Sayyid Ibrahim Ra'isi
| Shugaban ƙasa na takwas na Jamhuriyar Musulunci ta Iran | |
|---|---|
| Cikakken Suna | Sayyid Ibrahim Ra'isi Al-sadati |
| Laƙabi | Shahidin Jamhuriya, Shahidin Hidima |
| Nasaba | Zaidu Bin Ali |
| Tarihin Haihuwa | 23 Azar shekarar 1339Sh/1960 M. |
| Wurin Haihuwa | Mashhad Iran |
| Tarihin Shahada | 20 ga Mayu, 2024. |
| Wurin Shahada | Tabriz |
| Sanannun Dangi | Sayyid Ahmad Alamul Huda (Mahaifin matarsa) |
| Addini | Muslunci |
| Mazhaba | Shi'a Imamiyya |
| Aiki | Malamin Addini |
| Muƙamai | Shugaban ƙasar Iran da shugabancin ma'aikatar shari'a ta Iran, Hukumar Kula Da Haramin Imam Rida. Wakili a Majalisar Ƙwararru Ta Jagoranci |
| Bayan | Hassan Ruhani |
| Kafin | Mas'ud Fezeshkiyan |
| Malamai | Sayyid Mahmud Hashimi Shahrudi. Agha Mujtaba Tehrani. Ayatullahi Khamna'i |
| Rubuce-rubuce | Taƙrirat Darse Ƙawa'ide Fiƙhi. Irse Bi Waris. Ta'aruz Asli Wa Zahir Dar Fiƙhi Wa Ƙanun |
| Sa Hannu | |
Sayyid Ibrahim Ra'isi al-Sadati (1339-1403sh / 1960-2024m) wanda aka fi sani da Sayyid Ibrahim Ra'isi da kuma Shahid Ra'isi, malamin addini ne na mazhabar Shi'a kuma shugaban ƙasa na takwas na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Raisi ya kasance ɗalibin da ya yi karatu a Hauza (Makarantar Addini) da kuma jami'a, sannan memba ne a ƙungiyar Jami'atu Ruhaniyyat al-Mubariz (Ƙungiyar Malamai Ƴan Gwagwarmaya). Ya riƙe manyan muƙamai daban-daban a cikin tsarin mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran; waɗanda suka haɗa da: Shugaban Sashen Shari'a (Alƙalin Alƙalai), Babban Mai Shigar da Kara na Ƙasa (Attorney General), Shugaban Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Ƙasa, Mai Shigar da Kara a Kotun Musamman ta Malamai, Memba a Majalisar Fayyace Maslahar Tsarin Mulki., Wakili a Majalisar Ƙwararru ta Jagoranci, Har ila yau, ya yi shekaru uku yana shugabancin Hukumar Kula Da Haramin Imam Rida.
Raisi ya rasu ne a ranar 30 ga watan Ordibeheshti, 1403sh (19 ga Mayu, 2024m) sakamakon haɗarin jirgin sama, tare da wasu mutane bakwai; cikinsu har da Husaini Amir Abdullahiyan (Ministan Harkokin Waje na Iran), Sayyid Muhammad Ali Ale Hashim (Wakiliyar Jagora a lardin Azarbaigan ta Gabas), da Malek Rahmati (Gwamnan lardin Azarbaigan ta Gabas).
Saboda rasuwarsa a lokacin da yake kan hanyar yi wa al'umma hidima da ciyar da tsarin Musulunci gaba, ana kiransa da sunan "Shahidin Hidima".
