Ranar Ghadir (Larabci: عيد الغدير) dai shi ne ranar 18 ga Zul-Hijja kuma yana ɗaya daga cikin manyan bukukuwan ‘yan Shi’a , wanda ranar ne aka nada Imam Ali (A.S) a matsayin magajin Annabi (S.A.W). An ruwaito Hadisan Annabi (S.A.W) da Imamai (A.S) game da falalar wannan rana. Haka nan kuma a wannan rana an yi umarni da aiyuka kamar Azumi, karanta ziyarar Ghadir da ciyar da muminai 'Yan Shi'a na murnar wannan rana. Ana ba da hutun ranar Ghadir a hukumance a ƙasar Iran, kuma al'ummar ƙasar na zuwa ziyara gidajen Sharifai a wannan rana.

Bikin Idin Ghadir A filin Waliyin Asar Tehran Shekara 2021

Labarin Abin da Ya Faru A Ranar

Manzon Allah (S.A.W) ya tashi daga Madina zuwa Makka[1] a Zul-Qi'dah shekara ta 10 bayan hijiri kamari tare da dubban jama'a don yin aikin Hajji,[2] bayan kammala aikin Hajji sai ya ɗau hanyar garin Madina tare da Musulmi,suna isa wani guri da ake kira Ghadir Khum a ranar 18 ga Zul- Hijja[3] Jibrilu ya sauka bisa umarnin Allah ga Annabi (S.A.W)kuma ya umurci Manzon Allah (S.A.W) da ya gabatar da Ali (a.s) ga mutane a matsayin magajinsa.[4] dan haka yatara mahajjata kuma ya gabatar da Ali (a.s) a matsayin magajinsa ɗin.[5]

Falalar Ranar Ghadir

Dangane da falalar ranar Ghadir, an ruwaito wasu hadisai daga ma'asumai kamar:

  • Annabi (SAW) yana cewa: Ranar Ghadir khum ita ce mafificiyar Idin al’ummata kuma ita ce ranar da Allah Ya kammala addini kuma ya cika ni’ima ga Al’ummata, ya kuma amince da Musulunci a matsayin addininsu. Sheikh Saduq, Al-Amali, Al-Bathah Foundation, shafi na 188.
  • Imam Sadiƙ (A.S): Ghadir shi ne idi mafi girma da ɗaukaka ga musulmi, wanda ya cancanci godiya ga Allah a kowace sa’a kuma mutane su yi azumin godiya a ranar , domin azumin wannan rana yana daidai da ibadar shekara sittin[6]
  • Imam Sadiƙ (a.s) ya ce: “Ranar Ghadir Khum ita ce babbar Idin Allah, Allah bai aiko wani Annabi ba, face sai ya riƙi wannan rana a matsayin Idi kuma ya gane girmanta da falalarta, wato duk Annabawan Allah Sun shaida da wan nan rana tin kafin zuwanta. kuma Allah ya sanya wa wannan rana suna a sama, ranar alkawari da yarjejeniya a kan ƙasa, kuma duk wanda yazoyarci hajjatul wada'a ya shaida hakan.[7]
  • Imam Rida (A.S) yana cewa: “Ranar Ghadir ta fi shahara a tsakanin Mutanen sama fiye da mutanen duniya... Da mutane sun san ƙimar wannan rana kuma sun riƙeta sunyi aiki da abinda aka faɗa a ranar da babu shakka Mala’iku sun yi musabaha da su sau goma a kowace rana. rana." [8]

Nasibi Shafi'i daya daga cikin Malaman Ahlus-sunna cikin Littafin Madalibu Su'al ya bayyana cewa Ranar 18 ga watan Zil hijja Rana ce ta Idi [9] yace Rana ce da mutane suke taruwa suyi murna da biki, saboda lokacin da Manzon Allah ya `nada Ali a da wannan matsayi da kebantarsa da shi, babu wani mutum da yayi tarayya da shi a wannan matsayi nasa [10] a bayanin Ibn Khalkan cikin Littafin Wfayatul A'ayan, tareda Musta'ala Bn Muntasir daga Sarakun Misra cikin 18 ga watan Zul Hijja da ta kasance ranar Idin Ghadir [11]

