Iyyaka Na'abudu Wa Iyyaka Nasta'in
| bayanan aya | |
|---|---|
| akwai shi cikin sura | Suratul Hamdi |
| lambar aya | 5 |
| bayanan abin da yake ciki | |
| wurin sauka | Makka |
Iyyaka Na'abudu Wa Iyyaka Nasta'in, aya ta biyar cikin Suratul Hamdi, aya ce da take bayanin bauta da neman taimako daga Allah, malaman tafsiri suna cewa An kalli wannan ayar a matsayin mai nuni ga tauhidi na ibada da na ayyuka, da kuma korewar jabru da tafwiz. Daga cikin sauran batutuwan tafsiri na ayar akwai canza salon magana daga siffanta Allah zuwa yin magana da shi kai tsaye, da ma'anar amfani da sigar jam'i a cikin kalmomin «نعبد» (muna bauta wa) da «نستعین» (muna neman taimako). A wasu addu'o'i da sallolin mustahabbi, ciki har da Sallar Imam Zaman, an shawarci a karanta da maimaita wannan ayar.
Gabatarwa
Cikin ayar "Iyyaka Na'abudu Wa Iyyaka Nasta'i", salon magana ya canza daga siffanta Allah zuwa yin magana da shi kai tsaye. A cikin ayoyin da suka gabata, an bayyana Allah da siffofi kamar Ubangijin halittu, Mai rahama, Mai jin ƙai, da Mai mallakar ranar sakamako. Amma a wannan ayar, an juya daga bayanin game da shi zuwa yin magana da shi kai tsaye da kalmomin "Kai" (Iyyaka).[1] Abdullahi Jawadi Amoli, yana ɗaukar wannan canja salon magana matsayin alama da take nuna bawa ya kai ga matakin yin magana da Allah bayan sanin siffofinsa a cikin ayoyin da suka gabata.[2]
Allama Ɗabaɗaba'i yana ɗaukar lafazin «إِيَّاكَ نَعْبُدُ» matsayin mai bayanin bautar mutum da ɗamfaruwarsa da Allah haka kuma lafazin «وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ» mai bayyana buƙatuwar mutum ga taimakon Allah hatta a cikin ibada.[3] A cewarsa yin magana da Allah kai tsaye yana nuni ga wajabcin mai da hankali da kasancewar zuciya a cikin ibada.[4]
Karanta Wannan Aya Domin Kawar Da Damuwa
A cikin wasu addu'o'i da sallolin musthabbi, an yi umarni da karanta "Iyyaka Na'abudu Wa Iyyaka Nasta'in" domin biyan buƙata da kawar da damuwa.[5] Haka kuma cikin Sallar Imam Zaman, an ba da shawarar maimaita wannan aya sau ɗari a kowace raka'a idan aka kai gare ta a cikin Suratul Fatiha.[6]
A cikin ruwayar da aka naƙalto daga Imam Ali (A.S) ya kasance kafin fara yaƙi yana karanta addu'a wacce wannan aya ta kasance sashe daga cikinta[7] Haka kuma, a cikin wata ruwaya game da wasu yaƙe-yaƙen Annabi (S.A.W), ya zo cewa idan yaƙi ya tsananta, ta hanyar karanta zikiri «یا مالک یوم الدین، إیاک نعبد و إیاک نستعین» (Ya Mamallakin Ranar Sakamako, Kai kaɗai muke bautawa, kuma Kai kaɗai muke neman taimako), mala'iku suna zuwa don taimaka wa Annabi (S.A.W), kuma Musulmi sukan yi nasara a kan maƙiyansu.[8]
A wasu madogaran hadisai kuma, ya zo cewa wata rana Imam Sadiƙ (A.S) ya riƙa maimaita wata aya daga Alƙur'ani a cikin sallarsa har ya suma. Da ya farfaɗo, aka tambaye shi dalilin faruwar hakan, sai ya ce: Na ci gaba da maimaita ayar har na ji ta daga bakin Wanda Ya faɗe ta[9]Ƙazi Sa'id Ƙummi, bisa dogaro da wasu hujjoji, ya bayyana cewa ayar da ake nufi ita ce: "Iyyaka Na'abudu Wa Iyyaka Nasta'in".[10]
Shiryarwar Wannan Aya Zuwa Ga Tauhidi Na Ibada Da Na Aiki
Malaman tafsiri lafazin «إِيَّاكَ نَعْبُدُ» yana bayani kan tauhidi na ibada, ma'ana keɓantuwar ibada ga Allah shi kaɗai, haka lafazin «إِيَّاكَ نَسْتَعِينُ» yana bayani ga keɓance ikon yin tasiri mai zaman kansa ga Allah kaɗai.[11]
