Masak

Daga wikishia

Masak, (Larabci: المسخ) wani nu’in azaba ce wanda cikinta Mutum yake sauyawa daga mutum ya koma Dabba, cikin Masak Mutum ba ya rasa sura da fasalin halittarsa ta Mutum, bari dai kadai zahirin shakalin halittarsa ne yake zama misalin Dabba, cikin Masadir din Muslunci an ambaci wasu wurare dangane da Masak, mafi shahararsu yana cikin Kissar Ashabul Sabti. Kan asasin ayoyin Alkur’ani, hakika Ashbul Sabti sun kasance wasu Gungun Jama’a daga Banu Isra’ila wadanda aka Sauaya Halittarsu zuwa Birrai sakamakon sabawa umarnin Ubangiji a Ranar Asabar, kan asasin Riwayoyin Muslunci Hakika a Ranar Alkiyama nan ma za ayi Masak, wasu ba’ari Masu Zunubai za a sauyawa halittarsu zuwa Birrai da Aladu. Wasu ba’ari Malaman tafsiri sun tafi cewa Masak wanda Magana kansa ta zo a cikin Alkur’ani Masak na bayani da bada misali da ma’anar cewa wasu sakamakon aikata zunubi da suka yi suna samun Halin Dabbanci tare da su, sai dai cewa Akasarin Malaman Tafsiri basu yarda da wannan Magana ba sun tafi kan cewa Surarsu ce ta zahiri ma tana sauyawa zuwa Dabba

Bayani Kan Masak da Banbancinsa da Tanasuk

Masak yana da ma’anar canjawa surar wani abu zuwa zahiri Mara kyau mara dacewa, [1] Masak yana da banbanci da Tanasuk, Tanasuk yana da ma’anar bayan Ruhin Mutum ya rabu da Gangar jiki sai ya koma wata Gangar jikin, amma cikin Masak Ruhi baya Rabuwa da gangar jiki, kawai dai Shakali da zahirin surar ne suka sauyawa suka koma zuwa na Dabba [2]

Kiyaye Huwiyyar Mutum a cikin Masak

Malamai suna ganin canjawar zahirin surar Mutum bai nufin hakikarsa ta Mutum ta canja [3] saboda haka Masak baya nufin karewar Mutum da samar da wani Mutum daban daga Dabba ko kuma shigar da Ruhin Mutum cikin wata Dabba [4] bari dai Masak shine wata Sura ta shige cikin wata sura, a wannan lokaci da surori biyu suka shiga juna hakikar mutum tana nan bata kare ba, sannan sura Nau’in Dabbar tana nan a wannan lokaci dole ne ake kira shi da suna biyu Mutum da kuma Dabba [5] Shahid Mutahhari ya yi bayani Masak kamar haka: a ranar Alkiyama koma da wane shakali da sura muka ta shi, da jikinmu muka tashi ko da wani jikin daban, mu ne dai ba wasu daban ba, kawai dai zai iya yiwuwa zahirin shakalinmu da surarmu ta canja, ko da kuwa Ranar Alkiyama bisa dacewar Malakut na Ruhina za jirkita halitta ta in tashi da surar Dabba, duk da hakan dai ni ne dai ba wani daban ba kawai dai na zo da fasalin jikin Dabbobi [6]

Masak Kan Asasin Alkur’ani

Ku duba Makala mai Taken: Ashabul Sabti Cikin wasu ayoyin Alkur’ani Magana dangane da Jirkita halittar wasu Mutane ta zo, alal misali cikin aya ta 60 a Suratul Ma’ida Magana kan jirkita Halittar wasu Mutane zuwa Birrai da Aladu ta zo [7] haka kuma aya ta 65 cikin Suratul Bakara Ubangiji ya jirkita Halittar wasu Gungun Jama’a daga Banu Isra’ila wadanda ake kira Ashabul Sabti sakamakon Sabawa umarninsa na hana su Kamo kifi a Ranar Asabar, sai ya jirkita Halittarsu zuwa Birrai [8]

