Halal

Daga wikishia
Risala Ilmiyya

Halal (Larabci: الحلال) shi ne kishiyar Haram kuma yana nufin abin da ya halatta a shari'a da Hankali. A wasu madogaran Fikihu ana ganin kalmar halal daidai yake da Mubahi, amma a sabanin haka, sun ce halal yana daga cikin hukunce-hukuncen da ba su shafi ayyukan Mukallafi ba wato baya sahun wajibi ko mustahabbi ....kai tsaye. kuma shi Mubahi ne ya fi gama gari. fiye da halal Domin kowane mubah halal ne, amma ba duk halal bane Mubahi.. A wajen Malaman Fikihu, idan akwai kokwanton cewa wani abu haramun ne ko halal, to akan bahashi a halal bisa Ka'idar Hilliyya, A cikin Hadisai an yi umarni da a koyi hukunce-hukuncen halal da haram, saboda samun tsira, A shekarata 2007, an kafa Cibiyar Halal ta Duniya don yada al'adun Halal. Haka kuma an sanya ranar 17 ga watan Ramadan a matsayin ranar Halal ta duniya.

Ma'ana

ma'anar halal kihsiyar Haram shi ne abin da shari'a da Hankali suka yarda [1] da shi,[2] Ma'ana abin da ba haram bane aikata shi ko ƙin aikata shi ba lefi.[3] Halal a cikin lugga yana nufin konce wani ɗauri[4] A cewar Ali Akbar Karashi "Hal" yana nufin halal da buɗe wani ƙulli da akayi, kuma halal shi ne abin da aka kuncewa haramci.[5] A cewar wasu masu bincike, yin amfani da "Yajuz" a cikin maganganun Malaman Fikihu wani lokaci yana nufin "Yasihhu" (wato abun dai dai ne) wani lokaci kuma yana nufin "Yahillu" (abu halal ne) kuma ana amfani da shi a cikin abubuwan da Shari'a ba ta hana su ba[ [6] A cikin wata ruwaya da aka ruwaito daga Imam Sadiƙ (A.S) koyan hadisi kan halal da haram ga mutum mai gaskiya , ya fi duniya da zinari da azurfarda ke cikinta.Raqi, Al-Mahasin, Dar al-Kitb al-Islamiyah, juzu'i na 1, shafi.

Banbancin Halal da Mubahi

Wasu suna ganin kalmar Halal ta kasance daidai da "mubahi"[7] wasu kuma sun banbance tsakanin waɗannan kalmomi guda biyu[8] kuma sun ambaci bambance-bambance a gare su, waɗanda suka hada da; A cikin shari'a ana amfani da halal akan haram, Kuma bai shafi abubuwa kamar Wajibi ko farilla, Mustahabbi, Makruhi, da Mubahi ba[9] Don haka halal ya fi mubahi faɗi. Yana nufin duk wani mubah halal ne, amma ba kowane halal ba ne mubah Kamar: Makruhi halal ne amma ba mubah bane[10] Mubah yana daga cikin Ahkam Taklifi, kuma ana jingina shi kai tsaye zuwa ga ayyukan mutum na kai tsaye[11] amma halal yana daga cikin Ahkam Wada'i wanda ba kai tsaye yake tinkarar ayyukan mutum ba.[12] Halal na nufin kwance igiyar takunkumi da cire haramci Alhali mubah yana nufin ci gaba da faɗaɗa ayyuka ta fuskar aikatawa da barinsa.[13]

Abin da ake Nufi da Ka'idar Hilliya a Fikhu

Asalin Kasida: Ƙa'idar Hilliya Ka'ida ce ta Fikihu wadda cikin ta ake da shakka kan halacci ko haramcin wani abu.[14] A bisa wannan ƙa'ida idan aka samu shakku kan haram ko halal sai a yi hukunci da halascinsa.[15] Domin tabbatar da wannan ƙaida sai a koma aya ta 29 a cikin Suratul Baƙara, "Shi ne wanda ya halicci kome da ke cikin ƙasa dominku."[16] da hadisin da ya ce: "Kowane abu halal ne a gare ku, sai dai idan kun san haramun ne.[17]

Dukiyar Halal

wani Kuɗin Shiga na Halal ne da ake samu a cikin tsarin shari'a kuma a cikinsa ake kiyaye hakkin Allah kamar Khumusi da Zakka, haka nan kuma babu Hakkin Mutane cikinsa,[18] misali[19] a cikin ruwaya daga Imam Sadiƙ (A.S), wanda ya yi ƙoƙari domin ya sami halal, ana kamanta shi da wanda ya yi Jihadi a tafarkin Allah,[20] kuma ya zo a cikin hadisi daga Annabi (S.A.W) cewa Ibada tana da kashi saba'in, kuma mafi girmanta shi ne. neman halal.[21]