A cikin ayar wakilin suna na «ایاک» ya zo kafin fi'ili (Aiki). malaman tafsiri suna ɗaukar wannan jeri matsayin alama da ke tabbatar da keɓantuwar bauta da taimako ga Allah[12] Maimaita wannan wakilin suna kafin kowane ɗaya daga cikin fi'ili biyun yana nuna ƙarfafa wannan ma'ana.[13] Allama Ɗabaɗaba'i yana ganin cewa gabatar da Maf'ul (abin da ake aikatawa a kansa) kafin fi'ili, da kuma rashin ambaton wani sharaɗi ko takamaiman yanayi na ibada, suna nuna cewa bautar ta keɓanta ga Allah shi kaɗai, kuma mallaka ta haƙiƙa nasa ne shi kaɗai. [14]
A cikin wata ruwaya daga Imam Rida (A.S), an fassara kalmar «إِيَّاكَ نَعْبُدُ» (Kai kaɗai muke bautawa) da cewa tana bayyana tsarkake niyya wajen ibada da neman kusanci ga Allah. Amma kalmar «إِيَّاكَ نَسْتَعِينُ» (Kai kaɗai muke neman taimako) tana nufin roƙon Allah Ya ba mu ikon yin ibada da kuma neman taimakonsa.[15] A cewar wasu malaman tafsiri, keɓance neman taimako ga Allah ba ya saɓa wa neman taimakon wasu mutane ko yin tawassuli; domin neman irin wannan taimako ba yana nufin ɗaukar wasu a matsayin masu tasiri da kansu, ba tare da dogaro ga Allah ba.[16]
Nuna Rashin Ingancin Aƙidar Da Kuma Barin Mutum Ya Yi Komai Da Kansa
A cewar Abdullahi Jawadi Amoli, aya ta biyar a cikin Suratul Fatiha tana nuna rashin ingancin aƙidar tilastawa (Jabr) da kuma aƙidar barin mutum ya gudanar da al'amuransa da kansa ba tare da dogaro ga Allah ba (Tafwizd).
Dalili kuwa shi ne, kalmar «إِيَّاكَ نَعْبُدُ» (Kai kaɗai muke bautawa) tana nuna cewa mutum yana da zaɓi da ikon yin ibada, yayin da kalmar «إِيَّاكَ نَسْتَعِينُ» (Kai kaɗai muke neman taimako) take nuna cewa mutum yana dogaro da taimakon Allah.
Saboda haka, mutum ba abin tilastawa kawai ba ne, kuma ba ya wadatuwa da kansa wajen gudanar da ayyukansa har ya zama ba ya buƙatar taimakon Allah.[17] A cikin wata ruwaya kuma, Imam Sadiƙ (A.S) ya kafa hujja da wannan aya wajen bayyana rashin ingancin aƙidar barin mutum ya gudanar da al'amuransa gaba ɗaya da kansa, ba tare da dogaro ga Allah ba.[18]
Ma'anar Amfani Da Sigar Jam'i A Cikin Aya
A cikin aya ta biyar ta Suratul Fatiha, an yi amfani da kalmomin "muna bautawa" da "muna neman taimako" a sigar jam'i. Allama Ɗabaɗaba'i ya bayyana cewa amfani da sigar jam'i yana nuna nisantar son kai da ɗaukar kai a matsayin na musamman.[19]
Makarim Shirazi ya danganta amfani da sigar jam'i da kasancewar ibada aiki ne na gama-gari.[20] Muhsin Ƙara'ati kuwa ya danganta shi da sallar jam'i.[21]
Wasu masu bincike kuma sun danganta amfani da sigar jam'i a cikin kalmar ibada da yin ibada tare da waliyyan Allah, domin ibadar mutum shi kaɗai ba ta kai cikakkiyar cancantar bautar Allah ba.[22]
Bayanin kula
- ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Namuna, juzu'i na 1, shafi na 42.
- ↑ Jawadi Amoli, Tafsir Tasnim, juzu'i na 1, shafi na 416.
- ↑ Ɗabaɗaba'i, Almizan, juzu'i na 1, shafi na 26.
- ↑ Ɗabaɗaba'i, Almizan, juzu'i na 1, shafi na 26.
- ↑ Misali ku duba: Ɗabrisi, Makarim Akhlaƙ, juzu'i na 1, shafi na 325 da 352; Sayyid Ibn Ɗawus, Jamalul Usbu, shafi na 125.
- ↑ Sayyid Ibn Ɗawus, Muhajud Da'awat, shafi na 294, Ƙummi, Mafatihul Jinan, shafi na 94 da 786 da 790.
- ↑ Nasru Bin Muzahim, Waƙ'atu Siffin, shafi na 230.
- ↑ Abu Nu'aim, Dala'ilun Nubuwwa, juzu'i na 2, shafi na 460.
