Dakarun Kare Juyin juya halin Muslunci
| Wani sashe na Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran | |
![]() Alama ta sojojin kare juyin juya halin muslunci | |
| Sauran sunaye | Sepa |
|---|---|
| Kafawa | 22 Afrilu 1979 miladiyya |
| Waɗanda suka kafa | Imam Khomaini |
| Ƙarƙashin | Gwamnatin jamhuriyar muslunci ta Iran |
| Nau'in ayyuka | Soja,al'adu, raya ƙasa da kuma... |
| Ayyuka | Gadin juyin juya halin muslunci da nasarorinsa |
| Wuri | Tehran (Babban cibiyar kwamandanci) |
| Hali | Tana kan aiki |
Dakarun kare juyin juya halin muslunci, (Larabci: حرس الثورة الإسلامية الإيرانية) wata hukuma ce ta soja da aka kafa ta da manufar kare juyin juya halin muslunci na Iran da nasarorin da ya samar, an kafa wannan runduna a ranar 22 Afrilu 1979 miladiyya, bisa umarnin Imam Khomaini.
Dakarun kare juyin juya halin muslunci na Iran a ranar 17 Satumba 1985 miladiyya, bisa umarnin Imam Khomaini an faɗaɗa ayyukansu cikin rundunonin soja guda uku, sojan ƙasa, sojan sama da sojan ruwa, bayan a shekarar 1990 bisa umarnin Sayyid Ali Khamna'i jagoran jamhuriyar muslunci ta Iran an ƙara rundunoni uku cikinsu waɗanda ake kira da sunan dakarun ƙudus da ƙungiyar gwagwarmaya ta sa kai, a dunkule sun samu faɗaɗuwa zuwa runduna guda biyar, Dakarun kare juyin juya halin muslunci ƙari kan ayyukansu na soja, suna ayyuka a fagen tattara bayanan sirri, gine-gine, saƙafa da raya al'adu.
Daidai da asali na 110 daga dokokin muslunci, naɗi da kwaɓewa da karɓar murabus ɗin babban kwamandan Dakarun kare juyi juya halin muslunci yana ƙarƙashin ikon jagoran juyin juya halin muslunci na Iran, shugabancin wannan dakaru bisa hukuncin Sayyid Ali Khamna'i a ranar 8 Afrilu 2025 an miƙa shi ga Muhammad Fakfur.
Daular Amurka a ranar 8 Afrilu 2019, cikin jawabi da ta fitar a hukumance ta sanya dakarun kare juyin juya halin muslunci musamman dakarun ƙudus cikin jerin ƙungiyoyin ta'addanci na ƙasashen waje, babbar majalisar tsaro ta al'ummar ƙasar Iran, cikin ɗaukar matakai na martini, sun shelanta gwamnatin Amurka matsayin mai kare ta'addanci a faɗin duniya, tare da shelanta cibiyar Babban kwamandancin Amurka mai suna Satankon da yake yammancin Asiya, matsayin ƙungiyar ta'addanci.
Imam Khomaini ya kira Dakarun kare juyin juya halin muslunci da sunan sojojin muslunci, Sayyid Ali Khamna'i ya yi la'akari da wannan dakaru matsayin jigo da rukuni da ba za a taɓa raba su da juyin juya halin muslunci ba, idan aka rasa wannan dakaru to lallai juyin juya halin muslunci na Iran zai fuskanci barazanar babban hatsari.
