Jump to content

Kumaitu Bin Zaidi Al-asadi

Daga wikishia

Kumaitu Bin Zaidi Al-asadi (Larabci: کُمَیت بن زید اَسَدی) ya rayu daga shekara ta 60 zuwa 126 hijira, mawaƙi ne balarabe ɗan shi'a yana cikin fitattun mawaƙan Ahlul-baiti (A.S) ya yi zamani da Imam Sajjad da Baƙir da Sadiƙ (A.S)

Ƙasidarshi mai suna Hashimiyyat tana cikin fitattun waƙoƙinshi, ya yi magana kan maudu'i daban-daban, kamar falalar Bani Hashim, Waƙi'ar Ghadir, Shahadar Imam Husaini (A.S) da kuma abin da ya shafi mulkin Umayyawa, da abin da ya jawowa musulmi, wannan ƙasidu an rubuta su ne cikin shekara 15 zuwa 20 bayan Waƙi'ar Karbala.

Kumaitu ya sami kulawa ta Imam Zainul Abidin da Imam Baƙir waɗanda su ne Imami na huɗu da biyar a gun ƴan shi'a, sakamakon waƙoƙinshi, kuma ruwayoyin da suka kawo addu'ar Imamai a kanshi, amma duk da haka an ce ya yi wata waƙa ta yabo ga Banu Umayya saboda taƙiyya, domin kare kanshi.

Matsayi Da Muhimmanci

Kumaitu ɗan Zaid ɗan Khanis ɗan Makhalid, ko kuma ɗan Makhalid ɗan Zuwaibiyya ɗan Ƙaisi ɗan Ammar- ɗan Wuhaibi ɗan Ammar ɗan Subai'a ɗan Malik ɗan Sa'ad ɗan Sa'alaba ɗan Dudan ɗan Asad ɗan Khuzaima ɗan Mudrika ɗan Iliyas ɗan Madur ɗan Nazzar, kuma shi Kumaitu ɗa ne ga ƴar uwar Farazdaƙ mashahurin mawaƙin nan a lokacin daular Ummayyawa, kuma ya yi zamani da Sayyid Himyari mawaƙin nan ɗan shi'a wanda aka sani da tsattsauran ra'ayi,[1] an haifi Kumaitu a ƙarshan shekara ta 60 hijjira.[2]ya yi wafati a ƙarshan mulkin Marwan a ƙarshan mulkin Banu Ummayya a shekara ta 126 hijhira a Kufa. Kuma shi ne mutum na farko da aka binne a maƙabartar Bani Asad.

An bayyana Kumait ta hanyar Abu Al-Faraj Al-Isfahani a matsayin fitaccen mawaƙi, masani a harshen Larabci da kalmominsa, kuma mai ilimi game da tarihin Larabawa. Ya kasance mai kishi kan Qahṭān, kuma yana shiga cikin muhawarar waƙoƙi tare da sauran mawakan Larabawa. Waƙoƙin "Al-Hashimiyyat" suna daga cikin fitattun ayyukansa, kuma an ce adadin baitocinsa ya wuce dubu biyar, duk da cewa da yawa daga cikinsu babu su.

An ce Kumaitu ya kasance yana da kishi da san ƙabilar Adnan a cikin larabawa, kuma ya kasance yana rubuta waƙa kan sukar mawaƙan Yaman. Amma Abul Faraj Al'isfahani ya ce, abin da ya sa Kumaitu yake sukar mawaƙan Yaman saboda wani mawaƙi daga Yaman mai suna Hakim ɗan Ayyash Al'kalbi ya yi waƙa inda ya soki Imam Ali (A.S) da Bani Hashim, saboda tsoran Bani Umayya, a ƙoƙarin Kumaitu na kare Imam Ali (A.S) da Bani Hashim, sai ya shiga sukar mawaƙan Yaman.[3]


Alaƙarshi Da Ahlul-bait (A S)

Bisa ruwayoyin da ake da su, suna nuna cewa Kumaitu mawaƙi ne a lokacin mulkin Banu Ummayya, ya kasance mai girmama Ahlul-baiti (A.S) kuma Imam Ali Zainul Abidin da Imam Baƙir da Sadiƙ (A S) sun kasance suna girmama shi. An rawaito ruwayoyin da Imamai suka yi mishi addu'a. Kazalika an ce Kumaitu ba ya karɓar kuɗi ko dukiya kan waƙar da ya yi kan yabon Ahlul-baiti ( A.S) ya kasance yana neman riga daga Imam Zainul Abidin ko Imam Baƙir (A.S) domin ya yi tabarruki da ita.[4]

