Alwala
- Wannan wata ƙasida ce mai bayyanawa game da mafhumi na fiƙihu kuma ba za ta iya zama ma'auni na ayyukan addini ba. a Koma zuwa wasu tushen don ayyukan addini.
Alwala (Larabci: الوضوء) ita ce wanke fuska da hannaye tare da shafar kai da ƙafafuwa da nufin neman kusanci ga Allah da ibada ta musamman. Yin Alwala a kan kankin kansa mustahabbi ne kuma abu ne da ake so mutum ya kasance cikin sa. Amma tana daga sharaɗin ingantar sallah da ɗawafi da sauran ibadu da yinsu sai da alwala. ba ya halatta a taba layukan Alkur'ani da sunan Allah, in mutum bai da Alwala, Ana son a yi alwala a lokuta kamar zuwa masallaci da karatun Alƙur'ani mai girma. Kamar yadda majiyoyi na tarihi suka tabbatar da cewa, an bayar da hukunce-hukuncen alwala ne a Makka a farkon manzancin Manzon Allah (S.A.W). Aya ta shida a cikin suratul Ma'ida da kuma ruwayoyi sama da 400 na imamai maasumai, da suka shafi alwala. A cikin hadisai an ce, alwala da sabunta alwala suna haifar da tsarkake zunubai, gusar da fushi, da tsawon rai, da haskaka fuska a ranar Alƙiyama, da karuwar arziki.
Ana iya yin Alwala ta hanyoyi biyu, a ilimin fiƙihu ana kiran su tartibi da irtimasi, a alwalar tartibi itace wadda mu ke yi yau da kullum za a fara wanke fuska, sannan a wanke hannaye, sannan a shafi kai da ƙafafuwa. Alwalar irtimasi tana kama da alwalar yau da kullum wato tartibi, sai dai maimakon wanke fuska da hannaye za a tsoma su cikin ruwa da niyyar alwala, sannan a shafi kai da ƙafafuwa. Idan mutum ya ji rauni kuma bude shi da wuya ko kuma yana da illa, sai ya yi alwalar Jabira.
Shi'a da Ahlus-Sunna sun sami saɓani game da wanke hannu da kuma yanda ake shafar kai da ƙafa wajen alwala; Daga cikin abubuwan da ƴan Shi'a suke ganin wajibi ne a wanke hannu daga sama zuwa ƙasa, amma Ahlus-Sunnah sun yi imani da wanke hannu daga ƙasa zuwa sama. Kamar yadda ruwayoyi suka kawo, har zuwa ƙarshen halifancin Umar Bin Khaddab, babu wani babban bambanci a cikin alwala a tsakanin musulmi, kuma halifofi sun yi alwala irin tasu (hanyar Imami). Majiyoyin Musulunci sun ruwaito bambance-bambancen Shi'a da Ahlus-Sunna a cikin alwala daga zamanin Halifa na uku.
Sanin Mafhumi
Alwala tana nufin wanke fuska da hannaye da shafar kai da ƙafa ta hanya ta musamman da addini ya koya da nufin neman kusanci ga Allah da kuma cika umurnin Allah[1] da niyyar ibada kuma sharaɗi ne na gyaran sallah da ɗawafi, haka nan sharaɗin taba rubutun Alkur'ani.[2] Kamar yadda majiyoyi na tarihi suka ruwaito cewa, mala'ika Jibrilu ne ya koyar da alwala ga Manzon Allah (S.A.W) a Makka farkon turoshi da sakon Annabci, kuma Annabi Mafi Karamci (S.A.W) ya bayyana wa mutane.[3] Hukunce-hukunce da Hanyar yin alwala da kuma muhimmancinta ya zo a cikin Al ƙur'ani da hadisai[4]
Hukunce-Hukuncen Alwala
Ankawo umarnin yin alwala a aya ta shida a cikin suratul Ma'idah, don haka ake karanta da ayar Alwala:
[5] Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kun tashi yin sallah, to ku wanke fuskarku da hannayenku tare da gwiwar hannu, kuma ku shafa kanku da ƙafafunku har zuwa idon sawu.[6] Kaman yanda muka faɗa Yin alwala da akankin kanta mustahabbi ne[7] sai dai kuma ya zama wajibi yinta a lokacin yin sallah, sai sallar gawa, da yin Dawafi, da shafar layukan Alkur'ani,[8] da taba sunan Allah duk sai da Alwala, ihtiyaɗi na Wajibi shine lokacin taɓa sunayen A'imma da Hazrat Zahra (S) mutum ya yi alwala.[9] Se kuma zuwa Masallaci da haramin Imamai da karatun kur'ani da ɗaukan shi, da kawo wani sashe na jiki zuwa ga rufin kur'ani, da ziyartar Kaburbura.[10]
Nau'o'in Alwala
Ana iya yin Alwala a jere (tartibi) ko kuma irtimasi[11] kuma a wasu yanayi ya wajaba a yi ta ta hanyar Jabira.
