Jump to content

Ƙungiyar Jihadul-Islam

Daga wikishia
(an turo daga Jihadul Islam)
Harkatul Jihadil Islami A Falasɗinu
SunaHarkatul Jihadil Islami A Falasɗinu
Jagora a yanzuZiyad Nakhala
Wanda Ya KafaFathi Shaƙaƙi
Fitattun MutaneAbdul-Aziz Auda. Akram Al-ajuri. Nafiz Azam
ManufofiGwagwarmaya ɗauke da makami domin fatattakar Isra'ila da `yantar da dukkanin garuruwan Falasɗinu da ta mamaye tare da kafa daular Falasɗinu
MazhabaAhlus-Sunna
Shafin Yanar Gizohttps://jehad.ps
ƘasaFalasɗinu


Ƙungiyar Jihadul-Islam (Larabci:حركة الجهاد الإسلامي في فلسطين) ta Falasɗinu ɗaya ce daga cikin ƙungiyoyin gwagwarmayar Falasɗinawa, wanda aka gina ta bisa tasirin hanyar da Imam Khomaini, wadda ya yi imani cewa hanya ɗaya tilo wadda za a iya `yantar da yankunan Falasɗinu ita ce tsayawa tsayin daka da gwagwarmaya kan mamayar Isra'ila. tushen wannan yunƙuri shi ne imani da koyarwar Musulunci da kuma haramta imani da Isra'ila a matsayin ƙasa mai zaman kanta.

Fathi Shaƙaƙi ne ya kafa ƙungiyar Jihadul-Islam a shekarar 1981 a Gaza. Har ila yau, reshen sojojinta ya kai hare-hare da dama kan Isra'ila, haka ita ma Isra'ila ta kashe wasu kwamandojinsu, Babban sakataren wannan ƙungiya shi ne Ziyad Nakhala. Kafin shi Ramadan Abdullah, kafin Ramadan, Fathi Shaƙaƙi ne ke ɗaukar wannan nauyi. Wasu ƙasashe kamar Amurka da Ingila da kuma Tarayyar Turai sun sanya wannan ƙungiya cikin jerin ƙungiyoyin ta'addanci.

Gabatarwa da Kafa Wannan Ƙungiya

Harkar Jihadul islam ɗaya ce daga cikin muhimman ƙungiyoyin gwagwarmayar Falasɗinawa, waɗanda suke ganin gwagwarmaya da daƙiya shi ne hanya ɗaya tilo ta `yanta Ƙudus.[1] Kuma bata goyan bayan yarjejeniya da Isra'ila.[2] Wannan ƙungiyar ba takai Hamas da Fatahu samun magoya baya ba,[3] samuwar wannan ƙungiyar a garin Ƙudus ya temaka mata wajan cigaba sosai [4] Kamar yanda wasu kafafan yaɗa labarai suka ba da rahoto, wannan ƙungiyar ta ƙunshi ɓoyayyan tsari na sirri.[5]

Adawa da yarjejeniyar Oslo (2003), ƙauracewa zaɓen majalisar dokoki (2006), adawa da yarjejeniyar zaman lafiya ta Misra a shekara ta 2014, da matakin warware rikici tsakanin Hamas da gwamnatin Misra (2014) na daga cikin muhimman ayyukan siyasa da ƙungiyar Jihadul-Islam ta aiwatar[6]

An kafa Harkatul Jihadul islam a birnin Gaza a shekara ta 1981 a hannun Fathi Shaƙaƙi, likitan Bafalasɗine,[7] tare da haɗin gwiwar mutane irin su Abdul-Aziz Awda,, Ramadan Abdullah da Nafiz Azzam.[8] A shekarar 1987 a ka kori shuwagabannin ƙungiyar zuwa Lebanon a can suka haɗu da ƙungiyar Hizbullahi Lubnan ta ƙasar Labanon suka sami horo daga dakarun IRGC na Iran.

