Ƙarya
ƘARYA (Larabci: الكذب) tana daga cikin munanan ɗabi'u, kuma ƙarya na nufin faɗin wani abu da ya saɓawa gaskiya. Ƙarya tana daga cikin manya-manyan zunubai da Alƙur'ani da hadisai suka haramta, kuma ana lissafata a matsayin mabuɗin dukkan munanan ayyuka da kuma sanadin lalacewar imani. Ƙarya haramun ce, amma ana halastata a wasu lokuta; Daga cikin guraran da aka halasta ta shi ne : warware bambance-bambancen mutane ko saɓani , ko kare rayukansu da dukiyoyinsu. A cikin hadisai an ambaci abubuwan da ƙarya take haifarwa a duniya da lahira, Kamar zubewar mutunci da ƙasƙantuwa a idon mutane, talauci, azabar Ubangiji, halakar imani da tsinuwar Mala'iku,hassada, zullumi,rowa, raunin imani da sauran irin su da ƙarya takan iya haifarwa. Kula da ayoyi da ruwayoyi da sukayi Allah wadai da ita, suna daga cikin hanyoyin magance ƙarya.
Ma’anar Kalmar Ƙarya
Ƙarya tana ɗaya daga cikin munanan ɗabi'u kuma tana nufin faɗin wani abu da ba gaskiya ba.[1] ko kuma kawo magana daga wanda bai fada ba,[2] Ƙarya kishiyar gaskiya ce, kuma wanda yake ƙarya ana kiransa da sunan Maƙaryaci.[3]
Matsayi da Muhimmanci
tana daga cikin manya-manyan munanan ɗabi'u.[4] kuma mafi girman zunubai[5] a wasu ruwayoyin an kawota a matsayin mabuɗin dukkan sharri[6] kamar yadda Mullah Ahmad Naraƙi ya kawo ayoyi da ruwayoyi da dama da sukai nuni da hakan[7] Haka nan an keɓe babi daban-daban dangane da ƙarya a littattafan hadisi.[8] da littattafan Akhlaƙ, Misali, a cikin littafin Alkafi, a babin ƙarya, an ruwaito hadisai 22 na la’antar ƙarya.[9]
A cikin ruwayar Imam Sadik (A.S) da aka ruwaito kan karfin hankali da jahilci, faɗin gaskiya yana daga cikin ƙarfin hankali, ƙarya kuma tana daga cikin ƙarfin jahilci.[10] A cikin Alkur'ani an ambaci Maƙaryaci a matsayin wanda ya cancanci la'anar Allah da fushinsa,[11] a littattafan Akhlaƙ kuma a matsayin ɗaya daga cikin munanan ɗabi’u.[12]
Haka nan an ambaci ƙarya a cikin babin azumi, hajji, mu’amala da rantsuwa.[13] haka cikin littattafan fiƙihu, Misali ƙarya tana ɗaya daga cikin haramun kan wanda ya ɗaura ihrami, ( kayan mahajjata) wanda ya zo a cikin ayyukan Hajji,[14] haka nan kuma yin ƙarya ga Allah da Annabi (S.A.W) na daga cikin abin da yake ɓata azumi, wanda aka kawo a cikin bahasi na. hukunce-hukuncen azumi.[15]
Ƙarya Babban Zunubi Ne?
A wasu hadisai ana sanya ƙarya a cikin manya-manyan zunubai.[16] Don haka Shahid Sani yana ganin ta ɗaya daga cikin manya-manyan zunubai da suke sa mutum ya kauce wa adalci (adalci),[17] Amma Shaikh Ansari ya kawo hadisai.[18] daya nuna cewa ƙarya tana daga cikin manya-manyan zunubai da suke lalata aikin mutum.[19] yin ƙarya ga Allah da Annabi (S.A.W) suna daga cikin manya-manyan zunubai,[20] wasu daga cikin waɗannan hadisai sun yi nuni da cewa saboda girman ƙarya ne yasa aka kebanceta a manyan zunubai.[21]
Illoli Da Abubuwan Da Yasa Ake Yin Ƙarya.