Bikin Ranar Ghadir

 
Bikin Ranar Wilya a birnin Hajja kasar Yaman

Hassan Bn sabit shi ne mutum na farko a gaban Manzon Allah (S.A.W) a ranar Ghadir daya fara tashi yaya murna da wannan rana a cikin jama'ar musulmi da suka halarci Ghadir Khum kuma ya karanta waƙoƙinsa da ya rubuta da izinin manzon Allah.[12] Kamar yadda aka ruwaito a cikin Bihar al-Anwar daga Fayad bin Muhammad bin Umar ɗusi, Imam Rida (A.S) ya ɗauki ranar Ghadir a matsayin Idi. Yana azumi kuma yayi buɗa baki tare da sahabban sa, da kuma aika abinci da kyaututtuka ga iyalansu[13] Mas'udi masanin tarihi na ƙarni na hudu ya rubuta a cikin littafin dur Al-Tanbih wal-Ashraf cewa ‘ya’ya da ‘yan Shi’ar Imam Ali (A.S) suna girmama wannan rana [14] KulAini (ya rasu a shekara ta 328 bayan hijira), shi ma me rawaito hadisi na ƙarni na 4, ya ruwaito cewa ‘yan Shi’a suna biki a wan nan rana.[15] Domin nuna muhimmancin wannan idi, gwamnatin Alu Babawaihi ta ayyana shi a matsayin ranar hutu tare da ƙarfafa gwiwar hukumomin gwamnati da jama'a wajen gudanar da bukukuwa da kuma ƙawata garuruwa, [16] suna yin amfani da ganguna da kakaki wajen bukukuwan. suna zuwa gurare masu daraja su yi Salla raka'a biyu ta godiya, su yanka rakuma , da dare sai su kunna wuta a tsakar gida su yi murna.[17] Gardizi ya kawo a littafin sa wannan rana a matsayin ɗaya daga cikin manyan ranaku na Musulunci da bukukuwan ‘yan Shi’a.[18] A Kasar Misra, khalifofin zamanin daular Fatimiya suna girmama ranar har suna hutu a hukumance , A ƙasar Irantun shekara ta 907 miladiyya lokacin da Shah Ismail Safavi ya hau karagar mulki, Ghadir ya kasance hutu a hukumance. A shekara ta 487 bayan hijira, Anwa Mustali bin Mostanser (daya daga cikin sarakunan Masar) mubaya'a a ranar Ghadir.[19]

Haka nan malaman Ahlus-Sunna sun bayyana cewa Ghadeer Khum idi ne, kamar: Nasibi Shafi'i a cikin littafin Madalibul Al-Sual: Lokacin da Manzon Allah (S.A.W) ya dawo daga Hajjatul Wada' a ranar 18 ga watan Zul Hijjah, ya kasance a wani wuri (tafkin Ghadir/ruwa) tsakanin Makkah da Madina, wanda ake ce masa Khum anan yacewa mutane duk wanda nake maulansa to Alima maulansane, shi kanshi imam Ali (A.S)yayi wata waƙa ya ambaci sunan Ghadir Khum, Kuma daganan wannan rana ta zama Idi. Kuma ya zama lokaci da wurin da jama’a ke taruwa, domin kuwa lokaci ne da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ɗora Ali a kan wannan matsayi mai girma,wanda be sanya ko ɗaya daga cikin mutane a wannan matsayi ba [20] [Lura ta 1] Ibn Khalkan ya rubuta a cikin littafin wafayatul-Ayan a cikin tarihin mubaya’a da Mustali dan Mostansir cewa ya yi masa mubaya’a ne a ranar 18 ga Zul-Hijja, wato ranar Idi -Ghadir Khum.[21] Ghadir biki ne na hukuma a Iran [22] Haka nan kuma Idin Ghadir hutu ne na hukuma a wasu garuruwan Iraƙi kamar Karbala.[23]