Bayani kan Kumaitu Da Iyalinshi

Ana yi wa Kumaitu laƙabi da Abu Mustahil wanda shi ne babban ɗan ga Kumaitu, matarshi kuma sunanta Hubba ƴar Abdul-wahid ita ma ana yi mata laƙabi da Ummul Mustahil, shi Kumaitu yana da wani ɗan mai suna Jaishu, babu wanda ya san yarintar Kumaitu, amma ya kasance yana yaro a lokacin da Abdul-malik ɗan Marwan ya hau kan karagar mulki, amma daga dukkan alamu shi ba ɗan ƙabilar Asadiyya ba ne, ƙabila mai tarihi da fice, ta yi wu wannan shi ne dalilin da ya sa ba ya alfahari da ƙabilar Asadiyya, saboda haka kodayaushe yana dogaro da alfahari da kanshi, ya kasance mai basira, mai yawan ɗaukaka kanshi, duk da kasancewar shi bebe da kuma rashin kyan murya kuma ba ya iya rera waƙa da kyau, saboda haka idan ya buƙaci rera waƙa sai umarci ɗanshi Mustahil ya rera, ɗanshi Mustahil ya kasance mai fasaha da iya rera waƙa.[5]

Abubuwan Da Ya Keɓanta Da Su

Kumaitu yana da siffofi guda goma, wanda babu wani mawaƙi da yake da su, ya iya gabatar da bayani (lacca), malamin fiƙihu a Shi'a, mahardacin ƙur'ani, yana da kyan rubutu, ya iya jayya, shi ne wanda ya fara muƙabala a shi'a, ya iya jifa, mayaƙi ne kuma jarimi, ya kasance mai kyauta kuma mai riƙo da addini.[6][7]

Kumaitu ya kasance mai nuna kishi ga ƙabilar Adnan, mai yi wa mawaƙan Yaman zanbo, kuma sukar juna tsakaninshi da ƴan Yaman ta yaɗu a rayuwarshi da bayan mutuwarshi, kai har takai Di'ibil da ɗan Abi Uyaina sun yi mishi raddi kan ƙasidarshi mai suna Mazhaba bayan mutuwarshi, sai abu Albalƙa Albasari bawan Bani Hashim ya ba su amsa kan raddinsu ga Kumaitu,[8] kazalika akwai nuna alfahari da kuma muƙabala tsakanin shi da Hakim A'awar Al'kalbi.[9]

Kashe Shi

Kumaitu ya rasu a lokacin mulkin Marwan Bin Muhammad a shekara ta 126 hijira.[10]

  • Ga yadda aka labarta yadda ya mutu: A lokacin da Yusuf Bin Umar ya shiga gurin Kumait, sai Kumaitu ya yabi Yusuf Bin Umar bayan da ya kashe Zaidu Bin Ali, sai ya rera wannan waƙar; Albarah ta fita tana tafiya, amma sojoji sun kewaye Yusuf ɗan Umar, sojojin ƴan Yaman ne, sai suka nuna ƙabilanci ta goyan bayan Khalid, kuma suka soki Kumaitu a ciki da takubbansu, suka dake shi, suka ce zaka yi wa Sarki waƙa ba tare da ka nemi umarninshi ba, haka jini ya yi ta zuba daga Kumaitu har ya mutu.[11]
  • Mustahil dan Kumaitu ya ce, naje gurin babana a lokacin da ya kusan mutuwa, sai ya farfaɗo ya buɗa idonshi sai ya ce min, ina yi maka wasiyya da iyalan gidan Annabi Muhammad har sau uku.[12]

Inda Aka Binne Shi

Kumaitu ya yi wasiyya ga ɗanshi cewa, ya kai ɗana, na karanta a ruwaya cewa a Kufa ana haƙe kabari da tune mamata daga cikin kabarinsu, sai kuma a binne su a wani kabari, saboda haka kada ka binne ni a Kufa, amma idan na mutu ka kai ni wani guri da ake kira Makaran ka binne ni a can, haka kuma aka yi da Kumaitu ya mutu sai aka binneshi a can, shi ne mutum na farko da aka binne a can, gurin shi ne maƙabartar Bani Asad har zuwa yau.[13]

