Tawassuli
- Wannan ƙasida ce game da ma'anar tawassuli. Domin sanin tawassuli ku duba ƙasidar Tawassuli da Matattu.
Sanin Allah | |
---|---|
Tauhidi | Tabbatar Da Allah • Tauhidi Zati • Tauhidi Sifati • Tauhidi Af'ali • Tauhidi Ibadi • Siffofin Zati • Siffofin Fi'ili |
Rassa | Tawassuli • Ceto • Tabarruki • Istigasa |
Adalcin Allah | |
Husnu Wa Ƙubhu • Bada'u • Amrun Bainal Amraini | |
Annabta | |
Ismar Annabawa • Khatamiyyat • Annabin Muslunci • Mu'ujiza• Asalantuwar Kur'ani | |
Imamanci | |
Aƙidu | Ismar Annabawa • Wilaya Takwiniyya • Ilmul Gaibi • Khalifatullahi • Gaibar Imam Mahadi (A.F) • Mahadawiyya • Intizarul Faraj • Bayyana• Raja'a • Imamanci Na Nassi |
Imaman | Imam Ali • Imam Hassan • Imam Husaini • Imam Sajjad • Imam Baƙir • Imam Sadiƙ • Imam Kazim • Imam Rida • Imam Jawad • Imam Hadi • Imam Askari • Imam Mahadi |
Ma'ad | |
Barzahu • Ma'ad Jismani • Hashar • Siraɗi • Taɗayurul Kutub • Mizan | |
Fitattun Mas'aloli | |
Ahlil-Baiti • Ma'asumai Goma Sha Huɗu • Karama • Taƙiyya • Marja'iyya • Wilayatul Faƙihi • Imanin Mai Aikata Manyan Zunubai |
Tawassuli (Larabci:التَّوسل) shi ne tsanantuwa da wani mutum ko wani abu zuwa ga Allah domin neman biyan buƙata, tawassuli ɗaya ne daga cikin aƙidu da dukkanin musulmai suka yi tarayya a cikinsa, kan halascin yinsa malamai sun dogara da ayoyin kur'ani misalin ayar wasila da kuma sunnar Annabi (s.a.w), sirar musulmai, riwayoyin imamai ma'asumai (a.s) da kuma dalili na hankali, tawassuli yana da matsayi na musamman a wurin ƴan shi'a, ƴan shi'a ƙari kan tawassulin da Annabi (s.a.w) da imamai ma'asumai (a.s) suna yin tawassuli da dangin imamai (a.s) misalin matan imamai da uwayensu da ƴaƴansu, yayin da suka je ziyarar ƙaburburan imamai (a.s) suna karanta ziyara suna tawassali da su da salo daban-daban da ya zo cikin wannan ziyara. An ce imani da tawassuli wani abu da ya samuj yaɗuwa sosai tsakankanin firƙoƙin musulmai har zuwa ƙarni na takwas, a ƙarni na takwas ne wasu musulmai daga jama'ar salafiyya musammam ma Ibn taimiyya, suka fara shigo da shakku cikin ba'arin rabe-rabensa misalin tawassuli da zatin Annabi (s.a.w), tawassuli da bayin Allah salihai, tawassuli da muƙami da matsayinsu bayan wafatinsu, bayan shuɗewar ƙarnoni tare da yaɗuwar aƙidar wahabiyanci tawassuli ya fuskanci rashin amincewa sosai tsakankanin wasu musulmai.
Babban dalilin da ƴan salafiyya suke dogara da shi kan haramta tawassuli, shi ne wai ba a samu wani rahoto game da ayyuka misalin tawassuli daga sahabbai ba, mahangar salafiyya da wahabiyawa game da tawassuli ta samu suka daga ɓangaren shi'a da ahlus-sunna, shi'a da ahlus-sunna sun dogara da naƙali da rahotannin tarihi cikin tabbatar da cewa wasu sahabbai sun yi irin wannan tawassuli.