Alwala Tartibi
Ita ce Alwala ta jerantawa: na farko dole ne mutum ya wanke fuska; Daga wurin da gashi ke tsirowa har zuwa ƙarshen haɓa, faɗin hannu ɗaya. Sannan a wanke hannun dama da farko sannan a wanke hannun hagu, daga ɗan saman da gwiwar hannu take zuwa babban yatsan hannu. Bayan haka, da sauran damshin da ya rage daga wanke hannaye, sai a shafa kai a gaban kai da kuma saman goshi, sannan kuma da danshin daya rage zaashafi ƙafar dama da ƙafar hagu.[12]
Alwala irtimasi
Itace alwalar da mutum bayan niyya[13] ya sanya fuskarsa sannan ya sanya hannayensa a cikin ruwa da niyyar alwala, ya yi niyya yin alwala, sannan ya fitar da su daga cikin ruwan[14] bayan wanke fuska da hannaye, sau ya shafi kansa da ƙafarsa.[15]
Alwalar Jabira
Alwalar Jabira ita ce: Idan aka samu rauni ko karaya a ɗaya daga cikin sassan jiki da ake wankwa ko gogewa a cikin Alwala, kuma ba za a iya wankewa ko gogewa ba, to sai a yi Alwala kamar yadda aka saba, maimakon a wanke ko goge gun wanda ya samu rauni ko ya karye. sea shafi kan gun[16] Tufafi ne ko wani abu da ake amfani da shi don rufe rauni,[17] duk hakan ana yinsa ne sai idan baza a iya buɗe ciwan ba ko in aka zuba ruwa akwai cutuwa.[18]
A wasu lokuta, Taimama yana wajaba a maimakon alwala; Misali idan lokacin sallah ya ƙurewa mutum ta yadda yin alwala da salla zai sa lokacin sallar ya fita ko wani sashin lokacin ko rashin ruwan gaba ɗaya ko cutarwar da ruwan zai yiwa ciwan za a iya taimama amemakon alwala wanda ya yi wankan janaba inyanasan yayi Sallah alokacin ba buƙatar yin Alwala wankan ya isar masa, wato za maye gurbin alwala.
Ta yaya Alwala Take Baci?
Alwala tana ɓaci ta hanyoyi da dama, yazo acikin littattafan fiƙihu, abubuwan da suke ɓata alwala (abubuwan da suke warware alwala) ana kiransu da Hadasul Asgar (ƙaramin kari)[19] daga cikin su akwai:
- Fitar fitsari, najasa ko iska(tusa) daga mutum.
- Barci (idon kunnuwa ba za su ji ba, idanu ba su ganiba), hauka, buguwa da kayan maye.[20]
- Abubuwan da ke suke wajabbta wanka, Kamar janaba da shafar gawar Mamaci.[21][22]
A cewar Fadilul Mikda, wani malamin fiƙihu: Ahlus-Sunnah sun yi imanin cewa haɗuwar fata tsakanin namiji da mace wacce ba muharramanta ba yana ɓata alwala. Dalilinsu shine ƙiraar da ya karanta ‘lamastum' a cikin ayar “AuLamastum al-Nisa”[23] amma a cewar malaman fikihu ƴan Shi'a, “Lamastum” yana nufin jima'i.[24]
Bambancin Alwalar Shi'a da ta Ahlus-sunna
A wajen alwala akwai bambanci tsakanin `yan Shi'a da Ahlus-Sunna game da wanke hannu da kuma yadda ake shafar kai da ƙafa.[25] Bambance-bambancen da ke tsakanin yan Shi'a da Ahlus-Sunnah dangane da alwala galibi yana faruwa ne saboda sabanin fahimtar aya ta shida a cikin suratul Ma'idah, ko kuma saɓanin karantata,[26] ayar da aka ambata tana nufin wajibcin wanke hannaye tun daga sama har kasa.hakika `yan Shi'a tare da dogara da riwayoyin da suka zo daga Ma'asumai[27] sun fassara jumlar
da ma'anar wanke hannu daga sama zuwa kasa Sayyid al-Aghazi, Fiƙhu al-Sunnah, 1397 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 43. Sabanin mazhabobi guda hudu na Ahlus-Sunna waɗanda suka yi imani da wanke hannu daga kasa zuwa sama.