Aƙidar Kumaitu Da Ra'ayinshi A Siyasa

An san Kumaitu da shi'anci, ya yi fice da shi'anci ga Banu Hashim,[14] waƙoƙinshi fitattu ne kan iyalan gidan Manzo(A.S) saboda haka ne ma wasu marubuta da masu bincike suke ganin Kumaitu a matsayin mai goyan bayan wani ɓangare da yin siyasa, sakamakon ra'ayinshi na aƙida wanda ya saɓawa sarakunan Banu Umayya.[15]

Waƙoƙinshi Da Adabinshi

Daga ƙasidar da ya rerawa Imam Husaini (A.S)[16]

ومن أكبر الأحداث كانت مصيبة
علينا قتيلُ الأدعياء الملحّبُ
ومنعفر الخدين من آل هاشم
ألا حبّذا ذاك الجبين المتّرب
ومَن عجب لم أقضه أن خيلهم
فَدَتْکَ نُفوسُ القَومِ یا خَیرَ راکِعٍ
فَأَنزَلَ فیکَ اللّهُ خَیرَ وِلایَة
لأجوافها تحت العجاجة أزمل
هَماهم بالمستلئمين عوابس
كحدآن يوم الدّجن تعلو وتسفل
يحلئن عن ماء الفرات وظله
حسيناً ولم يشهر عليهن منصل
كأنَّ حسيناً والبهاليل حوله
لأسيافهم ما يختلي المتقبِّل
يخضن به من آل أحمد في الوغى
دما طل منهم كالبهيم المحجِّل
وغاب نبي الله عنهم وفقده
على الناس رزء ما هنالك مجلل
فلم أر مخذولاً أجلَّ مصيبة
وأوجب منه نصرة حين يخذل[16]


Kumaitu ya kasance mai yawan waƙoƙi, an ce a sanda ya mutu yawan baitikan waƙoƙinshi sun kai 5289 kamar yadda ya zo a cikin littafin Agani da littafin Ma'ahad juzi'i 2 shafi 31, ko kuma yana da ƙasidu fiye da dubu biyar kamar yadda ya zo a cikin kashafuz Zunun wanda shi kuma ya samo daga littafin Uyunul Akhbarir Rida,[17][18]

Al-asma'i ya tattara waƙoƙin Kumaitu wanda Ibn Sikkit ya ƙara kan abin da Al'asma'i ya tattara, wasu mutane sun rawaito daga Abi Muhammad Abdullahi Bin Yahaya wanda aka fi sani dan Kanasa Al'asadi ya rasu a shekara ta 207 shi kuma Ibn Kanasa ya rawaito daga Al'jizzi da Abi Al'musil da Abi Sadaƙa Al'asadiyyan, ya rubuta littafi ya sa mishi suna "Sariƙa Kumaitu Min Kur'ani Wa Gairihi" Ibn Sikkit ya rawaito daga malaminshi Nasran, sai Nasran ya ce, na karata waƙa Kumaitu ga Abi Hafsa Umar Bin Bukairi. Assukuri Abu Sa'id Alhasan Bin Husaini wanda ya rasu a shekara ta 275 hijira ya mai-maita waƙoƙin Kumaitu,[19] kamar yadda ya zo a cikin littafin Fihras na Ibn Nadim,[20] kazalika Muhammad Bin Anas ya kasance tare da waƙoƙin Kumaitu hakan ya zo a cikin Tarikhu Bin Asakir,[21][22]

Matsayin Kumaitu A Fagen Waƙa

An tambayi Ma'azu Ibn Jabal, wane ne ya fi kowa iya waƙa? Sai ya ce: daga cikin mawaƙan Jahiliyya ko mawaƙan Muslunci? Sai aka amsa mashi da cewa cikin mawaƙan Jahiliyya, sai ya ce Imru'ul Ƙaisi, Zuhuri, Ubaidu dan Al'abras, bayan haka sai suka ce mishi to daga cikin mawaƙan Muslunci fa? Sai ya ce Farazdaƙ da Jubairu, da Aktal da Ar-Ra'i, sai aka ce mishi ya kai baban Muhammad ba mu ga ka ambaci Kumaitu ba a cikin waɗanda ka ambata, sai ya kaɗa baki ya ce, ai wannan shi ne ya fi mawaƙan farko dana ƙarshe iya waƙa.[23]