Matsayin Tawassuli A Wurin Musulmai
Tawasulli ɗaya ne daga aƙidun da musulmai suka yi tarayya a cikinsa.[1] Ibn taimiyya ya tabbatar da cewa asalin halascin tawassuli abu ne baki ɗayan musulmi suka yi ittifaƙi a kansa.[2] taƙiyyud-dini subki (Wafati:756.h.ƙ) malami a mazhabar shafi'iyya ɗan asalin ƙasar misra, cikin littafin shifa'ul as-saƙam, yana ganin jayayya da jidali game da halascin tawassuli daidai yake da jidali cikin larurin addini.[3] jafar subhani malamin kalam na shi'a shi ma yana ganin asalin tawassuli da sabubba a rayuwar ɗan Adam wani abu ne na halittar ɗan Adam.[4]
Saɓanin Wahabiyawa Tare da Ba'arin Wasu Nau'ukan Tawassuli
Haƙiƙa tawassuli ya samu karɓuwa sosai tsakankanin firƙoƙin muslunci, ya yaɗu cikinsu kusan kamar yadda ya yaɗu wurin imamiyya da ƴan ɗariƙun sufaye, amma daga ƙarni na takwas bayan hijira aka samu wasu ba'arin malaman salafiyya musamman ibn taimiyya suka fara shigo da shakku kan wasu ba'arin nau'ukan tawassuli da ake yi. hakan ne ya haifar da buɗe ƙofar jayayya da jidali tsakanin ahlus-sunna da shi'a tare da salafiyya cikin asalin halascin tawassuli a muslunci, an yi rubuce-rubuce cikin yin martani kan mahangar ƴan salafiyya game da tawassuli.[5] daga jumlarsu waɗannan wallafe-wallafe akwai shifa'us as-saƙami na taƙiyyud-dini subki wanda ya wallafa cikin raddi kan malaman salafiyya cikin mas'alar tawassuli.[6]
A yanzu a ƙarni na goma sha biyar da muke cikin wahabiyawa na wanzan zamani tare da biyayya ga salafiyya sun nuna shakku kan ba'arin nau'ukan tawassuli; haka ne ya sanya malaman shi'a da ahlus-sunna suka tsunduma cikin bahasi kan tawassuli, cikin bincike da martani kan mahangar wahabiyawa suka yi wasu wallafe-wallafe.[7]
Himmatuwa Ta Musamman Da ƴan Shi'a Suke Da Ita Kan Tawassuli
Haƙiƙa tawassuli ya kasance wani abu da ƴan shi'a suke bashi kulawa ta musammam, ƙari kan tawassuli da Annabi (s.a.w) da imamai ma'asumai (a.s) ƴan shi'a sune tawassuli da wasu ɗaiɗaikun mutane daga iyalan imamai (a.s) misalin matansu, da uwayensu dama ƴaƴan imamai.[8] yayin kai ziyara ƙaburburan imamai (a.s) da ƴaƴan imamai, suna karanta ziyarori waɗanda suke tawassuli da s ta hanyoyi daban-daban.[9] Ana yin tawassuli cikin jam'i jama'a da kuma ɗaiɗaiku, du'a'u tawassul ɗaya ce daga addu'o'i da da galibi yan shi'a suke yinta daren kowacce ranar laraba cikin jam'i a masallaci, husainiyoyi da gidajensu. Cikin wannan addu'a suna tawassuli da ma'asumai goma sha huɗu.[10] wani lokaci su kan shirya walima tare da tawassuli domin samun biyan buƙata. Misali a ƙasar Iran wasu ba'arin mutane domin nemawa mara lafiyar cikinsu waraka ko neman wata buƙata suna shirya ciyar da abinci da sunan Imam Zainul-Abidin (A.S).[11] haka nan suna shirya walimar da sunan sayyada Ruƙayya domin neman wata buƙata da suke da ita, misalin aure, neman haihuwa, buƙata ta ƙudi da sauran buƙatunsu, wannan wani sanannen lamari ne tsakankanin al'ummar Iran.
Na'am su ma ahlus-sunna ba a barsu a baya ba, alal misali malam sam'ani marubucin tarihi masanin fiƙihu da hadisi ɗan mazhabar shafi'iyya a ƙarni na shida bayan hijira, ya kasance yana zuwa ƙabarin Imam Kazim (A.S) yana tawassuli da shi.[12] Abu Ali khallal daga malaman ahlus-sunna a ƙarni na uku bayan hijira, ya ce duk sanda na fuskanci wata matsala ina tafiya ƙabarin Musa ɗan Jafar ina yin tawassuli da shi, matsalata ta warware[13] an naƙalto daga Muhammad ɗan Idris shafi'i ɗaya daga Malaman fiƙihu huɗu na ahlus-sunna cewa ya siffanta ƙabarin Musa ɗan Jafar da magani mai warkarwa.[14]
Ma'anar Tawassuli Tare da Halascinsa A Shari'a
Tawassuli yana nufin akwai wani mutum ko wani abu da yake da wani matsayi na musammam a wurin ubangiji da muke sanya shi tsani da hanya zuwa samun amsa addu'o'inmu.[15] kalmar tawassuli a mahangar fasahar harshen larabci suna da ɗaya da kalmar wasila.[16] wasila shi ne wannan abu da ake amfani da shi domin kaiwa zuwa ga wani abu.[17] Tawassuli da istigasa wasu malamai suna ganin suna da ma'ana guda ɗaya.[18] wasu kuma suna ganin suna da bambancin ma'ana, da wannan bayani na cewa ita istigasa tana zuwa a halin da wurin tsanani, amma tawassuli bai keɓantu da cikin halin tsanani ba ya haɗa da halin sauki da kwanciyar hankali.[19]
Dalilai Kan Halascin Tawassuli