An ambaci dalilai da daban-daban na yin ƙarya; A cikin ruwaya ankawo cewa ƙarya tana da tushe daga ƙasƙancin rai,[22] haka nan, al’amura kamar raunin imani da fitintinu na Shaiɗan, kwaɗayi da hassada na daga cikin wasu dalilai, samun dukiya da matsayi suna daga cikin abubuwan da suke kwadaitar da yin ƙarya.[23]
Tasiri da Abubuwan da take Janyowa
Imam Hassan Askari (A.S)
جُعِلتِ الخَبائِثُ کُلها فی بَیت وَ جُعِل مِفتاحُها الکَذِبَ An sanya duk wata ƙazanta a cikin wani gida kuma karya ita ce makullin wannan gida
Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 69, shafi na 263
Kaɗan daga cikin illolin ƙarya sune: Tozarta maƙaryaci, An karɓo daga Imam Ali (A.S) yana cewa a nisanci abota da maƙaryaci, Domin koda yaushe a ƙarya yake ta yadda ba'a ma yarda da gaskiyarsa.[24]
Rugujewar imanin maƙaryaci: bisa ruwaya daga Imam Baƙir (A.S) ƙarya tana rushe Imani.[25] Hukuncin Ubangiji (Azabar Ubangiji ): An ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W.W) cewa ku nisanci ƙarya, ƙarya fasiƙanci ce kuma zalunci, kuma maƙaryaci da fajiri suna da matsayi na musamman a cikin wuta.[26] Da la’anar Mala’iku: An karbo daga Manzon Allah (S.A.W.W) cewa: “Duk lokacin da mumini ya yi ƙarya ba tare da wani uzuri ba, Mala’iku dubu saba’in za su la’ance shi, sai wani wari mai muni ya dinga fita daga zuciyarsa, wanda zai kai ga Al'arshin Allah, kuma Ubangiji Ya yi masa azaba saboda wannan ƙaryar, kuma za'a .” za a rubuta masa zina da mahaifiya sau saba’in”.[27] Haka nan rashin mutunci[28] talauci[29] da mantuwa[30] su ne sauran sakamakon ƙarya da suka zo a cikin hadisai. Kamar yadda Mulla Ahmed Naraƙi ya faɗa a cikin littafin Mi’irajus-Sa'ada cewa, ƙarya tana wulakanta mutum da ƙasƙantar dashi tare da zubar masa da mutunci a idon mutane da kuma sanya masa baƙin fyanti a duniya da lahira.[31]
Hanyoyi Da Dabarun Magance Ƙarya.
- Asalin makala: Karya don wata maslaha
Mulla Ahmad Naraƙi yana cewa idan ana son a magance ɗabi’ar ƙarya, dole ne a ɗauki matakin sanya gaskiya ta zama siffar din-din ɗin mutum; Ciki har da: 1 Kula da ayoyi da hadisai da suke bayanin hukuncin ƙarya. 2 Kula da illolin ƙarya na duniya da lahira, kamar azaba a lahira da wulaƙanta a duniya. 3 Tunani akan illa da fa'idar gaskiya. 4 Yin tunani kafin ka yi magana. 5 Nesantar tarayya da maƙaryata da masu aikata zunubi.[32]
Haka nan kamar yadda Nasir Makarim Shirazi, ɗaya daga maraji'an taƙlidi kuma malamim tafsirin Alkur’ani a littafinsa na Akhlaƙ cikin Alkur'ani ya ce:, ya kamata a yi maganin ƙarya ta hanyar magance tushenta. Misali, idan abin da ke sanya mutum ƙarya ,raunin imani ne ya kamata a ƙarfafa shi, idan kuma kwaɗayi ne da hassada a cire su. Haka nan kuma a nisanci mutanen da suke yin ƙarya ko wuraren da suke sanya mutum ƙarya.[33]
Wuraren Da Ya Halasta A yi ƙarya
Imam Ali (A.S)
لَا يَجِدُ عَبْدٌ طَعْمَ الْإِيمَانِ حَتَّى يَتْرُكَ الْكَذِبَ هَزْلَهُ وَ جِدَّهُ Bawa ba ya ɗanɗanon imani har sai ya bar wargi da ƙarairayi wanda yake yi cikin wasa da barkwanci da wanda yake yinsu da niyya
Kulaini, Al-kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 340, hadisi na 11.
