin tattakin Arbaeen , An karɓo daga Imam Sadik (A.S) [2]daga Sheikh Ɗusi a cikin Tahzibul-Ahkam [3] da Misbahul-Mutahajjid [4] da Sheikh Abbas ƙummi a cikin Mafatihul-jinan [5] sun rawaito “Ziyarat” Arbaeen a littattafan su.

TARIHI

Masu Tattaki kan hanyarsu zuwa karbala

Kamar yadda wasu masu bincike suka yi nuni da cewa, tattakin ranar Arba'in ya zama sanan ne tsakanin 'yan Shi'a tun zamanin Imamai Ma'asumai (A.S). Sayyid Muhammad Ali ƙadi Tabataba'i, a cikin littafinsa yayi bincike kan tattakin Arba'in na farko da aka farayi zuwa ga Sayyidush-Shuhada, ya bayyana ziyarar Imam Husaini a ranar Arba'in a matsayin Al'amari mai muhimmanci da ƴan Shi'a sukeyi tun zamanin Imamai, wanda suka yi riƙo da shi har a zamanin, Banu Umayya da Banu Abbas. [6]

An ce al'adar tattaki ta zama ruwan dare a zamanin Sheikh Ansari (1214-1281H) kuma malamai da dama sun tafi Karbala da ƙafa. Amma wannan al'ada an manta da ita a zamanin Mirza Hussein Nuri, sai dai ya yi ƙaƙari ya farfaɗo da ita. Muhaddis Nuri ya yi tattaki daga Najaf zuwa Karbala tare da ɗalibansa da sahabbansa na tsawon kwanaki uku. [7] Mawallafin littafin Adabuɗ-ɗuf a wani rahoto da ya bayar kan tattakin Arba'in , ya kwatanta yawan mutanan da suka halarci taron da aka yi da taro na Musulman Makka da kuma halartar tawagogi daban daban daga garare masu yawa, ya ambaci cewa a cikinsu wasu sun rera waƙoƙin yarukan Turkanci da Larabci da Farsi da Urdu. An buga Adabuɗ-ɗuf a shekara ta 1967/1388 bayan hijira kuma marubucin littafin ya ƙiyasta adadin maziyarta Arba'in ya kai sama da mutane miliyan ɗaya. [8]

Hana Tattakin Arba'in A Zamanin Saddam Husaini

A yayin tattakin Arbaeen na shekarar 2013, an gudanar da sallar jam'i mai tsawon kilomita 30 a kan hanyar Najaf zuwa Karbala, kuma dubban Masu ziyara ne suka halarta.

A ƙarshen ƙarni na 14, waɗanda ake kira da hizbu Ba'as a Iraƙi sunyi adawa da tattakin Arba'in, kuma a wasu lokuta ana muzgunawa masu tafiyar ta hanyoyi mabanbanta, Wannan batu ya sa yawan mutane ya ragu. An ce Ayatullah Sayyid Muhammad Sadar ya ayyana wajibcin tafiya zuwa tattakin zuwa Karbala a wancen lokacin. [9]

ƙara Kaimi Da Yawaitar Masu Tattaki

Ayatullahi Khamna'i: “Wani al’amari na musamman da ba a taba ganin irinsa ba a shekarun baya-bayan nan, shi wannan tattaki ... zuwa Karbala. Wannan yunkuri shi ne motsi na soyayya da imani. Haka nan muna kallon wannan yunkuri daga nesa, muna kuma burin samun irin rabon wadanda suka sami wannan nasarar suka aiwatar da wannan yunkuri.

