Tahajjud
Tahajjud (Larabci: التهجد) Kalma ce wacce ta zo a Kur'ani, tana nufin tsayuwar dare domin yin salla, da karatun alkur'ani, da ambaton Allah, da neman gafara.[1] Wannan kalmar ta zo a cikin Alƙur'ani a aya ta 79 suratul Isra'i﴿وَمِنَ اللَّيْلِ فَتَهَجَّدْ بِهِ. "Kuma da cikin dare ka ta shi ka yi sallah da shi (Kur'ani) ƙari ne a gareka.[2]
Allama Ɗabaɗaba'i yana ganin ma'anar tahajjudi shi ne, farkawa da dare bayan bacci.[3] kamar yadda Allama Majlisi ya ambata ana iya amfani da kalmar tahajjud akan sallar dare.[4] (381 AH) Shaik Saduƙ Allah ya ƙara yarda a gare shi ya tafi kan cewa sallar dare wajibi ce a kan Annabi Muhammad (S.A.W), bisa dogaro kan fi'lil Amr' a kalmar "فَتَهَجَّدْ" kuma mustahabbi ce ga dukkan musulmi.[5]
Allah ya umurci Annabinsa a cikin wannan ayar "قُمِ اللَّيْلَ إِلَّا قَلِيل" Ka tashi a cikin dare face kaɗan.[6] da ya raya dare wajan yi sallar nafila. Makarim Shirazi, mawallafin Tafsirul Amsal, ya yi imani da cewa Annabi Muhammad ya sami matsayi mai yawan godiya ga Allah makamin ceto da a ranar alƙiyama sabo da sallar na filla ta dare da yake yi da sauran ibadar shi.[7]
An rawaito ruwayoyi dangane da falalar Tahajjud, daga ciki akwai da abin da aka ruwaito daga Amirul Muminin (A.S) cewa sallar dare ta nasa lafiyar jiki kuma abun neman yardar Allah maɗaukacin sarki ce, da neman rahamar Allah, da kuma hanyar riko da ɗabi'un Manzon Allah (S.A.W).[8]
Bayanin kula
- ↑ Masalaei Poor, “Tahajjud”, shafi na 689.
- ↑ Suratul Isra'i, aya ta 79.
- ↑ Allama Tabatabai, Al-Mizan, juzu'i na 13, shafi na 175.
- ↑ Allama Al-Majlisi, Bihar Al-Anwar, juzu'i na 1, shafi na 222.
- ↑ Sheikh Al-Saduq, Man La Ihdhuruh Al-Faqih, juzu'i na 1, shafi na 484
- ↑ Suratul Muzzammil, aya ta 2.
- ↑ Makarim Al-Shirazi, Al-Athmal fi Tafsir kitabillahi munazzal, juzu'i na 9, shafi na 93.
- ↑ Allama Al-Majlisi, Bihar Al-Anwar, juzu'i na 87, shafi na 144.
Nassoshi
- Allama Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar Al-Anwar, Beirut, Dar Ihya Al-Arab Heritage, bugu na biyu, 1403H.
- Allama Tabatabai, Sayyed Muhammad Hussein, Al-Mizan a Tafsirin Alqur'ani, Beirut, Al-alami Publications Foundation, 1390H.
- Makarem Al-Shirazi, Nasser, Al-Amsal fi Tafsir Kitabillah Munazzal Qum, Mazhabar Imam Ali bin Abi Talib (A.S), 1379H.
- Sheikh Al-Saduq, Muhammad bin Ali Kitabut Tauhid 1413, 1413 Hijira.
- Abbas Mosallaee Pourتهجد، A cikin "Danšnamé Jahān Islām", Tahran, Bunyād Dā'iratul Ma'ārif Babban Islami, 1383 Sh.