Tarihin Rayuwa da Karatu
An haifi Sayyid Ibrahim Ra'isi a ranar 23 ga watan Azar shekara ta 1339 h. shamsi, wanda ya yi dai-dai da 14 ga watan Disamba 1960 miladiyya, a garin Mashad a yankin Naugan, salsalar nasabarsa tana danganewa zuwa ga Zaidu ɗan Ali, ya fara karatun hauza a Mashad a makarantar hauzar Nawab, sannan ya ci-gaba da karatu a shekarar 1975 a hauzar Ƙum, ya yi almajiranta a hannun manya-manyan malamai misalin Yadullahi Duzduzani, Sayyid Ali Muhaƙƙiƙ Damad, Ali Akbar Mishkini, Ahmed Baheshti, Murtada Muɗahhari da Husaini Nuri Hamadani.[1] Haka nan kuma ya shiga darasin karijul fiƙihu na Sayyid Muhammad Hassan Mar'ashi, Sayyid Mahmud Hashimi Shaharudi, Agha Mujtaba Tehrani, Ayatullahi Khamna'i da sauran manyan malamai..[2]
Ya kasance ɗalibi a makaranta Madraseh Ali Shahid Muɗahhari inda ya karanci fiƙihu da huƙuƙ.[3] a shekarar 1362 h. shamsi, ya auri Jamila ɗiyar babban limamin garin Mashad Sayyid Ahmad Alamul Huda.[4]
Tarihin Gwagwarmaya Tun Kafin Samun Nasarar Juyin Juya Hali A Iran
Kamar yanda aka naƙalto, haƙiƙa Sayyid Ibrahim Ra'isi shekaru gabanin kafa jamhuriyar muslunci a Iran, ya kasance yana ayyukan gwagwarmaya lamarin da yakai ga jami'an leƙen asirin fadar sarki shah suka kama shi.[5] Haka nan kuma ya kasance tare da rakiyar ba'arin ɗalibai yana zuwa ziyartar malaman addini da gwamnatin shah ta kora ta kai su wurare masu nisa daga inda suke, daga jumnlarsu akwai zuwa ganin Ayatullahi Khamna'i wanda aka kora zuwa garin Iranshahar Ra'isi ya je wannan gari don ziyartarsa,[6] bayan yaɗa wani rubutu na cin fuska kan Imam Khomaini a cikin jaridar Iɗɗila'at a 17 ga watan day shekara ta 1356, Ra'isi ya shiga taron nuna rashin amincewa kan wannan cin fuska, wanda aka fara shi daga makarantar Ayatullahi Burujardi (Madraseh Khan).[7] Haka kuma a watan Janairu shekara 1978 miladiyya, ya halarci taron malamai cikin nuna rashin amincewa da rufe filin sauka da tashin jirage don hana saukar jirgin da ya ɗauko Imam Khomaini don dawo da shi Iran.[8]
Shugabancin Haramin Imam Rida (A.S)

A shekarar 1394 bayan mutuwar Abbas Wa'iz Ɗabasi, ƙarƙashin umarnin jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Sayyid Ali Khamna'i an naɗa Ra'isi muƙamin mai kula da haramin Imam Rida (A.S)[10] har zuwa watan Farwardin shekara ta 1398/Maris 2019, ya ci-gaba da kasancewa a wannan muƙami[11] lokacin shugabancinsa ya samar tarin hidimomi ga wannan wuri mai tsarki, daga jumlarsu akwai samar da unguwannin maziyarta da suke kusa da haramin, tare da hidima samar musu da makwanci da abin ci da sauran hidimomi,[12] haka nan kuma samar da tsarin ɗaukar nauyin masu son zuwa ziyara garin Mashad, tare da fifita raunana cikinsu, samar da miƙatin Rida (Wurin ne da aka tane da shi don hutawar maziyarta) kan hanyoyin da suke tuƙewa ga garin Mashad, haka nan tsarin mahidimta matasa shima yana cikin sauran ci-gaba da ya kawo a wannan harami.[13]Ayatullahi Khamna'i cikin hukuncin umarnin naɗa Ra'isi kan muƙamin kula da haramin Iman Rida (A.S) da kulawa da al'amuran maziyarta, hidima ga maƙota musamman ma raunanan haramin Imam Rida (A.S) yaɗa ilimin kur'ani da mazhabar Ahlul-baiti (A.S) a duk duniya, samar da tsarin da zai taimakawa talakawan da suke cikin sassan ƙasar Iran amfana waƙafofin wannan harami mai tsarki, Kuma ya tsara harkokin tattalin arziki da sabis na wannan harami mai tsarki.