Ayyukan Ranar Ghadir

Asalin Makala

  • Azumi, kan asasin Abinda ya zo a riwayoyin daga Annabi (S.A.W) cikin Littafan Ahlus-sunna duk wanda ya yi azumi a Ranar 18 ga watan Zul Hijja Allah zai Bashi Ladan Azumin wata shida [24]]], Najaf da Zikar. Haka nan ‘yan Shi’a suna ganin daren Idin Ghadir a matsayin babban dare kuma suna raya daren
  • fadin wannan addu'a yayin da ka hadu da dan'uwanka Mumini(Alhamdulillahi Allazi Ja'alana minal Mutamassikin bi wilayati Amirul Muminin Ali wal A'immatu Alaihimu salam)[25]
  • Ziyartar Haramin Imam Aliyu (A.S) Wanka, karanta ziyarar Aminullahi,karanta Du'a Nudba, karanta ziyarar Ghadir [26]
  • Sanya Tufafi masu tsafta, sanya Turare, cancanda ado, sadar da zumunci, yalwatawa iyali, yin godiya ga Allah bisa wannan babbar ni'ima ta wilaya, yawaita salati, yawaita ibada, ciyar da Muminai, ba da abun buda baki ga Muminai da suka azumi a ranar,[27]
  • Yin sallar Ghadir: kan asasin abin da aka nakalti daga Imam Sadiƙ (A.S) Raka'a biyu ce kowacce raka'a za a karanta Fatiha da suratu Iklas kafa goma Ayatul Kursiyu Kafa goma, suratu Kadri kafa goma. ladanta daidai yake da Hajji dari Umara dari, sannan za a samu biyan bukatun duniya da lahira [28] anayin sallar a lokacin Azhuru akwai sabanin Malamai kan yinta cikin jam'i [29]

Ladubba da Al'adu

Al'adar ziyartar Sharifai ranar Ghadir `yan Shi'a a kasar Iran da wasu kasashen musulmi a ranar Ghadir suna zuwa ziyartar Sharifai, su ma Sharifan su na ba da kyaututtuka kan farin cikin wannan rana [30]

Ciyarwa a Ranar Ghadir Yan Shi'a a ranar Ghadir suna shirya walima a Masallatai da wuraren taro [31] haka gefen Tituna suna raba kayayyakin jika Makogoro duk saboda farin cikin wannan rana, kan asasin riwayoyi da suka zo cikin littafin Misbahu Mutahajjid an nakalto cewa ciyar da Mumini a wannan rana daidai yake da ladan ciyar da Annabawa Milyan da Shahidai Milyan da Siddikai Milyan [32] kan asasin riwayar Imam Rida (A.S) ya shirya Majalisi a ranar Ghadir ya kuma gayyaci kebantattun Sahabban sa domin yin Bude baki ya kuma aika da kayan abinci zuwa ga iyalan su.[33]

Kulla Abokantaka bisa ga abin da Shaik Abbas Qummi ya nakalto daga Ladubban ranar Ghadir akwai kulla yan uwantaka da yake nuni da soyayya da kauna tsakanin ma'abota wilaya Boroujerdi, Al-Sayyid Husayn, Jamiul Ahadis Shi'a, juzu'i na 7, shafi na 414. Sheikh Abbas Qomi, Mafatihu Aljinan, ayyukan Rose Eid Ghadir kan wannan asasi ne ya zama daya daga al'adun yan Shi'a a ranar Ghadir sun yi kokarin samar da takardar lasisin jeka nayika don lamintar da yan'uwantaka tsakanin Masoya iyalan gidan Annabi (S.A.W)[34] da kuma samar karfin gwiwar hadin kafadu da kai tsakanin Musulmi