Hukumar leƙen asiri ta Isra'ila watau Mossad ta kashe Fathi Shaƙaƙi babban sakataren ƙungiyar Jihadul-Islam a shekara ta 1995,[9] daga nan Ramadan Abdullah Shalah (Rasuwu: 2020) ya gaje shi. Ramadan Abdullahi ya taka rawar gani a fagen siyasar wannan yunƙuri.[10] Bayan rashin lafiyar Ramadan Abdullah, an naɗa Ziyad Nakhala a matsayin babban sakataren ƙungiyar a shekarar 2018.[11]

Fathi Shaƙaƙi; Wanda ya assasa kuma babban sakataren ƙungiyar jihadi na farko

Ƙa'idoji da Mamufofi

Ganawar da aka yi tsakanin Ziyad Al-Nakhla, babban sakataren jihad; Da Ismail Haniye, shugaban ofishin siyasa na Hamas

Jihadul islam ta ayyana ƙa'idojin ta , waɗanda da ta ginu a kansu : addinin Muslunci shi ne tushen imani da ayyukan wannan gwagwarmaya. A bisa waɗannan ƙa'idoji, dukkanin ƙasar Falasɗinu ƙasa ce ta Musulunci da Larabawa, sannan kuma amincewa da gwamnatin Isra'ila a wannan ƙasa haramun ne, kuma kasancewar Isra'ila a cikin Falasɗinu yana nufin mamayewa da rarraba ƙasashen Musulunci gabaɗaya.[12] Sannan duk wani tsarin mulki da zai nuna Isra'ila ce mai wannan ƙasar, ba za a yarda da shi ba[13]

Ƙungiyar Jihadul-Islam ta Falasɗinu ta bayyana babbar manufarta shi ne `yantar da Falasɗinu gaba ɗaya, ruguza gwamnatin Isra'ila da kafa gwamnatin Musulunci. Sauran manufofin wannan yunƙuri dai su ne: shirya al'ummar Falasɗinu zuwa jihadi na soji da na siyasa, da tsara al'ummar musulmin duniya da kwaɗaitar da su wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ga Falasɗinu, da ƙarfafa alaƙa tsakanin Musulmi da `yantar da su da haɗin kai da kira zuwa ga Musulunci da yaɗa koyarwarsa[14]

Harkar Jihadul Islam tana da haɗin gwiwar siyasa da soja da ƙungiyar Hamas,[15] Amma ba ta da dangantaka da ƙungiyar `yantar da Falasɗinu ta (Harkatu Tahir Falasɗiniyya), saboda tsarin ita wannan ƙungiya ta ba ruwansu da addini da kuma son yin sulhu da Isra'ila da kuma amincewa da ita.[16]

Ƙalubalantar Mamayar Da Isra'ila Ta Yi Wa Falasɗinu

Ƙudus Brigades (Saraya Al-ƙuds), shi ne reshen soja da tsaro na ƙungiyar Jihadul-islam, an kafa shi ne a ƙarni na ashirin. Kafin wannan sunan ana kiransa da dakarun Mujahidul-Islam kafin wannan ana kiransa da Kata'ib Saif al-Islam[17] Saraya al-ƙuds ita ce mafi girman rundunar soji a Gaza bayan reshen soja na Hamas[18] Isra'ila ta kashe wasu kwamandojin Jihadul-islam, waɗanda suka haɗa da: Fathi Shaƙaƙi (1995), Isam Barahma (1992), Hani Abid (1994), Mahmud Al-Khawaja (1995), Mahmud Ɗiwaliba (2002), Mahmud Zamɗa (2003), Bashir Al-Dabbash (2004), Khalid Al-Dahduh (2006 ), Daniyal Mansur (2014 AD)[19] da Hassam Abu Harbid (2021), kwamandan reshen soji na Saraya al-ƙuds [19]

Hare-Hare Da Ofireshin

Ɓangaran soja na Jihadul-islam ya kai hare-hare da dama kan yankuwan da Isra'ila ta mamaye,misalin u Baitul Lid, Dizengoff, Kafer Darum, Netsarim, Gabashin Jabaliya, Moraj[20] da Bashaer al-Intisar.[21]

Gwagwarmayar Neman Haƙƙi Ta Shekarar 1987 Miladiyya

A shekarar 1987 Harkar Jihadul-islam ta taka rawar gani a gwagwarmaya ta farko ta Falasdinu (1987).