Gabatarwa
Dakarun juyin juya halin muslunci, wata hukuma ce da ya ƙunshi manyan ma'aikatu, daga wakilcin Waliyul faƙihi a cikinsu, hukumar kula da bayanan sirri, rundunar sojojin ƙasa, sama da na ruwa, ƙungiyar gwagwarmayar da dakarun ƙudus da sauran ƙungiyoyi da suke ƙarƙashinsu.[1]
Bisa asali na 150 daga dokokin kundin tsarin muslunci na Iran, dakarun kare juyin juya halin muslunci da aka kafa tun farkon nasarar juyi, domin ci gaba da ayyukansu da ba da kariya ga juyi da nasarorinsu suna nan daram dam.[2] Har ila yau, bisa asali na 110 kundin dokokin Mulki, naɗi da cirewa da karɓar murabus ɗin babban kwamandan wannan dakaru, suna cikin ikon jagora.[3] A ranar 13 Yuni 2025 bisa hukuncin Sayyid Ali Khamna'i jagoran juyim juya halin muslunci an miƙa kwamdancin baki ɗayan rundunar dakarun kare juyin juya halin muslunci zuwa ga hannun Muhammad Fakfur. Cikin kalandar Iran an ayyana ranar 3 ga watan Sha'aban wace ta yi daidai da ranar haihuwar Imam Husaini (A.S) matsayin ranar dakarun kare juyin juya halin muslunci..[4]
Matsayi
Imam Khomaini ya kirayi Dakarun kare juyi da sunan sojojin muslunci, ya kuma buƙaci mutane su mara musu baya kuma su shiga cikin wannan aiki.[5] A cikin wata ganawa da ya yi tare da waɗannan Dakaru Imam ya bayyana gamsuwarSa da ayyukansu: "Ni na gamsu da ayyukan Dakarun kare juyi ba kuma zan taɓa canja ra'ayina kanku ba, da a ce babu ku da babu wannan ƙasa. Lallai ina matuƙar ganin ƙima da darajarku".[6]
Sayyid Ali Khamna'i, jagoran juyin juya halin muslunci na Iran, ya kwatanta dakarun kare juyin juya halin muslunci da ɗan ƙaramin yaro da aka haife shi a farkon zamanin juyin juya hali, ya girma kan gadon juyin juya halin muslunci, a yanzu kuma ya zama jigo cikin rukunan juyin juya hali da ba za a taɓa iya raba shi da wannan juyi ba, ta yadda da ace babu shi, to lallai zai zamana juyin juya halin zai fuskanci babbar barazanar hatsari.[7]
Ƙasar Amurka a ranar 8 Afrilu 2019 miladiyya. Tare da fitar da wani bayani daga shugaban ƙasar Amurka Donal Turom, a hukumance sun bayyana rundunar dakarun kare juyin juya halin muslunci musamman ma dakarun ƙudus a matsayin jerin layin ƙungiyoyin ta'addanci na ƙasashen waje.[8] Babbar majalisar shura ta tsaron al'ummar Iran cikin wani mataki na martani kan Amurka, sun ayyana babbar cibiyar kwamandancin tsaro ta Amurka da ake kira da sunan Santakom da take yammacin Asiya, a matsayin ƙungiyar ta'addanci.[9]
Taƙaitaccen Tarihi Da Kuma Yadda Aka Kafa Wannan Runduna
Dakarun kare juyin juya halin muslunci, wata hukuma ce ta soja da take aikin ba da tsaro da kariya kan juyin juya halin muslunci da abubuwan da ya samar, an kafa wannan runduna a ranar 21 Afrilu 1979 miladiyya bisa umarnin Imam Khomaini.[10]
Muhsin Rafiƙ Dusti (Shugaban gidauniyar raunana daga shekarar 1989-1999 miladiyya) cikin tarihinsa da ya rubuta ya bayyana cewa tunanin samar da wata runduna baya ga ta sojan ƙasa a karon farko ya samu ne a tunanin Muhammad Muntazari.[11] A cewar Rafiƙ Dusti da farko an fara da kafa ƙungiyoyi huɗu ƙarƙashin hadafi guda ɗaya na ba da kariya ga juyin juya halin muslunci, ko wace ɗaya daga cikinsu tana jin cewa kare juyin juya hali matsayin aikin da ya wajaba a wuyanta.[12] Waɗannan ƙungiyoyi guda huɗu daga ƙarshe sai aka haɗe wuri guda aka samar da sabuwar ƙungiya ta majalisar kwamandancin mai mutane goma sha biyu, cikin wata ganawa da wakilai uku daga cikinsu da suka yi da Imam Khomanai a birnin Ƙum, Imam ya umarci gwamnati mai ci a lokacin ta kafa runduna mai cin gashin kanta, da haka ne a ranar 23 Afrilu 1979 miladiyya, a hukumance aka kafa dakarun kare juyin juya halin muslunci.[13]