Sanin Littafi =

an yi rubuce-rubuce gameda Idul Ghadir

  • Idul Ghair Baina Subut wal-isbat,Talifin Allama Amini.
  • Idul Ghadir fi Ahadi Fatimiyin, talifin Muhammad Hadi Amini: wannan wani rubutu ne da akayi kan Ghadir a lokacin Daular Fatimiyya da ta kasance Mirsa [35]
  • Idul Ghadir Baina Subut wal-isbat

Bayanin kula

  1. Tusi, Tahhib al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 5, shafi na 474; Tabari, Tarikh al-Umm da al-Muluk, 1387H, juzu'i na 3, shafi na 148.
  2. Raqhani, Sharh al-Zarqani, 1417 AH, juzu'i na 4, shafi na 141; Tari, “Wani Tunani Kan Tarihin Wafatin Annabi” shafi na 3.
  3. Yaqoubi, Tarikh Al-Yaqoubi, Dar Sadir, juzu'i na 2, shafi na 112.
  4. Ayazi, Tafsir Alqur'an Majeed, 1422H, shafi na 184; Ayashi, Tafsir Ayashi, Maktab ilmiyya islamiyya, juzu'i na 1, shafi na 332.
  5. Ibn Athir, usdul Ghabah, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 605; Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Juzu'i na 1, shafi na 295; Belazari,
  6. Hurrul Ameli, wasal al-Shia, 1416 AH, juzu'i na 10, shafi na 443.
  7. Har Ameli, Vasal al-Shia, 1416 AH, juzu'i na 8, shafi na 89.
  8. Tusi, Tahzeeb al-Ahkam, 1365, juzu'i na 6, shafi.24.
  9. Nasibi, Madalibul-Su'al, 1419 Hijira, shafi na 64.
  10. Nasibi, Madalibul-Su'al, 1419 Hijira, shafi na 79
  11. Ibn Khalkan, Wafayatul A'ayan, Dar Sader, juzu'i na 17, shafi na 180.
  12. Sayyid Radhi, Kasa'isu A'Imama, 1406q, shafi na 42.
  13. Tusi, Misbah al-Mutahjad, 1411H, juzu’i na 2, shafi na 752.
  14. Masoudi, Al-Tanbiyyah wa Al-Ashraf, 1357H, shafi na 221.
  15. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 149.
  16. Ibn Kathir, al-Badaiya wa al-Nahaiya, 1408H, juzu'i na 11, shafi na 276.
  17. Ibn Jozi, al-Muntazem fi Tarikh al-Umm da al-Muluk, 1412 AH, juzu'i na 15, shafi na 14.
  18. Gardizi, Zain al-Akhbar, 1363, shafi na 466.
  19. Amini, Eid al-Ghadir fi Ahadi Fatimayin, 1376, shafi na 64-65.
  20. Nikzad Tehrani da Hamzah, Tashayyu wa Tarik ijtima'iyyeh Iraniyan dar Asri Safawi, shafi na 131.
  21. لایحه قانونی تعیین تعطیلات رسمی کشور، وبسایت مرکز پژوهش‌های مجلس شورای اسلامی.
  22. «حال و هوای نجف اشرف در عید غدیر و تعطیلی ۱۰ استان عراق»، خبرگزاری تسنیم.
  23. Thaalabi, Thamar al-Qulob, 1424H, shafi na 511.
  24. Khatib al-Baghdadi, Tarik Baghdad, Dar al-Kitab al-Alamiya, juzu'i na 8, shafi na 284.
  25. Qomi, Mufatih al-Janan, karkashin ayyukan 18 ga watan Zul-Hijjah.
  26. Shahidi I, Al-Mazar, 1410H, shafi na 64.
  27. Qomi, Mufatih al-Janan, karkashin ayyukan 18 ga watan Zul-Hijjah.
  28. Tusi, Tahzeeb al-Ahkam, 1365, juzu'i na 3, shafi na 143.
  29. Bahrani, Alhada'ek Annadira, Islamic Publishing Corporation, juzu'i na 11, shafi na 87.
  30. «عید سادات و سیادت در فرهنگ ایرانی»، جوان آنلاین.
  31. «برپایی سفره‌های اطعام غدیر در مساجد استان زنجان»، خبرگزاری شبستان.
  32. Tusi, Misbah al-Mutahjad, 1411H, juzu’i na 2, shafi na 758.
  33. Tusi, Misbah al-Mutahjad, 1411H, juzu’i na 2, shafi na 752.
  34. «احیای سنت غدیریِ عقد اخوت در پویش برادرانه»، خبرگزاری شبستان.
  35. Amini, Eid al-Ghadir fi Ahadi Fatimayin, 1376, shafi na 41.