Jawabin Abdul-Aziz Auda a masallacin Izzud-din Ƙassam na daga cikin muhimman abubuwa a farkon wannan intifada.[22] Isra'ila ta bayyana Ramadan Abdullah a (2000) a matsayin shugaban aiwatar da hare-hare kanta.[23] Shigar da dakarun sojan Jihadul-islam cikin wannan intifada[24] shi ne musabbabin kisan wasu kwamandojin rundunar sojansu da Isra'ila ta yi.

Tarayya a Cikin Yaƙin Tufanul Al-Aƙsa

A cewar wasu kafofin watsa labarai na Turai, ƙungiyar Jihadul-Islam ta shiga cikin yaƙin ɗufan Al-aƙsa (2023), wanda ya yi sanadin mutuwar Isra'ilawa 1400 tare da kame wasu daruruwan Isra'ilawa[25] inji Isra'ila[26] Wannan ƙungiyar ta bayyana cewa ta kama mutane sama da 30 kuma ta hanyar musayan fursunoni kaɗai za ta sake su.[27]

Ba'arin wasu kasashe misalin Amurka, Ingila, Kanada da Japan da kuma tarayyar kasahsen turai sun sanya ƙungiyar Jidaul Islam cikin jerin Kungiyoyin ta'addanci.[28]

Tasirantyuwa Da Juyin Juya halin Muslunci Na Iran

Tun Farko kafa ƙungiyar Jihadul Muslunci ta tasIrantu da tunanin juyin juya halin muslunci na Iran karkashin jagorancin Imam Khomaini.[29] bisa wannan tunani ne suka rike muslunci da koyarwarsa matsayin fitila da jagora cikin gwagwarmaya da jihadi.[30] Fathi Shaƙaƙi gabanin kafa wannan kungiya, ya rubuta littafi mai taken (Imam Al-Khomaini Al-Halli Al-Islami Wal Al-Badil) ma'ana Imam Khomaini hanya samun warwara ta muslunci, da wannan dalili ne Kasar Misra ta kama shi ta tsare shi[31] Ya bayyana tunanin Imam Khomaini da juyin juya halinsa a matsayin mafi kyawun madadin sauran hanyoyin cimma manufofin duniyar musulmi musamman 'yancin Falasɗinu[32] Jihadi domin wannan yunƙuri na goyon bayan Imam Khomaini da tunaninsa da ƙarfafa haɗin kan Shi'a da Ahlus-Sunna ana zarginsa da cewa ya zama shi'a.[33] ƙungiyar jihadil Islami ta nesanta kanta da wannan zargi tare da bayyana cewa sun dora dukkanin ayyunkansa kan koyar mazhabobin Ahlus-sunna[34]

A cewar Khalid al-Baɗash, memba a ofishin siyasa na ƙungiyar Jihadul-Islam, Iran ita ce babbar mai goyon bayan wannan yunƙuri na gwagwarmayar Falasɗinu,[35] Taimakon Iran ya kama daga kuɗi, makaman yaƙi, koyar da sojoji dabarun yaƙi, da al'amuran siyasa[36]Cibiyar Nazarin Siyasar Larabawa, ta bayyana cewa, Harkatul Jihadul Islami rta kasance `yar kallo a lokacin yaƙin basasar Siriya (Farawa: 2011). da kuma harin da ƙawancen ƙasashen Larabawa suka kai wa ƙungiyar Ansarullah ta Yaman (Farawa: 2015), wanda ya sa dangantakarta da Iran ta yi sanyi na wani lokaci[37]