Domin tabbatar da halascin tawassuli an jingina da dalilan da bayanai kamar haka:
- Kur'ani: cikin ayar wasila Allah ya umarci muminai da su riƙi wasila domin kaiwa zuwa gareshi.[20] haka nan cikin aya ta 64 suratul nisa'I an umarci masu zunubai da su je wurin Annabi (s.a.w) su roƙeshi ya nema musu gafara wurin ubangiji.[21] daga cikin sauran ayoyin da aka dogara da su kan halascin yin tawassuli akwai aya ta 97 suratul yusuf.[22] wacce kan asasinta ƴaƴan Annabi yaƙub sun roƙi babansu ya nema musu gafara.[23]
- Riwayoyi: akwai riwayoyi masu tarin yawa da aka naƙalto daga litattafan shi'a da ahlus-sunna.[24] da suke shiryarwa kan halascin tawassuli a shari'ar muslunci.[25]
- Sirar musulmai: sirar musulmai tun farkon muslunci da kuma sirar sahabbai tana nuna cewa yin tawassuli da Annabi (s.a.w) ya kasance karɓaɓɓe tun wancan lokacin.[26] alal misali cikin littafin sahihu bukhari akwai wani ɓangare ɗauke da taken “Abwabu Istisƙa” da aka dawwana shi ƙarƙashinsa an naƙalto riwayoyi daban-daban da suke ba da labarin yadda sahabbai suka yi tawassuli da Annabi (s.a.w) ta fuskacin addu'a domin neman saukar ruwan sama.[27]
- Dalili na hankali: tawassuli ko kamun ƙafa, yana kusanta bawa zuwa ga ubangijinsa, kuma shi kusanci zuwa gareshi shi ne ƙarshen ƙololuwar buri da buƙatar mutum cikin ayyukan ibadarsa, saboda idan babu samun kusanci gareshi, haƙiƙa mutum zai ta rabauta da farin cikin duniya da lahira ba; a gefe guda wannan kusanci shima idan babu wasila da tsani ba zai taɓa samuwa ba, saboda haka farin ciki da rabauta a duniya da lahiraya dogara ne kan tawassuli da kuma wasila.[28]
Wahabiyawa BasuYarda da Yin Tawassuli da Annabi (S.A.W) Da Salihan Bayi ba
Yin tawassulu da Annabi (s.a.w) da salihan bayin Allah, shi ne alal misali masu tawassuli su ce:
“Ya Allah lallai ni ina tawassuli da kamun ƙafa da annabinka ka biya buƙatata”[29]
Kan asasin fatawar darul itfa na misra game da tawassuli:
Haƙiƙa yin tawassuli da Annabawa da waliyyai da salihan bayin Allah, da neman tabarruki da taimako daga garesu, ya halasta kuma mustahabbi ne, akwai dalilai daga kur'ani, da sunna da aikin sahabban annabi kan halascinsa da kasancewarsa mustahabbi. Haka kuma kamar yanda yin tawassuli da su ya kasance halas, haka yin tawassuli da muƙami da matsayinsu shima abu ne da ya halasta, rashin yardar wasu tsirarun mutane cikin wannan mas'ala abu ne da bai da wata ƙima.
A cewar Isa ɗan Abdullahi himyari, mai bincike ɗan mazhabar malikiyya daga ƙasar emarat (Dubai) wannan nau'in tawassuli tun daga ƙarni na takwas ya fara fuskantar rashin amincewar jama'a daga salafiyya, sai dai cewa tun wancan lokaci aka malaman muslunci suka tsayu kyam tare da ba da yankakkiyar amsa ga masu inkarin wannan nau'in tawassuli, sai rigima ta kwaranye ta tafi, sai dai cewa kuma ta ƙara dawowa daa baya ta ɓangaren wahabiyawa da suka ƙara bijiro da ita tare da nuna cewa wannan nau'in tawassuli gurbataccen tawassuli ne.[31] alal misali Muhammad nasib rufa'i(Wafati:1412.h.ƙ) daga wahabiyawan ƙasar siriya, ya bayyana cewa bai inganta ba ayi tawassuli da annabawa da waliyyan Allah, wannan aiki kafirci ne kuma bidi'a ce, kamar yanda ya faɗa.[32] malam rufa'I domin bayyana bidi'antuwar wannan nau'in tawassuli yana cewa babu kowanne irin dalili daga kur'ani da sunna da yake tabbatar da halascin wannan aiki.[33]
Suka Kan Mahangar Wahabiyawa daga Malaman Muslunci
Taƙiyyud-dini Subki, malamin mazhabar shafi'iyya a ƙarni na takwas bayan hijira, yana cewa akwai riwayoyi mutawatirai masu tarin yawa kan halascin yin tawassuli da istigasa da Annabi (s.a.w) da salihan bayin Allah.[34] Ali ɗan Abdullahi samhudi (Wafati:911.h.ƙ) malamin mazhabar shafi'iyya mutumin ƙasar misra, cikin littafin “Wafa'ul Al-wafa'i” ya yi da'awar ijma'i kan tawassuli da Annabi (s.a.w) da kuma salihan bayin Allah.[35] sun dogara ne da ba'arin wasu riwayoyi da aka naƙalto su a ingantattun litattafan ahlus-sunna.[36] daga jumlarsu kan asasin wata riwaya da aka naƙaltota a littafin sahihu bukhari cewa Umar ɗan khaɗɗabi ya yi tawassuli da Abbas ɗan Abdul-muɗallabi baffan annabi domin neman saukar ruwan sama.[37] Riwayoyi masu yawa sun zo daga Imaman Shi'a (A.S) kan halascin tawassuli da Annabi da waliyyan Allah. Cikin ba'arin waɗannan riwayoyi su kansu ahlul-baiti (a.s) an gabatar su matsayin wasila zuwa ga Allah.[38] alal misali du'a'u tawassul ana daga cikin addu'o'i da ake tawassuli da ma'asumai goma sha huɗu domin biyan buƙata.[39]