Nassoshi

  • Tusi, Tahzib al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 5, shafi na 474; Tabari, Tarikh al-Umm wa al-Muluk, 1387H, juzu'i na 3, shafi na 148.
  • Zarqani, Sharh al-Zarqani, 1417 AH, juzu'i na 4, shafi 141; Tari, Ta'ammul fi Wafatin Annabiyi”, shafi na 3.
  • Yaqoubi, Tarikh Al-Yaqoubi, Dar Sadir, juzu'i na 2, shafi na 112.
  • Ayazi, Tafsir Alqur'an, 1422H, shafi na 184; Ayashi, Tafsir Ayashi, Maktabu ilmiyya Islamiyya, juzu'i na 1, shafi na 332.
  • Ibn Athir, usdul Ghabah, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 605; Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Juzu'i na 1, shafi na 295; Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 111-110; Ibn Kathir, al-Badaiya wa al-Nahaiya, 1407H, juzu'i na 7, shafi na 349.
  • Sheikh Sadouq, Al-Mali, Al-Baath Foundation, shafi na 188.
  • Hurrul Ameli, wasael al-Shia, 1416 AH, juzu'i na 10, shafi na 443.
  • Haramili, Vasal al-Shia, 1416 AH, juzu'i na 8, shafi na 89.
  • Tusi, Tahzeeb al-Ahkam, 1365, juzu'i na 6, shafi.24.
  • Nasibi, Madalubl al-Sual, 1419 Hijira, shafi na 64.
  • Nasibi,Madalubul Al-Sual, 1419 AH, shafi na 79.
  • Ibn Khalkan, Wafayatul Al-Ayan, Dar Sadir, juzu'i na 17, shafi na 180.
  • "Buki 10 Jashanu Eidul Ghadir - 2", kamfanin dillancin labarai na Barna.
  • Sayyid Razi, Kasa'is A'imama, 1406H, shafi na 42.
  • Tusi, Misbah al-Mutahjad, 1411H, juzu’i na 2, shafi na 752.
  • Masoudi, Al-Tanbiyyah wa Al-Ashraf, 1357H, shafi na 221.
  • Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 149.
  • Ibn Kathir, al-Badaiya wa al-Nahaiya, 1408H, juzu'i na 11, shafi na 276.
  • Ibn Jozi, al-Muntazem fi Tarikh al-Umm da al-Muluk, 1412 AH, juzu'i na 15, shafi na 14.
  • Gardizi, Zain al-Akhbar, 1363, shafi na 466.
  • Amini, Eid al-Ghadir fi Ahadi zFatimiyin, 1376, shafi na 64-65.
  • Nikzad Tehrani da Hamzah, Tarik Tashayyu wa Ijtima Iraniyan fi Asri Safawi", shafi na 131.
  • Kudirin doka na kayyade ranakun hutu na kasar, gidan yanar gizon Cibiyar Bincike na Majalisar Musulunci.
  • "Halin Najaf Ashraf a lokacin Eid al-Ghadir da kuma rufe larduna 10 na Iraki", kamfanin dillancin labarai na Tasnim.
  • Thaalabi, Thamar al-Qulob, 1424H, shafi na 511.
  • Khatib al-Baghdadi, Tarihin Baghdad, Dar al-Kitab al-Alamiya, juzu'i na 8, shafi na 284.
  • Qomi, Mufatih al-Janan, karkashin ayyukan 18 ga watan Zul-Hijjah.