A ranar 23 Agusta 1985 miladiyya, bisa umarnin Imam Khomani, dakarun kare juyin juya halin muslunci, suka faɗaɗa ayyukansu zuwa rundunoni uku, daga sojan ƙasa, sojan sama da sojan ruwa.[14] A shekarar 1990 miladiyya, bisa umarnin Sayyid Ali Khamna'i an ƙara sabbin rundunoni guda biyu cikinsu, su ne dakarun ƙudus da gwagwarmayar sa kai ta al'umma, da wannan ne adadinsu ya zama rundunoni guda biyar.[15]
Tsarin Ƙungiya
Dakarun kare juyin juya halin muslunci sun kasance da wannan sharhi kamar haka:
Rundunar Sojan Ƙasa
Rundunar sojan ƙasa da ake kira da suna na aro (Nazasa) a hukumance sun fara aiki daga shekarar 1985 ƙarƙashin kwamandancin Yahaya Rahim Safawi. Runduna da rukunin wannan sojoji an kafa su cikin larduna daban-daban cikin daidai ta da sojojin ƙasa.[16] Muhammad Fakfur, na bakwai cikin kwamandojin wannan runduna, a ranar 21 Afrilu 2009, bisa hukuncin Sayyid Ali Khamna'i an naɗa shi kwamanda rundunar dakarun kare juyin juya halin muslunci.[17]
Rundunar Sojan Ruwa
Rundunar sojan ruwa ta dakarun kare juyin juya halin muslunci da ake kira da suna na aro (Nadasa) a shekarar 1985 miladiyya lokacin yaƙin Iran da Iraƙi suka fara aiki ƙarƙashin kwamdancin Husaini Alayi.[18] Cikin jumlar ayyukansu, akwai kariya da kuma tsaron kan iyakokon ƙasar Iran na teku a gaban hare-haren baƙi ƴan ƙasar waje.[19] Ali Rida Tangasiri a ranar 23 Agusta 2018 miladiyya, bisa hukuncin jagora an naɗa shi kwamandancin wannan runduna.[20]
Rundunar Sararin Samaniya
Rundunar sararin samaniya na dakarun kare juyin juya halin muslunci, sun fara aiki daga shekarar 1985 miladiyya, tare da ƙara sashen sararin samaniya da sojan sama a shekarar 2009 miladiyya, aka kafa rundunar sojan sararin samaniya na dakarun kare juyin juya halin muslunci.[21] Wannan runduna ana kiranta da taƙaitacce sun ana (Nahasa), daɗi kan ayyukan da ofireshin na sama, an miƙa ayyukan makamai masu linzami da kula da sararin samaniya gare su.[22]
Amir Ali Haj Zade, a shekarar 2019 miladiyya, bisa hukuncin jogoran Iran an naɗa shi kwamandan wannan runduna.[23] Dakarun kula da sararin samaniya na dakarun kare juyi a ranar 14 Afrilu[24]miladiyya,[25] cikin martani kan mataki na tsokana da Isra'ila ta ɗauka a kan jamhuriyar muslunci ta Iran, a karo na farko wannan runduna ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa daga ƙasar Iran zuwa Isra'ila kan cibiyoyin tsaro da na soja, ana kiran wannan ofireshin da sunan (Ofireshin Wa'adus Sadiƙ 1 da 2). Haka nan wannan runduna cikin raddi da ta yi kan kisan ƙasim Sulaimani babban kwamandan dakarun ƙudus a wancan lokaci, sun ƙaddamar da farmaki kan sansanin soja na Amurka da yake Bagdad.[26] A ranar 13 Yuni 2025 Isra'ila ta kai farmaki kan Amir Ali Haj Zade da wasu adadin kwamandojin wannan runduna tare da hallaka su. Ayatullahi Khamna'i, ya naɗa Sayyid Husaini Musawi Iftikari matsayin sabon kwamandan wannan runduna. Wannan runduna cikin martaninsu ga kisan gilla da kuma keta alfarmar kan ƙasar Iran da Isra'ila ta aikata, a watan Yuni 2025, sun ƙaddamar da ofireshin na Wa'adus Sadiƙ 3.