Bidi'antar da Tawassuli da Matattu a Wurin Ibn Taimiyya da Wahabiyyawa
- Tushen ƙasida: Tawassuli da Matattu
A ra'ayin Ibn taimiyya baya halasta yin tawassuli da annabawa da waliyyan Allah bayan mutuwarsu, kuma yin haka aiki na bidi'a; a cewarsa babu wani sahabi ko wani magabaci da ya aikata haka, kuma babu dalili kan halascin aikata haka.[40] haka nan Muhammad ɗan Abdul-wahab wanda ya assasa firƙar wahabiyya.[41] cikin biyayya gare shi malaman wahabiyawa suka bidi'antar da shirkantar da yin tawassuli da annabawa da waliyyan Allah bayan mutuwarsu.[42]
Halascin Yin Tawassuli da Matattu a Mahangar Malaman Muslunci
Ita ma wannan mahanga ta samu daga malaman shi'a da ahlus-sunna. Muhammad ɗan Ali Shaukani (Wafati:1250.h.ƙ) malamin fiƙihu ɗan mazhabar zaidiyya, ya kafga hujja da da ijma'in sahabbai kan yin tawassuli da Annabi (s.a.w) lokacin da yake raye da bayan wafatinsa, ya ce babu wani sahabi da ya yi inkarin halascin wannan nau'in tawassuli.[43] haka nan Ahmad ƙasɗalani (Wafati:923.h.ƙ) masanin tarihi da hadisi ɗan mazhabar shafi'iyya daga ƙasar misra, ya ce ba a san adadin yawan hadisai da suka zo game da halascin yin tawassuli da Annabi (s.a.w) a lokacion rayuwarsa da bayan wafatinsa.[44] a cewar samhudi cikin yin tawassuli da Annabi (s.a.w) babu bambanci a lokacin rayuwarsa ne ko bayan wafatinsa.[45] ya yi ishara da wasu riwayoyi daga madogaran ahlus-sunna da suke nuna cewa sahabbai kan al'amura daban-daban sun yi tawassuli da Annabi (s.a.w) bayan wafatinsa.[46]
Jafar subhani, haƙiƙa sirar musulmai ta kasance kan haka kamar yanda suke tawassuli da kamun ƙafa da Annabi (s.a.w) lokacin da yake a raye haka suka kasane suna yi bayan wafatinsa.[47] Muhammad ɗan zahid kausari (Wafati:1371.h.ƙ) malamin a mazhabar hanafiyya ɗan ƙasar turkiyya, ya ce masu inkarin tawassuli da annabawa da salihan bayin Allahbayan wafatinsu, suna Imani ne da ƙarewar ruhi bayan mutuwa kuma suna inkarin ranar alƙiyama da rayuwar lahira.[48] sannan keɓance riwayoyin halascin tawassuli da iya lokacin rayuwar waɗanda ake kamun ƙafa da su ba komai bane sai jirkita waɗannan riwayoyi da kuma yin tawilinsu ba tare da dalili ba.[49]
Shirkantar Yin Tawassuli da Muƙami da Matsayin Annabi da Waliyyan Allah
Taƙiyyud-dini subki:
Tawassuli da neman agajin Annabi (s.a.w) aiki mai kyau kuma halastacce. Halascinsa da kyawuntarsa abu ne sananne a addinance, abu da ya kasance aiki annabawa da manzanni da kuma sirar magabata nagari da malaman addini dama dukkanin musulmai. Babu wani lokaci babu wani addini da ya hana yin haka, har zuwan Ibn taimiyya ya jefawa raunana mutane shubuha kan halascin tawassuli [Tsokaci 1] ya assasa sabuwar bidi'a da ba taɓa samunta a zamanin da ya gabata ba.
Tawasuuli da muƙami da matsayin Annabi (s.a.w) shi ne masu yin tawassuli su ce:
Ya Allah lallai ni ina tawassuli zuwa gareka don matsayin Muhammad (s.a.w) da alfarmarsa a wurinka ka biya min buƙatata.[51] Muhammad nasib rufa'I, daga wahabiyawa, yana kan ra'ayin cewa babu dalili kan halascin neman kusanci zuwa ga Allah ta hanyar riƙo da wasilar muƙami da alfarmar Manzon Allah (s.a.w) da waliyyan Allah, kuma babu wani daga cikin sahabbai da ya taɓa yin haka.[52] Abdul-aziz bin baz (Wafati:1270.h.ƙ) mufti na wahabiyawa ɗan ƙasar saudiyya shima yana ganin irin wannan nau'in tawassuli matsayin bidi'a da shirka ya kuma ba da fatawa kan haramcin yinsa.[53]
Suka Kan Mahangar Wahabiya Da Malaman Muslunci Suka Yi
Wannan mahanga ta samu suka daga malaman shi'a da ahlus-sunna. A ra'ayin samhudi yin tawassuli da muƙamin Annabi (s.a.w) da albarkar samuwarsa a wurin Allah, ta kasance sirar annabawa da magabata nagargaru a kowanne zamani, babu bambanci gabanin halittarsa ne ko bayan halittarsa koma bayan wafatinsa ya kasance.[54] shahabud-dini alusi (Wafati:1270.h.ƙ) malamin tafsiri ɗan shafi'iyya, shima ya kasance yana ganin halascin yin tawassuli da muƙami da matsayin Annabi (s.a.w) da salihan bayin Allah da suke da matsayi da muƙami.[55] Jafar subhani daga malaman shi'a yana cewa: tawassuli da matsayi da muƙamin annabawa da salihan bayin Allah baya nufin suna da wani haƙƙi na zatin kan Allah da ya zama lazimi ba da har za a lissafa hakan a shirka; bari dai dukkanin haƙƙi yana ta'allaƙuwa da Allah ne, shi kuma Allah ta fuskacin falala da karamcinsa ya yi kyautar wannan muƙami ga ba'arin bayinsa.[56]
