Jump to content

Badrud-Dini Al-Husi

Daga wikishia
Badrud-Dini Al-Husi
NasabaJikokin Imam Hassan
Tarihin Haihuwa17 Jumada al-Awwal 1345 Hijira
Wurin HaihuwaYaman unguwar Zahyiyan yankin Sa'ada
Tarihin Shahada2010 kalandar Miladiyya dai-dai da 1431 Hijira
Sanannun DangiHusaini Al-husi (Ɗansa) Abdul-malik Al-husi
MazhabaShi'a Zaidiyya
AikiKafa ƙungiyar Hizbul Haƙƙi da Hizbu Shababul Mumin
Rubuce-rubuceAl-taisiru Fi At-tafsir. Al-majmu'atul Wafiya Fil Fi'atil Bagiya. Fada'ilul Ale Muhammad Alaihimus salam. Ahadisu Mukhtara Fi Fada'ili Alel Baiti. Alu Muhammad Laisu Kullu Ummati


Badrud-Dini Al-Husi (Larabci:السيد بدر الدين بن أمير الدين بن الحسين بن محمد الحوثي) Ɗaya ne daga cikin malaman mazhabar zaidiyya kuma jagoran na tarbiyyar ruhi ga tafiyar harkatu Ansarullahi Yaman. Shi ne mahaifin Husaini Al-Husi wanda ya kafa Harkar Ansarullah. Bayan kashe Husaini, Har ila yau sai ɗansa dai Abdul-Malik Al-Husi, ya karɓi ragamar jagorancin wannan ƙungiya.

Badrud-dini Al-Husi na ɗaya daga cikin masu goyon bayan juyin juya halin Musulunci na Iran, da kuma goyon bayan haɗin kan Musulunci da goyon bayan Falasɗinu. Ya rubuta littattafai da dama, ciki har da Al-Taisir fi Al-Tafsir. An tattara ayyuka da rubuce-rubucen Badrud-Dini game da Wahabiyanci a cikin Kundin Silsilatuz Zahabiyya Fi Raddi Alal Wahabiyya.

Abdul Malik Al-Husi shugaban ƙungiyar Ansarullah ɗane na uku a wajansa.

Matsayi Da Muhimmancinsa

Badrud-Dini Al-Husi shugaba mai tafiyar da Harkatu Ansarullahi Yaman.[1] ana ɗaukarsa ɗaya ɗaga cikin malamai kuma maraj'ai.[2] masu tafsiri na mazhabar Zaidiyya Jarudiyya.[3]

Al-Husi yana ɗaya daga cikin masu kare haɗin kan Musulunci.[4] Ya kasance mai himma wajen tunkarar tunani da aƙidar masu adawa da musulunci.[5] yana da littattafai da ya rubuta masu yawa kan asalin addinin musulunci da raddi kan aƙidar wahabiyanci.[6]

Nau'in Tunaninsa

Badar al-Din Husi ya kasance mai ba da muhimmanci ga batun Falasɗinu da fuskantar Isra'ila, yana ganin ya zama dole a tallafawa waɗanda ake zalunta.[7] Ya goyi bayan matsayin ɗansa Husaini wajen fuskantar Amurka ta hanyar taken ƙauracewa siyan kayayyakin Amurka da Isra'ila.[8] Badr al-Din yana ganin haɗin kan Musulmai ya zama wajibi don tunkarar babban hatsarin da musulmi suke fuskanta,[9] ya kuma so ya ɗauki matakin da ya dace wajen fuskantar makircin Amurka da Isra'ila da fuskantarsu.[10]

Ana ganin aƙidar Al-Husi tafi kusa-kusa da ta aƙidun Shi'a Imamiyya,[11] sannan yana ganin wasu daga maƙiyan Imam Ali (A.S) waɗanda suka san gaskiyar abin da Annabi ya faɗa. Amma suka juya masa baya a matsayin Kafirai.[12]

Goyan Baya Da Tasirintuwa Da Juyin juya halin Muslunci Na Iran

Badrud-Dini Al-Husi lokacin taron hadin kai da aka yi a Iran shekara 1374 h. shamsi

Badr al-Din Husi yana ɗaya daga cikin masu goyon bayan juyin juya halin Musulunci na Iran,[13] An ce ya yi bikin murnar nasarar da sojojin Iran suka samu a yaƙin Iran da Iraƙi ta hanyar harba harsasai a sama saboda nuna farin da murna a fili,[14] Haka nan kafa ƙungiyar Ansarullah da fara ayyukanta ya samo asaline daga juyin juya halin Musulunci na Iran,[15] Ana ganin manufofinsa da na ƴaƴansa suna dacewa da manufofin siyasar Iran.[16]