Dakarun Ƙudus
Wannan dakaru wanda aka fi sani da rundunar ƙudus, domin tabbatar da manufar faɗaɗa ayyuka a wajen iyakokin jamhuriyar muslunci ta Iran ne aka kafa wannan runduna a shekarar 1990, ƙarƙashin kwamandancin Ahmad Wahidi da umarnin Ayatullahi Khamna'i.[27] an naɗa Isma'il Ƙa'ani kwamandancin wannan runduna bisa hukuncin jogoran Iran a ranar 3 Janairu 2020 miladiyya, bayan shahadar Ƙasim Sulaimani,[28] Kula da kuma saisaita ƙungiyoyin gwagwarmaya misalin Hizbullahi Lubnan, Hashadush Sha'abi Iraƙ, Dakarun Faɗimiyyun Afganinstan da Harkatu Ansarullahi Yaman[29] domin yaƙi da Amurka da Isra'ila da shirinsu[30] Hallarar soja da masu ba da shawara a ƙasashe daban-daban misalin Bosniya, Afganistan da Labanun,[31] da kuma samar da runduna masu yaƙi da Da'ish a Iraƙi da Siriya,[32] suna daga ayyukan wannan runduna.
Ƙungiyar Dakarun Sa Kai Raunana
ƙaungiyar sojan sa kai da suke ƙarƙashin kulawar dakarun kare juyin juya halin muslunci na Iran, ƙarƙashin kwamandancin jagoran Iran domin ba da tsaro da kariya ga juyin juya halin muslunci da abubuwan da ta samar a ranar 26 Nuwamba 1979 miladiyya, bisa umarnin Imam Khomaini aka kafa wannan ƙungiya, bayan rattaba hannun majalisar shura a shekarar 1980 wannan ƙungiya ta samu lamincewa a hukumance.[33] Rundunar gwagwarmaya na ƴan sa kai a shekarar 1990 ne Sayyid Ali Khamna'i, ya shigar da wannan runduna cikin dakarun kare juyin juya halin muslunci.[34] A ranar 4 Oktoba 2009 miladiyya ne aka canja sunan wannan ƙungiya daga "Rundunar gwagwarmaya ta Basij" zuwa "Rundunar gwagwarmaya Basij raunana".[35]
Sauran Ayyuka
Ba'arin ayyuka da ba na soja ba na dakarun kare juyin juya halin muslunci, sun kasance kamar haka:
Ayyuka Tattara Bayanan Sirri
Ayyukan tattara bayanan sirri na dakarun kare juyin juya halin muslunci cikin hukuma mai suna (Hukumar tattaro bayanai ta dakaru kare juyi).[36] Sashen bayanan sirri na dakarun kare juyi, lokaci ɗaya da kafa wannan hukuma mai suna hukumar taimakon bayanai da bincike na dakarun kare juyi suka fara aiki, aikinsu shi ne sa idanu kan ƙungiyoyi masu adawa da juyin juya hali.[37] A shekarar 1984 tare da kafa ma'aikatar leƙen asiri, dakarun kare juyi na sashen bayanan sirri su ma an komar da su cikin wannan ma'aikata, kuma hukumar tana aikin tattara bayanan soja, sannan a iya cewa a aikace ta zama sashen leƙen asiri da bayanan sirri na wannan ƙungiya.[38] Cikin tsakiyar shekarar 1991 wannan runduna ta ɗauki nauyi ayyukan soja, ayyukan tsaro ƙarƙashin taken "Sashen leƙen asiri na rundunar haɗin gwiwa ta dakarun kare juyi" kuma a shekarar 2009 wannan sashe ya samu bunƙasa zuwa cikakkiyar hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin muslunc ƙarƙashin kwamandancin Husaini Ɗa'ib.[39]

Ayyukan Raya Ƙasa