Masak kan wasu Ba’arin Hawariyawa

Kan asasin Ayoyin Alkur’ani, Hawariyawan Hazrat Isa (A.S) sun nemi Allah ya saukar musu da ka`baki daga Sama [9] bayan ya saukar musu da abin da suka nema ya amsa addu’arsu sai yace: idan wani Mutum daga cikinku ya kafirta bayan saukar da wannan Ka`baki, lallai zan azabtar da shi da azabar da ban taba azabtar da wani da ita ba [10] wasu ba’arin Malaman tafsiri kan karshen wannan aya sun ce wasu adadi daga Hawariyun tare da saukar musu da Ka`baki daga sama sai suka yi ha’inci, shi kuma Ubangiji ya jirkita halittarsu [11] sai dai cewa wasu ba’ari Malamai kamar misalin Allama Tabataba’i bai yarda da batun jirkita halittar wasu cikin Hawariyawa ba, ya bayyana cewa hakan yana cin karo da ayar Alkur’ani [12]

Yanayin Tabbatuwa

Batun ta wanne irin yanayi Masak ya faru a Duniya, akwai maganganu daban-daban, amma Akasarin Malaman Tafsiri sun tafi kan cewa abin da Alkur’ani yake nufi daga Masak shi ne jikin Mutum ya jirkita zuwa fasalin jikin wata Dabba, amma wasu kuma suna ganin kadai Masak yana kasancewa cikin Badinin Mutum ba abin da yake sauyawa daga halittarsa. Mujahid Bn Jubair wanda ya mutu shekara ta 102 h kamari ya ce: Masak wanda Magana kansa ta zo a Alkur’ani misali ne kawai kamar dai misalin ayar

«کمَثَلِ الْحِمارِ یحْمِلُ أَسْفاراً»

Kamar misalin Jaki da yake dauke da litattafai. [13]-[14] haka an nakalto daga Abdur-Razak Kashani shima yana ganin Masak kadai cikin Badini, a wani bayanin Yahudawa an riga an jirkita Halittarsu a surarsu ta zahiri zaka gansu kamar Mutane amma a hakika ba Mutane bane [15] Rashid Rida da Muhammad Abduhu [16] daga Malaman Tafsiri na Ahlus-sunna suma suna kan wannan ra’ayi [17] sai dai cewa Akasairin Malaman Tafsiri sun tafi kan cewa Masak da ya zo a Alkur’ani ya zo da ma’anarsa ta hakika, ma’ana jirkita Zahirin surar Mutum ta hakika zuwa wani abu daban, [18] Allama Majlisi ya ce akwai riwayoyi mutawatirai da suke shiryarwa kan haka [19] Masu goyan bayan wannan ra’ayi musammam cikin batun cewa abu ne mai wuyar faruwa daga wannan nau’in Masak, sun kafa hujja da cewa yarda da Masak tare da faruwar Mujiza a hannun Annabawa ya kasance, lallai wani aiki ba za a iya kore yiwuwarsa ba, bari dai daga cikin sharuddan Mu’ujiza shi ne kasancewarta sabanin abin da aka al’adantu kansa aka saba da shi [20]

Masak din Mutane a Ranar Alkiyama

Kan asasin adadin wasu Hadisai, a ranar Alkiyama ma za a jirkita halittar wasu gungun Jama’a za su tashi da siffar Dabbobi, alal misali an rawaito cewa Mu’azu Bn Jabal cikin ayar

«یوْمَ ینْفَخُ فِی الصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْواجاً»

Ranar da za a busa Kaho zaku tashi Jama’a Jama’a. [21] an tambayi Annabin Muslunci (S.A.W) ya bada amsa: (wasu daga cikin wadannan mutane za su tashi da Siffar Birrai, wasunku kuma da Siffar Aladu) [22] A wata riwaya daga Imam Bakir (A.S): Mutanen da Suke Karyata Kadar (kaddara) din Allah za su tashi daga Kabarinsu da sura da siffar Birrai da Aladu) [23]

Masak kan Ruhi

Cikin Tunanin Wasu ba’arin Masu bincike daga Musulmai, suna ganin zai iya yiwuwa Mutum a jirkita Mutum a Ruhinsa zuwa Dabba, wasu Malaman Tafsiri suna wannan aya:

«أُولئِک کالْأَنْعامِ بَلْ هُمْ أَضَل»

Wadancananka kamar Misalin Dabbobi suke bari dai sun fi Dabbobi bata. [24] Tana ishara zuwa ga wannan mas’ala da jirkita Ruhin Mutum zuwa Dabba [25] A cewar Murtada Mutahhari, hakikar Mutum musamam ma Halayensa suna damfare da shi, idan mutum ya ji halayen wasu Dabbobi masu kai hari cikin Ruhinsa, to a hakika an jirkita Ruhinsa zuwa wannan Dabba. [26]

Samfurin Masak daga cikin Riwayoyi

Cikin Ba’arin wasu litattafan Shi’a da Ahlus-Sunna an kawo rahoto dangane da Masak wasu daidaikun Mutane banda wanda Masak dinsu ya zo cikin Alkur’ani, alal misali a cikin wata riwaya daga littafin Alkhesal talifin Shaik Saduk, Dabbobi goma sha uku daga jumlarsu an ambaci sunayen Kunama Jemage da Dubbi, da farko sun kasance Mutane bayan jirkita halittarsu sai suka zama wadannan Dabbobi [27] haka kuma Tabarani daga Malaman Ahlus-Sunna a karni na uku zuwa na hudu h kamari ya nakalto wani Hadisi daga Annabin Muslunci (S.A.W) cewa zamanin da zai zo nan gaba za a jirkita Halittar Wasu daga cikin Musulmai zuwa Birrai da Aladu. [28]

Karshen Mutanen da aka Jirkita Halittarsu

Kan asasin Riwayoyin Muslunci Hakika Mutanen da Magana kan Jirkita Halittarsu ta zo cikin Alkur’ani, basa wuce kwanaki uku suke mutuwa, kuma tsatsonsu bai wanzu ba [29] Sadarul Muta’allihin ya rubuta cewa Musulmai sun yi Ijma’i kan wannan Mas’ala cewa Dabbobi na wannan zamani ba sa daga Halittun da akayi Masak dinsu, saboda Mutanen da aka yi Masak dinsu basa wuce kwanaki uku a duniya suke mutuwa, sannan babu wani abu da ya wanzu daga zuriyarsu. [30]

Bayanin kula

  1. Ibn Manzoor, Lasan al-Arab, 1414 AH, juzu'i na 3, shafi na 55
  2. Sobhani, Manshur Aka'id Imamiyya, 1376, shafi na 195.
  3. Motahari,Majmu'eh Asar, 1368, juzu'i na 4, shafi na 703; Javadi Ameli, Tasnim 2008, juzu'i na 5, shafi na 148.
  4. Javadi Ameli, Tasnim, 2008, juzu'i.5, shafi na 148.
  5. Javadi Amoli, Tasnim, 2008, juzu'i na 5, shafi 132.
  6. Motahari, Majmu'eh Asar, 1368, juzu'i na 4, shafi na 703.
  7. Makarem, Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 4, shafi.443.
  8. Makarem, Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 1, shafi na 297.
  9. Suratul Ma’edah, aya ta:112.
  10. Suratul Ma’edah, aya ta:115.
  11. Alousi, Ruh al-Ma'ani, 1415 AH, juzu'i na 3, shafi na 342; Ayashi, Kitab al-Tafseer, 1380 AH, juzu'i na 1, shafi na 351.
  12. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 6, shafi na 239.
  13. Suratul Juma, aya ta 5.
  14. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 1, shafi na 264.
  15. Javadi Ameli, Tasnim, 2008, juzu'i.5, shafi 133
  16. Mughniyeh, Tafsir al-Kashif, 1424 AH, juzu'i na 1, shafi na 121.
  17. Duba Rashid Reza, al-Manar, 1990, juzu'i na 1, shafi na 285.
  18. Mughniyeh, Tafsir al-Kashif, 1424 AH, juzu'i na 1, shafi na 121.
  19. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403, juzu'i na 58, shafi na 111.
  20. Shaker wa Miri, "Mahiyat Azab Masak dar Amuzehaye dini", shafi na 30.
  21. Suratul Nabaa, aya ta 18.
  22. Qortubi, Al-Jamae Al-Ahkam al-Qur'an, 1364, juzu'i na 19, shafi na 175.
  23. Sheikh Sadouq, Thawab al-Amal, 1406H, shafi na 212.
  24. Suratul A'araf, aya ta:179.
  25. Mir Jahani, Tafsir Umm Al-Ketab, shafi na 270.
  26. Motahari, Majmu'eh Asar, 1368, juzu'i na 23, shafi na 105.
  27. Sheikh Sadouq, Al-Khesal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 493.
  28. Tabarani, Al-Mu'jam Al-Kabir, 1415 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 245 da 246.
  29. Sheikh Sadouq, Ayoun Akhbar Al-Reza, 1378H, juzu'i na 1, shafi na 271.
  30. Sadr al-Mutalahin, Tafsirul Al-Kur’an A* Ibn Manzoor, Muhammad bin Makram, harshen Larabci, mai bincike kuma mai bincike: Mir Damadi, Jamaluddin, Beirut, Darul Fikr na bugawa da bugawa da kuma al-Tuziya, Dar Sadir, bugu na uku, 1414H.