«اربعین، شکوه بیعتی مجدد با امام حسین»، خبرگزاری تسنیم

A shekara ta 1397 bayan hijira (daidai da 1977miladi), Hizbu ba'as ta ƙasar Iraƙi ta hana gudanar da bukukuwan addini da gudanar da tattaki zuwa Karbala; [10] Amma mutan garin najaf a 15 ga safar na wannan shekarar suka fara shirin tafiya Karbala. [11] Wannan yunƙuri dai ya gamu da martanin gwamnatin Sadam Hussein, inda aka kashe mutane da dama, sannan kuma aka ɗaure wasu dayawa daga cikinsu [12] an yankewa Sayyid Muhammad Baƙir Hakim ɗaurin rai da rai a gidan kaso, [13] wasu daga malamai kuma suna gudu zuwa wasu ƙasashen, amma duk da haka sai da aka yanke musu hukuncin kisa. [14]

ƙarin Yawan Maziyartan Tattakin Arba'in

Bayan faɗuwar hizbu ba'as ta Iraƙi a shekara ta 2003, an sake farfaɗo da tattakin Arba'in a ƙasar Iraƙi, a kowace shekara mutane fiye da na shekarar da ta gabata ne ke shiga cikin tafiyar.[15] A cikin shekarun da suka biyo baya, adadin maziyartan da suka halarci wannan muzaharar ya kai sama da mutane miliyan goma; [16] ta yadda ake ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin manya-manyan jerin gwano ko tarukan addini na duniya. [17]

A shekara ta 1395H (2016 miladiyya) hubbaran Sayyiduna Abbas (A.S) suka sanar a cikin wata sanarwa cewa a cikin kwanaki goma sha uku da suka rage zuwa Arba'in (wato daga 7 Safar zuwa 20 Safar) fiye da mutane miliyan goma sha ɗaya da dubu dari biyu ne suka shiga Karbala. [18] A shekara ta 1397 H. (2018) Hukumar hubbaran Imam Hussain (A.S) sun sanar a cikin wata sanarwa cewa a cikin kwanaki goma da suka rage zuwa Arba'in (daga 10 zuwa 20 Safar), fiye da mutane miliyan goma sha daya da dubu dari takwas da hamsin ne suka shiga garin daga manyan ƙofofin Karbala. Waɗanda suka shigo Karbala daga ƙananun tituna ko kuma ba su shiga tsakiyar birnin ba saboda wani dalili (wani yanki mai nisan kilomita uku daga wurin haramin) ba a kidaya su a cikin wannan kididdigar ba dan haka maziyartan zasufi adadin da aka faɗa. [19] Dangane da yawan maziyartan an kawo wata ƙidayar a gidajen yanar gizo da kafafen yaɗa labarai, Wasu rahotanni sun sanar da halartar maziyarta ‘yan Shi’a miliyan 15 a wannan muzaharar. [20]

A shekara ta 1401 AH/1444, wacce ita ce shekara ta farko ba tare da takurar da aka shiga a corona ba, bayan wasu ‘yan shekarun da aka yi fama da annobar corona ɗin, kamfanin dillancin labarai ya sanar da adadin maziyarta zuwa Karbala sama da miliyan 21. [21]

Maziyartan `Yan ƙasashen Waje

Ƙididdigar ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar Iraki ta nuna cewa a shekarar 2018 akalla maziyarta ƴan ƙasashen waje miliyan ɗaya da dubu 300 ne suka zo ƙasar Iraƙi dan su halarci muzaharar Arba'in, [22] A ƙididdigar da gomnatin iraƙi tayi ashekara ta 2018 yawan mutanan yakai miliyan ɗaya da 800 [23] A shekarata 2022 yawan maziyartan ƴan ƙasar waje ya kai miliyan biyar, [24] daga cikinsu miliyan uku da dubu 500 Iraniyawa ne. [25]

Yanayi Da Nisan Tafiya

Hanyar Tattakn Arba'in a Kasar Iraki

Maziyartan ƙasar Iraƙi na tashi daga garuruwansu zuwa Karbala; Amma mafi yawan maziyartan da suke daga Iran da wasu ƴan ƙasashen masubi ta cikin Iran suna zaɓar hanyar Najaf zuwa Karbala don tattaki.Tayin tafiya a kan babbar hanyar yanada nisan kusan kilomita 80, wanda yawanci yana ɗaukar kwanaki biyu zuwa uku. Akwai ginshiƙai(maukibi na saukar baƙi) ko tanti 1452 akan hanyar Najaf zuwa Karbala. [26]

