Jump to content

Ranar Ƙudus Ta Duniya

Daga wikishia
Ranar Ƙudus Ta Duniya
Lokacin da aka shiryaJuma'a ta ƙarshen Ramadan
Tushe na tarihiSaƙon Imam Khomaini


Ranar ƙudus ta duniya, (Larabci: يوم القدس العالمي) ita ce Juma'a ta ƙarshe wa watan Ramadan na ko wace shekara, wace Imam Khomaini a shekarar 1358shamsi/1980 miladiyya, (Ramadan 1399 h, ƙ) a hukumance ya keɓance wannan rana matsayin ranar goyan bayan Falasɗinu, tare da neman al'ummar musulmi su yi tarayya cikin raya wannan rana a faɗin duk duniya domin katse hannun ta'addancin Sahayoniyya da masu goyan bayansu. Sanyawa Juma'ar ƙarshen watan Ramadan sunan ranar ƙudus, ta samu goyan bayan masu tunani da ma'abota fasaha, a yau ƙari kan ƙasar Iran, cikin ƙasashen daban-daban na duniya ana shirya taron jerin gwano ranar ƙudus, bisa rahotan majiyoyin labarai, ana shirya wannan muzahara a ƙasashe 80.

A shekarar 2014 da 2018 miladiyya an shirya taron gasar ƙasa da ƙasa na zanen barkwanci na ranar ƙudus ta duniya a ƙasar Iran.

Matsayi Da Taƙaitaccen Tarihi

Ranar ƙudus ko ranar ƙudus ta duniya, wannan suna ya samu ne ta hannun Imam Khomaini a hukumance domin nuna goyan baya ga al'ummar Falasɗinu, Imam Khomaini a ranar 16 Mordad 1358 shamsi/7 Agusta 1980 miladiyya (13 Ramadan 1399, h, ƙ) cikin wani saƙo da ya aikawa al'ummar musulmi na Iran da duniya baki ɗaya, ya sanyawa Juma'a ta ƙarshen Ramadan suna ranar ƙudus, ya kuma buƙaci al'ummar musulmi na duk duniya da daulolin musulmi su haɗu kafaɗa da kafaɗa.[1] domin datse hannun ta'addancin Isra'ila da masu goya mata baya.[1] Saƙo da aka ambata a baya ya kasance raddi da martani kan harin da sojojin Isra'ila suka kai kan Masallacin Al-Aksa da kuma harin bom da suka kai kan ƙasar Labanun.[2]

Bayan gudanar da jerin gwano na ranar ƙudus na farko da aka yi a shekarar 1980 miladiyya a Tehran, a wannan taro an karanta saƙon wasiƙar Yasir Arafat. Har ila yau Mahadi Bazargan, firaminista na farko na daular wucin gadi ta Iran, Abdul-Halim Khaddam ministan harkokin waje na Siriya a lokacin, Sayyid Ali Khamna'i da Muhammad Mujtahid Shabastari sun gabatar da jawabi a wannan taro.[3] Kafin wannan jerin gwanon ranar ƙudus, mutane 25 daga masu tunani da marubuta, daga jumlarsu Darawishi Ashuri, Darawish Shayegan, Simin Daneshur Mahrejuyi da Ahmad Shamelo, cikin wani jawabi sun sanar da cewa za su kasance kafaɗa da kafaɗada tare da duk masu rajin neman ƴanci da kafa dimokraɗiyya ta hanyar shiga muzaharar ƙudus.[4]

Ranar ƙudus ta duniya, cikin jawabin jagororin juyin juya halin Muslunci na Iran, Imam Khomaini, Sayyid Ali Khamna'i, maraji'an taƙlidi na Shi'a da Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren Hizbullahi Lubnan, rana ce da take da matsayi na musamman, Imam Khomaini, yana ganin ranar ƙudus matsayin rana ta Muslunci da daular muslunci, bawai kaɗai ranar Falasɗinu ba kawai.[5] Tare da la'akari da wannan rana matsayin sharar fage na Shirin tashi tsaye na baki ɗayan al'ummar Musulmi da kuma kafa ƙungiyar gungun raunana a baki ɗayan faɗin duk duniya.[6] Sayyid Ali Khamna'i, jagoran jamhuriyar Muslunci ta Iran, yana da ra'ayin cewa raya ranar ƙudus da girmama ta, zai sanya Falasɗinawa su ji cewa ba su kasance marasa gata ba a lokacin da Isra'ila take musu ruwan bama-bamai, haka zai ƙarfafa gwiwarsu su ci gaba da gwagwarmaya neman ƴancinsu.[7]