  • Shahidi I, Al-Mazar, 1410H, shafi na 64.
  • Qomi, Mufatih al-Janan, karkashin ayyukan 18 ga watan Zul-Hijjah.
  • Tusi, Tahzeeb al-Ahkam, 1365, juzu'i na 3, shafi na 143.
  • Bahrani, al-Hadaiq al-Nadrah, Al-Nashar al-Islami Foundation, juzu'i na 11, shafi na 87.
  • "Eid Sadat da Mulki a Al'adun Iran", Javan Online.
  • «برپایی سفره‌های اطعام غدیر در مساجد استان زنجان»، خبرگزاری شبستان، درج مطلب، ۱۸ تیر ۱۴۰۱ش، مشاهده ۱۹ ین ۱۴فرورد۰۲ش.
  • Tusi, Misbah al-Mutahjad, 1411H, juzu’i na 2, shafi na 758.
  • Tusi, Misbah al-Mutahjad, 1411H, juzu’i na 2, shafi na 752.
  • Al-Jordi, Al-Sayyid Hossein, Jama'i Ahadith Shi'a, juzu'i na 7, shafi na 414. Sheikh Abbas Qomi, Mufatih al-jinan, ayyukan Idi na Ghadir
  • " «احیای سنت غدیریِ عقد اخوت در پویش برادرانه»، خبرگزاری شبستان. تاریخ انتشار: ۴ مرداد ۱۴۰۰ش، تاریخ بازدید: ۱۵ خرداد ۱۴۰۲ش..
  • Amini, Eid al-Ghadir a zamanin Fatimayin, 1376, shafi na 41.
  • Nassoshi
  • Ibn Athir, Ali Ibn Muhammad, Asad al-Ghaba fi Marafah Sahabah, Beirut, Darul Fikr, 1409H.
  • Ibn Jozi, Abul Faraj, Al-Muntazem fi Tarikh al-Umms va al-Muluk, wanda Muhammad Abd al-Qadir Atta ya yi bincike a Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, bugu na farko, 1412H.
  • Ibn Khalkan, Ahmad bin Muhammad,Wafayat A'ayan, bincike na Ehsan Abbas, Qum, Al-Sharif al-Razi, 1364.
  • Ibn Kathir, Ismail bin Omar, al-Badaiya wa al-Nahaiya, Bija, Darul Fikr, 1407H.
  • " «احیای سنت غدیریِ عقد اخوت در پویش برادرانه»، خبرگزاری شبستان. تاریخ انتشار: ۴ مرداد ۱۴۰۰ش، تاریخ بازدید: ۱۵ خرداد ۱۴۰۲ش..
  • Amini, Abdul Hossein, Al-Ghadir Fi Al-Kitab da Sunnah, Qum, Al-Ghadir Center for Islamic Studies, bugun farko, 1416 Hijira.
  • Amini, Mohammad Hadi, Eid al-Ghadir a zamanin Fatimiyya, Tehran, Mu’assasa Al-Afaq, 1376/1417H.
  • Ayazi, Al-Sayyid Muhammad Ali, Tafsirin Al-Qur'an al-Majid al-Mustajharj Man Tarath al-Sheikh al-Mufid, Qum, Cibiyar Wallafa na ofishin yada farfagandar Musulunci, 1422H.
  • Bahrani, Yusuf bin Ahmad, al-Hadaiq al-Nadrah fi Ahkam al-Utrah al-Tahira, bincike ta Mohammad Taqi Irwani, Qum, Al-Nashar al-Islami Foundation of Jamaat al-Madrasin, Beta.
  • Balazori, Ahmad bin Yahya, Ansab al-Ashraf, wanda Sohail Zakkar da Riaz al-Zarkali suka yi bincike a Beirut, Darul Fikr, 1417H.
  • ".
  • «برپایی سفره‌های اطعام غدیر در مساجد استان زنجان»، خبرگزاری شبستان، درج مطلب، ۱۸ تیر ۱۴۰۱ش، مشاهده ۱۹ ین ۱۴فرورد۰