Darul ifta misra, cikin amsa da suka bayar kan tawassuli da muƙami da matsayin Annabi (s.a.w) tare da jingina da aya ta 35 suratul ma'ida da aya ta 57 suratul isra'I da kuma ba'arin wasu riwayoyi sun ba da fatawa cewa babu bambanci tsakanin tawassuli da Annabi (s.a.w) da kuma tawassuli da muƙami da matsayinsa da na sauran annabawa, dukkaninsu suna daga halastattun abubuwa da shari'ance, halascin yinsu ya tabbata cikin kur'ani da sunna.[57]
Ittifaƙin Musulmai Kan Halascin Tawassuli Da Kur'ani da Sunayen Allah
Tawassuli da sunayen Allah da siffofinsa his ne kamar haka mai tawassuli ya ce:
Ya Allah lallai ni ina roƙonka da sunanka ya Allahu ya rahmanu ya rahimu, ka tseratar da mu daga wuta ya ubangiji.[58] an ce babu wani saɓani tsakanin musulmai cikin halascin wannan nau'in tawassuli.[59] cikin aya ta 80 suratul a'araf ubangiji ya ba da umarni da ake kira shi da kyawawan sunayen Allah.[60] haka kuma ance akwai tarin riwayoyi daga Annabi (s.a.w) da Imamai ma'asumai (a.s).[61] kan halascin wannan nau'in tawassuli.[62] tawasssuli da su.[63] haka kuma cikin wata riwaya an yi umarni da karanta wannan addu'a a dararen ƙadri.[64]
Tawassuli da Kur'ani
Tawassuli da Kur'ani shi ne mai tawassuli ya ce:
Ya Allah lallai ni ina roƙonka da littafinka saukakke da abin da yake cikinsa akwai sunanka mafi girma da kuma kyawawan sunayenka… ka sanya ni daga waɗanda kake ƴantar da su daga wuta.[65] cikin wasu ba'arin riwayoyi da suka zo a madogaran shi'a da ahlus-sunna.[66] tawassuli da kur'ani domin neman kusancin ubangiji ko neman wata buƙata daga gareshi abu ne da ya halasta.[67] haka nan cikin wata riwaya daga Imamai ma'asumai (a.s) an yi umarni cikin kamun ƙafa da kur'ani, a lokacin tarukan karatun kur'ani ta hanyar ɗora shi a ka a daren lailatul ƙadri.[68]
Tawassuli da kyawawan ayyuka shima ɗaya ne daga nau'ukan tawassuli.[69] cikin wata riwaya da aka naƙalto daga Imam Ali (a.s) haƙiƙa ayyuka misalin Imani da Allah da Annabi (s.a.w), yin jihadi da cikin tafarkin Alla, tsayar da sallah ba da zakka, azumi, hajji, sadar da zumunci da ba da sadaƙa suna cikin mafi alherin wasila da tsani zuwa ga Allah.[70] neman addu'a daga wani mutum da albarkar samuwarsa, fatan samun amsa addu'arsa suna daga sauran nau'ukan tawassuli da malamai suka halasta shi sakamakon dogara da ayoyin kur'ani da ba'arin riwayoyi.[71]
Nazari
Akwai tarin rubuce-rubuce da wallafe-wallafe da malaman muslunci suka yi kan mas'alar tawassuli, ba'arinsu sune kamar haka:
- At-Tawassul Mafhumuhu wa hukmuhu fish Ash-Shari'ati Al-Islamiyya Al-Garra: na Jafar subhani. Marubucin ya kawo dalilai daga kur'ani da riwayoyi kan halascin kowanne nau'i daga tawassuli tare da bincike da suka kan mahangar masu imkarin waɗannan nau'ukan tawassuli.[72]
- At-Ta'ammul fi haƙiƙatil At-Tawassul: na Isa bn Abdullahi Himyari, wannan littafi ya tattaro babuka guda biyu, marubucin ya yi bincike tare da suka kan dalilan masu inkarin tawassuli da kuma bayanin halascin tawassuli bisa la'akari da kur'ani da riwayoyi daga madogaran riwayoyin ahlus-sunna da kuma mahangar malamai.[73] sayyid murtada fadil ya tarjama wannan littafi zuwa harshen farisanci da sunan “Darangi dar haƙiƙat tawassul” muaɗabba'ar mash'ar ta buga shi.[74]
- Mahaƙul At-Taƙawwul fi mas'alati At-tawassul: na Muhammad zahid kausari (Wafati:1371:.h.ƙ) malami daga mazhabar hanafiyya kuma yana cikin mutanen da suka shahara da yin suka kan Ibn Taimiyya da tunanunnukan salafiyya. Marubcin ya yi bahasi cikin shafi 22 kan tabbatar da halascin tawassuli da istigasa tare da jingina da kur'ani da sunnar Annabi (s.a.w) da sirar sahabbai.[75]
Bayanin kula
- ↑ Subaki, Shifa al-Saqam, 1419 AH, shafi na 293.
- ↑ Ibn Taimiyyah, Ka'idatul Al-Jalila fi Al-Tawassil wa Al-Wasila, 1422H, shafi na 16.
- ↑ Subaki, Shifa' al-Saqam, 1419 AH, p. 318.
- ↑ Subhani, Al-Tawaussl ..., 1374, shafi na 18.
- ↑ Hamyairi, al-Taammul fi Haqiqa al-Tawassul, 1428 AH, shafi 48; Paktchi, 'Tosul', shafi na 362.
- ↑ Subaki, Shifa al-Saqam, 1419 AH, shafi na 59-61.
- ↑ Ma'amouri, 'Nakhde tawassul as suwe Salafiyyah', shafi na 367-368.
