Aya Ta 128 Suratul Tauba
| bayanan aya | |
|---|---|
| akwai shi cikin sura | Suratul Tauba |
| lambar aya | 128 |
| juzu’i | 11 |
| bayanan abin da yake ciki | |
| wurin sauka | Madina |
| game da | Bayanin ba'arin halaye da siffofin Annabi (S.A.W) |
| ayoyi masu alaqa | Aya ta 6 Suratul Kahafi, aya ta 3 suratul Shu'ara, aya ta 8 suratul Faɗir, aya ta 6 suratul Fussilat |
Aya ta 128 suratul Tauba, (Larabci: الآية 128 من سورة التوبة) aya ce da tattaro surori daga halayen Annabi (S.A.W) cikin mu'amalarsa tare da mutane[1] kan asasin wannan aya, ya fito daga cikin wannan mutane, yana damuwa matuƙa da wahalhalun da mutane suke fuskanta, ya sadaukar da baki ɗayan samuwarsa cikin shiriyar da su, kuma shi mai tausayi da jin ƙai ga muminai.
Lallai wani manzo ya zo muku daga cikinku, yana jin zafi da damuwa idan ya ganku cikin wahala, yana matuƙar ƙoƙari wajen kula da ku, kuma ga muminai shi mai tausayi ne da jin ƙai. Suratul Tauba aya ta 128.
Hali na farko: bisa wannan aya, haƙiƙa Annabi ya fito cikin wnanan al'umma,[2] nau'insu ɗaya[3] kuma mutum mai asali da dangi.[4] Nasir Makarim Shirazi da Jafar Subhani, sun saɓa da malaman tafsiri da suka fassara wannan aya da cewa tana nuni da kasancewar Annabi cikakke Balarabe, sun bayyana cewa haƙiƙa shi Kur'ani ba ruwansa da ƙabilar mutum.[5]
Siffa ta biyu: Annabi (S.A.W) yana matuƙar damuwa da wahalar da mutane suke sha hatta waɗannan da ma ba musulmi ba kai hatta dabbobi[6] raɗaɗi da wahalar halittu tana damunsa.[7] da wannan dalili ma ake kiransa mai tausayawa al'umma.[8]
Siffa ta uku: Annabi mai fatan alheri da tsiran al'umma, muminai da ma waɗanda ba muminai ba.[9] Malaman tafsiri game da wannan batu suna cewa Annabi ne da yake tsananin ƙaunar mutanen da son ganinsu cikin farin ciki, mutum ne mai tausayin kowa da kowa.[10]
Siffa ta huɗu da biyar: Annabi mai tausayi da jin ƙai.[11] Ana cewa «رئوف» ishara ce zuwa soyayya da ta keɓantu da muminai ita kuma «رحیم» ishara ce ga rahama zuwa ga masu lefi[12] Tausayi da jin ƙai da ya wuce iyaka[13] Shi kaɗai ne Annabin Muslunci (S.A.W) da Allah ya kira shi da sunaye guda biyu “Ra'uf” da “Rahim” ma'ana mai tausayi da jin ƙai.[14]
Bayanin kula
- ↑ Makarem Shirazi, Payame Qur'an, 2007, juzu'i. 7, shafi. 296.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Numno, 1371, juzu'i. 8, shafi. 206.
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i. 9, shafi. 411; Kashani, Manhaj al-Sadiqin, Tehran, juzu'i. 4, shafi. 348; Qurashi Banabi, Tafsiri Ahsan al-Hadith, 1375 AH, juzu'i. 4, shafi. 339.
- ↑ Abul Fatuh Razi, Rouz al-Janan, 1408 AH, juzu'i na 10, shafi na 86.
- ↑ Sobhani, Manshroud Javid, Qom, juzu'i. 7, shafi. 366; Makarem Shirazi, Tafsir Nomune, 1371, juzu'i. 8, shafi. 206.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir al-Numno, 1371 AH, juzu'i. 8, shafi. 207; Kashfi, Tafsir al-Husseini (Mawahebul Aliyya), Noor Littattafai, shafi. 440; Abul-Futuh Razi, Rawd al-jinan, 1408 AH, juzu'i. 10, shafi. 87.
- ↑ Mughniyah, Al-Tafsir Al-Kashif, 1424 AH, juzu'i. 4, shafi. 124.
- ↑ Qaraati, Tafsir al-Noor, 2009, juzu'i. 3, shafi. 529.
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i. 9, shafi. 411; Tabarsi, Majma' al-Bayan, 1372 AH, Vol. 5, shafi. 130.
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i. 9, shafi. 411; Tabarsi, Majma' al-Bayan, 1372 AH, juzu'i. 5, shafi. 130.
- ↑ Mughniyah, Tafsir al-Kashif, 1424 AH, vol. 4, shafi. 124; Qurashi Banabi, Tafsirul Ahsan al-Hadith, 1375 AH, juzu'i. 4, shafi. 339.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Nomune, 1371, juzu'i. 8, shafi. 208.
- ↑ Qurashi Banabi, Tafsiri Ahsan al-Hadith, 1375, juzu'i. 4, shafi. 339.
- ↑ Qaraati, Tafsir Noor, 2009, juzu'i. 3, shafi. 529; Kashfi, Tafsir Hosseini (Mawahebul Aliyya), Noor Littattafai, shafi. 440.
Nassoshi
- Abul-Futuh Razi, Hussein bn Ali, Rawd al-jinan wa Ruh al-jinan fi Tafsir al-Quran, Mashhad, Astan Quds Razavi, 1408 AH.
- Sabhani, Jafar, Manshor al-Javid, Kum, Imam Sadiq (AS) Foundation, Beta.
- Tabatabai, Sayyid Muhammad Hussein, Al-Mizan fi Tafsiril Quran, Beirut, Al-Alami Publishing House, 1390H.
- Tabarsi, Fadl ibn Hassan, Majma’ al-Bayan fi Tafsir al-Quran, Tehran, Nasser Khosrow, 1372H.
- Qaraati, Mohsen, Tafsir al-Nur, Tehran, Cibiyar Al'adu ta Alqur'ani, 1388H.
- Qorashi Banabi, Ali Akbar, Tafsir al-Ahsan al-Hadith, Tehran, Bissat Foundation, 1375 AH.
- Kashani, Fathullah ibn Shukrallah, Manhaj al-Sadiqin fi Ilzam al-Mukhlafin, Tehran, Islamiya Bookstore, Beta.
- Kashifi, Hussein bin Ali, Tafsir al-Husayn (Mawahebul Aliyya), Saravan, Noor Bookstore, Bitta.
- Mughniyeh, Mohammad Javad, Tafsir al-Kashif, Tehran, Dar al-Kitab al-Islami, 1424H.
- Makarim Shirazi, Nasser, Payame Quran, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiyyah, 1386H.
- Makarim Shirazi, Nasser, Tafsir al-Numno, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiyyah, 1371H.
- Makarim Shirazi, Nasser, Ghoftare al-Masomin (AS), wanda Sayyid Muhammad Abdullahzadeh, Qum, Madrasa al-Imam Ali bn Abi Talib (AS), ya shirya kuma ya shirya shi, 1387H.