Tashar Talabishin

Cibiyar sadarwar tauraron ɗan Adam ta Falasɗinu Alyoum tana da alaƙa da ƙungiyar Jihadul-slami, wanda babbar cibiyarta ke a Gaza. An sanar da matsalolin kuɗi a matsayin dalilin rufe ofishin wannan cibiyar sadarwa na Urushalim (2015),.[38] daga nan a shekarar 2016 Isra'ila ta rufe ta gabaki ɗaya.[39]

Ƙungiyoyin Ƙawancen Gwagwarmaya
Layi Suna Kafawa Wanda Ya Kafa Fitattun Mutane Shugaba Mazhaba Tushe Logo Kafofin Labarai
1 Harkatu Amal 1974m Imam Musa Sadar Musɗafa Camaran Nabihu Birri Shi'a Labanun
Tashar Talabijin Ta NBC
2 Ƙungiyar Jihadul-Islam 1981m Fatahi Shaƙaƙi Ramadan Abdullahi Husam Abu Harbid Ziyad Nakhala Ahlus-Sunna Gaza
Tashar Falasɗinil Yaumi
3 Hizbullahi Lubnan 1982m Sayyid Abbas Musawi Sayyid Hassan Nasrullah Na'im Ƙasim Shi'a Labanun Example Tashar Al-Manar
4 Failaƙ Badar 1985m Adnan Ibrahim Abu Mahadi Al-Muhandis Hadi Al-Amiri Shi'a Iraƙ
Tashar Al-Ghadir
5 Hamar (Harkar gwagwarmayar Muslunci) 1987m Shaik Ahmad Yasin Abdul-Aziz Rantisi Isma'il Haniyye Kwamitin wucin gadi na Hamas Ahlus-Sunna Falasɗinu
6 Dakarun Ƙudus (Failak Ƙudus) 1990m Sayyid Ali Khamna'i Ahmad Wahidi Ƙasim Sulaimani Isma'il Ƙa'ani Shi'a Iran
7 Harkatu Ansarullahi Yaman 1990m Husaini Al-Husi Badrud-Dini Al-Husi Abdul-Malik Al-Husi Zaidiyya Yaman
Shabakatu Al-Masira
8 Kata'ibu Hizbullahi Iraƙ 2003m Abu Mahadi Al-Muhandis Abu Husaini Humaidawi Abu Baƙir As-sa'idi Arzan Allawi Ahmad Muhsin Farhi Alhumaidawi Shi'a Iraƙ
Shabakatu Al-Ittija
9 Kata'ibu Sayyidush Shuhada Iraƙ 2003m Abu Musɗafa Khazali Haj Abu Yusuf Abu Ala Al-wala'i Shi'a Iraƙ
10 Asa'ibu Ahlil Haƙƙi | 200m Ƙaisu Khazali Abdul_hadi Addaraji Muhammad Al-bahadili Ƙaisu Khazali Shi'a Iraƙ Example Shabakatu Al-Ahad
11 Harkatu Nujaba 2013m Akram Ka'abi Abu Isa Iƙlim Mushataƙ Kazim Alhawari Akram Ka'abi Shi'a Iraƙ
12 Dakarun Zainabiyyu 2013m Wasu jama'a daga Fakistan Zainab Ali Jafari Aƙid Malik Muɗahhar Husaini Shi'a Fakistan
13 Dakarun Faɗimiyyun 2013m Wasu mutane daga mayaƙan Afganistan Ali Rida Tawassuli Sayyid Muhammad Husaini Sayyid Ahmad Sadat Shi'a Afganistan
14 Hashadush Sha'abi 2014m Hadi Amiri Abu Mahadi Al-Muhandis Falihu Fayyaz Shi'a Iraƙ