- ↑ Alizadeh, "Tawassuli dar tahaqquq tarikhi", shafi na 368.
- ↑ Alizadeh, "Tawassuli dar tahaqquq tarikhi", shafi na 369.
- ↑ Alizadeh, "Tawassuli dar tahaqquq tarikhi", shafi na 369.
- ↑ Alizadeh, "Tawassuli dar tahaqquq tarikhi", shafi na 369.
- ↑ Samani, Al-Ansab, 1382H, juzu'i na 12, shafi 479.
- ↑ Baghdadi, Tarikh Baghdad, vol. 1, shafi na 133.
- ↑ Al-Ka'bi, Al-Imam Musa ibn al-Kazim (A.S)), Sira wa Tarikh, 1430 A.H., shafi na 216.
- ↑ Al-Himyari, Al-Tamil fi Haqiqat al-Tawassul, 1428 A.H., shafi na 16.
- ↑ Johari, al-Sihahu Taj al-Lughab wa Sihah al-Arabiyya, a ƙarƙashin kalmar "wasl".
- ↑ Johari, al-Sihahu Taj al-Lughab wa Sihah al-Arabiyya, a ƙarƙashin kalmar "wasl".
- ↑ Sabki, Shifa al-Saqam, shafi na 314.
- ↑ Abdel-Rahman Abdel-Moneim, Mujam Al-Mustalahat wa Alfaz al-fikhiyya, Dar Al-Fadila, shafi na 150.
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, 1363, juzu'i na 5, shafi na 328; Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 11, shafi na 349.
- ↑ Sobhani, Manshur Javed, 1390, juzu'i na 7, shafi.412; Suratul Nisa'i, aya ta 64.
- ↑ Makarem Shirazi, Ayat al-Walaiya fi Qur'an, 1425 AH, 201.
- ↑ Suratul Yusuf, aya ta:97.
- ↑ Misali, duba Samhoudi, Wafaa al-Wafa Ba Akhbar Dar al-Mustafi, 1419 AH, juzu'i na 4, shafi na 196; Tirmizi, Sunan Tirmidhi, 1395 AH, juzu'i na 5, shafi 539; Sheikh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 AH, shafi 416; Sayyid Bin Tavus, Al-Iqbal, 1376, shafi na 177; Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 36, shafi na 15-21.
- ↑ ↑ Makarem Shirazi, Ayat al-Walaiya fi al-Qur'an, 1425 AH, shafi na 203.
- ↑ ↑ Subhani, al-Tawassul, shafi na 107.
- ↑ Bukhari, Sahihul Bukhari, 1422 AH, Juzu'i na 2, shafi na 26-32.
- ↑ Al-Himyari, Al-Taammil fi haqiqat al-Tawassul, 1428 A.H., shafi na 76.
- ↑ Subhani, al-Tawassul, shafi na 69.
- ↑ «حكم التوسل بالأنبياء والأولياء والصالحين وطلب المدد منهم»، سایت دار الإفتاء المصریة.
- ↑ Al-Himyari, Al-Tamil fi hakikat al-Tawassul, 1428 A.H., shafi na 48.
- ↑ Rifai, At-tawassul ila Haqiqatil Tawassuli, 1399H, shafi na 185.
- ↑ Rifai, At-tawassul ila Haqiqatil Tawassuli, 1399H, shafi na 186
- ↑ Subaki, Shifa al-Saqam, 1419 AH, shafi na 305.
- ↑ Samhudi, Wafa al-Wafa, 1419 AH, juzu'i na 4, shafi na 196.
- ↑ Sabki, Shifa Al-Saqam, shafi na 305; Samhudi, Wafa al-Wafa, 1419 AH, juzu'i na 4, shafi na 196.
- ↑ Bukhari, Sahihul Bukhari, 1422H, juzu'i na 2, shafi na 27.
- ↑ Misali, duba Qommi, Tafsirin Qommi, 1404 AH, Juzu'i na 1, shafi na 168; Bahrani, al-Barhan fi tafsirin al-kur'ani, 1415 AH, juzu'i na 2, shafi 292.
- ↑ Allameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 102, shafi na 247-249.
- ↑ Ibn Taimiyyah, Majmu'a Rasa'il wal al-m,asa'il, Kwamitin Tarihi na Larabawa, juzu'i na 1, shafi na 22-23.
- ↑ Abdul-Wahhab, Kashf al-Subhat, 1418 AH, shafi na 51-52.
- ↑ Misali, duba Ibn Baaz, al-Tawassul al-Mashruu wa tawassul al-Mamnu'u, 1428 AH, shafi na 35-36.
- ↑ Shoukani, Al-Dur al-Nazid, Dar Ibn Huzaimah, shafi na 200
- ↑ Qastlani, al-Muwahab al-Ladiniyyah, vol. 3, shafi na 606.
- ↑ Samhudi, Wafa al-Wafa, 1419 AH, juzu'i na 4, shafi na 195.
- ↑ Samhudi, Wafa al-Wafa, 1419 BC, juzu'i na 4, shafi na 195-196.
- ↑ Al-Tawassal - Al-Tosal 1374, p. 52.
- ↑ Kothari, Mahaqul At-taqawwuli fi mas'alatil tawassuli, Laburaren Tarihi na Al-Azhari, shafi na 4.
- ↑ Kothari, Mahaqul At-taqawwuli fi mas'alatil tawassuli, Laburaren Tarihi na Al-Azhari, shafi na 5.