Ayyukan Siyasa
Ibrahim Ra'isi bayan nasarar juyin juya halin muslunci a ƙasar Iran, tun yana ɗan shekara 20 da haihuwa ya fara kutsawa cikin ayyukan hidima ga al'umma, ya fara aiki a ma'aikatar shari'a da muƙamin majistare na yankin karaj, Na dan wani lokaci, ya kula da ofishin masu gabatar da ƙara na Hamadan..[14] Sauran muƙaman da ya jagoranta za su iya kasancewa kamar haka:
- Mai gabatar da kara na Tehran daga 1368 zuwa 1373.[15]
- Shugaban Hukumar Bincike ta ƙasa ta 1373 zuwa 1383[16]
- Shugaban Hukumar Bincike ta ƙasa ta 1373 zuwa 1383.[17]
- Wakilin al'ummar Khorasan ta Kudu a majalisar kwararrun jagoranci tun 2005.[18]
- Babban mai gabatar da ƙara na ƙasar daga 1393 zuwa 1394[19]
- Memba a majalisar fayyace maslahar hukuma daga shekara 1396.
- Shugaban Hukumar Shari'a ta Iran daga 1397 zuwa 1400.[20]
- Shugaban ƙasar Iran tun 1400.[21]
- Kasancewa memba a majalisar malamai ƴan gwagwarmaya a shekara 1376 bisa shawarar Ayatullahi Mahadawi Keni..[22]
Goyan Bayan Falasɗinu Da Gwagwarmaya

Sayyid Ibrahim Ra'isi yana cikin fitattun fuskokin ƴan gwagwarmaya, a farkon fara shugabancin ƙasar Iran ya yi tafiya zuwa ƙasar Siriya tare da abokanen rakiya, a babban birnin Damashƙi ya gana da jagororin gwagwarmayar kwato ƴancin Falasɗinu da ma Hizbullahi lubnan. Shi ne farkon shugaban ƙasar Iran da tun bayan yaƙin cikin gida na Siriya ya yi tafiya zuwa wannan ƙasa. A rahotan kamfanin dillancin labarai na irna, Ra'isi tsawon kwanaki 165 da fara ofireshin ɗin ɗufanul al-aƙsa da kuma harin Isra'ila ta kai a Gaza, ya dauki matakai sama da 100 don tallafawa Gaza da kungiyoyin gwagwarmayar Falasɗinu..[24] Har ila yau, a zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 78, ya kebe wani bangare na jawabin nasa kan batun mamayar Palastinu da mamayar da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta yi wa wasu sassan Lebanon da Siriya.[25]
Shin ba lokaci ba ne da za a kawo ƙarshen shekaru 75 na mamayar kasar Falasɗinu da zaluncin wannan al'ummar da ake zalunta da kisan mata da ƙananan yara da haƙƙoƙin al'ummar Falasɗinu?[26]
Kowarwa Da Kuma Rubuce-rubucensa
Ibrahim Ra'isi a zamanin da yake shugabancin haramin Imam Rida (A.S) a Mashad ya kasance yana bada darasin bahasil karijul fiƙihu, haka kuma ya koyar da litattafan fiƙihu, ƙawa'idul fiƙihil ƙada'i da fiƙihul iƙtisad a hauzozin ilimi na tehran da jami'o'i daban-daban misalin jami'ar Imam Sadiƙ (A.S) da jami'ar shahid beheshti.[27] Sayyid Ibrahim ya walllafa taƙriri cikin darasin ƙawa'idul fiƙihi (Mujalladi uku da ya ƙunshi shari'a, tattalin arziƙi da ibada) da kuma bahasin gado wanda bashi da magaji, ta'arudul asli da zahir cikin fiƙihu da doka.[28] Haka nan an wallafa litattafai daban-daban cikin batutuwan haƙƙoƙi, tattalin arziƙi, fiƙihu, adalcin zamantakewa da tsarin rayuwa.[29]
Rasuwa Sakamakon Hatsarin Jirgi