Bayanin kula

  1. «حدث الساعة.. معلومات تهمک معرفتها عن الجهاد الإسلامی التی أنجبت أسری عملیة جلبوع»، Gidan yanar gizo na gidan labarai na Al Jazeera.
  2. «نشأت بمصر، ولعبت دوراً کبیراً بالانتفاضة.. قصة حرکة الجهاد وسر استهداف إسرائیل لها بحربها الأخیرة»،Gidan yanar gizon Larabci Post.
  3. «نشأت بمصر، ولعبت دوراً کبیراً بالانتفاضة.. قصة حرکة الجهاد وسر استهداف إسرائیل لها بحربها الأخیرة»Gidan yanar gizon Larabci Post.
  4. «نشأت بمصر، ولعبت دوراً کبیراً بالانتفاضة.. قصة حرکة الجهاد وسر استهداف إسرائیل لها بحربها الأخیرة»، Gidan yanar gizon Larabci Post
  5. «رويكرد جهاد اسلامي فلسطين در مبارزه با اسرائيل و تفاوت‌هايش با حماس در چيست؟»Gidan yanar gizo na Euronews.
  6. «رویکرد جهاد اسلامی فلسطین در مبارزه با اسرائیل و تفاوت‌هایش با حماس در چیست؟»، Gidan yanar gizo na Euronews.
  7. «حرکة الجهاد الإسلامی»، Gidan yanar gizo na gidan labarai na Al Jazeera.
  8. «نشأت بمصر، ولعبت دوراً کبیراً بالانتفاضة.. قصة حرکة الجهاد وسر استهداف إسرائیل لها بحربها الأخیرة», Shafin Larabci Post.
  9. «تاریخ حرکة الجهاد الإسلامی فی فلسطین موضوعًا لمحاضرة وحدة الدراسات الاستراتیجیة»،Yanar Gizo na Cibiyar Bincike da Nazarin Larabci
  10. «ما هی حرکة "الجهاد الإسلامی" التی تتهمها إسرائیل بقصف المستشفی المعمدانی فی غزة؟»، France24 website.
  11. «ما هی حرکة "الجهاد الإسلامی" التی تتهمها إسرائیل بقصف المستشفی المعمدانی فی غزة؟»، France24 website..
  12. «نبذة عن حرکة الجهاد الإسلامی فی فلسطین»Gidan yanar gizo na Aljazeera News Network.
  13. «نبذة عن حرکة الجهاد الإسلامی فی فلسطین»،Gidan yanar gizo na Aljazeera News Network.
  14. «نبذة عن حرکة الجهاد الإسلامی فی فلسطین»، Gidan yanar gizo na Aljazeera News Network
  15. «ما هی حرکة الجهاد الإسلامی وما علاقتها بحماس؟»، Shafin Al-Hurrah.
  16. «رویکرد جهاد اسلامی فلسطین در مبارزه با اسرائیل و تفاوت‌هایش با حماس در چیست؟»،Gidan yanar gizo na Euronews.
  17. «حدث الساعة.. معلومات تهمک معرفتها عن الجهاد الإسلامی التی أنجبت أسری عملیة جلبوع»Gidan yanar gizo na Aljazeera News Network.
  18. «حرکة الجهاد الإسلامی»،TRT Yanar Gizo na Larabci.
  19. «حدث الساعة.. معلومات تهمک معرفتها عن الجهاد الإسلامی التی أنجبت أسری عملیة جلبوع»،Gidan yanar gizo na gidan labarai na Al Jazeera.
  20. «حدث الساعة.. معلومات تهمک معرفتها عن الجهاد الإسلامی التی أنجبت أسری عملیة جلبوع»،Gidan yanar gizo na gidan labarai na Al Jazeera.
  21. «نشأت بمصر، ولعبت دوراً کبیراً بالانتفاضة.. قصة حرکة الجهاد وسر استهداف إسرائیل لها بحربها الأخیرة»، Gidan yanar gizon Larabci Post.