- ↑ Subaki, Shifa al-Saqam, shafi na 293.
- ↑ Sobhani, Ayineh Wahabiyat, 1375, shafi na 146
- ↑ Rifai, Al-tawassul ila haqiqatil Tawassul, 1399 Hijira, shafi na 188-189.
- ↑ Ibn Baz, Majmoo' Fataawa Ibn Baz, vol. 5, shafi 322.
- ↑ Samhoudi, Wafa al-Wafa, 1419 A.C., vol. 4, p. 193.
- ↑ Alusi, Tafsir Ruh al-Ma'ani, vol. 6, shafi na 128.
- ↑ Sobhani, Al-Tawassul, mafhumuhu wa aksamuhu wa hukmuhu fish shari'a al-islmaiyya al-garra, 1374, shafi na 82.
- ↑ «حکم التوسل بالأنبیاء والأولیاء والصالحین وطلب المدد منهم»، سایت دار الإفتاء المصریة.
- ↑ Al-Kaf'ami, al-Misbah, 1409 A.H., shafi na 247;
- ↑ Sobhani, Al-Tawassul..., 1374, shafi na 24; Himyari, al-Taammul fi Haqiqa al-Tawassul, 1428 AH, shafi 44.
- ↑ Subhani, Al-Tawassul..., 1374H, shafi na 22; Albani, Tawassuli, anwa'ihi a ahkamihi, 1421 Q.H. shafi na 30.
- ↑ Alal misali, ka duba al-Tirmidhi, Sunan al-Tirmidhi, vol. 5, shafi na 539, al-Shaykh al-Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 A.H., shafi na 416, da Kuma
- ↑ Sobhani, Al-Tawassul..., 1374, shafi na 22; Hamiri, al-Taammul fi Haqiqa al-Tawassul, 1428 AH, shafi 44.
- ↑ Al-Kafa'mi, al-Misbah, 1409/1999, shafi na 247.
- ↑ Alal misali, ka duba Allameh Majlisi, Zad al-Ma'ad, 1423 A.H., shafi na 27.↑
- ↑ Sayyid bin Tawus, Al-Iqbal, 1376H, juzu'i na 1, shafi na 346.
- ↑ Misali, duba Ibn Hanbal, Musnad Ahmad, 1421, Juzu'i na 33, shafi na 146; Seyed Bin Tavus, Al-Iqbal, 1376, juzu'i na 1, shafi na 346.
- ↑ Subhani, Al-Tawassul..., 1374, shafi na 25-26.
- ↑ Alal misali, ka duba al-Shaykh al-Mufid, al-Muqna'a, 1413 A.H., shafi na 190.
- ↑ Misali, duba Sobhani, Al-Tawassul..., 1374, shafi na 27-32 da 39; Himyari, al-Taflam fi Haqiqah al-Tawassul, 1428 AH, shafi na 45-48.
- ↑ Misali, duba Nahj al-Balagheh, Tashihu Sobhi Saleh, 1374, Khutbah 110, shafi na 163.
- ↑ Misali, duba Sobhani, Al-Tawassul..., 1374, shafi na 27-32 da 39; Himyari, al-Taammul fi Haqiqah al-Tasl, 1428 AH, shafi na 45-48.
- ↑ Subhani, Al-Tawassul..., 1374, shafi na 117.
- ↑ Al-Himyari, Al-Tamil fi haqiqatil al-Tawassul, 1428 A.H., shafi na 8-11.
- ↑ Himyari, Darangi dar Haqeeq Tawassul, 2013, shafi na 13.
- ↑ Kawthari, Mahaqul At-taqawwuli fi mas'lati at-tawassuli, Al-Azhar Heritage Library, shafi na 4-11.
Tsokaci
- ↑ Ibn Taimiyyah ya rubuta littafi mai suna “Ka'idatul Al-jalila fi Tawassuli wa Wasila,” tawassuli ya rabu gida uku: Ma'anar tawassul shi ne kusantar ubanguiji ta hanyar tsanantuwa da i biyayyarsa. wannan wani nau'i ne na tawassuli yana ganinsa asalinsa addini. kuma babu wani musulmi da yake inkarinsa. Ya roke shi akan addu'ar Annabi (SAW) a lokacin rayuwarsa, da cetonsa a ranar lahira. yana wani imani wannan nau'in tawassuli an same shi daga sahabbai, tawassuli da zatin Annabi(s.a.w) da neman wani abu. hakika ibn taimiyya yana ganin haramcin nau'in wannan tawassuli, yana raya cewa babu wani sahabi da aikata haka,(ibn taimiyya qa'ida jalila fi tawassul wal wasila,1422.1 shafina na 87-88
Nassoshi
- Alousi, Mahmoud bin Abdullah, Tafsirin Ruh al-Ma'ani, Beirut, Darul Katb al-Alamiya, 1415H.
- Ibn Baaz, Abdul Aziz, Al-Tawsal al-Mashru'u wa Tawassl al-Mamunoo, Riyadh, Bina, 1428H.
- Ibn Baaz, Abd al-Aziz, Fatawi Ibn Baaz, Riyadh, Darul Qasim Publishing House, 1420H.
- Ibn Taimiyyah, Taqi al-Din Abu al-Abbas, Al-Qa'ad al-Jalila fi al-Tawassul wal al-Wasilah, Bija, Mazhabar Al-Furqan, bugu na farko, 1422H.