  • Tari, Jalil, “Ta'ammul fi wafati Annabi”, Rubu’in Tarihin Musulunci, Quarterly, Kum, Jami’ar Baqir Al-Uloom, 1379.
  • Thaalabi, Abd al-Malik bin Muhammad, Simarul Kulub fi al-Mazaf da al-Mansoob, Muhammad Abu al-Fazl Ibrahim ya yi bincike a Beirut, Mazhabar Asriyah, 1424H.
  • "Halin Najaf Ashraf a lokacin Eid al-Ghadir da kuma rufe larduna 10 na Iraki", kamfanin dillancin labarai na Tasnim, wanda aka buga a ranar 27 ga Yuli, 1401, wanda aka gani a ranar 19 ga Afrilu, 1402.
  • Hurrul Amili, Muhammad bin Hasan, Al-Wasael al-Shi'a, Al-Bait Foundation for Revival of Tradition, Qum, 1416H.
  • Khatib al-Baghdadi, Tarihin Baghdad, bincike na Mustafa Abdul Qadir Atta, Dar al-Kitab al-Alamiya, Beirut, B.T.A.
  • Rizqani, Muhammad bin Abd al-Baqi, Sharh al-Allamah al-Zarqani Ali al-Mahaweh al-Lundaniyyah in Menah al-Muhammadiya, Beirut, Dar al-Kutb al-Alamiya, 1417 AH.
  • Sayyed Ibn Tawoos, Ali Ibn Musa, Iqbal al-Amal, Al-Nashar al-Taabi Publishing Center of Al-Alam Al-Islami School, Qom, 1377.
  • Sayyid Razi, Muhammad bin Hussain, Kasa'isul A'Imamai, Mashhad, kofar Razawi, Majma al-Pakhuh al-Islami, 1406H.
  • Shahid Awwal, Muhammad bin Makki, al-Mazar, bisa kokarin Sayyid Mohammad Baqer Mohd Abtahi, Qum, Imam al-Mahdi (AS), 1410H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Al-Mali, Al-Baath Foundation.
  • Tousi, Mohammad Bin Hassan, Tahzib Al-Ahkam, Seyyed Hassan Mousavi, Khorsan, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, Misbah al-Mutahjad da Selah al-Mutabbad, Fiqh al-Shi'a Foundation, bugu na farko, 1411H.
  • Ayyashi, Mohammad Bin Massoud, Tafsir Ayyashi, Rasouli Mahalati Research, Tehran, Islamic Theological School, Beta.
  • Qomi, Mufatih al-Jannan.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, al-Kafi, Ali Akbar Ghafari, Dar al-Kitab al-Islamiya, Tehran, 1407H.
  • Gardizi, Abu Syed, Zain Al-Akhbar, Tehran, Littafin Duniya, Mujalladi na 1, 1363.
  • Kudirin doka don tantance hukunce-hukuncen hukuma na ƙasar, gidan yanar gizon Cibiyar Nazarin Majalisar Islama, wanda aka duba ranar 19 ga Afrilu, 1402.
  • "لایحه قانونی تعیین تعطیلات رسمی کشور، وبسایت مرکز پژوهش‌های مجلس شورای اسلامی، مشاهده ۱۹ فروردین ۱۴۰۲ش.
  • Masoudi, Ali bin Hossein, Tabiyeh wa al-Ashraf, Dar al-Sawi, Alkahira, 1357H.
  • " «مهمانی ۱۰ کیلومتری به مناسبت عید غدیر - ۲»، خبرگزاری برنا، درج مطلب ۲۷ تیر ۱۴۰۱، مشاهده ۱۹ فروردین ۱۴۰۲ش.