Bayanin kula

  1. Meshkini, musdalhat Fiqhi, 1419H, shafi na 216.
  2. مکارم شیرازی، دائرة المعارف فقه مقارن، ۱۳۸۵ش، ج۱، ص۴۳۰.
  3. Abdel Moneim, Mujamu Mustalhat Fikhi wa alfaz, Dar Al-Fadila, Kashi na 1, shafi na 585.
  4. Rajeb Esfahani, Al-Mufardat, karkashin kalmar "Hal"
  5. Qureshi, ƙamus Kur'an, ƙarƙashin kalmar "mafita".
  6. Hafnawi, Gunjineh Mustalhat fikhi wa Usuli, 1395, shafi.89.
  7. Muassaseh dayireeh fikhi islami,Muasuatu fikhi islamiya juz 2 shafi na 83
  8. Muassaseh dayireeh fikhi islami,Muasuatu fikhi islamiya juz 2 shafi na 84
  9. Saadi, Kamus Fiqhu lugga wa isdilahan, 1408 s, shafi na 99.
  10. Saadi, Kamus Fiqhu lugga wa Isdilahan, 1408 s, shafi na 99
  11. Sadr, duruss fi ilimil usuli, 1406 AH, juzu'i na 1, shafi na 53; Islamic Fiqh Encyclopaedia Institute, Persian Fiqh Farhang, 1387, juzu'i na 1, shafi na 218.
  12. Centre for Islamic Information and Resources, Usul Fiqh Dictionary, 2009, juzu'i na 1, shafi na 106.
  13. muassaseh dayireh fikhi islami,mausu'eh fikhi islami,1464q juz na 2 shafi na 84
  14. Dubi Valai, Farhang Tashrihi isdilahat usuli, 2007, juzu'i 1, shafi na 85.
  15. muassatu dayiratu fikhi islamiya, mausuatu fikhi islamiya, 1463 juz na 13 shafi na 320
  16. Fazel Toni, Al-Wafieh, 1412 AH, shafi na 185.
  17. Kulaini, Al-Kafi, 1430 AH, juzu'i na 10, shafi na 542; Fazel Lankarani, Bayanin Sharia, 1426 AH, shafi na 193
  18. Nakashe rizki halal dar salamati ma'anawi insan az didgahe ayar wa riwayat shafi na 3
  19. Nuri, Mustadrak Al-Wasail, 1408 s, juzu'i na 13, shafi na 12.
  20. Qazi Noman Maghrib, Da'aim al-Islam, 1385 AH, juzu'i na 2, shafi na 15.
  21. Nuri, Mustadrak Al-Wasail, 1408 s, juzu'i na 13, shafi na 12.

Nassoshi

  • "muassaseh Halal Jahani",https://halalworldinstitute.org/about/3?lang=fa#.Yt6P-b1BzIU gidan yanar gizon Cibiyar Halal ta Duniya, wanda aka duba ranar 3 ga Agusta, 1401.
  • Abdul Moneim, Mahmoud Abdul Rahman, Al-Tarmidhom da Al-Alfaz Al-Fiqhiyyah, Cairo, Dar Al-Fadilah, Bita.
  • Barqi, Ahmad bin Mohammad, Al-Mahasen, Kum, Dar al-Katb al-Islamiyya, Bita.
  • Cibiyar Bayani da Albarkatun Musulunci, Kamus na Ka'idodin Fikihu, Qum, Cibiyar Bincike na Kimiyya da Al'adun Musulunci, 2009.
  • Cibiyar Encyclopaedia ta Musulunci, Al-Musua Fiqhiyah, Qum, Cibiyar Encyclopaedia ta Musulunci, 1423H.
  • Fazil Lankarani, Muhammad, Bayanin Shari'ah a cikin Rubutun Al-Wasila (Al-Ijtihad da Taqlid), Qum, Cibiyar Shari'a ta Imams Athar (AS), 1426H.
  • Fazil Toni, Abdullah bin Muhammad, Al-Wafiyah fi Usul al-Fiqh, Qom, Majmael al-Fikr al-Islami, bugu na farko, 1412H.
  • Hafnawi, Mohammad Ibrahim, The Treasury of Legal and Usuli Terms, Faiz Mohammad Baloch, Torbat Jam, Khwaja Abdullah Ansari Publications, fassara, 1395.
  • Issazadeh, Issa da Nikzad Issazadeh, "Matsayin Halal Rizk a cikin lafiyar ruhi na mutum daga mahangar ayoyi da hadisai", batu na musamman na kimiyyar lafiya, fitowa ta 1, fall 2018.
  • Kobari, Mahmoud, Halal wa Haram, Fethian Publications, 2013.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-kafi, Qum, Dabul-Hadith Publishing House, bugun farko, 1430H.
  • Meshkini, Ali, Tafsirin Fiqhu, Qum, bugun Al-Hadi, 1419H.
  • Noori, Mirzahosein, Mostadrak al-Wasail, Qum, Al-Bait Foundation, 1408 AH.
  • Qorshi, Sayyid Ali Akbar, Kamus Quran, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiyya, bugu na 6, 1371.
  • Rajeb Esfahani, Hossein bin Muhammad, al-Mufardat fi Gharib al-Qur'an, Damascus, Dar al-Qalam, 1412H.
  • Saadi, Abu al-Jeib, al-Qamoos al-Figha lugga wa alfaz, Damascus, Darul Fikr, 1408H.
  • Sadr, Muhammad Baqir, Darus fi ilm al-usul, Beirut, Dar al-Kitab al-Lebanani, 1406H.
  • Valai, Issa, Farhang tashrih Usul, Tehran, Gidan Bugawa Nei, 2007.
  • https://halalworld.co/2015/07/05/%D8%A8%D8%B2%D8%B1%DA%AF%D8%AF%D8%A7%D8%B4%D8%AA-%D8%B1%D9%88%D8%B2-%D8%AC%D9%87%D8%A7%D9%86%D9%8A-%D8%AD%D9%84%D8%A7%D9%84/, Cibiyar Halal ta Duniya, duba: Agusta 3, 1401.
  • https://iqna.ir/fa/news/1461694Kamfanin dillancin labaran iqna ya labarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iqna cewa, a ranar 27 ga watan Oktoban shekarar 2013, za a gudanar da taron "Ranar Halal ta Duniya" karo na biyu a ranar 3 ga watan Agustan shekara ta 1401.
  • muassaseh Fiki islami, Ilimin Fikihu na Farisa, Qum,Fikihu islamiyeh, 1387.
  • muassaseh Ilim Fiqhu islamiyyeh, Ilimin Fiqhu na Musulunci, Qum, Cibiyar Ilimin Fiqhu ta Musulunci, 1424H.