Ranar 30 ga watan Urdibeheshti shekara 1403, Sayyid Ibrahim Ra'isi ya yi tafiya cikin jirgi mai saukar ungulu zuwa yankin azerbaijan sharƙi domin kai shi bikin buɗe ɗaya daga cikin ayyukan raya ƙasa, cikin kan hanyarsa ta dawowa a daidai yankin da yake tsakanin garuruwan warzaƙan da julfa ya fuskanci ibtila'in hatsarin jirgi, cikin wannan jirgi mai saukar ungulu akwai Husaini Abdullahiyan ministan harkokin wajen ƙasar Iran, da kuma Sayyid Ali Ale Hashim wakilin waliyul faƙihi a garin Azerbaijan sharƙi..[30] bayan yaɗuwar labarin wannan hatsari, gungu-gungun jama'ar ƙasar Iran sun taru a wuraren ibada misalin haramin Imam Rida (A.S),[31] haramin Sayyada Ma'asuma (A.S),[32] haramin Shah Cerag domin yi musu addu'a da Allah ya kuɓutar da su.[33] washegari 31 ga watan Urdibehesti aka gano ɓaraguzan wannan jirgi da suke ciki, bayan nan kafofin yaɗa labarin ƙasar Iran suka sanar da cewa shugaban Iran tare da waɗanda suke tare sun rasa rayukansu sakamakon wannan hatsari.[34]
cikin al'adar jamhuriyar muslunci ta Iran, mutanen da suke rasa rayukansu a lokacin sauke wazifar da take wuyansu ana ƙirga su cikin shahidai, da wannan dalili ne aka kira Sayyid Ra'isi da waɗanda suke kasance tare da sunan shahidai.
Tasiri Da Martani
Mutuwar Ra'isi ta yi tasiri da martani daban-daban. Haramin Imam Rida (A.S) ya soke shirye-shiryen da ya shirya na Maulidin Imam Rida (A.S). Har ila yau, an maye gurbin koren tutar haramin da bakar tuta, A cikin sakon ta'aziyyar nasa, Ayatullah Khamna'i ya kira Rai'si malami mujahidi da rasuwarsa a matsayin shahada tare da ayyana zaman makoki na kwanaki biyar a kasar Iran.[35] Masana harkokin siyasa da na addini da suka hada da Ayatullah Sistani daga mahukuntan birnin Najaf da kuma shugabannin ƙasashe daban-daban sun bayyana alhininsu kan rasuwar shugaban na Iran. Haka kuma a Lebanon da Siriya na tsawon kwanaki uku[36] da ƙasar Fakistan[37] Kuma kasar Iraƙ ta ayyana ranar Juma'a ranar makoki.
Bayanin kula
- ↑ Najafi, ruwayar zabe na sha biyu, shafi na 186-188, an nakalto daga«روایت حجتالاسلام رئیسی از دوران مبارزه علیه رژیم پهلوی/ شکلگیری هستههای مبارزاتی طلاب در قم / ماجرای دیدار با آیتالله خامنهای در ایرانشهر», Cibiyar Takardun Juyin Musulunci.
- ↑ «Tarihin Rayuwa: Seyyed Ebrahim Raisi, Kamfanin Dillancin Labarai na Hamshahri.
- ↑ «Fage da tarihin Hojjatoleslam Raisi, Kamfanin Dillancin Labarai na Rediyo da Talabijin..
- ↑ «Tarihin Rayuwa: Seyyed Ebrahim Raisi”, Kamfanin Dillancin Labarai na Hamshahri.
- ↑ Najafi, ruwayar zabe na sha biyu, shafi na 186-188, an nakalto daga«روایت حجتالاسلام رئیسی از دوران مبارزه علیه رژیم پهلوی/ شکلگیری هستههای مبارزاتی طلاب در قم / ماجرای دیدار با آیتالله خامنهای در ایرانشهر»، Cibiyar Takardun Juyin Musulunci.
- ↑ Najafi, ruwayar zabe na sha biyu, shafi na 186-188, an nakalto daga «روایت حجتالاسلام رئیسی از دوران مبارزه علیه رژیم پهلوی/ شکلگیری هستههای مبارزاتی طلاب در قم / ماجرای دیدار با آیتالله خامنهای در ایرانشهر»،Cibiyar Takardun Juyin Musulunci.