Ayyukan gine-gine da raya ƙasa na dakarun kare juyin juya halin muslunci yana ƙarƙashin kulawar kwamdancin raya ƙasa na Khatamul Anbiya.[40] wata hukuma ce mai kama da daula wace a shekarar 1989 aka kafa ƙarƙashin kwamdancin Muhsin Rizayi (Babban kwamandan runduna a wancan lokaci) an kafa wannan sashe ne da manufar tarayya cikin lamarin sabunta gine-ginen ƙasa bayan kallafaffen yaƙi shekaru takwas tsakanin Iran da Iraƙi.[41] Sayyid Husaini Hush Sadat 13 Maris 2021 miladiyya an naɗa shi a gurbin Sa'id Muhammad matsayin kwamandan wannan sashe.[42]
Ayyukan Al'adu Na Kafofin Watsa Labarai
Ayyukan al'adu da watsa labarai na dakarun kare juyin juya halin muslunci yana kasancewa ƙarƙashin kulawar sashen kwamandancin al'adu da zamantakewa Baƙiyyatullahi (A.S).[43] Muhammad Ali Jafari a ranar 21 Afrilu 2019 miladiyya, bisa hukuncin jagoran Iran an naɗa shi kwamandan wannan sashe.[44] bisa faɗin Muhammad Ali Fur Mukhtar (Wakilin majalisa a wa'adi na 9 da 10 kuma tsohon soja) sashen al'adu da zamantakewa na Baƙiyyatullahi (A.S) kai tsaye yana ƙarƙashin jagorancin jagoran Iran, kuma na kafa shi da manufar ayyuka a fagen yaƙi, al'adu da ayyukan kafofin watsa labarai, da kuma kiyaye nasarorin juyin juya halin muslunci da yaɗa su da kuma yaƙi da lalacewa da taɓarɓarewar al'adu ta hanyar amfani da salon na kayan aiki na zamani da kafofin watsa labarai..[45]
Bayanin kula
- ↑ «متن کامل آییننامه انضباطی نیروهای مسلح جمهوری اسلامی ایران»،Yanar Gizo na Kungiyar Shari'a na Sojojin Soja.
- ↑ «قانون اساسی جمهوری اسلامی ایران»، Yanar Gizo na Cibiyar Bincike na Majalisar Shura ta Musulunci.
- ↑ «قانون اساسی جمهوری اسلامی ایران»، Yanar Gizo na Cibiyar Bincike na Majalisar Shurar Musulunci.
- ↑ «ولادت امام حسین (ع) و روز پاسدار در سال ۹۹ چه روزی است؟»، Shafin Taqweem.
- ↑ Imam Khomaini, Sahifeh Noor, Juz. 9, shafi. 25.
- ↑ Imam Khumaini, Sahifeh Noor, Juz. 8, shafi. 258.
- ↑ Namayendagi Wali Faqihi, Sepahe Az Didgahe Maqame Mu'azzam Rahbari, 1992, shafi na 9-11.
- ↑ «کاخ سفید رسماً سپاه پاسداران را «سازمان تروریستی» اعلام کرد»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ «از اقدام آمریکا در تروریستی خواندن سپاه تا واکنش ایران/ تحلیلهای کارشناسان و واکنشهای جهانی»، Shafin labarai na Shafaqna.
- ↑ «سپاه پاسداران چگونه تأسیس شد و فرماندهانش چه کسانی بودند؟»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ «سپاه پاسداران چگونه تأسیس شد و فرماندهانش چه کسانی بودند؟»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ «سپاه پاسداران چگونه تأسیس شد و فرماندهانش چه کسانی بودند؟»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ Nazarpour, "Naqshe Sepahe Pasidarane Inqilab Islami Dar Tadawume Inqilabe Islami," shafi. 49.
- ↑ Tolai, Mudiriyate Tahawwul Wa Ta'ali; Mutala'e Mauridi Sepahe Inqilabe Islami, 2016, shafi. 6
- ↑ Tolai, Mudiriyate Tahawwul Wa Ta'ali; Mutala'e Mauridi Sepahe Inqilabe Islami, 2016, shafi. 7
- ↑ «نیروی زمینی سپاه»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ «فرماندهان نیروی زمینی سپاه از ابتدای انقلاب تا کنون را بشناسید»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan.
