Daran 21 Ga Ramadan
Daren 21 g watan ramadan (Larabci:الليلة الحادية والعشرون من رمضان) Daren shahadar Imam Ali (A.S) yana ɗaya daga cikin raneku masu muhimmanci a kalandar Shi'a. Kamar yadda rahotannin tarihi suka nuna cewa Ibn muljam muradi ya sari Imam Ali (A.S) a daren 19 ga watan Ramadan, kuma Imam ya yi shahada a daren 21.[1] a wasu garuruwa a cikin ƙasar Iran ana yin zaman makoki da ta'aziyya[2] da ake kira ta'aziyar ƙanbar da Sayyidina Ali (A.S).[3]
Kamar yadda majiyoyin Shi'a suka ruwaito cewa, dararen 21, tare da 19 da 23, yana daga cikin dararen da ake kyautata zaton faruwar daren lailatul ƙadari a cikin su.[4] don haka 'yan Shi'a suke kwana a gidaje da masallatai. Husaini da sauran wuraren addini don raya wannan dararen.[5] Kamar yadda Sheikh Abbas ƙommi ya faɗa a cikin littafin Mafatihul al-Jinan cewa falalar daren 21 ya fi daren 19 ga watan Ramadan, ga wasu ayyuka da ake so yi a cikin wannan dare; mai bi:
1Raya daren 2. Wankan daran lailatul ƙadri. 3. Sallar daren lailatul Kaɗri. 4. Sallah raka'a ɗari. 5. Ɗora ƙur'ani a ka. 6. Tawassuli da Ma'asumai goma sha huɗu.[6]
Wasu ƴan Shi'a suna raba hadaya da buɗa baki da sahur a daren 21.[7] A birnin Lorestan na kasar Iran, ana dafa wani hadaya ta musamman a wannan dare, wanda ake kira halwa na ashirin da daya..[8]
Bayanin kula
- ↑ Mofid, Al-Arshad, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 9.
- ↑ Majidi Khamene, 'shabhaye ƙadr dar Iran', shafi na 19.
- ↑ Majidi Khamene, 'shabhaye ƙadr a Iran', shafi na 20.
- ↑ Majlisi, Mir'atul al-uƙool, 1404 BC, juzu'i na 16, shafi 381
- ↑ Majidi Khamene, 'shabhaye ƙadr dar Iran', shafi na 20
- ↑ ↑ ƙomi, Mufatih al-jinan, ayyukan lailatul ƙadari, ayyuka na musamman na dare ashirin da daya.
- ↑ Majidi Khamene, 'shabhaye ƙadr dar Iran', shafi na 2
- ↑ «آئینهای رمضان در استانها - ۳۶ رسوم شب شهادت امام علی؛ بوی حلوای ۲۱ رمضان خانهها را معطر میکند»، خبرگزاری مهر.
Nassoshi
- ƙomi, Sheikh Abbas, Mufatih al-Jinan, Kum, Aswah, Bita.
- Majlesi, Muhammad Baƙir bin Muhammad Taƙi, Miryah al-Aƙool fi Sharh Akhbar al-Ar-Rasul, Darul-Kitab al-Islamiyya, Al-Muttabah Marwi, 1404 H.
مجیدی خامنه، فریده، «شبهای قدر در ایران»، در مجله گلستان قرآن، شماره ۳۷، آذر ۱۳۷۹ش.
- مفید، محمد بن محمد، الارشاد فی معرفة حججالله علی العباد، تصحیح، مؤسسة آل البیت علیهمالسلام، قم، کنگره شیخ مفید، چاپ اول، ۱۴۱۳ق.
- «آئینهای رمضان در استانها - ۳۶ رسوم شب شهادت امام علی؛ بوی حلوای ۲۱ رمضان خانهها را معطر میکند»، خبرگزاری مهر، تاریخ درج مطلب: ۶ تیر ۱۳۹۵ش، تاریخ بازدید: ۲۲ اسفند ۱۴۰۲ش.