Rida

Daga wikishia

Rida ɗaya daga cikin Mafi shaharar laƙubban Ali Bn Musa Rida (A.S) [1] ma’anarsa shi ne wanda aka zaɓa ake so. [2] kan asasin riwayar da ta zo cikin littafin Uyun Akhbar Rida, Allah ne ya yi wa Imammi Na takwas laƙabi da Rida, cikin wannan riwaya ya zo cewa Ahmad Bn Nasar Bazanɗi ya tambayi Imam Jawad (A.S) wasu Jama’a suna raya cewa Mamun ya baiwa Mahaifinka laƙabin Rida saboda ya yarda ya karɓi Mukamin Waliyul Ahad (muƙamin mai jiran gado) sai Imam jawad cikin bashi amsa ya ce: na rantse da Allah ƙarya ce suke faɗi, sun aje abu ba a muhallinsa ba, Allah ne ya sanyawa Ali Bn Musa (A.S) wannan laƙabin, saboda ya samu yardar Allah a Sama, a ƙasa kuma ya samu yardar Manzon Allah (S.A.W) da yardar sauran Imamai (A.S) [3] cikin cigaban riwayar ya zo cewa Bazanɗi ya tambayi Imam (A.S) ashe sauran Iyayenka ba su kansance yardaddun Allah da Manzonsa ba? To ta yaya cikinsu Mahaifinka kaɗai akewa laƙabi da Rida? Sai Imam ya ce: saboda shi ne mutum wanda ya samu yarda daga masoya da maƙiya masu dacewa da shi da masu saɓawa da shi, babu wani daga iyayensa da suka samu haka, da wannan dalili ne daga cikinsu shi kaɗai akewa laƙabi da Rida [4] [yadasht1] haka kuma bisa rahotan wata riwaya daga Salmanu Bn Hafsu Maruzi cikin littafin Uyun Akhbar Ar-Rida an naƙalto cewa Mahaifinsa Imam Kazim (A.S) ne ya sa masa laƙabin Rida. [5] Kan asasi rahotan ba’arin wasu litattafan Tarihi ya zo cewa lokacin da Ali Bn Musa (A.S) ya karɓi muƙamin Waliyul Ahad sai Mamun ya yi masa laƙabi da Rida. [6]

«اَلرِّضا مِنْ آلِ مُحَمَّد»

Yardajje daga Alu Muhammad. [7] A cewar Wilfrod Madlung Masanin Muslunci da Shi’anci mutumin ƙasar Jamus wanda aka Haifa shekara 1930 m, laƙabin (Rida Min Ali Muhammad) tun kafinsa an yi amfani da wannan laƙabi kan mutanen da dukkanin Musulmi suka yarda da halifancinsu.[8] Sayyid Murtada Amili Mai bincike kuma Marubucin Tarihin rayuwa A’imma wanda ya rayu tsakanin shekara 1346-1441 h ƙamari, bisa dogara da wasiƙar Fadlu Bn Sahal Wazirin Mamun wacce ya aika zuwa ga Imam Ali Bn wacce cikinta ya yi amfani da laƙabin Rida, Malamin ya yi imani kan cewa Mamun ya amfani da wannan wasiƙa ne ya ciro laƙabin Rida ya yi amafani da shi kan Imam Ali Bn Musa (A.S) ya kuma ayyana laƙabin Rida a hukumance kan Imam Ali Bn Musa (A.S) [9] Ayatullahi Jawadi Amoli ya fassara laƙabin Rida ga Imami na takwas da cewa keɓantattun laƙubba ne na Allah, duk wani mutum idan ya so yarda da wani yana samun yarda ne ta hanyar Failar Rida, da wannan dalili ne babu wani Mutum cikin kowanne hali da zai samu yarda kan wani ko kan wani mutum sai da tsani da wasiɗar babban muƙami na Rida. [10]

Bayanin kula

 1. Amin, Ayan al-Shia, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi na 13
 2. Sahib bin Abbad, Al-Muhait fi al-Laghha, 1414 AH, juzu'i na 8, shafi na 42.
 3. Sadouƙ, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 13.
 4. Attardi, Musnad al-Imam al-Reza (a.s.), 1406H, shafi na 10.
 5. Sadouƙ, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 1, shafi na 14.
 6. Ibn Athir, Al-Kamel, 1385 Hijira, juzu'i na 6, shafi na 326.
 7. Sabt bin Jozi, Tazkira Al-Khawas, 1418H, shafi na 315.
 8. Madelong, “Farwande Ali bin Musa al-Reza”, shafi na 7
 9. Ameli, Al-Hayat al-Siyasiya na Imam al-Reza (a.s.), Al-Nashar al-Islami Foundation, shafi na 204.
 10. <a class="eɗternal teɗt" href="https://jaɓadi.esra.ir/fa/w/%D8%A7%D9%85%D8%A7%D9%85-%D8%B1%D8%B6%D8%A7%D8%9B-%D8%B9%D8%A7%D9%84%D9%85-%D8%A2%D9%84-%D9%85%D8%AD%D9%85%D8%AF-%D8%B5%D9%84%DB%8C-%D8%A7%D9%84%D9%84%D9%87-%D8%B9%D9%84%DB%8C%D9%87-%D9%88-%D8%A2%D9%84%D9%87-%D9%88-%D8%B3%D9%84">امام رضا؛ عالم آل محمد(ص) معنای پرافتخار لقب «رضا»</a>

Nassoshi

 • Ibn Athir, Ali bin Muhammad, Al-Kamal fi al-Tarikh, Dar Sader, Beirut, bugun farko, 1385H.
 • Amin, Seyyed Mohsen, Ayan al-Shi'a, Beirut, Dar al-Taarif, 1403H.
 • Sabat bin Jozi, Yusuf bin Ghazaughli, Tazkira al-khawas min umma fi zikr khaizat al-ayama, ƙom, Manshurat al-Sharif al-Razi, 1418 AH.
 • Saheb bin Ebad, Ismail, Al-Muhait fi al-Laghha, Muhammad Hasan Al-Yasin, Beirut, Alam al-Katab, 1414 AH.
 • Sadouƙ, Mohammad Bin Ali, Ayoun Akhbar al-Reza, Tehran, Nash Jahan, 1378H.
 • عاملی، سید جعفر مرتضی، الحیاة السیاسیة للامام الرضا(ع) دراسة و تحلیل، مؤسسة النشر الاسلامی، بی‌تا.
 • Atardi, Azizullah, Masnad al-Imam al-Reza, Mashhad, Astan ƙuds Razaɓi, 1406H.
 • مادلونگ، ویلفرد، «پرونده: علی بن موسی الرضا(ع)»، ترجمه احمد نمائی، اطلاعات حکمت و معرفت، سال سوم، ش۸، آبان ۱۳۸۷ش.
 • Mustafid da Ghaffari, Hamid Reza da Ali Akbar, Ayun Al-Akhbar Al-Reza, Tehran, bugun farko, 1372.
 • امام رضا؛ عالم آل محمد(ص) معنای پرافتخار لقب «رضا»، پایگاه اطلاع‌رسانی اسراء، تاریخ انتشار: ۵ آبان ۱۳۹۸ش.