- ↑ «نیروی دریایی سپاه»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ «آمادگی کامل برای دفاع از مرزهای آبی و امنیت کشور داریم»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Mahsreq.
- ↑ «سردار تنگسیری را بیشتر بشناسید»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai naDifa'u Muqaddas
- ↑ «نیروی هوافضای سپاه»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ «نیروی هوافضای سپاه»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ «فرماندهان نیروی هوافضای سپاه از ابتدای تاسیس تا کنون را بشناسید»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan.
- ↑ «دهها فروند پهپاد و موشک به سمت سرزمینهای اشغالی شلیک شد»، Kamfanin Dillancin Labarai na IRNA.
- ↑ «بیانیه سپاه پاسداران انقلاب اسلامی درخصوص عملیات موشکی علیه اسرائیل»، Al-Alam.
- ↑ «انتقام سخت با شلیک دهها موشک به پایگاه آمریکایی عینالاسد»،Kamfanin Dillancin Labarai na IRNA.
- ↑ Bahman, "Naqshe Niruye Qudus Dar Halli Bohranhaye Garbe Asiya," shafi. 24.
- ↑ «فرمانده جدید نیروی قدس سپاه را بیشتر بشناسید»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ Bahman, "Naqshe Niruye Qudus Dar Halli Bohranhaye Garbe Asiya," shafi. 16-19.
- ↑ خسروشاهین، «بازدارندگی محور مقاوم
- ↑ «نیروی قدس در کدام جنگها حضور یافت؟»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Mahsreq.
- ↑ Nejabat, "Guruhek Tororisti Da'ish Wa Amniyat Islami Iran," shafi na gaba. 112
- ↑ «سازمان بسیج مستضعفین»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ «نیروی قدس سپاه چگونه شکل گرفت؟»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
- ↑ «چگونگی شکلگیری سازمان بسیج مستضعفین»، Gidan yanar gizon Matasa 'Yan Jarida.
- ↑ «سازمان بسیج مستضعفین»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ «نیروی قدس سپاه چگونه شکل گرفت؟», Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
- ↑ «چگونگی شکلگیری سازمان بسیج مستضعفین»،Gidan yanar gizon Matasa 'Yan Jarida.
- ↑ «چگونگی شکلگیری سازمان بسیج مستضعفین»،Gidan yanar gizon Matasa `Yan Jarida.
- ↑ «قرارگاه خاتم الانبیاء»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ «قرارگاه خاتم الانبیاء»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim
- ↑ «آیین تکریم و معارفه فرمانده قرارگاه سازندگی خاتم الانبیا(ص) برگزار شد»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Jamhuriyar Musulunci.
- ↑ «پرسشها و ابهامات دربارۀ قرارگاه فرهنگی اجتماعی حضرت بقیه الله»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Insaf.
- ↑ «جنگ نرم»، سایت Khamenei.ir.
- ↑ «پرسشها و ابهامات دربارۀ قرارگاه فرهنگی اجتماعی حضرت بقیه الله»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Insaf.
Nassoshi
- «آمادگی کامل برای دفاع از مرزهای آبی و امنیت کشور داریم»،Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Mashareq, kwanan watan aikawa: Janairu 25, 2020, kwanan wata ziyarar: Yuli 18, 2021.
- «آیین تکریم و معارفه فرمانده قرارگاه سازندگی خاتم الانبیا(ص) برگزار شد»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Jamhuriyar Musulunci, kwanan watan da aka buga: Maris 13, 2020, kwanan wata ziyara: Agusta 23, 2021.
- «از اقدام آمریکا در تروریستی خواندن سپاه تا واکنش ایران/ تحلیلهای کارشناسان و واکنشهای جهانی»،Shafin labarai na Shafaqna, ranar aikawa: Afrilu 19, 2019, kwanan wata ziyarar: Agusta 25, 2019.
- «اساسنامه سپاه پاسداران انقلاب اسلامی»، Cibiyar Nazarin Majalisar Shura Musulunci, kwanan wata: Yuli 15, 1401.