Ƙarya haramun ce[34] Amma kuma ana ganin halal ne kuma wajibi ne a cikin al’amuran da suke da fa’ida mai muhimmanci:[35] A cikin larura: Idan larurar (Dole ko gaggawa ), ce ya halatta a yi ƙarya,[36] kamar lokacin da rai ke cikin haɗari ko dukiya.[37] Gyara tsakanin mutum biyu: Yin ƙarya da nufin gyara da sulhu tsakanin mutane ya halatta.[38] A lokacin yaƙi da maƙiya: A bisa hadisai, ya halatta a yi ƙarya a cikin yaƙi don yaudarar abokan gaba.[39]
Alƙawarin Ƙarya Ga Matarka Da ƴaƴanka
Kamar yadda wasu ruwayoyi suka ce, ya halatta a yi wa matar aure alkawarin ƙarya[40] Don haka a cikin littattafan Akhlaƙ yin alkawarin ƙarya ga mata da ‘ya’ya baya daga haramcin yin ƙarya, kuma ya halasta[41] sai dai malaman shi'a basu halarta hakan ba.[42] Hakan nan malaman sun ce ruwayoyin da wasu malamai sukai amfani da su wajan halascin sun saɓawa ayoyin Alkur'ani da suka yi umarni da cika Alƙawari.[43] da kuma hadisan da suka hana yin Alƙawari ba tare da niyyar cikawa ba.[44] hakanan aiki da irin waɗannan Hadisai suna haifar da mummunar tarbiyya da kwaɗaitar da yara kan yin ƙarya da karya alkawari.[45]
Bayanin kula
- ↑ Mustafawi, Tahaqiq fi Kelamat al-Qur'an, 1367, juzu'i na 10, shafi na 33.
- ↑ Shearani, Nasar Touba, Islamia Publications, juzu'i na 2, shafi na 331.
- ↑ Mustafawi, Tahaqiq fi Kelamat al-Qur’an, 1367, juzu’i na 10, shafi na 33.
- ↑ Naraghi, Mi'raj al-Saadah, Hijira, shafi na 573.
- ↑ Alal misali, duba Naraghi, Jame al-Saadat, Cibiyar Harkokin Jarida ta Kimiyya, juzu'i na 2, shafi na 332.
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 69, shafi na 263.
- ↑ Naraghi, Mi'raj al-Saadah, Hijira, shafi na 573.
- ↑ Misali, duba Kulaini, al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 338-343.
- ↑ Duba Kulaini, al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 338-343.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi na 21.
- ↑ Suratul Nur, aya ta 7
- ↑ Alal misali, duba Naraghi, Jame al-Saadat, Scientific Press, Vol.2, shafi.332-338.
- ↑ Duba Imam Khumaini, Tahrir Al Wasila, Cibiyar Edita da Bugawa ta Imam Khumaini, Juzu'i na 2, shafi na 111-110.
- ↑ Imam Khumaini, Tahrir Al Wasila, Imam Khumaini Cibiyar Gyara da Bugawa, Juzu'i na 1, shafi na 399.
- ↑ Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa al-Wuthghati, 1420 AH, juzu'i na 3, shafi na 549.
- ↑ Duba Sheikh Ansari, Makaseb, Tarath al-Sheikh al-Azam, juzu'i na 2, shafi na 12.
- ↑ Shahid Sani, Al-Rawda Al-Bahiya, 1398 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 129.
- ↑ Misali, duba Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi.338, h2.
- ↑ Sheikh Ansari, Makasab, Tarath al-Sheikh al-Azam, juzu'i na 2, shafi na 13 da 14.
- ↑ Duba Muhaddith Nuri, Wasa'il al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 12, shafi 248.
- ↑ Sheikh Ansari, Makasab, Tarath al-Sheikh al-Azam, juzu'i na 2, shafi na 13.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 69, shafi na 262.
- ↑ Makarem Shirazi,Akhlak dar Kur’an, 1377, juzu’i na 3, shafi na 234-236.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407, Juzu'i na 2, shafi na 14.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi.339, h4.
- ↑ Muhaddith Nouri, Mostadrak al-Wasail, 1408 AH, juzu'i na 9, shafi na 88.
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 69, shafi na 263.
