Babul Al-Hawa'iji (Laƙabi)

Daga wikishia
(an turo daga Babul hawa'iji)

Babul Al-Hawa’iji, (arabic: باب الحوائج) mutumin da ake samun biyan buƙata ta hanyar kamun ƙafa da shi, Babul Al-Hawa’iji ɗaya ne daga cikin laƙubban Imam Kazim (A.S), Hazrat Abbas (A.S) da Ali Asgar (A.S) saboda wasu ba’arin ƴan Shi’a sun yi imani da cewa ana samun biyan buƙata cikin yin tawassuli da kamun ƙafa da waɗannan mutane guda uku.

Babul Al-Hawa’iji Laƙabin Wanene?

Babul Al-Hawa’iji a A cikin gamammiyar al’adar ƴan Shi’a laƙabi ne na Imam Musa Bn Jafar (A.S) Imami na bakwai, [1] Abbas bn Ali (A.S) daga Shahidan waƙi’ar karbala, [2] da Ali Asgar ɗan Imam Husaini (A.S) wanda shima ya yi shahada a filin Karbala, [3] Muhammad Ali Ardubadi wanda ya rasu shekarar 1380 h ƙamari, cikin littafin Hayatu Abil Fadli Al-Abbas ya yi bayani ƙarara kan shaharar wannan laƙabi ga Hazrat Abbas (A.S) [4] Mujtaba Tehrani Mujtahidul Shi’a, ya ce ƙari kan waɗannan mutane guda uku ana amfani da wannan laƙabi kan Ruƙayya ƴar Imam Husaini (A.S) [5] Babul Al-Hawa’iji ma’ana ƙofar buƙata, kinaya ce zuwa ƙofar da ake samun biyan buƙatu. [6]

Menene Yasa Ake Yi Wa Imam Kazim (A.S) Laƙabi Da Babul Al-Hawa’iji

Amfani da Babul Al-Hawa’iji kan Imami na bakwai ba shi da asali daga hadisi, bisa bayanin Ibn Shahre Ashub wanda ya rasu shekara 588 h ƙamari, cikin littafin Al-manaƙib Ale Abi ɗalib bayan binne Imam Kazim (A.S) a maƙabartar ƙuraishawa a Bagdad an canja sunan ɗaya daga ƙofofin shiga Maƙabarta wacce ake kira da ƙofar Tinu zuwa sunan Babu Al-Hawa’iji, [7] haka kuma a cewar Ibn Hajar Haitami wanda ya rasu shekarar 974 h ƙamari, daga Malaman Ahlus-sunna, Imam Kazim (A.S) a wurin mutanen ƙasar Iraƙi ya shahara da laƙabin babul Al-Hawa’iji, [8] wanda ake samun biyan buƙata cikin yin tawassuli da shi, [9] a rubutun Da’iratul Al-Ma’rif Tashayyu, Ahlus-sunna da Shi’a suna ziyartar ƙabarin Imam Kazim (A.S) suna tawassuli tare da kamun ƙafa da shi domin samun biyan buƙatunsu. [10]

Bayanin kula

  1. Dehkhoda, Luggatnameh, Zailu Kalmeh"Bab al-Hawaij".
  2. Dehkhoda, Luggatnameh, Zailu Kalmeh"Bab al-Hawaij".
  3. Muhaddi, Farhang Ashura, 2008, shafi na 348.
  4. Urdubadi, Hayat Abi Al-Fazl al-Abbas, 1436 AH, shafi na 133.
  5. ذکر توسل حضرت رقیه(س)، مؤسسه پژوهشی فرهنگی مصابیح الهدی.
  6. Anuri, Farhang Sokhon, 2013, shafi na 705.
  7. Ibn Shahr Ashub, Manaƙib Al Abi Talib, 1376 Hijira, Mujalladi na 3, shafi na 438.
  8. Ibn Hajjar Haytami, Al-Sawai'ƙ al-Muhriƙa, Makarantar Alkahira, shafi na 203.
  9. Shablanji, Noor Al-Absar, Al-Sharif Al-Radhi, shafi na 331.
  10. Shahidi, "Bab Al-Hawaij", shafi na 11.

Nassoshi

  • *ذکر توسل حضرت رقیه(س)، مؤسسه پژوهشی فرهنگی
  • Anuri, Hassan, Farhang Bozor Sokhon, Tehran, Sokhon Publications, 2013.
  • Dehkhoda, Ali Akbar,Luggatnameh.
  • Ibn Hajr Hitami, al-Sawa'iƙ al-Muhriƙa fi Raddi Ala Ahle Albida'i wal Al-zandaƙa, Alkahira, Bita.
  • Ibnshahrashob, Muhammad Bin Ali, Manaƙib Al Abi Talib, Najaf, Al-Haydriya Press, 1376H.
  • Mohaddisi, Javad, Farhang Ashura, ƙom, Ma'oruf Publishing House, 2008.
  • Shablanji, Momin bin Hasan, Noor Al-Absar fi Manaƙib Al-Bayt al-Nabi al-Mukhtar, Allah ya jiƙansa, ƙum, al-Sharif al-Radhi, Bita.
  • Shahidi, Abdul Hossein, "Bab al-Hawaij", in Shi'i Al-Ma'arf, juzu'i na 3, Tehran, Hekmat Publications, 2013.
  • Urdubadi, Muhammad Ali, Hayatu Abi Al-Fazl Al-Abbas, dar Mausu'ati Allama al-Urdbadi, Dar al-Kafil, Karbala, 1436H.