- «انفجار نفتکش بریجتون توسط رزمندگان ایرانی، تیر آخر در جنگ نفتکشها»، Gidan yanar gizon Matasa 'Yan Jarida, ranar aikawa: Agusta 24, 2020, kwanan wata ziyara: Agusta 2, 2019.
- «انهدام ناو یک میلیارد دلاری "ساموئل بیرابرتز"»،Gidan yanar gizon Matasa 'Yan Jarida, kwanan watan aikawa: Satumba 29, 2015, kwanan wata ziyara: Agusta 2, 2011.
- «ایران از کدام گروههای مجاهد شیعه و سنی افغانستانی حمایت کرد؟»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Anna, ranar aikawa: Mayu 11, 2019, kwanan wata ziyara: Agusta 2, 2019.
- Imam Khomeini, Ruhollah, Sahifeh Noor, Tehran, Cibiyar Tattara da Buga Ayyukan Imam Khumaini, 2010.
- Bahman, Shoaib, "Nakshe Niruye Qudus Dar Halli Bohrane Garbe Asiya," Mutala't Rahburde Jahane Islami, Na 69, Bahar 2017.
- «پرسشها و ابهامات دربارۀ قرارگاه فرهنگی اجتماعی حضرت بقیه الله»، Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Ensaf, kwanan watan aikawa: Mayu 25, 2019, kwanan wata ziyarar: Agusta 25, 2019.
- Tolaei, Mohammad, Mudiriyate Tahawwul Wa Ta'ali, Mutala'at Mauridi Sepahe Pasidarane Inqilabe Islami, Tehran, Jami'ar Imam Husaini (A.S), 2016.
- «جزئیاتی کامل از انهدام پهپاد آمریکایی در خلیج فارس»، Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr, ranar aikawa: Yuli 25, 2019, ranar ziyarar: Agusta 2, 2019.
- «جنگ نرم»، Gidan yanar gizon Khamenei.ir, ranar aikawa: Mayu 1, 2019, kwanan wata ziyarar: Agusta 2, 2021.
- «چگونگی شکلگیری سازمان بسیج مستضعفین»، سایت باشگاه خبرنگاران جوان.،Gidan yanar gizon Matasa 'Yan Jarida, kwanan watan aikawa: Disamba 16, 2012,
- «حفظ آرمانهای نهضت اسلامی با تشکیل کمیتههای انقلاب», Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kwanan watan shiga: Fabrairu 13, 2019, kwanan wata: Agusta 26, 2019.
- Khosrowshahin, Hadi,«بازدارندگی محور مقاومت»،Ranar shigarwa: Janairu 29, 2018, ranar ziyarar: Oktoba 14, 2024, an nakalto daga Jaridar Sazandegi.
- «دهها فروند پهپاد و موشک به سمت سرزمینهای اشغالی شلیک شد», Kamfanin Dillancin Labarai na IRNA, Ranar shiga: 16 ga Afrilu 1403, Ranar ziyarta: 16 ga Afrilu 1403.
- «انتقام سخت با شلیک دهها موشک به پایگاه آمریکایی عینالاسد»، Kamfanin Dillancin Labarai na IRNA, Ranar shigowa: Janairu 8, 2019, Ranar ziyarta: Disamba 19, 2023.
- Zarepour, Javad Wa Digaran., "Ira'eh Cehaecub Hukumekarani Danesh Dar Qarargahe Sazendagi Khatame Anbiya (S.A.W), Mudiriyate Rahburdi Danesh Sazimane, No. 4, Spring 2019.
- «بیانیه سپاه پاسداران انقلاب اسلامی درخصوص عملیات موشکی علیه اسرائیل»، Al-Alam, kwanan shiga: Oktoba 1, 1403, kwanan wata ziyara: Oktoba 25, 1403.
- «سازمان حفاظت اطلاعات سپاه؛ دو دهه خوشنامی و گمنامی»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Masrheq, kwanan wata: Fabrairu 10, 2010, kwanan wata ziyara: Agusta 2, 2011.
- «سازمان بسیج مستضعفین»،Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, kwanan wata ziyara: Agusta 3, 1401.
