Jump to content

Mu Al'ummar Imam Husaini Ne

Daga wikishia

Mu al'ummar Imam Husaini ne, (Larabci: نحن أمة الإمام الحسين (ع)) wani kamfen ne da take cikin gayyara taron jama'a da ya kasance a goman farkon watan Muharram shekarar 2020 miladiyya, a Iran[1] Wannan jumla an ciro ta ne daga jawaban Ƙasim Sulaimani.[2] ƙasim Sulaimani babban kwamandan Dakarun ƙudus[3] kuma daga cikin kwamandojin yaƙin Iraƙ da Iran[4] wanda a watan Disamba 2018 ya rabauta da samun shahada sakamakon harin ta'addanci da Amurka ta kai a kansa a ƙasar Iraƙ.

Jumlar mu al'ummar Imam Husaini ne, da aka nuna a filin Wali Asri Tehran. watan Muharram shekarar 2023

Wannan kamfen an fara shi ne bayan kira da gidauniyar kula da kuma yaɗa ayyukan shahid ƙasim Sulaimani ta yi..[5] Cikin wannan kamfenan buƙaci mutane su rera taken makokin Muharram da kamfen ɗin “Mu al'ummar Imam Husaini ne” haka nan an tara taimako ƙarƙashin wannan take ga talakwa masu rangwamen gata da kuma wanda bala'o'in annobar cutar Korona ya shafa[6]

Da wannan munasaba ne jumlar aka nuna “Mu al'ummar Imam Husaini ne” a wannan kamfen a zanen bango da aka kafa a filin Wali Asri da yake a babban birnin Tehran[7] Cikin garuruwan daban-daban na Iran an shirya tarurruka misalin tashar salati (ƙaramar tasha ta ba da kyauta) rubuta jumloli da saƙonni[8] ko kuma raba tutocin da suke ɗauke da rubutun “Mu al'ummar Imam Husaini ne”[9] Jaridar Kihan a ranar 27 Agusta 2020 miladiyya ta yi fashin baƙi kan makoki da taken “Mu al'ummar Imam Husaini ne”.[10]

Bayanin kula

Nassoshi