- ↑ «شرح زندگی سید ابراهیم رئیسی »،Saiyid Ibrahim Raisi Information Center.
- ↑ Najafi, ruwayar zabe na sha biyu, shafi na 186-188, an nakalto daga«روایت حجتالاسلام رئیسی از دوران مبارزه علیه رژیم پهلوی/ شکلگیری هستههای مبارزاتی طلاب در قم / ماجرای دیدار با آیتالله خامنهای در ایرانشهر»، Cibiyar Takardun Juyin Musulunci.
- ↑ «روایت حجتالاسلام رئیسی از دوران مبارزه علیه رژیم پهلوی/ شکلگیری هستههای مبارزاتی طلاب در قم / ماجرای دیدار با آیتالله خامنهای در ایرانشهر»،Cibiyar Takardun Juyin Musulunci.
- ↑ «انتصاب حجتالاسلام رئیسی به تولیت آستان قدس رضوی»Ofishin kiyayewa da buga ayyukan mai girma Ayatullah Khamenei.
- ↑ Ku duba:«انتصاب حجتالاسلام رئیسی به تولیت آستان قدس رضوی»Ofishin kiyayewa da buga ayyukan mai girma Ayatullah Khamenei
- ↑ «نگاهی به عملكرد سه ساله حجت الاسلام رئیسی در آستان قدس رضوی»،Kamfanin labarai na IRNA.
- ↑ Ku duba:«نگاهی به عملكرد سه ساله حجت الاسلام رئیسی در آستان قدس رضوی»، Kamfanin labarai na IRNA
- ↑ «شرح زندگی سید ابراهیم رئیسی »،Saiyid Ibrahim Raisi Information Center.
- ↑ «"Zindaginameh: Seyed Ebrahim Raisi", Kamfanin Dillancin Labarai na Hamshahri.
- ↑ "Zindaginameh: Seyed Ebrahim Raisi", Kamfanin Dillancin Labarai na Hamshahri.
- ↑ "Zindaginameh: Seyed Ebrahim Raisi", Kamfanin Dillancin Labarai na Hamshahri.
- ↑ "Zindaginameh: Seyed Ebrahim Raisi", Kamfanin Dillancin Labarai na Hamshahri.
- ↑ "Zindaginameh: Seyed Ebrahim Raisi", Kamfanin Dillancin Labarai na Hamshahri.
- ↑ "Zindaginameh: Seyed Ebrahim Raisi", Kamfanin Dillancin Labarai na Hamshahri.
- ↑ "Zindaginameh: Seyed Ebrahim Raisi", Kamfanin Dillancin Labarai na Hamshahri.
- ↑ «شرح زندگی سید ابراهیم رئیسی »، Saiyid Ibrahim Raisi Information Center.
- ↑ «متن کامل سخنرانی رئیسی در سازمان ملل»، Insaf News.
- ↑ «بیش از۱۰۰موضعگیری درحمایت از غزه/ رئیسی چگونه دست مدعیان حقوق بشر را روکرد»، Kamfanin dillancin labarai na IRNA.
- ↑ «متن کامل سخنرانی رئیسی در سازمان ملل»، Insaf News.
- ↑ «متن کامل سخنرانی رئیسی در سازمان ملل»، Insaf News.
- ↑ "ZSindagi nameh: Seyed Ebrahim Raisi", Kamfanin Dillancin Labarai na Hamshahri.
- ↑ «سوابق و زندگینامه حجت الاسلام و المسلمین رئیسی»،Kamfanin dillancin labarai na Sida wa Sima.
- ↑ "Zindagi nameh: Seyed Ebrahim Raisi", Kamfanin Dillancin Labarai na Hamshahri..
- ↑ «بالگرد حامل رئیس جمهور دچار سانحه شد/با ۲ نفر از سرنشینان بالگرد رئیسجمهور ارتباط برقرار شد»،Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA.
- ↑ "Addu'ar maziyartan haramin Motahar Razavi ga lafiyar shugaban kasa da abokan tafiyarsa", kamfanin dillancin labarai na Mehr.
- ↑ "Yin Addu'a a Haramin Hazrat Masoumeh (A.S) domin samun lafiyar Raisi da abokan tafiyarsa", Kamfanin Dillancin Labarai na Elekht.
