Ayar Khairul Bariyya
| bayanan aya | |
|---|---|
| sunan aya | َAyar Kahirul Bariyya |
| akwai shi cikin sura | Bayyina |
| lambar aya | 7 |
| juzu’i | 30 |
| bayanan abin da yake ciki | |
| wurin sauka | Madina |
| maudu’i | Aƙida |
| game da | Girmamar matsayin Imam Ali (A.S) da Shi'a |
Ayar khairul bariyya, (Larabci: سورة البينة) bayyina aya ta 7, tana daga cikin ayoyi da suka sauka game da sha'anin Imam Ali (A.S). kan asasin wata riwaya da ta zo a madogaran Shi'a da Ahlus-Sunna da aka naƙalto daga Annabi (S.A.W) ma'anar jumlar "Khairul bariyya" shi ne mafi alherin halittu, sune Imam Ali (A.S) da mabiyansa.
Ba'arin malaman tafsiri sun fitar da natija daga wannan aya da cewa mutanen da suka kasance daga muminai da salihai suna da fifiko hatta kan mala'iku, saboda kalmar "Albariyya" tana tattaro dukkanin halittu.
Aya Da Tarjama
Aya ta bakwai suratul Bayyina aya ce da ta shahara da ayar Khairul bariyya.[1]
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أُولَئِكَ هُمْ خَيْرُ الْبَرِيَّةِ
Lalle ne waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan nagari, su ne mafi alherin halittu.
(Quran: Bayyina: Aya ta 7)
Matsayi Da Muhimmanci
Samfuri:Ƙuote box Ayar khiarul bariyya ana lissafa ta cikin falalar Imam Ali (A.S).[2] An naƙalto daga Ibn Abbas cewa wannan aya ta sauka ne game da Imam Ali (A.S).[3] A faɗin malaman Shi'a, Imam Ali (A.S) a lokacin zaman kwamitin shura mai mutum shida domin ayyana magajin Umar ya kafa hujja da wannan aya kan gaskiya da cancantuwa da halifanci da kuma cewa sha'anin saukar ayar ta ya kasance game da Imam Ali (A.S).[4]
Ayatullahi Makarim Shirazi (Haihuwa:1926m), daga cikin shahararrun malaman tafsiri na Shi'a, tare da jingina da wata riwaya daga Annabi da take magana kan sha'anin saukar wannan aya cikinta an yi magana game da Alah da mabiyansa,[5] Malamin ya ce kalmar Shi'a tun lokacin Annabi (S.A.W) aka fara bijiro da ita, kuma abin nufi daga Shi'a a cikin wannan riwaya, sune wasu keɓantattun mabiyan Imam Ali (A.S).[6]
Ma'anar Khairul Bariyya
Cikin litattafan riwaya na Shi'a da Ahlus-Sunna, akwai hadisai da aka naƙalto daga Annabi (S.A.W) wanda cikinsu aka fassara khairul bariyya (Mafi alherin halittu) a matsayin Imam Ali (A.S) da ƴanshi'arsa[7] Hakim Haskani (Rasuwa: 490H) daga malaman Ahlus-Sunna, a cikin littafin Shawahidut Tanzil ya kawo fiye da riwayoyi 20 tare da mabambantan sanadi.[8] Daga cikin ya naƙalto daga Ibn Abbas cewa a lokacin da wannan aya ta sauka Annabi (S.A.W) ya cewa Imam Ali (A.S) kai da ƴanshi'arka ku ne mafi alherin halittu. A ranar alƙiyama kai da ƴanshi'arka zaku zo cikin halin farin ciki da yarda Allah kuma yardaddu.[9]
Gaɓoɓin Tafsiri
Daga cikin gaɓoɓin tafsiri masu jan hankali da malaman tafsiri suka fitar da natijoji daga gare su, shi ne cewa mutane masu imani kuma salihai suna da fifiko hatta kan mala'iku, saboda kalmar “Albariyya” cikin jumlar khairul bariyya (Mafi alherin halittu) ta haɗa da dukkanin halittu.[10]
Saukar Wannan Aya A Makka
Kan Asasin ba'arin riwayoyi, ayar khairul bariyya ta sauka ne a lokacin da Annabi yake a Makka a cikin masallacin harami.[11] Bisa abin da ya zo a littafin tafsirin Al-Amsal, wannan mas'ala ba ta cin karo tare da kasancer saukar ayar a Madina, saboda zai iya yiwuwa surar ta sauka ne a Madina ita kuma wannan aya ta sauka ne cikin tafiye-tafiyen da Annabi (S.A.W) ya yi daga Madina zuwa Makka.[12]
Bayanin kula
- ↑ Allama Hilli, Nahj al-Haƙƙ, 1402ƙ, S 189.
- ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Numune, 1374Sh, J 27, S 213.
- ↑ Nagah kunid be Haskani, Shawahid al-Tanzil, 1410-1411ƙ, J2, S473; Shushtari, Ihƙaƙ al-Haƙƙ, 1409ƙ, J 20, S 27.
- ↑ Tabari, al-Mustarshid, 1415ƙ, S354; Istarabadi, Ta’wil al-Ayat al-Zahira, 1409ƙ, S 803.
- ↑ Suyuti, al-Durr al-Manthur, 1404ƙ, J 8, S 589; Amini, al-Ghadir, 1416ƙ, J2, S57 wa 58.
- ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Numune, 1374Sh, J 27, S 213-214.
- ↑ Suyuti, al-Durr al-Manthur, 1404ƙ, J6, S379; Istarabadi, Ta’wil al-Ayat al-Zahira, 1409ƙ, S80-803; Alusi, Ruh al-Ma’ani, 1415ƙ, J 15, S 432
- ↑ Ku duba: Haskani, Shawahid al-Tanzil, 1410-1411ƙ, J 2, S 459-473.
- ↑ Haskani, Shawahid al-Tanzil, 1410-1411ƙ, J 2, S 461.
- ↑ Tabataba’i, al-Mizan, 1417ƙ, J 20, S3 40; Makarim Shirazi, Tafsir Numune, 1374Sh, J27, S209.
- ↑ Haskani, Shawahid al-Tanzil, 1410-1411ƙ, J 2, S 467.
- ↑ Nagah kunid be Makarim Shirazi, Tafsir Numune, 1374Sh, J27, S212.
Nassoshi
- Alusi, Mahmoud bn Abdullahi, Ruhul Ma’ani fi Tafsirin Alkur’ani Al’azim da Sab’ul Mathani, bincike Ali Abdulbari Atiyya, Beirut, Mawallafar Darul Kutubul Ilimiyya, Muhammad Ali Baydun, 1415ƙ.
- Ibn Asakir, Tarikh Dimashƙ, bincike Amru bn Ghurama Al-Umrawi, Beirut, Mawallafar Darul Fikr, 1415ƙ.
- Istarabadi, Sayyid Ali, Ta’wilul Ayatis Zahira fi Fadailil ‘Itratit Tahira, Nazari Husain Ustaduli, Ƙum, Mawallafar yaɗa Musulunci, 1409ƙ.
- Amini, Abdulhusain, Al-Ghadir fi Al-Kitab was Sunnah wal Adab, Ƙum, Cibiyar Ghadirdomin nazarin Musulunci, 1416ƙ.
- Haskani, Ubaidullah bn Abdullahi, Shawahidut Tanzil li ƙawa’idut Tafsil fi Al-Ayatin Nazila fi Ahlul Bayt, bincike Muhammad Baƙir Mahmudi, Beirut, Tehran, Ma'aikatar sakafa da shiryarwar Musulunci, 1410–1411ƙ.
- Suyuti, Abdurrahman bn Abi Bakr, Mawallafar Ad-Durrul Manthur fi Tafsiril Ma’thur, Ƙum, Ofishin Mar’ashi Najafi, 1404ƙ.
- Shushtari, ƙadi Nurullah, Ihƙaƙ al-Haƙƙi wa Izhaƙ al-Batil, Ƙum, Ofishin Ayatullah al-Mar’ashi Najafi, 1409ƙ.
- Tabataba’i, Sayyid Muhammad Husain, Al-Mizan fi Tafsiril ƙur’an, Ƙum, Mawallafar Islami, 1417ƙ.
- Tabari, Muhammad bn Jarir, Al-Mustarshid fi Imamat Ali bn Abi Talib (AS), gyara Ahmad Mahmudi, Ƙum, Mawallafar Kushanpur, 1415ƙ.
- Allama Hilli, Hasan bn Yusuf, Nahjul Haƙƙ wa Kashful Sidƙ, Beirut, Darul Kitab al-Lubnani, 1402ƙ.
- Makarem Shirazi, Naser, Tafsir Namune, Tehran, wallafar Darul Kutubul Islamiyya, 1374Sh.
Sadarwa Ta Waje
- Babban Dandalin Ilimomin Dan AdamInsaniشیعه در قرآن؛ تفسیر آیه هفت سوره بینه از منظر فریقین