Haka nan a tsarin malaman fikihun Shi'a dole ne wanke hannun dama ya kasance kafin na hagu.[28] Mazhabobin Ahlus-Sunnah guda hudu suna ganin wanke kafafu tare da idon sawu a matsayin wajibi ne a cikin alwala,[36] Shi'a sun yi imani da shafar ƙafa tun daga kan yatsu har zuwa saman ƙafa a maimakon wankewa.[29] Hakanan kuma wajibi ne, kamar shafa kai, daga danshin alwala,[30] haka nan Malikiyya da Hanafiyyah ma raayinsu kenan amma a ganin Hanafiyyah da Shafiyyah jerantawa ba wajibi ne a cikin alwala. Amma ƴan Shi'a da sauran mazhabobin Ahlul Sunna suna ganin wajibi ne a kiyaye jerantasu.[31]
Yan Shi'a da Ahlus-Sunnah sun sami saɓani game da shafan kai; Ɗaya daga cikinsu shi ne, a wajen ƴan Shi'a,yin shafar kai koyayane indai ya isa a ce masa shafa to ya wadatar, kuma mustahabbi[32] ana so ya zama iya yatsun hannun dama guda uku, ba fiye da haka ba, kuma ba zai yiwu a shafa da sabon ruwa ba se ruwanda aka wanke hannun hagu dashi yayi ragowa, Mazhabobin Ahlus-Sunnah daban-daban suna da ra'ayi mabanbanta kan yadda ake shafar kai,[33] kamar yadda fiƙihu n Hanbali ya nuna, shafar gaba ɗaya har da kunnuwa biyu wajibi ne,[34] kuma za ayi amfani da sabon ruwa wajan yin shafar kan.[35] acikin fikihun Malikiyya, dole ne a goge gaba ɗayan kai[36] kuma a fi ƙhun Hanafiyya wajibi ne a goge kaso ɗaya a huɗu na kai. Ya wadatar.sai dai kuma dole ai shafar da sabon ruwa.[37] sai dai kuma a fikhun Shafi'iyya za a shafi wani mikdari ne daga Kai kuma dole ne ayi shafar da sabon ruwa[38] Shafa akan khuffain(takalmi) na daga cikin abinda akeda saɓani tsakanin sunnah da shia wanda ƴan Shi'a ba su ganin dai-dai ne yin hakan[39] kuma sun kawo aya ta 6 a cikin suratul Ma'ida da hadisai, kaman haka:[40] Imam Kazim (a.s.), a cikin martani ga wasiƙar Ali Ibn Yaƙtin wanda yake da matsayi na musamman a Halifanci na Abbasiyawa ya wajabta masa yin alwala kamar Ahlus-Sunnah (saboda taƙiyya)[41] wato kare rai , don kada Haruna Rashid ya san cewa shi ɗan Shi'a ne.[42] Imam Kazim (A.S), a baya ya nemi Ali bin Yaƙtin da ya ci gaba da zama a cikin gwamnatin Abbasiyawa saboda yi wa ƴan Shi'a hidima[43] yayin da ya hana sauran ƴan Shi'a haɗin kai da Abbasiyawa[44]
Fara Samin Sabanin Ra'ayi Ya Samo Asali daga Zamanin Khalifa Usman
Wasu malaman tarihi suna ganin babu wani bambanci a cikin alwala a tsakanin musulmi a zamanin Manzon Allah (S.A.W)[45] kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Waalihi wasallam) ya yi alwala ta hanyar shafar ƙafafunsa maimakon wankewa. Hakan a zamanin khlifa Abubakar ma hakanne sea zamanin khalifancin umar Bn khddab aka sami wani hadisi na masahu khuffaini (shafar ƙafa a kan takalmi) .amma babu wani hadisi da ke nuni da saɓani game da alwala kafin nan.[46]