Nasir Makarim Shirazi daga maraji'an taƙlidi na Shi'a, yana ganin cewa wajibi ne shiga muzaharar ƙudus kuma wajibi ne na shari'a, mace tana iya zuwa wannan jerin gwano ko da kuwa mijinta bai ba ta izini ba.[8] Yana da ra'ayin cewa ya kamata ranar ƙudus ta zama wani babban taron nuna rashin amincewa mai ƙarfin gaske, ya juya ya zama nuna rashin yadda na kowa da kowa kan masu kwace da ƴan mamaya.[9] A ra'ayin Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren ƙungiyar Hizbullahi Lubnan, Isra'ila bawai kaɗai hatsari ce ga Falasɗinu ba, bari dai hatsari ce ga zaman lafiya, sulhu da cin gashin kai na baki ɗayan ƙasashen duniya.[10]

Saƙon Imam Khomaini
Bismillahir Rahmanir Rahim. Na sha bayyana barazanar Isra’ila ga Musulmi. Yanzu ta ƙara kai hari kan `yan uwanmu maza da mata na Falasɗinu da Lebanon. Ina kira ga dukkan Musulmai da su tashi tsaye su haɗa kai domin dakatar da mamayar Isra’ila. Ranar Juma'a ta ƙarshe a Ramadan—Ranar Ƙudus—ta zama rana ta haɗin kai da goyon baya ga Falasɗinu. Allah ya ba Musulmai nasara kan Kafirai

[11]

Taron Ranar Ƙudus

Ana shirya muzaharar ranar ƙudus a ƙasashe daban-daban, daga jumlarsu akwai Malesiya, Indiya, Turkiyya, Kanada, Norway, Azerbaijan, Sudan, Ingila, Bahrain, Bosniya da Hezgobiniya, Tunisiya, Fakistan, Astiraliya, Jamus, Kuwait, Afrika ta kudu, Seweden, Banazuwala, Yaman da Girka.[12] Bisa rahotan majiyoyin kafofin watsa labarai, haƙiƙa taron ranar ƙudus ana shirya a fiye da ƙasashe 80 daga ƙasashen musulmi da wanda ba na musulmi ba.[13]

Taron ranar ƙudus ana yinsa a Juma'a ta ƙarshen watan Ramadan.[14]] Kafofin labarai na duniya suna naɗo rahotannin yadda wannan taro yake gudana a ƙasashe daban-daban na duniya.[15] A ƙasashen yamma, sakamakon Juma'a rana tana cikin ranakun aiki a mako, suna shirya wannan taro a ranakun hutu na ƙarshen mako, ranar Asabar ko Lahadi.[16] Na'am shirya taron ranar ƙudus ta duniya ya fuskanci cikas a wasu ƙasashe sakamakon matsin lamba daga masu mulki a ƙasashen.[17]

Abubuwan Da Suka Shafi Fasahar Zane-Zane

Farkon taron gasa na ƙasa da ƙasa na fasahar zanen barkwanci na ranar ƙudus ta duniya, ya kasanmce a shekarar 1393 shamsi/2014 miladiyya, wannan taro ta ƙunshi sashe na asali guda biyu: ranar ƙudus da sashe na musamman: Harkokin takfiriyya domin sa wa a manta da Falasɗinu, wanda aka shirya da ya tattaro mutane 200 daga ƙasashe 33 na duniya, an gabatar da ayyuka fiye da guda 500.[18] Cikin wannan taro hukumomi da cibiyoyin labarai daga jumlarsu har da kamfanin dillancin labarai na Abna, Ofishin kula da takardu na gwagwarmayar Falasɗinum cibiyar fasaha ta jamhuriyar Muslunci ta Iran duka sun halarci wannan taro..[19]


Taron gaza na ƙasa da ƙasa na fasahar zanen barkwanci na ranar ƙudus ta duniya, ya guda a shekarar 1397 shamsi/2018 miladiyya, tare da halartar fiye ma'abota fasaha 120 daga ƙasashe 27 na duniya, sannan a gabatar da ayyuka guda 316 game da ranar ƙudus ta duniya, tare da Allah wadai da matakan daular Amurka cikin shelanta Baitul Muƙaddas matsayin babban birnin daular Isra'ila[20]