Badrud-dini ya je Iran tare da ɗansa Husaini a shekara ta 1994 miladiyya.[17] Wasu sun bayyana cewa ya koma ƙasar Yaman a shekara ta 2002 mildaiyya.[18] wasu kuma sun ce ya zauna a Iran na tsawon shekara ɗaya.[19] wasu suna ganin a wannan zaman da ya yi a a Iran ya tasirantu da mazhabar Shi'a Imamiyya, don haka ne ake ɗaukar Harkatu Ansarullahi Yaman a matsayin ƙungiyar Shi'a Imamiyya. sai dai cewa su Husawa ana ɓangaren sun yi watsi da wannan iƙirari kuma suna jaddada matsayinsu na ƴan Zaidiyya.[20]

Ayyukan Siyasa

Bayan shahadar ɗansa Husaini, Badar al-Din ya karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar Ansarullah,[21] tare da taimakon wasu malaman Zaidiyya ya kafa ƙungiyar Hizb al-Haƙƙi,[22] Al-Husi ya kasance daga manyan masu tafiyar da wannan ƙungiya,[23] ya bar wannan jam'iyya ya kafa wata ƙungiyar mai suna Shabab al-Mu'umin.[24]

Rashawa da Cin hanci da rashin ƙwarewa cikin tafiyarwar gwamnati mai ci, da shisshigi na ƙasashen waje, musamman Amurka, a Yaman sune dalilan da sanya Badrud-din Al-Husi ya kira almajiransa su yi gwagwarmaya sauya gwamnati mai ci. [25] Wannan al'amari ya sa gwamnati ta kai hari gidansa hakan ya tilasta masa ya bar ƙasar.[26]

An ce an sha kai hari don a kashe Badarud-din sau da dama. A lokacin da aka kai masa hari a ƙauyen Al-Kharbi, an kashe wasu adadi daga danginsa da ƴan uwansa,[27] sai dai kuma ba a yi nasarar kashe shi ba, hakan ya faru a shekara ta 2005 wanda ya janyo yaƙi a tsakanin ƴan Husi da gwamnatin Yaman, an dakatar da yaƙin a lokacin da ake zaton an kashe Badrud-din[28]

Halaye da Ɗabi'unsa

Malaman da sukai zamani da Badarul-din Al-Husi sun yaba da halayensa masu kyau.[29] Majdud-Din Mu'ayyidi yana ganinsa a matsayin malami mai fa'ida kuma ya yaba wa tunaninsa,[30] Hussaini bin Hasan ya siffanta shi da taƙawa da zuhdu da ƙasƙantar da kai da ibada.[31] Har ila yau, kamar yadda Abdul-Malik Husi ya ce, Badarul-din yana da ilimin kur'ani mai girma,[32] Kuma bawa alƙur'ani mai girma muhimmanci ne ya sa ake kiransa da faƙihul-ƙur'an.[33]

Rubuce-rubuce

Badarul-din al-Husi yana da ayyuka da dama, waɗanda adadinsu ya kai kusan littafi 100.[34] A cikin littafinsa akwai Al-Taisir fi al-Tafsir, ya yi amfani da hanyar tafsirin Ƙur'ani da Ƙur'ani da tafsirin ƙur'ani da ruwaya bisa hadisai na Annabi (S.A.W) da Imam Ali (AS),[35] ya yi sharhi mai tsayi da bincike mai zurfi kan hadisin kashe Ammar Yasir da ƴan ta'adda suka yi a cikin littafin Al-Majmu'ul-Wafiyyah fil-Fi'a tul-Bagiya.[36]

Ya rubuta littafan Fadai'ul Muhammad (S.A.W), wanda ake kira da ahadis Mukhtara fi Fadai'l Alil-Bait Wa Ale Muhammad Laisu Kulu al-Umma da Ayat al-Mawada,[37] game da Ahlul Baiti. An buga ayyukansa da littattafan sa na raddi kan Wahabiyanci a cikin tarin littafin Al-Salsila Al-zahabiyyah fi rad ala Al-Wahhabiyya[38]

Tarihin Rayuwa

An haife shi 17 Jimada Awwal shekara ta 1345 bayan hijira a garin Dahyan na ƙasar Yaman, kuma ya girma a garin Sa'ada wadda ita ce babbar cibiyar Zaidiyya a ƙasar Yaman,[39] nasabar sa tana komawa ga Hassan Musanna ɗan Imam Hassan (A.S),[40] nasabar sauran mutan garin Sa'ada yana komawa ne ga Husaini ɗan Muhammad wanda ya yi hijira daga birnin Hus zuwa Dahyan.[41]

