Ƙissar Rahba

Daga wikishia

Ƙissar Rahba (Larabci: يوم الرحبة) ko Munashadar Rahba ƙissa ce da take ishara zuwa ga shaida da wasu adadin Sahabbai suka bayar kan cewa lallai sun ji hadisin Ghadir da kunnuwansu daga Manzon Allah (S.A.W), wannan lamari ya faru ne bayan da Imam Ali (A.S) ya buƙace su da bayar da shaida daga adadin Sahabbai da adadinsu ya kasance tsakanin Mutum 12 zuwa 30, an naƙalto wannan ƙissa cikin litattafan Shi’a da Ahlus-sunna.

Ƙissar Da Kuma Dalilin Sanya Suna

A cewar Allama Amini, a shekara ta 25 bayan hijira dangane da abin da aka naƙalto daga kasancewar Annabi (S.A.W) ya gabatar da Imam Ali (A.S) kan Sauran Sahabbai, an samu wasu mutane sun tuhume shi kan wannan Magana tare da yin jayayya da shi dangane da Halifancinsa, da wannan dalili ne Imam Ali (A.S) ya hallara a Filin Kufa domin kare haƙƙinsa da kuma yin martani da raddi kan waɗanda suke jayayya da shi cikin lamarin Halifancinsa, ya haɗa su da Allah kan su tuna da hadisin Ghadir [1] da wannan dalili ne ake kiran ranar Rahba da sunan Munashadatu Rahba (rantsuwar Rahhba) saboda Hazrat Ali (A.S) a farkon fara maganarsa ya yi amfani da kalmar Anshidullaha (ina rantsuwa da Allah) ya nemi waɗanda suka hallara a wannan wuri su bada shaida da hadisin Ghadir, [2] [yadash 1] Munashada tana nufin rantsuwa da Allah. [3] Bayan ya gama Magana, sai wasu daga cikin Sahabba suka miƙe tsaye suka bada Shaida da cewa eh lallai sun ji hadisin Ghadir daga bakin Annabi (S.A.W), na’am a wasu Masadir an naƙalto cewa wasu daga cikinsu misalin Zaidu Bn Arƙam ba su yarda sun bada shaida ba, sai Hazrat ya la’ance su, [4] na’am Sayyid Muhsin Amin ya rubuta cewa riwayoyin da suke naƙalto cewa Zaidu ya noƙe bai bada shaida ba kuskure aka yi cikin naƙalinsu, Barra’u Bn Azib ne yaƙi bada shaida ba Zaidu Bn Arƙam ba, saboda shi Zaidu Bn Arƙam daga gare shi ne aka rawaito da yawan riwayoyin Ghadir, kuma ya kasance yana fifita Hazrat Ali (A.S) kan sauran Sahabbai haka ya kasance daga kebantattun Mataimakan Hazrat Ali (A.S). [5]

Waɗanda Suka Bada Shaida

an samu Mabambantan naƙali kan adadin Sahabban da suka bada shaida kan cewa lallai sun ji Hadisin Ghadir daga Annabi (S.A.W), mafi karancin adadinsu shi ne mutane goma sha biyu, mafi yawansu shi ne adadin mutane talatin, Allama Amini ya ambaci adadin waɗanda suka bada shidai da aka naƙalto su a cikin litattafan Ahlus-sunna sun kasance mutane ashirin da huɗu, [6] an naƙalto daga Ahmad Bn Hanbal cewa adadin waɗanda suka bada shaida ya kai mutane talatin. [7] Abu Amra Ansari, Abu Al-Hasim Bn Al-Tihan, Abu Ayyub Ansari, Khuzaimatu Bn Sabit Ansari (ZU Shahadataini), Sahal Bn Hanif, Abu Sa’id Khudri, Sahal Bn Sa’ad Ansari, Abdullahi Bn Sabit Ansari (Khadimul Rasul) Ubaidu Bn Azib Ansari, Addi Bn Hatim, Najiyatu Bn Amru Khuza’I, Nu’uman Bn Ijlan suna daga cikin mafi shaharar cikin waɗanda suka bada shaida. [8]