- Ibn Taimiyyah, Taqi al-Din Abu al-Abbas, Majmu Al-Rasa'illi wal al-Masail, Bija, Al-Tarath al-Arabi Committee, Bita.
- Albani, Muhammad Naser al-Din, Al-Tawassul, anwa'uhu wa ahkamuhu, Riyadh, Mazhabar Al-Maarif, 1421H.
- Bahrani, Hashim bin Suleiman, al-Barhan fi Tafsir Qur'an, Qum, Ba'ath Foundation, 1415H.
- Bukhari, Muhammad bin Ismail, Sahih Bukhari, Damascus, Dar Tawq al-Najah, 1422H.
- Bin Hanbal, Ahmad bin Muhammad, Musnad Ahmad, Alkahira, Darul Hadith, 1421H.
- Paktchi, Ahmed, "Tusul", Big Islamic Encyclopaedia,
- Tirmizi, Muhammad bin Isa, Sunan Tirmidhi, Egypt, Mustafa Al-Babi Al-Halabi School and Press Company, 1395 AH.
- Taghi al-Din Subki, Ali bin Abdulkafi, Shifa al-Saqam fi Ziyarat Khair al-Anam, bincike na Seyyed Mohammad Reza Jalali, Qum, Mashaar Publishing House, bugu na 4, 1419H.
- Johari, Abu Nasr Ismail bin Hamad, Sahaha Taj al-Lagha da Sahaha al-Arabiyyah, Beirut, Dar al-Alam Lalmayain, bugu na 4, 1407H.
- Himyari, Isa bin Abdullah, al-Taammul fi Haqiqa al-Tawassil, Bija, Binna, 1428H.
- Taghi al-Din Subki, Ali bin Abdulkafi, Shifa al-Saqam fi Ziyarat Khair al-Anam, bincike na Seyyed Mohammad Reza Jalali, Qum, Mashaar Publishing House, bugu na 4, 1419H.
- Johari, Abu Nasr Ismail bin Hamad, Sahaha Taj al-Lagha da Sahaha al-Arabiyyah, Beirut, Dar al-Alam Lalmayain, bugu na 4, 1407H.
- Himyari, Isa bin Abdullah, al-Taammul fi Haqiqa al-Tawassil, Bija, Binna, 1428H.
Sobhani, Jafar, Ayaineh Wahabiyat, Tehran, Mashaar Publishing House, 1375.
- Sobhani, Jafar, Al-Tawassul, Mafhumuhu, Aqsamahu, wa hukumuhu fi shari'ati algarra, Qum, Madba'a ta Mashaar, 1374.
- Sobhani, Jafar, Al-Towassul, Beirut, Al-Dar al-Islamiya, Bita.
- Sobhani, Jafar, Manshur Javid, Qum, Cibiyar Imam Sadiq (AS), 1390.
- Samhoudi, Ali bin Abdullah, Wafaa al-Wafa in Akhbar Dar al-Mustafa, Beirut, Dar al-Katb al-Alamiya, 1419 AH.
- Seyd bin Tawoos, Ali bin Musa, Al-Iqbal Bal amal al-Hasannah, Qum, ofishin yada farfagandar Musulunci, bugu na farko, 1376.
- Shokani, Muhammad bin Ali, Al-Dar al-Nazid Fi Ikhlas Kalma al-Tawhid, Bija, Dar Ibn Hazimah, Bita.
- Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Misbah al-Mutahajjid, Beirut, Shi'a Fiqh Foundation, 1411 AH.
- Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Maqna'a, Qum, Sheikh Mofid's World Hazara Congress, 1413H.
- Tabatabaei, Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Qom, Ismailian Publishing House, 1363.
- Abd al-Moneim, Mahmoud Abd al-Rahman, Maajim al-Thirdim al-Alfaz al-Fiqhiyyah, Cairo, Dar al-Fadilah, Bita.
- Abd al-Wahab, Muhammad, Kashf al-Shabhat, Arabia, Ministry of Islamic Affairs, Endowments, Da'awah and Guidance, bugun farko, 1418 AH.
- Allameh Majlisi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, Beirut, Al-Wafa Foundation, 1403 AH.
- Allameh Majlisi, Mohammad Baqer, Zad al-Maad, Beirut, Al-Alami Institute for Press, 1423 AH.
- Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, al-Tafsir al-Kabir, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1420H.
- Qastlani, Ahmad bin Muhammad, Al-Mawahab al-Ladunniya a Meneh al-Muhammadiya, Beirut, Al-Maktab al-Islami, 1425H.
- Qommi, Ali Ibn Ibrahim, Tafsir Qommi, Qum, Darul Katab, bugu na uku, 1404H.
- Kafami, Ibrahim bin Ali, al-Misbah, Janna al-Aman al-Waqiyyah da Janna al-Iman al-Baqiyyah, Kum, Darul-Razi, 1405H.
- Kothari, Mohammad Zahid, Muhaq al-Taqqul fi Masala al-Tawassil, Alkahira, Al-Maktab Al-Azhari Laltrath, Bita.
- Ma'amouri, "Nakhade Tawassul az suye Salafiyyah", Big Islamic Encyclopaedia,
- Makaram Shirazi, Nasser, Ayat al-Walaiya fi Qur'an, Qum, Imam Ali Ibn Abi Talib (a.s.) makaranta, 1425H.
- Nahj al-Balagheh, Tashihu Sobhi Saleh, Qum, Cibiyar Nazarin Musulunci, 1374 ya gyara.