Nassoshi

  • Alousi, Seyyed Mahmoud, Ruh al-Ma'ani fi Tafsirin Kur'an al-'Azeem, bincike: Atiya, Ali Abdulbari, Beirut, Dar al-Kitab Al-Alamiya, bugu na farko, 1415H.
  • Javadi Amoli, Abdullah, Tasnim, Qom, Israa, 2008.
  • Rashid Reza, Al-Manar, Masar, Al-Masriyya Al-Katab, 1990.
  • Sobhani, Jafar, Manshur Aka'id Imamiyya, Qum, Cibiyar Imam Sadik (a.s.), 1376.

l-Karim, 1366, juzu’i na 3, shafi na 468.

  • شیخ صدوق، الخصال،Mai bincike kuma mai karantawa: Ghafari, Ali Akbar, Qom, Ofishin wallafe-wallafen Musulunci, bugu na farko, 1362.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Thawab al-Aqbam da Aqab al-Amal, Qum, Dar al-Sharif al-Razi Llanshar, bugu na biyu, 1406H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Ayoun Akhbar al-Reza (AS), mai bincike kuma mai bincike: Mehdi Lajurdi, Tehran, Nash Jahan, bugun farko, 1378.
  • Sadr al-Mutalahin, Muhammad bin Ibrahim, Tafsirul Al-Qur'an Al-Karim, research: Muhammad Khajawi, Bidar Publications, Qum, bugu na biyu, 1366.
  • Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsirin Al-Qur'an, Qum, Islamic Publications Office, bugu na biyar, 1417H.
  • Tabarani, Abu al-Qasim, al-Mu'jam Al-Kabir, mai bincike: Hamdi bin Abdul Majid al-Salfi, Alkahira, Ibn Taimiyyah, 1415 AH.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, مجمع البیان فی تفسیر القرآن،Gabatarwa: Mohammad Javad Balaghi, Tehran, Nasser Khosrow, bugu na uku, 1372.
  • Ayashi, Muhammad bin Mas'ud, al-Tafseer, mai bincike kuma mai bincike: Hashim Rasouli Mahalati, Tehran, Al-Mattaba Al-Alamiya, bugu na farko, 1380H.
  • Qurtubi, Muhammad bin Ahmad, Al-Jamei Law Ahkam al-Qur'an, Tehran, Nasser Khosrow Publications, bugun farko, 1364.
  • مجلسی، محمد باقر، بحار الانوار، Beirut, Dar Ehiya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
  • Motahari, Morteza, tarin ayyuka, Tehran, Sadra Publishing House, 1368.
  • Mughniyeh, Mohammad Javad, Tafsir al-Kashif, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiyya, bugun farko, 1424H.
  • مکارم شیرازی، Nasir, تفسیر نمونه،Tehran, Darul-e-Kitab al-Islamiyya, bugu na 10, 1371.
  • Mirjahani Seyyed Hasan, Tafsir Umm al-Ketab, Tehran, Sadr, Beta.