Matakin Karatu

Badrud-Dini Al-Husi ya yi karatunsa a Sa'ada tare da mahaifinsa Amirud-Dini Husaini Al-Husi Rasuwa: 1394 Hijiriya) da kawunsa Hassan bin Hussein Husi (ya rasu: 1388 AH).[42] Ya kuma amfana sosai da Abdul-Aziz Ghalibi da Yahaya bin Husani Husi.[43] Badarud-din ya sami iznin ijtihadi daga wasu malamai, waɗanda sunayensu ya zo a cikin littafin Miftahul Asanid na Al-Zaidiyya.[44]

Rasuwa

Badrud-Dini tare da ƴaƴansa da kuma shugabannin Ansarullahi

Badrud-din Husi ya mutu a ƙarshen shekara ta 2010. mutanen Husi sun ce dalilin mutuwarsa shi ne cutar hunhu. Ƙungiyar Al-ƙa'ida a Yamen ta yi iƙirarin kashe shi a wani farmaki da ta kai,[45] wasu kafafen yaɗa labaran duniya ba su amince da iƙirarin kashe Badrud-din a hannun ƙungiyar alƙa'ida ba.[46]

Ƴaƴansa

Wasu rahotanni sun bayyana cewa Badarud-din al-Husi yana da mata huɗu.[47] kuma yana da ƴaƴa mata bakwai da maza goma sha uku[48] yara mazan sune Hussein, Yahya, Abdul ƙadir, Muhammad, Ahmad, Hamid, Amirud_Din, Ibrahim, Abdul Malik, Ali ,Abdul Khaliƙ , AbduS-Salam da Najmud-din,[49] An kashe Husaini, wanda ya kafa ƙungiyar Ansarullah ta Yaman, da Abdulƙadir da Ali a yaƙi,[50] kuma an kashe Ibrahim a wani kai hari.[51] Abdul Malik kuma shi ne shugaban ƙungiyar Ansarullah ta ƙasar Yemen na uku a halin yanzu.[52]