Dangane da abin da ya zo a cikin Kanzul Al-ummal[47] da wasu littattafai, [58] wasu masu bincike sun yi imanin cewa bambancin alwala ya bayyana a tsakanin musulmi tun zamanin halifa na uku (Usman)[48] Sayyid Ali Shahristani, yayin da yake ishara da saɓanin Imam Ali (A.S) da Umar bin Khaɗɗab game da shafar khoffai ,yana ganin cewa halifa na biyu saɓanin Usman Bn Affan, bai wanke kafafunsa a alwala ba, sai dai ya shafe sune[49] Dangane da ayar alwala, da hadisan da su ka zo kan alwala, ƴan Shi'a sun yi imani da cewa Annabi (S.A.W) da sahabban sa sun kasance suna shafar ƙafar su wajen yin alwala maimakon wanke ta da tafarkin Ahlus-Sunna su ka yi imani akai.[50] Akwai kuma hadisai dangane da wanke hannu daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce, alwalar Annabi ta na kama da ta ƴan Shi'a wajan wanke hannu daga sama zuwa ƙasa.[51] hadisain wanke ƙafa a cikin alwala, waɗanda Ahlus-Sunnah suka kawo, sunada rauni da rashin tushe; Ban da hakama ma ya saɓa wa ayar alwala.[52]
Ladubba, Mustahabbai, Falaloli
Yayin alwala, anayin la'akari da abubuwa da yawa na mustahabbi; Ciki har da:
- Wanke baki kafin alwala (wato aswaki) Annabi (S.A.W) ya yi wasiyya da yin aswaki kafin kowace alwala a wasiyyarsa ga Imam Ali (A.S)[64].
- Ambaton sunan Allah a farkon alwala[53]
- Kurkure baki da shakar hanci.[54]
- halarto da zuciya a yayin yin alwalar.
- Karanta Suratul Kadri yayin da ake alwala,
- karanta Ayar Kursiyu bayan gama alwala.
- Ajiye butar ruwan alwala a gefen dama.[55]
Kamar yadda ya zo a hadisai daga Imam Ali (a.s.) yana karanta addu'o'i yayin alwala. A bisa waɗannan hadisai, duk wanda ya karanta waɗannan addu'o'in yana alwala, Allah zai halicci mala'ika daga kowace digon ruwan alwalarsa, yana mai tasbihi da tsarkake ubangiji da Kabbara kuma yadinga rubuta lada ga wanda ya yi alwala har zuwa ranar Alkiyama.[56] Ayyukanda ake aikatawa yayin da ake wanke kowace gaɓa ta alwala sune ;
- 1. Zuba ruwa da hannun dama a hannun hagu da furta: Godiya ga Allah, wanda ya tsarkake ruwan, bai sanya shi najasa ba;[57]
- 2. Tsarki: Ya Allah ka kare min farjina, ka kiyaye shi kuma ka lullube shi ka kiyayeni da shiga wuta.[58]
- 3. Shaƙar hanci: Ya Allah kada ka haramtamin ƙanshin Aljannah, kuma ka sanya ni amasujin ƙamshinta.[59]
- 4. Kurkure baki; Allah! Ka sanya harshena ya zama abin ambatonka, kuma ka sanya ni cikin waɗanda ka yarda da su.[60]
- 5. Wanke fuska: Ya Allah ka haskaka fuskata ranar da fuskoki ke duhu.kuma kada kabar fuskata tai dubu ranarda fuskoki ke haske.[61]
- 6. Wanke hannun dama: Ya Allah! Ka ba ni aikina a hannun damana, kada kabani da hannun hagu.[62]
- 7. Wanke hannun hagu: Ya Allah! Kada ka sanya aikina a hannun hagu na, sa'an nan kada ka sanya na kasa karɓa gaba ɗaya ,kuma ina neman tsarinka daga tufafi masu zafi na gidan wuta.[63]
- 8. Shafar kai: Ya Allah ka cikani da rahamarKa, da albarkarKa, da gafararka.[64]
- 9. Shafar ƙafafuwa: Ya Allah! Ka tabbatar da ƙafafunaa kan tafarkin siraɗi a ranar da ƙafafu suke gocewa, kuma ka sanya himmata da ƙoƙarina cikin abin da ka yarda da shi kuma ka yarda da ni.[65]
A cikin ruwayoyin Shi'a da Sunna, an ruwaito hadisai sama da 400 game da hukunce-hukuncen alwala, da sifofinta da falalolinta daga Manzon Allah (SAW) da limaman Shi'a:[66] A bisa haka, alwala tana gogewa mutum Zunubai,[67] kawar da fushi,[68] tsawon rai, haskaka fuska a ranar Mahshar,[69] da ƙaruwar arziki.[70]Haka nan akwai ruwayoyi dangane da falalar sabunta alwala a kodayaushe[71] da kuma alwala a dede take da tuba.[72]
Bayanin kula
- ↑ Fallahzadeh, Ahkam Addini, 2006, shafi 44-45; Hosseini Dashti, "Wudhu", dar Ma-arif Ma-arifi, juzu'i na 10, shafi na 370.