Har ila yau, akwai wata hanyar daga Najaf zuwa Karbala, wadda aka fi sani da "Ɗariƙul-furat" , wasu maziyarta Arba'in suna isa Karbala ta wannan hanya. Hanyar ta ratsa ta cikin tsaunukan da ke gaban kogin Furat kuma nisanta ya kai kilomita 89. A da can malaman Najaf sun kasance suna bin wannan hanya a lokacin Arba'in. Ɗaya daga cikin dalilan amfani da wannan hanya da malamai suka yi shi ne haramcin da aka yi a lokacin sadam husaini na tafiya Arba'in da kuma tattaki. [27]

Ɗabi'u Da Al'adu

Tafiyar Arba'in a Iraƙi tana tare al'adu da dabi'u masu yawa mabanbanta, ciki har da rera waƙoƙi da hidima ga maziyarta da makiyayan gefan kogin Furat sukeyi. Waƙar Husekhani : Ɗaya daga cikin al'adun Iraƙi a kan hanyar zuwa Karbala a ranar Arba'in , Huse waƙoƙi ne da ƙasidu na musamman na ƙabilun Larabawa a kudancin Iraƙi. Waɗannan waƙoƙi suna bayyana jarumtaka da girma , kuma ana amfani da su ne don zaburar da mazaje zuwa ga yin aiki tuƙuru, . Bayan mawaƙin ya karanta, masu sauraro ma zasu dinga maimaita wa sai suyi zagaye cikin da'ira. [28]

Farkon fara taron: Ya rage fara gudanar da zaman makokin Arba'in da kwana biyar tare da isowar jerin gwano da maziyarta ake fara ƙasidun huse, Bayan haka za'a gabatar da ƙungiyoyin hidima da masu dukan ƙirji suma su shiga, ana fara gudanar da babban taron ne da misalin ƙarfe biyu na ranar Arbaeen. Maziyarta suna tsayawa a kusa da ƙofar hubbaren Imam Husaini (A.S) suna rera ƙasidu da yin kuka a lokacin da suke bugun ƙirji, sannan a ƙarshe sai su ɗaga hannayensu a matsayin alamar gaisuwa. [29]

Hidima ga maziyarta: A lokacin tattakin Arba'in makiyayan kogin Furat suna kafa manyan tantuna a kan hanyar tafiya wadda suke kira “maukib” ko mudif, suna ba da masauki a cikinsu domin tarba da cin abinci da hutawa. [30] masu shirya wannan babban taro suna yiwa maziyarta hidima kyauta. masu shiryawa da gudanar da wannan jerin gwano mutanen garine ba tare da saka hannun gwamnati ba. [31]