- ↑ Sayyid Ibn Ɗawus, Falahus Sa'il, shafi na 107 da 108.
- ↑ Ƙazi Sa'id Ƙummi, Asrarul Ibadat, shafi na 61.
- ↑ Misali ku duba, Makarim Shirazi, Tafsir Namuna, juzu'i na 1, shafi na 42 da 43.
- ↑ Sharif Kashani, Zubdatut Tafsir, juzu'i na 1, shafi na 29; Jawadi Amoli, Tafsir Tasnim, juzu'i na 1, shafi na 421; Makarim Shirazi, Tafsir Namuna, juzu'i na 1, shafi na 43.
- ↑ Jawadi Amoli, Tafsir Tasnim, juzu'i na 1, shafi na 420.
- ↑ Ɗabaɗaba'i, Almizan, juzu'i na 1, shafi na 25.
- ↑ Shaik Ɗusi, Man La Yahduruhul Faƙihu, juzu'i na 1, shafi na 310.
- ↑ Jawadi Amoli, Tafsir Tasnim, juzu'i na 1, shafi na 446; Makarim Shirazi, Tafsir Namuna, juzu'i na 4, shafi na 364-366.
- ↑ Jawadi Amoli, Tafsir Tasnin, juzu'i na 1, shafi na 455.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i na 89, shafi na 239.
- ↑ Ɗabaɗaba'i, Almizan, juzu'i na 1, shafi na 26.
- ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Namuna, juzu'i na 1, shafi na 44
- ↑ Ƙara'ati, Tafsir Nur, juzu'i na 1, shafi na 32.
- ↑ «راز کاربرد ضمیر جمع در آیه «ایاک نعبد و ایاک نستعین»، Kamfanin dillancin labarai na Iqna.
Nassoshi
- «راز کاربرد ضمیر جمع در آیه ایاک نعبد و ایاک نستعین»، (Sirrin wakilin suna na jam'i cikin ayar Iyyaka na'abudu wa iyyaka nasta'in), Kamfanin dillancin labarai na Iqna. Ranar buga labarin: 5 Oktoba 2020M. Ranar ziyarar shafin: 27 Oktoba 2026M.
- Abdullah Jawadi Amoli, Tafsir Tasnim, Qom: Mawallafar Isra, 1395Sh.
- Abu Nu'aim Isfahani, Ahmad Bin Abdullah, Dalailun Nubuwwa, Beirut: Dar al-Nafa'is, 1412H.
- Ɗabaɗaba'i, Sayyid Muhammad Husaini, Almizan fi Tafsiril Qur'an, Beirut: Cibiyaral-A'lami lil-Matbu'at, 1390H.
- Ɗabrisi, Hassan Bin Fadl, Makarimul Akhlaƙ, Qom: al-Sharif al-Radi, 1370Sh.
- Majlisi, Muhammad Baƙir, Bihar al-Anwar, Beirut: Dar Ihya al-Turash, 1403H.
- Ƙara'ati, Muhsin, Tafsir Nur, Qom: Markaz Farhangi Dars-hayi az Qur'an, 1383Sh.
- Ƙazi Sa'id Ƙummi, Asrarul Ibadat wa Haƙiƙat as-Salat, Tehran: Jami'ar Tehran, 1339Sh.
- Ƙummi, Shaik Abbas Mafatihul Jinan, Qom: Majma' Ihya as-Saƙafa al-Islamiyya, ba tare da shekarar bugawa ba.
- Makarim Shirazi, Nasir, Tafsir Namuna, Tehran: Dar al-Kutub al-Islamiyya, 1380Sh.
- Nasr Bin Muzahim, Waƙ'atu Siffin, Qom: Maktabat Ayatullah al-Mar'ashi al-Najafi, bugu na biyu, 1404H.
- Sayyid Ibn Ɗawus, Ali Bin Musa, Falahus Sa'il wa Najah al-Masa'il, Qom: Bustan Kitab, bugu na farko, 1406H.
- Sayyid Ibn Ɗawus, Ali Bin Musa, Jamalul Usbu'i Wa Kamal al-Amal al-Mashru, Qom: Dar al-Rida, 1330H.
- Sayyid Ibn Ɗawus, Ali Bin Musa, Muhajud Da'awat wa Manhaj al-Ibadat, binciken Abu Ɗalib Kermani da Muhammad Hassan Muharrir, Qom: Dar al-Zakhair, 1411H.
- Shaik Ɗusi, Man La Yahduruhu Faƙihu, Qom: Ofishin Intisharate Islami, 1413H.
- Sharif Kashani, Fathullah, Zubdatut Tafasir, Qom: Cibiyar al-Ma'arif al-Islamiyya, ba tare da shekarar bugawa ba.