- ↑ "Addu'ar maziyarta na Shahcharagh don samun lafiyar shugaban kasa da abokansa", kamfanin dillancin labarai na Mehr.
- ↑ آیتالله رئیسی و هیئت همراه به ملکوت اعلی پیوستند، Kamfanin Dillancin Labarai na Tasneem.
- ↑ «پیام تسلیت رهبر انقلاب اسلامی و اعلام عزای عمومی در پی درگذشت شهادتگونه رئیسجمهور و همراهان گرامی ایشان»،Ofishin kiyayewa da buga ayukkan mai girma Ayatullah Khamenei.
- ↑ «۳ روز عزای عمومی در سوریه اعلام شد»،Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr.
- ↑ «ایرانی صدر کے انتقال پر پاکستان میں قومی پرچم سرنگوں»، jang.com.
Nassoshi
- «روایت حجتالاسلام رئیسی از دوران مبارزه علیه رژیم پهلوی/ شکلگیری هستههای مبارزاتی طلاب در قم / ماجرای دیدار با آیتالله خامنهای در ایرانشهر»، (Labarin Hujjatul Islam Raisi game da zamanin gwagwarmayar yaƙi da mulkin Pahlavi / Yadda ɗaliban Hauza suka kafa rukunoni na gwagwarmaya a birnin Qum / Labarin ganawarsa da Ayatullah Khamenei a birnin Iranshahr) Cibiyar Takardun Juyin Juya Halin Musulunci, kwanan watan shiga: 23 ga Yuni, 2021; Ranar dubawa: 19 ga Mayu, 2024M.
- «سوابق و زندگینامه حجت الاسلام و المسلمین رئیسی», ("Tarihin rayuwa da ayyukan Hujjatul Islam wal Muslimin Raisi")Hukumar Labarai ta IRIB (Sada wa Sima), Ranar dubawa: 19 ga Mayu, 2024M.
- «انتصاب حجتالاسلام رئیسی به تولیت آستان قدس رضوی»، (Naɗin Hujjatul Islam Raisi a matsayin Shugaban Gidauniyar Astana Quds Razavi)Ofishin kiyayewa da wallafa ayyukan Ayatullahil Uzma Khamenei, Ranar wallafa: 7 ga Maris, 2016; Ranar dubawa: 19 ga Mayu, 2024M.
- «انتصاب حجتالاسلام والمسلمین سیدابراهیم رئیسی به ریاست قوه قضائیه»، Ofishin kiyayewa da buga ayukkan Mai girma Ayatullah Khamenei, ranar shiga: 16 ga Maris, 2018, ranar ziyarar: 20 ga Mayu, 2024.
- «زندگینامه: سید ابراهیم رئیسی»، (Tarihin Rayuwa: Sayyid Ibrahim Raisi) Kamfanin dillancin labarai na Hamshahri, ranar shigowa: Yuni 21, 1401, kwanan wata: Mayu 30, 1403.
- «بالگرد حامل رئیس جمهور دچار سانحه شد/با ۲ نفر از سرنشینان بالگرد رئیسجمهور ارتباط برقرار شد», (Jirgi mai saukar ungulu da yake ɗauke da shugaban ƙasa ya yi haɗari / An samu tuntuɓa da mutum biyu daga cikin waɗanda ke cikin jirgin shugaban ƙasar) ISNA, Ranar shiga: 19 ga Mayu, 2024; Ranar dubawa: 19 ga Mayu, 2024M.
- «دعای زائران حرم مطهر رضوی برای سلامتی رئیس جمهور و همراهانش»، (Addu'o'in masu ziyarar harami mai tsarki na Razavi domin lafiya da amincin shugaban ƙasa da sauran mutanen da ke tare da shi) Kamfanin dillancin labarai na Mehr, kwanan wata: 19 ga Mayu, 2024; Ranar dubawa: 20 ga Mayu, 2024M.
