Godiya
godiya nuna yabawa ta hanyar fatar baki da aiki kan ni'imomin Allah. Arifan musulmai sun kasa godiya zuwa nau'i uku, godita ta zuciya da ta fatar baki da kuma a aikace: godiya ta fatar baki iƙirari ce da ni'ima, godiya ta zuciya shi ne sanin ni'imomin Allah da nuna yabawa ta hanyar biyayya ga Allah da kuma cikin mu'amala da aiki. Bisa abin da ya zo daga ayoyin kur'ani da riwayoyi ita godiya amfaninta ya dawowa ga shi kansa mai yinta, godiya ko rashin godiya bai da wani amfani ko cutarwa ga Allah ta'ala; saboda shi Allah ya wadatu daga mutum da kuma dukkanin ayyukansa, kan wannan asasi ne ita godiya da nuna yabawa kan ni'ima yana zama sababin samun albarka da ƙaruwarta. Imam Ali (A.S) ya kira sifffanta godiya matsayin wata alama ta Imani da kuma taƙawa kuma ta kasance sababin tabbatuwar ni'imomi.
Sanin Ma'anar Godiya Da Kuma Matsayinta
Godiya na nufin tunawa da kuma nuna sanin ni'imomin Allah cikin bayyanar da hakan a zuciya ko kan harshe ko kuma a aikace.[1] a cikin ayoyin kur'ani jumlolin misalin:
ko kuma «لِيَبْلُوَنِي أَأَشْكُرُ أَمْ أَكْفُرُ»[3] sun zo game da godiya kishiya ga kafircewa domin ɗaya daga cikin ma'ana kafirci shi butulci da ɓoye ni'ima, ana cewa shi kafiri ya lulluɓa mayafi kan ni'imomin Allah ya ɓoye su, shi kuma mimini yana ya ye mayafi ya bayyana da ni'imomin da Allah ya yi kansa, ma'ana yana yin furuci da kuma nuna sani da tunawa da ni'imomi, ma'ana Kalmar ‘Shukru” ta ƙunshi Imani da ni'ima, shi kuma dama shukru (nuna godiya) yana kasancewa tare da wani nau'i na girmamawa da tunawa da ni'omomi saɓanin kufru (Kafirci) wanda yake da ma'anar mantuwa da kuma ɓoye ni'imomi.[4] Imam Sadiƙ (A.S) cikin wani shahararren hadisi wanda ya lissafa dakarun hankali da na jahilci, ya ambaci godiya cikin dakaru na hankali, kishiyarta kuma ma'ana (Kafirci) cikin jerin dakarun jahilci.[5]
An afi amfani da kalma shukru (godiya) cikin mabambantan maudu'ai; daga jumlarsu godiya kan ni'imomi na zahiri,[6] godiya kan addini da tauhidi,[7] godiya kan samuwar Allah da iyaye[8] da godiya game da afuwar Allah da gafararsa.[9]
Cikin riwayoyin ma'asumai nan ma an yi bayanin godiya da misdaƙan godiya; Imam Ali (A.S) ya yi bayani cewa godiya alama ce ta Imani[10] da taƙawa[11] kuma sababi ce ibtila'i da jarrabawa,[12] ado,[13] sababi samun ƙarin arziƙi[14] da lamintar da tabbatuwar ni'ima.[15] haka nan an naƙalto daga gare shi cewa wajibi musulmi su kasance masu nuna godiya cikin ko wane hali.[16]
Natijoji Da Sakamakon Godiya
- Ku duba: Aya Ta 7 Suratul Ibrahim
Bisa abin da ya zo daga kur'ani,[17] ita godiya amfaninta yana dawo ga mai yinta, godiya ko rashin godiya mai cutarwa ko amfanar da Allah; saboda shi Allah ya wadatu daga dukkanin wani amfani kuma ya girmama daga mutum ya cutar da shi da rashin godiya. Kishiyar hakan shi mutum ne yake samun amfani idan ya yi godiya domin godiya ta kasance sababin amun albarka.[18] haka nan ita godiya sababin shiriya ce zuwa ga hanya madaidaiciya.[19] kishiyar haka shi rashin godiya yana zama sanadiyyar jawowa kai azaba.[20]
Bayanin Kula
- ↑ Rajeb Isfahani, Al-Mufradat fi Gharib Al-Qur’an, shafi na 265.
- ↑ Suratul Baqarah, aya ta:152.
- ↑ Suratul Naml, aya ta 40.
- ↑ Farahidi, Al-Ain, shafi na 347.
- ↑ Kulayni, Kafi, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi na 21. ↑
- ↑ Suratul Nahl, aya ta 14, 78, 114 da 21; Suratul Baqarah, aya ta 72; Suratul Lukman, aya ta 31; Suratul Shura, aya ta 33; Suratul Rum, aya ta 46; Suratul A'araf, aya ta 10; Suratul Saba, aya ta 13 da ta 15; Suratul Yunus, aya ta 60; Suratul Yasin, aya ta 35; Suratul Furqaan, aya ta 62.
- ↑ Suratul Yusuf, aya ta 38; Suratul Ibrahim, aya ta 5.
- ↑ Suratul Lukman, aya ta 14.
- ↑ Suratul Baqarah, aya ta:53.
- ↑ Nahj al-Balagha, Hikmat 325.
- ↑ Nahj al-Balagha, hadisi na 184.
- ↑ Nahj al-Balagha, Huduba ta 90.
- ↑ Nahj al-Balagha, Hikmat 333.
- ↑ Nahj al-Balagha, Hikmat 130 and 147.
- ↑ Nahj al-Balagha, Hikmat 238 and 13.
- ↑ Nahj al-Balagha, Hikmat 265.
- ↑ Suratul Naml, aya ta 4; Suratul Lukman, aya ta 12; Suratul Zumar, aya ta 7.
- ↑ Suratul Ibrahim, aya ta 7.
- ↑ Suratul Nahl, aya ta 121.
- ↑ Suratul Ibrahim, aya ta 5; Suratul Nisa’i, aya ta 147; Suratul Saba, aya ta 15 da ta 16.
Nassoshi
- Alqur'ani mai girma.
- Farahidi, Khalil bin Ahmad, Al-Ain, Mehdi Makhzoumi da Ibrahim Samrai suka yi bincike, Qom, 1410.
- Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Usul Kafi, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya, 1407H.
- Nahj al-Balagha, edited by Faiz al-Islam, Tehran, Faiz al-Islam Publications, 1374.
- Ragheb Esfahani, Al-Mufardat fi Gharib al-Qur'an.