Bayanin kula

  1. وفاة بدرالدین الحوثی احد ابرز مرجعیات الطائفه الشیعیه الزیدیه فی الیمن»، Shafin yanar gizo na Al-Alam News Network;«جماعة الحوثیین.. حرکة یمنیه جمعت بین الزیدیه و النهج الایرانی و الحکم العائلی»،Gidan yanar gizon Al Jazeera News Network
  2. Wajih, A'alam al-Mu'allifin al-Zaydiyyah, 1420 AH, shafi na 263.
  3. «السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»، Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman
  4. Sheikh Hosseini, Janbashe Ansarullah Yemen, shafi na 98.
  5. «السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»، Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman
  6. «العلامة الربانی بدرالدین الحوثی.. حائط صد امام التکفیریین»،‌Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman
  7. «السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»، Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman
  8. السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»، Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman
  9. «السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»،Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman
  10. «وفاة بدرالدین الحوثی احد ابرز مرجعیات الطائفه الشیعیه الزیدیه فی الیمن»،Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman
  11. «الحوثیون فرقه جارودیه تحولت من الزیدیه الی التشیع تؤمن بدور الیمن بحروب القیامه و تهاجم الصحابه و ترتبط بایران»،Gidan yanar gizo na gidan yanar gizo na CNN Larabci
  12. Houthi, Rasa'ilu Sayyid Badar al-Din al-Houthi, shafi na 67
  13. Sheikh Hosseini, Janbashe Ansarullah Yemen, shafi na 99
  14. Sheikh Hosseini, Janbashe Ansarullah Yemen, shafi na 112
  15. «الحوثیون فرقه جارودیه تحولت من الزیدیه الی التشیع تؤمن بدور الیمن بحروب القیامه و تهاجم الصحابه و ترتبط بایران»،Gidan yanar gizo na gidan yanar gizo na CNN Larabci
  16. «الحوثیون فرقه جارودیه تحولت من الزیدیه الی التشیع تؤمن بدور الیمن بحروب القیامه و تهاجم الصحابه و ترتبط بایران»، Gidan yanar gizo na gidan yanar gizo na CNN Larabci.
  17. Sheikh Hosseini, Janbashe Ansarullah Yemen, shafi na 152
  18. Sheikh Hosseini, Janbashe Ansarullah Yemen, shafi na 152
  19. «عن الیمن و الغزو الوهابی السعودی»، Shafin yanar gizo na Al-Mayadeen News Network
  20. جماعة الحوثیین.. حرکة یمنیه جمعت بین الزدیه و النهج الایرانی و الحکم العائلی»Gidan yanar gizon Al Jazeera News Network
  21. جماعة الحوثیین.. حرکة یمنیه جمعت بین الزدیه و النهج الایرانی و الحکم العائلی»،Gidan yanar gizon Al Jazeera News Network
  22. Sheikh Husseini, Janbashe Ansarullah Yemen, shafi. 101.
  23. «الحوثیون.. فرقه جارودیه تحولت من الزیدیه الی التشیع تؤمن بدور الیمن بحروب القیامه و تهاجم الصحابه و ترتبط بایران، وبگاه شبکه خبری CNN عرب
  24. Sheikh Husseini, Janbashe Ansarullah Yemen, shafi. 102.
  25. Sheikh Husseini, Janbashe Ansarullah Yemen, shafi. 154.
  26. Sheikh Husseini, Janbashe Ansarullah Yemen, shafi. 155.
  27. Sheikh Hosseini, Janbashe Ansarullah Yemen, shafi na 155.
  28. «من ..حسین بدرالدین حوثی الی ..اخیه عبدالملک.. تقریر»،Shafin Labarai na Waj El-Iman.
  29. «السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»، Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman.
  30. السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»،Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman
  31. «السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman
  32. «السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»، Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman
  33. السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»،Gidan yanar gizo na Al'adun Al-Qur'ani
  34. Sheikh Hosseini, Janbashe Ansarullah Yemen, shafi na 101.
  35. «العلامه بدرالدین الحوثی.. انموذج للعالم المسلم و دوره تجاه دینه و امته», Kamfanin Dillancin Labarai na Sabat
  36. Hosseini Ashkuri, Mu'allifat Al-Zaydiyyeh's, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 430
  37. Vajiya, I'lam Al-Mu'allifin Al-Zaidiyya. 1420 AH, shafi na 263-264.
  38. «السلسلة الذهبیه فی الرد علی الوهابیه ج۱.. للسید العلامة المجاهد بدرالدین بن امیرالدین الحوثی», Shafin Majalisar Musulunci na Al-Zaidi
  39. Vajiya, Al-Alam Al=Mu'allifn Al-Zaidiyyah, 1420H, shafi na 263.
  40. «السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»،Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman
  41. «السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»،Gidan Yanar Giza gizo na Kundin Sakafar da Al'adun Al-Qur'ani.
  42. «السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»،Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman
  43. «السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»، Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman.
  44. «السید العلامه بدرالدین بن امیرالدین الحوثی»،Yanar Gizo na Kungiyar Malaman Yaman.
  45. «الحوثیون.. فرقه جارودیه تحولت من الزیدیه الی التشیع تؤمن بدور الیمن بحروب القیامه و تهاجم الصحابه و ترتبط بایران»، Gidan yanar gizo na gidan yanar gizo na CNN Larabci
  46. Ku duba «الحوثیون.. فرقه جارودیه تحولت من الزیدیه الی التشیع تؤمن بدور الیمن بحروب القیامه و تهاجم الصحابه و ترتبط بایران»، Gidan yanar gizo na gidan yanar gizo na CNN Larabci «وفاة بدرالدین الحوثی ابرز مرجعیات الطائفة الشیعیه»،Shafin yanar gizo na gidan labarai na France 24
  47. «لماذا لم تؤول قیادة تنظیم الحوثی الی محمد بدرالدین؟»،Gidan yanar gizon Al-Masdar Online.
  48. «لماذا لم تؤول قیادة تنظیم الحوثی الی محمد بدرالدین؟»، Gidan yanar gizon Al-Masdar Online.
  49. «لماذا لم تؤول قیادة تنظیم الحوثی الی محمد بدرالدین؟»Gidan yanar gizon Al-Masdar Online.
  50. «لماذا لم تؤول قیادة تنظیم الحوثی الی محمد بدرالدین؟»،Gidan yanar gizon Al-Masdar Online.
  51. الیمن: الحوثیون ینعون شقیق زعیمهم بعد تعرضه للاغتیال»Shafin yanar gizo na Faransa 24.
  52. الیمن: الحوثیون ینعون شقیق زعیمهم بعد تعرضه للاغتیال»Shafin yanar gizo na Faransa 24.

Nassoshi