- «برگزاری دعا در حرم حضرت معصومه (س) برای سلامتی رئیسی و همراهان»، (Gudanar da addu'o'i a haramin Hazrat Ma'asuma (s.a) domin lafiya da amincin Raisi da sauran mutanen da ke tare da shi) Kamfanin Dillancin Labarai na Entebakh, ranar shigarwa: 19 ga Mayu, 2024; Ranar dubawa: 20 ga Mayu, 2024M.
- «دعای توسل زوار شاهچراغ برای سلامتی رییس جمهور و همراهانش»، (Addu'ar 'Tawassuli' da maziyartan Shah-Cheragh suka gudanar domin lafiya da amincin shugaban ƙasa da sauran mutanen da ke tare da shi) Kamfanin dillancin labarai na Mehr, kwanan wata:19 ga Mayu, 2024; Ranar dubawa: 20 ga Mayu, 2024M.
- رئیسی و هیئت همراه به ملکوت اعلی پیوستند، (Ayatullah Raisi da tawagar da ke tare da shi sun riga mu gidan gaskiya) Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, kwanan watan bugawa: Mayu 20, 1403, kwanan wata ziyara: Mayu 31, 1403.
- «شرح زندگی سید ابراهیم رئیسی »، Saiyid Ebrahim Raisi Yanar Gizo, kwanan wata ziyara: 19 ga Mayu, 2024; Ranar dubawa: 20 ga Mayu, 2024M.
- «پیام تسلیت رهبر انقلاب اسلامی و اعلام عزای عمومی در پی درگذشت شهادتگونه رئیسجمهور و همراهان گرامی ایشان»، (Saƙon ta'aziyyar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci da kuma sanar da zaman makoki na ƙasa baki ɗaya biyo bayan rasuwa mai kama da shahada ta shugaban ƙasa da tawagarsa mai daraja) Ofishin kiyayewa da buga ayukkan Jagora Ayatullah Khamenei, Ranar Shiga: 19 ga Mayu, 2024; Ranar dubawa: 20 ga Mayu, 2024M.
- «ایرانی صدر کے انتقال پر پاکستان میں قومی پرچم سرنگوں»، (An saukar da tutar ƙasa kasa-kasa a Pakistan sakamakon rasuwar shugaban ƙasar Iran) jang.com. Ranar shigarwa: Mayu 20, 2024, kwanan wata ziyara: Mayu 20, 2024M.
- «۳ روز عزای عمومی در سوریه اعلام شد»، (An sanar da zaman makoki na ƙasa har na tsawon kwanaki 3 a ƙasar Siriya) Kamfanin dillancin labarai na Mehr, kwanan wata: 20 ga Mayu, 2024; Ranar dubawa: 20 ga Mayu, 2024M.
- «متن کامل سخنرانی رئیسی در سازمان ملل»، (Cikakken jawabin Raisi a Majalisar Ɗinkin Duniya) Labaran Ensaf, kwanan watan shigarwa: Satumba 19, 1402, kwanan wata ziyara: Mayu 31, 1403.
- Shugabannin Hukumar Shari'a Ta Iran
- Shugabannin Jamhuriyar Musulunci
- Malaman Shi'a Daga Mashad
- Mutanen Da Suka Yi Karatu A Hauza Ilmiyya Ta Ƙum (Bayan Shekara 1300 Kalandar Farsi)
- Mutanen Da Suka Yi Karatu A Hauza Ilmiyya Ta Mashad
- Wakilan Majalisar Kwararrun Jagoranci A Iran (Daura Ta Huɗu)
- Wakilan Majalisar Kwararrun Jagoranci A Iran (Daura Ta Biyar)
- Wakilan Majalisar Kwararrun Jagoranci A Iran (Daura Ta Shida)
- Membobin Majalisar Fayyace Maslahar Gwamnatin Iran
- Masu Gabatar Da Ƙara Na Iran
- Masu Kula Da Haramin Imam Rida
- Mutanen Da Suka Rasu A Shekarar 1403 Kalandar Farsi
- Mutanen Da Aka Binne A Haramin Imam Rida
- Mutanen Da Suka Rasu A Shekarar 2024 Kalandar Miladiya
- Mutanen Da Suka Rasu A Shekarar 1445 (Hijira)