Amini ya ce: Gaskiyar da take babu jayayya kanta ita ce, waƙar Kumaitu sabuwa ce kan waƙoƙin mu na Larabci, saboda Kumaitu a cikin waƙoƙinshi yana nuni kan matakai na hanakali wanda larabawa suka ɗauka da kuma kafa hujja ta hanyar waƙa, wannan abu ne sabo a cikin waƙarmu ta Larabci, a lokacin mulkin Banu Umayya Kumaitu ya shahara, kuma shi ne mawaƙi na farko da aka sami waƙarshi kan wata aƙida ta masamman a lokacin mulkin Umayyawa.[24]

Daga cikin abin da ya keɓanta da waƙarshi, shi ne cewa waƙa ta zama jiki a gare shi ta gasgatu da shi, kuma yana amfani da ita wajan haɓɓaka tinanin larabawa domin iya tsara tinaninsu.[25]

Diwanin Kwamait

Kumaitu yana da diwani na waƙa wanda Dr Muhammad Nabil Duraifi ya tattara kuma ya yi sharhi kanshi, kuma madaba'a ta Darus Sadar a Berut ta buga.

Hashimiyyat

Tushen Ƙasida: Hashimiyyat

Bakandamiyar Kwamait, ita ce Al-hashimiyyat, an san Kumaitu da biyayya ga iyalan gidan manzo (A.S) waƙarshi mafi kyau ya yi ta ne kan iyalan gidan manzo, wanda ake kira da Hashimiyyat, wannan waƙa akwaita a cikin Diwanin Kumaituko kuma a cikin Raudar Muktara Ma'a Alawiyyat Saba'a na Ibn Abil Hadid Al'mu'utazil, ga farkon waƙar:

من لـقلب مـتيم مستهام
غير مـا صبوة ولا أحلام
طربت وما شوقا إلى البيض أطرب
ولا لعباً مني وذو الشوق يلعب
أنـى ومـــــــن أيــن آبك الطرب
من حيث لا صبوة ولا ريب

Tarjama: Ga zuciyar da ta kamu da soyayya, ba tare da sha'awa ko mafarki ba. Na yi farin ciki ba don sha'awar kyawawan mata ba, kuma ba don wasa ba, yayin da mai sha'awa ke wasa. Daga ina kuma ta yaya farin ciki ya zo maka, daga inda babu sha'awa ko shakka. [26]


Karin Magana

Ba'arin baitukansa sun shahara har ta kai ga ana buga misali da kuma karin magana da su, daga cikinsu akwai misalin:

فيا موقداً ناراً لغيرك ضوءها
ويا حاطباً في حبل غيرك تحطب

Tarjama: Ya kai wannan mai kunna wuta, ka sani waninka ne zai amfana da haskenta. Ya Kai mai tattara itace cikin igiyar waninka

Da baitunsa:

إذا لم يكن إلا الأسنة مركب
فلا رأي للمضطر إلا ركوبها

Tarjama: Idan babu abin hawa sai mashi, To ba zaɓi ga wanda ya tilastu da shi sai hawan shi.

Da Baitunsa:

وهل ظنون امرئ إلا كأسهمه
والنبل إن هي تخطئ مرة تصب

Tarjama: Shin tunanin mutum ba kamar kibiyoyinsa ba ne, Kuma kibiya idan ta yi kuskure sau ɗaya, tana samun nasara.[27]

Balaga

Sharifur Radi yana da dalilai da yawa wanda ya ke nuna cewa Shi'irin Kumaitu yana cikin ɗabaƙa ta farko=farko,[28]