Wuri Da Lokaci

Abin da ake nufi da Rahba wani fili ne da yake tsakiyar Masallacin Kufa, wanda a galibin lokuta a wannan fili ne Imam Ali (A.S) yake zama ya yi Alƙalanci ko wa’azi, [9] kamar yanda aka bayyana a zamanin Zayad Bn Abihi sakamakon tsananin tsoro marawaitan Hadisi maimakon ambaton sunan Imam Ali (A.S) suna amfani da sunan (Sahibul Rahba), 10 duk da cewa Rahba zai iya kasancewa tana da wasu Misdaƙan daban. [10] ƙissar Rahba ta faru ne a shekara ta 35 bayan hijira, [11] a farkon Halifanci Imam Ali (A.S), a cikin riwayar da Ya’ala Bn Mu’alla ya naƙalto, ya zo cewa: Lokacin da Amirul Muminin (A.S) ya shiga Kufa, ya yi wannan munazarar. [12]

Alameh Amini ya ambaci adadin maruwaitan Manasheda na Rahba – wadanda suka rawaito domin Xabaqoqin da za su zo daga bayan – kamar 18, daga cikinsu huxu Sahabbai ne, goma sha hudu kuma Taabi’in ne. [13]:

Sahabbai: 1-Haba bin Joyn Arani 2-Zaid bin Arqam 3-Amer bin Wathla 4-Yaali bin Marra bin Wahb Thaghafi Tabi'ai: 1-Abu Suleiman Al-muezzin 2-Asgba bin Nabateh 3-Zazan Abu Amr 4-Zar bin Habish 5-Ziyad bin Abi Ziyad 6-Zayd bin Yathi Hamdani 7-Sa'id bin Abi Hadan 8-Saeed bin Wahb Hamdani 9-Abu Amara Abd Khair bin Yazid Hamdani 10-Abd al-Rahman bin Abi Laili 11-Amr Dhi Marra 12-Umira bin Saad Hamdani 13-Hani bin Hani Hamdani 14-Haritha bin Nasr [14]

Bayanin kula

  1. Amini, Al-Ghadir, 1416 Hijira, Mujalladi na 1, shafi na 339.
  2. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 4, shafi na 74.
  3. Dehkhoda,Luggatname, zaili "Manashed"
  4. Halabi, Sireh Halabiyeh, 1353 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 308.
  5. Al-Amin, Ayan al-Shia, juzu'i na 7, shafi na 88.
  6. Amini, Al-Ghadir, 1416 AH, Juzu'i na 1, shafi na 376-377.
  7. Amini, Al-Ghadir, 1416 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 377.
  8. Amini, Al-Ghadir, 1416 AH, Juzu'i na 1, shafi na 376-377.
  9. Matrazi, Maghreb, juzu'i na 1, shafi na 324.
  10. Hosseini Tehrani, ImamShinasi, 1427 AH, juzu'i na 9, shafi na 41.
  11. Amini, Al-Ghadir, 1416 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 377.
  12. Hosseini Tehrani, Imamshinasi, 1427 AH, juzu'i na 9, shafi na 41.
  13. Amini, Al-Ghadir, 1416 Hijira, Mujalladi na 1, shafi na 339.
  14. Amini, Al-Ghadir, 1416 AH, Juzu'i na 1, shafi na 339-376.

Nassoshi

  • Abd al-Hamid bin Hebatullah, Sharh Nahj Al-Balaghah, Qum, wanda maktabat Ayatullahi Uzma Al-Mar'ashi Al-Najafi ta buga, 1404H.
  • Amini, Abdul Hossein, Al-Ghadir, Qum, Al-Ghadir center, 1416 AH.
  • Hosseini Tehrani, Seyed Mohammad Hossein, Imamshinasi, Mashhad, Allamah Tabatabai bugu, 1427H.
  • Halabi Shafi'i, Ali bin Burhan al-Din, Sire Halabiyyah, Masar, 1353H.
  • Madani, Ali Khan bin Ahmad, bugu na farko, Mashhad, Al-Al-Bait Lahia Al-Trath Foundation, 2004.
  • Mutarzi, Nasser bin Abd al-Said, Maghreb, Edited by Mahmoud Fakhouri da Abd al-Hamid Mukhtar, Aleppo, School of Osama bin Zayd, 1979.