- ↑ Fallahzadeh, Ahkam Addini, 2006, shafi 44-45; Hosseini Dashti, "Wudhu", dar Ma-arif Ma-arifi, juzu'i na 10, shafi na 370
- ↑ Misali: Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabiwiyah, Dar al-Marifah, juzu'i na 1, shafi na 244; Tabari, Tarikh al-Umm da al-Muluk, 1387H, juzu'i na 2, shafi na 307.
- ↑ Sobhani, “Alwudu fi Kitab wa-Sunnah” shafi na 4.
- ↑ Suratul Ma'idah, aya ta 6.
- ↑ Suratul Ma'idah, aya ta 6.
- ↑ Sheikh Ansari, Kitab al-Tahara, 1415 AH, juzu'i na 2, shafi na 82.
- ↑ Faiz Kashani, Moatasim al-Shia, 1429 AH, juzu'i na 1, shafi na 241.
- ↑ Fallahzadeh, Ahkam Addin, 2006, shafi na 50.
- ↑ Fallahzadeh, Ahkam Addin, 2006, shafi na 50
- ↑ Tabatabaei Yazdi, Al-orwa Al-Wusghati, mawallafi Maktabatu Ayatullah Uzma Al-Sayed Al-Sistani, juzu'i na 1, shafi na 169-170; Makarem Shirazi, sharh Risaleh Jawanan, 1390, shafi na 38.
- ↑ Mu'assaseh Dayireh Maref Fikh Islami, Farhang Fi ƙh, 1426 AH, juzu'i na 1, shafi na 347.
- ↑ Mirzai ƙomi, Jame al-Shatt, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 32.
- ↑ «وضوی ارتماسی»، مرکز تنظیم و نشر آثار آیت الله بهجت.
- ↑ Mirzai ƙomi, Jame al-Shatt, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 32.
- ↑ Imam Khumaini, Tawzihul al-Masael, 1426H, shafi na 61.
- ↑ Falahzadeh, Ahkam Mubtala be Hujjaj, 1389 AH, shafi na 37 da 38.
- ↑ Falahzadeh, Ahkam Mubtala be Hujjaj, 1389 AH, shafi na 47-48
- ↑ Ibn Idris Hali, Al-Sarair, 1410 ƙ., Kashi na 1, shafi na 135.
- ↑ Najafi, Jawahirul Kalam, 1362, juzu'i na 3, shafi na 230.
- ↑ Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila,
- ↑ Cibiyar Gyara da Buga Ayyukan Imam Khumaini, juzu'i na 1, shafi na 50
- ↑ «غسلهایی که کفایت از وضو میکنند»،
- ↑ Faiz Kashani, Rasail, 1429 AH, Juzu'i na 2, Rasala 4, shafi na 22.
- ↑ Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa Al-Waghti, 1419 AH, juzu'i na 1, shafi na 330-331; Faiz Kashani, Moatasim al-Shia, 1429 AH, juzu'i na 1, shafi na 241
- ↑ Hosseini, “Alwudu dar Didgahe Mazahib Islami” shafi na 6.
- ↑ Hosseini, “Alwudu az Didgahe Mazahib Islami” shafi na 9.
- ↑ Hosseini, “Alwudu az Didgahe Mazahib Islami” shafi na 16
- ↑ Sayyid al-Aghazi, Fi ƙhu al-Sunnah, 1397 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 48.
- ↑ Sayyid al-Aghazi, Fi ƙhu al-Sunnah, 1397 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 44.
- ↑ Sayyid al-Aghazi, Fi ƙhu al-Sunnah, 1397 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 44.
- ↑ Hosseini, “Alwudu az Didgahe Mazahib Islami” shafi na 11-12
- ↑ ƙomi, “Fihk Hajji; cegunagi baina Farikaini(3) Masahu, shafi na 47-48.