Alaƙar Kumaitu Da Ahlul-Baiti

Kumaitu ya kasance baya karɓar kyauta daga iyalan gidan manzo (A.S) sai dai ko abin da zai nemi tabarukki da shi, ya zo cewa ya mayarwa da Imam Sajjad (A.S) Darhami 4000, lokuta da daman gaske ya mayarwa Imam Baƙir (A.S) kuma ya nemi riga daga wajen Imam domin neman albarka, kazalika ya mayarwa da Imam Sadiƙ (A.S) Dinare1000 da kayan sawa, sai ya buƙaci da ya girmama shi ta hanyar ba shi kayan da ya taɓa jikin Imam domin neman albarka, ya mayarwa da Abdullahi Bin Husain filinshi wanda ya bashi takardarshi, kudin filin ya kai kimanin Dinare 4000. Kazalika ya mayarwa da Abdullahi Jafar abin da ya tara mishi daga Banu Hashim, wanda an ƙaddara shi da ya kai kimanin Darhami 100,000.[29]

Addu'ar Ahlulbaiti Da Ƙarfafawa Kansa

Kumaitu saboda iklasinshi ya sami addu'a daga Ahlul-bait (A.S) wanda hakan ya ke nuna goyan bayansu gare shi, ba a yi wa wani addu'a ba kamar yadda aka yi wa Kwamait. Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya nemawa Kumaitu rahama, kamar yadda ya zo a cikin hadisin Albayadil Marra, kuma ya nemi Allah ya sakami shi da alheri kuma ya yabe shi kamar yadda ya zo a cikin Manami Nasar Bin Muzahim, ya ce da shi Allah ya yi maka albarka da kai da mutananka.

Imam Sajjad (A.S) ya yi addu'a gare shi ya ce; Allah ya sa Kumait uya rayu cikin farin ciki kuma ya karbi rayuwarshi a mastayin shahidi, ka nuna mishi sakamakonshi da gaggawa, kuma ka yi mishi sakamako a hankali. Kazalika Abu Jaafar Albakir (A.S) ya yi mishi addu'a a gurare daban-daban, kamar a lokacin zaman Mina, yana mai kallon Ka'aba yana neman mishi rahama da gafara sau da yawa, yana cewa ba zaka gushe ba Allah yana gafarta maka da goyan bayanka da Ruhil ƙudus.[30]

Yabon Kumaitu Ga Banu Umayya

Bayan Kumaitu ya shirya ƙasida ga Banu Hashim kan yabon iyalan gidan manzo, sakamakon haka ake jinsu a ko ina, hakan yasa Kumaitu cikin hatsari, sai ya nemi izinin Imam Baƙir (A.S) kan cewa zai yabi Banu Umayya domin ya kare kanshi, mai littafin Agani yana cewa Kumaitu ya tura ni zuwa ga Abu Ja'afar(A.S) na ce mic shi Kumaitu ne ya turo ni gurinka cewa ya sabbabawa kanshi wata matsala, shin zaka ba shi dama da izini ya yabi Banu Umayya? Sai Imam ya ce eh yana da ƴanci ya fadi duk abin da ya ke so. Sai ya shirya wannan waƙar:

فالآن صرت إلى أمية
والأمور إلى المصاير

Tarjama: Yanzu na koma zuwa Umayya, Kuma al'amura suna komawa ne ga makoma.[31]