Ku Duba

Bayanin kula

  1. Imam Khomeini, Littafin “Ṣaḥīfat al-Imām”, Shekara ta 1389 H.S., Juzu’i na 9, Shafi na 267
  2. Adami, “Tasir Tahdidhaye Guruhe Daga Salafi-Takfiri Bar Amniyate Hasti shenakti, shafi na 13.
  3. «سخنرانان روز قدس در سال ۵۸ چه کسانی بودند؟»، Shafin yanar gizo na Tārīkh-e Irān.
  4. «سخنرانان روز قدس در سال ۵۸ چه کسانی بودند؟»، Shafain yanar na Tārīkh-e Irān.
  5. Imam Khomeini, Littafin “Ṣaḥīfat al-Imām”, Shekara ta 1389 H.S., Juzu’i na 9, Shafi na 278
  6. Imam Khomeini, Littafin “Ṣaḥīfat al-Imām”, Shekara ta 1389 H.S., Juzu’i na 9, Shafi na 28
  7. «بیانات در خطبه‌های نماز جمعه», Gidan Yanar Gizo na Ofishin Kula da Kare Ayyukan Ayatullah Khamenei.
  8. آیت‌الله العظمی مکارم شیرازی: شرکت در راهپیمایی روز قدس وجوب شرعی دارد
  9. «شرکت در راهپیمایی روز قدس واجب است»، Shafin Tabnak.
  10. «سخنرانی سید حسن نصرالله، دبیر کل حزب الله لبنان، در روز جهانی قدس»Sayit na"Moqawama.ir" — Shafin Yanar Gizo na Ƙungiyar Hizbullah ta Lebanon
  11. Imam Khomeini, Littafin “Ṣaḥīfat al-Imām”, Shekara ta 1389 H.S., Juzu’i na 9, Shafi na 267
  12. «جهان و روز جهانی قدس»،Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
  13. «روز قدس از نگاه رسانه‌های دنیا»، Shafin yanar gizo na shabake Khabar
  14. «مراسم روز قدس در لندن»، Shafin BBC.
  15. «حضور ۵۰۰۰ رسانه خارجی برای پوشش راهپیمایی روز قدس در ایران...»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Al-Alam.
  16. «مراسم روز قدس در لندن»، Shafin BBC.
  17. «محدودیت‎ها و موانع برگزاری روز جهانی قدس در خارج از کشور»، سایت قدسنا؛ «علل مخالفت برخی دولت‌های اسلامی...»، Shafin Qudsuna
  18. «بیانیه هیأت داوران اولین جشنواره...»،Kamfanin dillancin labarai na Abna.
  19. «بیانیه هیأت داوران اولین جشنواره...»، Kamfanin dillancin labarai na Abna.
  20. «برگزیدگان دومین جشنواره بین‌المللی کاریکاتور روز جهانی قدس معرفی شدند»Shafin Honar Online.

Nassoshi

  • Adami, Ali, da Reza Niknam, "Tasiri Tahdidhaye Guruhe Salafi-Takfiri Bar Amniyate Hasti Shenakti," a cikin Mujallar Nazarin Siyasa ta Duniyar Musulunci, No. 19, Fall 2016.
  • An gabatar da wadanda suka yi nasara a bikin ranar Quds na duniya karo na biyu," gidan yanar gizon Honaronline, ranar bugawa: Satumba 28, 2018, ranar ziyarar: Yuni 2, 2019.
  • Jawabi a cikin Hudubar Juma'a", a gidan yanar gizon ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei, ranar shigowa: 16 Farvardin 1370, ranar ziyarar: 2 Khordos 2019.
  • Sanarwar alkali na bikin Batun Ranar Quds na Duniya na Farko + Sunayen Wadanda Suka Yi Nasara", Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA, Ranar bugawa: Oktoba 5, 2014, Ranar ziyarar: Yuni 2, 2019.
  • "Sama da kafafan yada labarai na kasashen waje 5,000 ne ke bayar da rahotanni kan muzaharar ranar Qudus ta duniya a garuruwa daban-daban na Iran.", shafin yanar gizon Al-Alam, ranar shigowa: Yuni 8, 2018, ranar ziyarar: Yuni 2, 2019.
  • Jawabin Sayyid Hassan Nasrallah – A ranar Quds ta Duniya, shugaban Hizbullah na Lebanon ya gabatar da jawabi a shafin Islamic Resistance Lebanon, inda ya jaddada goyon bayan juriya da adawa da mamayar Isra’ila.
  • Shafin Tabnak – Ya bayyana cewa halartar zanga-zangar Ranar Quds wajib ne a addini, inda malamai suka bayyana cewa mata na da 'yancin halarta duk da rashin amincewar maza.
  • Ṣaḥīfat al-Imām – Wani littafi da ke tattara jawaban Imam Khomeini, wanda aka wallafa a shekarar 1389 H.S. daga Cibiyar Tsare da Watsa Ayyukan Imam Khomeini.
  • Shafin Qodsna (1) – Ya nazarci dalilan da yasa wasu gwamnatocin Musulmai ke ƙin gudanar da bukukuwan Quds ta Duniya a ƙasashensu; saboda siyasa, tsoro ko matsin lamba daga kasashen yamma.
  • Shafin Qodsna (2) – Ya bayyana ƙalubale da ƙuntatawa da ake fuskanta wajen shirya Ranar Quds a ƙasashen da ba Iran ba, musamman dangane da dokoki da matsin lamba daga gwamnati.
  • Shafin BBC Persian – Ya ruwaito yadda aka gudanar da taron Quds a birnin London, inda Musulmai da masu goyon bayan Falasɗinu suka gudanar da zanga-zanga cikin lumana.