- «سپاه پاسداران چگونه تأسیس شد و فرماندهانش چه کسانی بودند؟»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, kwanan wata: Mayu 2, 2017, ranar ziyarar: Yuli 16, 2011.
- «سردار سرلشگر حسین سلامی»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, ranar ziyarar: Yuli 16, 2011.
- «سردار تنگسیری را بیشتر بشناسید»، سایت خبرگزاری دفاع مقدس، تاریخ درج مطلب: ۳ شهریور ۱۳۹۸ش، تاریخ بازدید: ۲ مرداد ۱۴۰۰ش.
- Shafiee, Nozar da Ahmad Moradi, "Tasir Jange 33 Ruze Lubnan Bar Mauqa'iyat Mandiqe Iran," Tahqiqat siyasi wa Bainal Milali na Siyasa, No. 1, Spring 2009.
- «عملیاتهای نیروی دریایی سپاه و دستاوردهای آن در دوران دفاع مقدس», Gidan Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Sacred Defence, kwanan watan aikawa: Oktoba 3, 2020, kwanan wata ziyara: Agusta 1, 2021.
- «فرماندهان نیروی زمینی سپاه از ابتدای انقلاب تا کنون را بشناسید»، Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan, kwanan wata: Yuni 19, 2014, kwanan wata: Yuli 19, 2011.
- «فرماندهان نیروی هوافضای سپاه از ابتدای تاسیس تا کنون را بشناسید»، Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan, kwanan wata: Yuni 20, 2016, kwanan wata: Agusta 2, 2011.
- «فرمانده جدید نیروی قدس سپاه را بیشتر بشناسید»،Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, kwanan watan aikawa: Janairu 3, 2019, kwanan wata ziyara: Agusta 2, 2019.
- Foroughi Jahromi, Mohammad Ghasem, Sepahe Dar Guzare Inqiabe (Makta Sepa), Tehran, Cibiyar Nazarin Musulunci, 2014.
- «قانون اساسی جمهوری اسلامی ایران»، Yanar Gizo na Cibiyar Bincike na Majalisar Shura ta Musulunci, ranar ziyarar: 15 ga Yuli, 1401.
- «قرارگاه خاتم الانبیاء»، سایت خبرگزاری تسنیم.، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, kwanan wata ziyara: 2 ga Agusta 1401.
- Nejabat, Seyed Ali, "Guruhek Tororisti Da'ish Wa Amnyat Milli Jamhuriye Islami Iran; Cales'ha Wa Fursatha," Siyasa Quarterly, No. 6, 2015.
- «متن کامل آییننامه انضباطی نیروهای مسلح جمهوری اسلامی ایران»،Yanar Gizo na Rundunar Sojojin Soja, kwanan watan aikawa: Janairu 1, 2012, kwanan wata ziyara: Yuli 15, 2011.
- Nazarpour, Mehdi, "Naqshe Sepah Pasidarane Inqilabe Islami Dar Tadawume Islami," Mujallar Hasoon, No. 17, Fall 2008.
- Wakilin Jagora, Sepahe Az Didgahe Maqam Muazzam Rahbari, Tehran, Cibiyar Nazarin Musulunci, 1992.
«نیروی زمینی سپاه»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, kwanan wata ziyara: Yuli 16, 2017.
- «نیروی دریایی سپاه»Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, kwanan wata ziyara: Yuli 18, 2011.
- «نیروی هوافضای سپاه»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, kwanan wata ziyara: Agusta 3, 1401.
- «نیروی قدس در کدام جنگها حضور یافت؟»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Masreq, ranar aikawa: Fabrairu 26, 2019, kwanan wata ziyara: Agusta 2, 2019.
- «نیروی قدس سپاه چگونه شکل گرفت؟»،Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Fars, kwanan watan aikawa: Fabrairu 25, 2019, kwanan wata ziyara: Agusta 2, 2019.
- «یک ادغام در سازمان اطلاعات سپاه»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Mashreq, ranar aikawa: Mayu 18, 2019, kwanan wata ziyarar: Agusta 2, 2019.
[[end}}