Bayanin kula

1. Sheikh Mufid, Al-mazar-Manasik Al-mazar, 1413 AH, shafi na 53; Sheikh Tusi, Tahzeeb al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 6, shafi na 52.
2. Sheikh Tusi, Tahzeeb al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 6, shafi na 113.
3. Sheikh Tusi, Tahzeeb al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 6, shafi na 113 da 114.
4. Sheikh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 788-790.
5. Mufatih al-jinan, Ziarat na Arbaeen, Babin Hajji, shafi na 642.
6. ƙazi Tabatabai, Tahƙiƙ darbaraye Awwal kan Arbaeen Sayyed al-Shahda, 1368, shafi na 2.
7. «زندگی‌نامه میرزا حسین نوری»
8. Shabar, Adab al-Taf wa Shu'ara Al-Hussein (A.S), 1401H, juzu'i na 1, shafi na 41.
9. Mazaheri, Farhang Sauge Shi'a, 1395, shafi na 102.
10. Momin, Sanat al-Jumar, 2004, shafi na 165.
11. Asadi, Mujaz Tarikh Iraƙ Al-Siyasi Al-Hadith, 2001, shafi na 101.
12. Wiley, Nahadat Islami Shi'ayane Iraƙ, 1373, shafi na 81.
13. Asadi, Mujaz Tarikh Al-Siyasi Iraƙ Al-Hadith, 2001, shafi na 103.
14. Wiley, Nehdat Islami Shi'ayane Iraƙ, 1373, shafi 82.
15. Mazaheri, Farhng Sauge Shi'i, 1395, shafi na 102.
16. «اربعین، شکوه بیعتی مجدد با امام حسین»
17. گزارش روزنامه فرانسوی لوموند از مراسم اربعین در کربلا
18. أعداد الزائرین المشاة نهاراً فی أربعینیة الإمام الحسین(علیه‌السلام)
19. الکشف عن الاحصائیة الاولیة لاعداد الزائرین بحسب ما رصدته کامیرات العتبة الحسینیة
20. «۱۵ میلیون شیعه در حال رسیدن به کربلا»
21. تعداد زائران اربعین اعلام شد
22. «تعداد زائر غیرعراقی در اربعین»
23. دخول أکثر من ملیون وثمانمائة الف زائر عربی واجنبی حتی یوم ۱۹ من صفر الخیر
24. آمار رسمی عراق: شمار زائران اربعین امسال از ۲۰ میلیون گذشت
25. رکوردهایی که در اربعین ۱۴۰۱ش به دست آمد
26. رکوردهایی که در اربعین ۱۴۰۱ش به دست آمد
27. پیاده روی اربعین از مسیر طریق العلما به کربلا
28. Abazari, “Arba’in Husaini dar sairi wa sukhane Buzrgan”, shafi na 146.
29. Abazari, “Arba’in Husaini dar sairi wa sukhane Buzrgan”, shafi na 147.
30. Abazari, “Arba’in Husaini dar sairi wa sukhane Buzrgan”, shafi na 163.
31. Mazaheri, Farhang Sauge Shi'i, 1395, shafi na 100.

