Ali Bn Abi Rafi'i

Daga wikishia

Ali ɗan Abi Rafi'i (arabic: علي بن أبي رافع) marubuci ne kuma mai kula da baitul-mali a zamanin halifancin imam Ali (A.S) mahaifinsa abu rafi'i sanannan sahabin Manzon Allah (S.A.W) ne.

Ali Bn Rafi'i tabi'i ne kuma ɗaya daga mabiyan Imam Ali (A.S), a faɗar Sayyid Muhsin Amin yana daga cikin waɗanda suka halarci yaƙin Jamal, Siffin da Nahrawan a cikin tawagar Imam Ali (A.S),[1] haka nan Sayyid Muhsin Amin yana ganin shi ne mutum na fako da ya fara rubuta littafi kan fiƙihu.[2] Ahmad Bn Ali Malamin shi'a masanin Rijal ya ce , littafinsa ya ƙunshi babun Alwala da sallah, da sauran mas'alolin fiƙihu.[3] a cewar Sayyid Muhsin Amin yana daga cikin manyan ƴan shi'a da suka san fiƙihu kuma ya koyane a gun Imam Ali (A.S).[4]

Ali bin Abi Rafi'i shi ne marubucin Imam Ali (A.S) kuma ya kasance mai kula da baitul-mali a zamaninsa. Kamar yanda aka rawaito daga gare shi, a lokacin da yake aiki a ma’ajinyar kuɗi zamanin Imam Ali (AS) bisa buƙutar wata yarinya daga yaran Imam Ali (A.S) ya bata aron wata sarƙar wuya, saboda za tai amfani da ita a bikin babbar sallah, wadda tana daga cikin ganimar Yaƙin Jamal, A lokacin da imam Ali ya samu labari , sai ya kira Ibn Abi Rafi’i ya ce da shi ya mayar da abin wuyan Baitul-Mali, idan kuma ya maimaita hakan za a hukunta shi. Ya kuma ce da ace ƴata bata bada wani abu jingina ba ta karɓi abin wuyan, da ita ce macen Hashimawa ta farko da za'a fara hukuntawa.[5] An kawo wannan ruwayar a cikin bahasin aron abu daga baitul-mali cikin a littattafan fiƙihu .

Bayanin kula

  1. Amin, Ayan al-Shia, 1406 AH, juzu'i na 8, shafi na 151.
  2. Amin, Ayan al-Shia, 1406 AH, juzu'i na 8, shafi na 151.
  3. Najashi, Rizal, 1397 AH, shafi na 5.
  4. Amin, Ayan al-Shia, 1406 AH, juzu'i na 8, shafi na 151.
  5. Tusi, Tahzeeb al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 10, shafi na 151.

Nassoshi

  • امین، محسن، اعیان الشیعة، بیروت، دارالتعارف، ۱۴۰۶ق/۱۹۸۶م.
  • شیخ طوسی، محمد بن حسن، تهذیب الاحکام، تحقیق حسن موسوی خرسان، دارالکتب الاسلامیه، تهران، ۱۴۰۷ق.
  • نجاشی، احمد بن علی، رجال، قم، مکتبة الداوری، ۱۳۹۷ق.