- ↑ ƙomi, “Fihk Hajji; cegunagi baina Farikaini(3) Masahu, shafi na 48
- ↑ ƙomi, “Fihk Hajji; cegunagi baina Farikaini(3) Masahu, shafi na 48
- ↑ ƙomi, “Fihk Hajji; cegunagi baina Farikaini(3) Masahu, shafi na 48
- ↑ ƙomi, “Fikh Hajji; cegunagi baina Farikaini(3) Masahu, shafi na 48
- ↑ ƙomi, “Fihk Hajji; cegunagi baina Farikaini(3) Masahu, shafi na 48
- ↑ Amadi, Al-Mashahu fi alwudu Rasul Sallalahu Alahihi wa-sallam , shafi na 132.
- ↑ Subhani, Silsila Masael Alfikhiyya, ƙom, Kashi na 2, shafi 9-12.
- ↑ . Sheikh Mufid, Al-Irshad, 1413 AH, Juzu'i na 2, 227-228.
- ↑ Kashi, Rizal Kashshi, 1409 AH, shafi na 441.
- ↑ Kashi, Rizal Kashshi, 1409 AH, shafi na 441.
- ↑ Kashshi, Rizal Kashshi, 1409 AH, shafi na 441.
- ↑ Shahristani, Limaza Iktilaf fil Wudu'u, 1426 s, shafi na 31.
- ↑ Amadi, Al-Mushh Fi Wudu Al-Rasul, 1420 AH, shafi 80-82.
- ↑ Shahristani, Limaza Iktilaf fil Wudu'u, 1426 s, shafi na 31.
- ↑ Shahristani, limaza Iktilaf fil Wudu'u, 1426 ƙ, shafi na 32.
- ↑ Mut ƙi Hindi, Kanz al-Amal, 1406 ƙ, Juzu’i na 9, shafi na 443, H2.
- ↑ Shahristani, Limaza Iktilaf fil Wudu'u, 1426 s, shafi na 33.
- ↑ Shahristani, Limaza Iktilaf fil Wudu'u, 1426 s, shafi na 33
- ↑ Shahristani, Limaza Iktilaf fil Wudu'u, 1426 s, shafi na 34-35
- ↑ Sheikh Sadou ƙ, Man La Yahdrah al-Fa ƙih, Jamia Modaresin Publications, Mujalladi na 1, shafi na 43, Hadisi na 87.
- ↑ Hurrul Amili, Wasael al-Shia, 1374, juzu'i na 1, shafi na 396, h. 1036, shafi na 397, hadisi na 1038.
- ↑ Tabatabaei Yazdi, al-urwa al-Wughta, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 370-368.
- ↑ Kulaini, Farou Kafi, 2008, juzu'i na 1, shafi 184.
- ↑ Sabzevari, Mahezab Al-Ahkam, Dar al-Tafseer, juzu'i na 2, shafi na 220.
- ↑ Kulaini, Furu'u Kafi, 2008, juzu'i na 1, shafi 183.
- ↑ Kulaini, Furu'u Kafi, 2008, juzu'i na 1, shafi 183.
- ↑ Kulaini, Furu'u Kafi, 2008, juzu'i na 1, shafi 183.
- ↑ Kulaini, Furu'u Kafi, 2008, juzu'i na 1, shafi 183.
- ↑ Kulaini, Furu'u Kafi, 2008, juzu'i na 1, shafi 183.
- ↑ Kulaini, Furu'u Kafi, 2008, juzu'i na 1, shafi 183.
- ↑ Kulaini, Furu'u Kafi, 2008, juzu'i na 1, shafi 183.
- ↑ Kulaini, Furu'u Kafi, 2008, juzu'i na 1, shafi 183.
- ↑ نگاه کنید به: «جستجوگر حدیثی میزان».
- ↑ Ghazali, ehya Ulum al-Din, Dar al-Kitab al-Arabi, juzu'i na 2, shafi na 48.
- ↑ Muhaddith Nouri, Mustadrak Al-Wasail, 1407 ƙ, Part 1, shafi na 353.
- ↑ Sheikh Mofid, Amali, 1403 AH, juzu'i na 1, shafi na 60, h5.
- ↑ Maghribi, Da'aim al-Islam, 1385 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 100.
- ↑ Mut ƙi Hindi, Kanz al-Amal, 1405 ƙ, juzu’i na 16, shafi na 129, shafi.
- ↑ Sheikh Sadou ƙ, Man La Yahzara Al-Fa ƙih, Kum Seminary Association, Mujalladi na 1, shafi na 41.