Nassoshi

• ‌«آمار رسمی عراق: شمار زائران اربعین امسال از ۲۰ میلیون گذشت»، حوزه نمایندگی ولی فقیه در امور حج و زیارت، تاریخ درج مطلب: ۲۴ شهریور ۱۴۰۱ش، تاریخ بازدید: ۲۸ مرداد ۱۴۰۲ش.
• "Ijtima Arbaeen Hosseini 20 miliyon duniya ra mutahawwil kohar kard", kamfanin dillancin labarai na Ilna, kwanan watan shiga labarin: Nuwamba 15, 2014, ranar shiga: Oktoba 24, 2017.
• Abazari, Abdur Rahim, " Piyadeh Rawai Arbaeen Hosseini dar sairi wa Sukhane Buzurghan,", a cikin mujallar Farhang Ziarat, shekara ta biyar, lamba 19 da 20, bazara da kaka 2013.
• Arbab ƙommi, Mohammad, Arbain Hosseinieh, Tehran, Esveh Publications, 1372.
• "Arbain, Shukuhe Bai'ati mujaddad ba Imam Husaini,", kamfanin dillancin labarai na Tasnim, ranar shiga labarin: 29 Disamba 1392, ranar shiga: 24 Oktoba 1397.
• Al-Asadi, Mukhtar, Mujaz Tarikh Iraki Al-Siyasi al-Hadith, Cibiyar Nazarin Al-Shaheedin Al-Sadreen da Al-Baƙah, 2001.
• Al-Momin, Ali, Sanat al-Jamr, Beirut, Al-Maƙrez al-Islami al-Mawdeen, 2004.
• «پیاده‌روی زائران اربعین در استان بوشهر»، خبرگزاری مهر، تاریخ درج مطلب: ۲۵ مرداد ۱۴۰۱ش، تاریخ بازدید: ۱۱شهریور ۱۴۰۲ش.
• «تعداد زائران اربعین اعلام شد»، خبرگزای ایسنا، تاریخ درج مطلب: ۲۶ شهریور ۱۴۰۱ش، تاریخ بازدید: ۲۸ مرداد ۱۴۰۲ش.
• «تعداد زائر غیرعراقی در اربعین»، خبرگزاری فردا، تاریخ درج مطلب: ۲ دی ۱۳۹۲ش، تاریخ بازدید: ۲۴ مهر ۱۳۹۷ش.
• «جمعیت زائران کربلا در اربعین حسینی امسال از مرز ۲۷ میلیون نفر گذشت»، سایت سازمان حج و زیارت، تاریخ درج مطلب: ۱۲ آذر ۱۳۹۴ش، تاریخ بازدید: ۲۴ مهر ۱۳۹۷ش.
• «چرا پیاده‌روی اربعین ثواب دارد»، خبرگزاری ایسنا، تاریخ درج مطلب: ۱۷ آذر ۱۳۹۳ش، تاریخ بازدید: ۲۴ مهر ۱۳۹۷ش.
• «زندگینامه میرزا حسین نوری»، سایت بلاغ، تاریخ درج مطلب: ۸ فروردین ۱۳۹۵ش، تاریخ بازدید: ۲۴ مهر ۱۳۹۷ش.
• «زندگینامه حاج محمد ارباب قمی»، پایگاه اطلاع رسانی حوزه، تاریخ درج مطلب: ۱۸ مهر ۱۳۸۷ش، تاریخ بازدید: ۱۹ مهر ۱۴۰۱ش.
• «رکوردهایی که در اربعین ۱۴۰۱ش به دست آمد»، خبرگزاری فارس، تاریخ درج مطلب: ۸ فروردین ۱۴۰۲ش، تاریخ بازدید: ۲۸ مرداد ۱۴۰۲ش.
• «سرآغاز؛ الگوى مفهومى پیاده‌روی اربعین از نگاه رهبر معظم انقلاب»، خبرگزاری میزان، تاریخ انتشار: ۱۴ مهر ۱۳۹۸ش، تاریخ یازدید: ۱۷ شهریور ۱۴۰۱ش.
• شبر، سید جواد، ادب الطف و شعراء الحسین(ع)، بیروت، دار المرتضی، ۱۴۰۱ق.
• شریف رازی، محمد، گنجینه دانشمندان، تهران، کتابفروشی اسلامیه، ۱۳۵۲ش.
• شیخ طوسی، محمد بن حسن، تهذیب الاحکام، تهران، دار الکتب الاسلامیه، ۱۴۰۷ ق.
• شیخ طوسی، محمد بن حسن، مصباح المتهجّد و سلاح المتعبّد، بیروت، مؤسسة فقه الشیعة، چاپ اول، ۱۴۱۱ق.
• ‌ شیخ مفید، محمد بن محمد، المزار-مناسک المزار، قم، کنگره جهانى هزاره شیخ مفید، چاپ اول، ۱۴۱۳ق.
• قاضی طباطبایی، سید محمدعلی، تحقیق درباره اول اربعین حضرت سیدالشهدا(ع)، قم، بنیاد علمی و فرهنگی شیهد آیت الله قاضی طباطبایی، ۱۳۶۸ش.
• قمی، عباس، مفاتیح الجنان.
• ««مشایه الاهواز» بزرگ‌ترین کاروان زائران طریق الحسین(ع)»، خبرگزاری فارس، تاریخ درج مطلب: ۲۴مهر ۱۳۹۶ش، تاریخ بازدید: ۱۱شهریور ۱۴۰۲ش.
• مظاهری، محسن حسام، فرهنگ سوگ شیعی، تهران، نشر خیمه، ۱۳۹۵ش.
• ویلی، جویس ان، نهضت اسلامی شیعیان عراق، ترجمه مهوش غلامی، موسسه اطلاعات، ۱۳۷۳ش.
• «۱۵ میلیون شیعه در حال رسیدن به کربلا»، سایت فردا، تاریخ درج مطلب: ۲ دی ۱۳۹۲ش، تاریخ بازدید: ۲۴ مهر ۱۳۹۷ش.