  22. «نشأت بمصر، ولعبت دوراً کبیراً بالانتفاضة.. قصة حرکة الجهاد وسر استهداف إسرائیل لها بحربها الأخیرة», Shafin Larabci Post.
  23. «نشأت بمصر، ولعبت دوراً کبیراً بالانتفاضة.. قصة حرکة الجهاد وسر استهداف إسرائیل لها بحربها الأخیرة»، , Shafin Larabci Post..
  24. الشریف، «حرکة الجهاد الإسلامی فی فلسطین», Gidan yanar gizon Cibiyar Nazarin Falasdinu.
  25. «ما هی حرکة "الجهاد الإسلامی" التی تتهمها إسرائیل بقصف المستشفی المعمدانی فی غزة؟»، وبگاه FRANCE.24.
  26. «رویکرد جهاد اسلامی فلسطین در مبارزه با اسرائیل و تفاوت‌هایش با حماس در چیست؟»، Gidan yanar gizo na Euronews.
  27. «ما هی حرکة "الجهاد الإسلامی" التی تتهمها إسرائیل بقصف المستشفی المعمدانی فی غزة؟»Gidan yanar gizo na Faransa 24.
  28. «درباره جهاد اسلامی فلسطین و گردان‌های قدس چه می‌دانیم؟»، وGidan yanar gizo na yanar gizo na labarai na Euronews.
  29. «حرکة الجهاد الإسلامی», Gidan yanar gizon TRT na Larabci.
  30. ابو طه، «تأثیر امام خمینی و انقلاب اسلامی در اندیشه و عملکرد جنبش جهاد اسلامی فلسطین»، Portal Imam Khumaini.
  31. Arabsorkhi, «جنبش جهاد اسلامی فلسطین از آغاز تا امروز»،Yanar Gizo na Ƙungiyar Ƙungiyoyin Kare Falasdinawa.
  32. Abu Taha «تأثیر امام خمینی و انقلاب اسلامی در اندیشه و عملکرد جنبش جهاد اسلامی فلسطین»، Portal Imam Khumaini.
  33. Abu Taha«تأثیر امام خمینی و انقلاب اسلامی در اندیشه و عملکرد جنبش جهاد اسلامی فلسطین»، Portal Imam Khumaini.
  34. Abu Taha «تأثیر امام خمینی و انقلاب اسلامی در اندیشه و عملکرد جنبش جهاد اسلامی فلسطین»، Portal Imam Khumaini.
  35. «فی حوار مع الجزیرة نت خالد البطش یوضح مکاسب الجهاد من الحرب ودور حماس والعلاقة مع إیران»Gidan yanar gizon Al Jazeera News Network.
  36. «فی حوار مع الجزیرة نت خالد البطش یوضح مکاسب الجهاد من الحرب ودور حماس والعلاقة مع إیران»،Gidan yanar gizon Al Jazeera News Network.
  37. «تاریخ حرکة الجهاد الإسلامی فی فلسطین موضوعًا لمحاضرة وحدة الدراسات الاستراتیجیة», Yanar Gizo na Cibiyar Bincike da Nazarin Siyasa ta Larabawa.
  38. «حدث الساعة.. معلومات تهمک معرفتها عن الجهاد الإسلامی التی أنجبت أسری عملیة جلبوع»،Gidan yanar gizo na Aljazeera News Network.
  39. «حدث الساعة.. معلومات تهمک معرفتها عن الجهاد الإسلامی التی أنجبت أسری عملیة جلبوع»Gidan yanar gizon Al Jazeera News Network.

Nassoshi

Hamid, Arabsorkhi «جنبش جهاد اسلامی فلسطین از آغاز تا امروز»، Yanar Gizo na Society for Defence of Palestine People, ranar shigarwa: 25 May 1401, kwanan wata ziyara: 10 Nuwamba 1403.