- ↑ Muhaddith Nouri, Mustadrak al-Wasail, 1408H, juzu'i na 9, shafi na 87.
- ↑ Qommi, Safina al-Bihar, 1363, juzu'i na 7, shafi na 455.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, Juzu'i na 2, shafi na 341, h.
- ↑ Naraghi, Mi'raj al-Saadah, Hijira, shafi na 573.
- ↑ Naraghi, Meraj al-Saadah, Hijira, shafi na 578-580
- ↑ Makarem Shirazi,Akhlak dar Alkur’an, 1377, juzu’i na 3, shafi na 235-236.
- ↑ Sheikh Ansari, Makasab, Tarath al-Sheikh al-Azam, juzu'i na 2, shafi na 11.
- ↑ Naraghi, Mi'raj al-Saadah, Hijira, shafi na 575.
- ↑ Sheikh Ansari, Makasab, Tarath al-Sheikh al-Azam, juzu'i na 2, shafi na 21.
- ↑ Sheikh Ansari, Makasab, Tarath al-Sheikh al-Azam, juzu'i na 2, shafi na 21.
- ↑ Sheikh Ansari, Makasab, Tarath al-Sheikh al-Azam, juzu'i na 2, shafi na 31.
- ↑ Sadouq, Man Laihzara al-Faqih, Tehran, juzu'i na 4, shafi na 359.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407H, juzu'i na 2, shafi na 342, H. 18.
- ↑ Alal misali, duba Naraghi, Jame al-Saadat, Cibiyar Harkokin Jarida ta Kimiyya, juzu'i na 2, shafi na 236-237.
- ↑ Duba Imam Khumaini, al-Makasib al-Muharma, 2013, juzu'i na 2, shafi na 140; Tabatabai Hakim, Minhaj al-Salehin (Al-Mahshi lal-Hakim), juzu'i na 2, shafi na 15.
- ↑ Suratul Isra, aya ta 34.
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 101, shafi na 73.
- ↑ Irvani, "Aslu Sadakat dar Kur'an wa tahil mawarid jawazi kizbi", shafi na 126.
Nassoshi
Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Al-Makasib al-Muharmah, Qum, Cibiyar Tsara da Buga Ayyukan Imam Khumaini (a.s), 1381. Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Tahrir al-Wasila, Tehran, Imam Khumaini Works Editing and Publishing Institute, Beta. Kulaini, Muhammad bin Yaqub, al-Kafi, Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya, bugun 4, 1407H. Majlisi, Mohammad Baqer, Bihar Al-Anwar, Beirut, Al-Wafa Institute, 1403 AH. Makarem Shirazi, Nassar, akhlak dar Alkur’an, Qum, Mazhabar Imam Ali Bin Abi Talib, 1377. Mostafavi, Hassan, Bincike a cikin kalmomin Kur'ani mai girma, Tehran, Ma'aikatar Al'adu da Jagorar Musulunci, Babban Sashen Cibiyoyi da Alakar Al'adu, 1368. Muhaddith Nouri, Mostadrak al-Wasa'il, Qum, Al-Bait Institute, 1408H. Naraghi, Ahmed bin Mohammad Mahdi, Littafin Me'raj al-Saada, gabatarwa ta Mohammad Naqdi, Qum, Hijrat Publications Institute, Beta. Naraghi, Mohammad Mahdi, Jame al-Sadat, ta'alik Mohammad Kalanter, Beirut, Cibiyar Kimiyya don Jarida, bugu na 4, Beirut, Beta. Qomi, Sheikh Abbas, Safina Al-Bihar, Tehran, Farahani, 1363. Sadouq, Mohammad Bin Ali, Man Laihzara Al-Faqih, Tehran, Sadouq Publishing House, 1367-1369. Shahid Thani, Sharh al-Ma'a, wanda Sayyed Mohammad Kalantar ya yi bincike, bugu na biyu, 1398H. Shearani, Abolhassan, Tubi's Prose or the Dictionary of the Words of the Holy Quran, Tehran, Islamia Publications, Beta. Sheikh Ansari, Morteza, al-Makasab, Tarath al-Sheikh al-Azam, Bita. Tabatabaei Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-Arwa Al-Wathaghi, Al-Nashar al-Islami Foundation, bugu na farko, 1420H.