Bayanin kula

  1. "Al-Ghadir" na Al-Amini. juz 2 shafi na 195
  2. Al-Aghani" na Al-Isfahani juz 17 shafi na 30
  3. Abu al-Faraj al-Isfahani, Al-Aghani, 1994M, Juzu'i na 17, Shafi na 28.
  4. Amin, A'yan al-Shi'a, 1403H, Juzu'i na 9, Shafi na 34; Amini, Al-Ghadir, 1368H, Juzu'i na 4, Shafi na 32.
  5. Al-Asadi, Diwan al-Kumait, Shafi na 8.
  6. Ibn Asakir, Tarikh Madinati Dimashk, Juzu'i na 50, Shafi na 232.
  7. Al-Baghdadi, Khazanat al-Adab, Juzu'i na 1, Shafi na 153-154
  8. Al-Isfahani, Al-Aghani, Juzu'i na 17, Shafi na 5.
  9. Amini, Al-Ghadir, Juzu'i na 2, Shafi na 197.
  10. Al-Isfahani, Al-Aghani, Juzu'i na 17, Shafi na 30.
  11. Al-Isfahani, Al-Aghani, Juzu'i na 17, Shafi na 30.
  12. Al-Isfahani, Al-Aghani, Juzu'i na 17, Shafi na 30
  13. Al-Isfahani, Al-Aghani, Juzu'i na 17, Shafi na 30.
  14. Al-Isfahani, Al-Aghani, Juzu'i na 5, Shafi na 17.
  15. Al-Fakhouri, Al-Jami' fi Tarikh al-Adab al-Arabi, Shafi na 458.
  16. Shubbar, Adab al-Tuff, Juzu'i na 1, Shafi na 181
  17. Ibn Shakir, Uyun al-Akhbar, Juzu'i na 1, Shafi na 397.
  18. Amini, Al-Ghadir, Juzu'i na 2, Shafi na 166.
  19. Ibn al-Nadim, Al-Fihrist, Shafi na 183
  20. Ibn al-Nadim, Al-Fihrist: Shafi na 107 da 225. .
  21. Ibn Asakir, Tarikh Ibn Asakir, Juzu'i na 4, Shafi na 429
  22. Amini, Al-Ghadir, Juzu'i na 2, Shafi na 166.
  23. Al-Isfahani, Al-Aghani, Juzu'i na 17, Shafi na 26.
  24. Al-Amin, A'yan al-Shi'a, Juzu'i na 9, Shafi na 36.
  25. Al-Fakhouri, Al-Jami' fi Tarikh al-Adab al-Arabi, Shafi na 458.
  26. "Al-Rawdah Al-Mukhtarah" na Al-Dhahabi.
  27. Mausu'atul Shi'iril Arabi, Sa'alabi, Al-I'jaz wa al-Ijaz shafi na 98
  28. Sharif al-Radi, Al-Majazat al-Nabawiyyah, Shafi na 193-218-279-323-337.
  29. Amini, Al-Ghadir, Juzu'i na 2, Shafi na 199.
  30. Amini, Al-Ghadir, Juzu'i na 2, Shafi na 199.
  31. "Al-Ghadir" na Al-Amini. juz 2 shafi na 200

Nassoshi

  • Ibn Asakir, Ali bin al-Hasan, "Tarikh Madinati Dimashk", gyara: Ali Shiri, Beirut, Dar al-Fikr, 1415 H.
  • Al-Asadi, Kumait bin Zaid, "Diwan al-Kumait bin Zaid al-Asadi", gyara: Muhammad Nabil Tarifi, Beirut, Dar Sader, bugu na 1, 2000 M.
  • Al-Isfahani, Abu al-Faraj, Ali bin al-Husayn bin Muhammad bin Ahmad bin al-Haytham al-Marwani al-Umayyad, "Al-Aghani", Beirut, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, ba tare da shekara ba.
  • Al-Amini, Abdul Husayn bin Ahmad al-Amini al-Tabrizi al-Najafi, "Al-Ghadir", Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, bugu na 4, 1977 M
  • Al-Baghdadi, Abdul Qadir bin Umar, "Khazanat al-Adab", gyara: Muhammad Nabil Tarifi/Emil Badi' al-Ya'qub, Beirut, Dar al-Kutub al-Ilmiyya, bugu na 1, 1998 M.
  • Al-Dhahabi, Muhammad bin Ahmad, "Al-Rawdah al-Mukhtarah" (Sharhin Qasa'id Hashimiyyat al-Kumait da Alawiyyat Ibn Abi al-Hadid), Beirut, Mu'assasat al-A'lami, ba tare da shekara ba.
  • Al-Dhahabi, Muhammad bin Ahmad, "Siyar A'lam al-Nubala", gyara: Shu'ayb al-Arna'ut / Husayn al-Asad, Beirut, Mu'assasat al-Risala, bugu na 9, 1993 M.
  • Al-Sharif al-adi, Muhammad bin al-Husayn, "Al-Majazat al-Nabawiyyah", gyara: Muhammad al-Zayni, Qum, Manshurat Maktabat Basirati, ba tare da shekara ba.
  • Al-Fakhouri, Hanna, "Al-Jami' fi Tarikh al-Adab al-Arabi", Beirut, Dar al-Jil, 1986 M.
  • Al-Qummi, Muhammad bin al-Hasan, "Al-Aqd al-Nadid wa al-Durr al-Farid", Qum, Dar al-Hadith li al-Tiba'a wa al-Nashr, 1423 H.
  • "Mawsu'at al-Shi'r al-Arabi", Mu'assasat Muhammad bin Rashid Al Maktoum, ba tare da shekara ba, 2009 M.