Nassoshi
- Amadi, Mohammad Hasan, Al-Mashah fi Wudhu al-Rasul: Dirasatu mukarana baina Mazahib Islamiya, Beirut, Darul-Mustafa don farfado da al'ada, 1420 AH.
- Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Tahrir al-Wasila, Imam Khumaini Editing and Publishing Institute, Tehran, Beta.
- Ibn Idris Hilli, Muhammad Bin Mansour, Al-Sara'er al-Hawi na Tahrir al-Fatawi, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci da ke da alaka da kungiyar malamai ta ƙum Seminary Society, 1410H.
- Ibn Hisham, Abdul Malik, Al-Sirah Al-Nabiwiyah, bincike na Mustafa Al-Sa ƙ ƙa da Ibrahim Al-Abiari da Abdul Hafiz Shibli, Beirut, Dar al-Marafa, Beta.
- Behbahani, Abdul Karim, masahu Faha dar wudu'u, fassara ta ƙungiyar masu fassara, ƙum, Majalisar Duniya ta Ahlul-Baiti, 1395.
- Payandeh, Abul ƙasem, Nahj al-Fasaha, bincike na Seyyed Hashem Rasouli Mahalati, bugun Danya Danesh.
- Hurru Amili, Muhammad bin Hassan, Tafsilu Rasael shia ila tahsili masael Shari'ah, ƙum, Mu'assasa ta Al-Baiti don Rayar da Al'ada, 1416H/1374H.
- Hosseini Dashti, Sayyid Mustafa, "wudu'u", dar Maarif Maarif, Juzu'i na 10, Tehran, Cibiyar Al'adu ta Arayeh, 1379.
- Hosseini, Hamid, “Wudu'u az Didgahe Mazahib Islami”, Mujallar Mudala'at Takribi Mazahib islami, lamba 17.
- Sobhani, Jafar, “Alwudu fi kitab wa Sunnah”, Silsila Masael fikhiyya, ƙom bazara 2003.
- Sobhani, Jafar, Silsilar Al-Masail al-Fi ƙhiyyah, Kum, Bina, Bita.
- Sabzevari, Seyyed Abdul Ali, Mahezab al-Ahkam Fi Bayan Halal da Haram, ƙom, Dar al-Tafseer, Bita.
- Sayyed Eɗ, Fi ƙh al-Sunnah, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, 1397H.
- Shahrashtani, Seyyed Ali, Lamat al-Ikhtlaaf fi al-Wudhu, Talkhis Fais Attar, Tehran, Mashaar, 1426 AH.
- Sheikh Ansari, Morteza bin Mohammad Amin, Kitab al-Tahara, ƙum, Majalisar Dinkin Duniya na tunawa da Sheikh Azam Ansari, 1415H.
- Sheikh Sadou ƙ, Muhammad Bin Ali, Man La Yahdrah al-Fa ƙih, Sheikh Hossein Al-Alami, Beirut, Al-Alami Publishing House, 1406 H.
- Sheikh Mufid, Muhammad bin Muhammad, al-Amali, bincike na Ali Akbar Ghafari, ƙom, Jamia Modaresin Publications, [1403 AH/1362 AH].
- Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Irshad fi Marafah Hajjullah Ali Al-Abad, gyara ta Cibiyar Al-Bait, ƙum, Sheikh Mofid Congress, 1413 AH.
- Tabatabaei Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-Arwa Al-Waghhi Fima Tam Beh Al-Balawi (Al-Mahshi), bincike na Ahmad Mohseni Sabzevari, ƙum, Ofishin Daba'ar Musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta Kum Seminary Society, 1419 AH.
- Tabatabaei Yazdi, Sayyed Mohammad Kazem, Al-Arwa Al-Waghhi, Makarantar Ayatullah Azami Al-Sayed Al-Sistani.
- Tabatabaei Yazdi, Al-Uruwa al-Wa ƙhi tare da Ta'ali ƙ al-Imam al-Khomeini, Tehran, Cibiyar Gyara da Buga Ayyukan Imam Khumaini, 1422H.
- Tabari, Muhammad bin Jarir, Tariku Al’umam wa Al-Mulkok, Binciken Muhammad Abulfazl Ibrahim, Beirut, Darul Trath, 1387 Hijira/1967 Miladiyya.
- Ayyashi, Muhammad Bin Masoud, Tafsir Ayyashi, bincike na Seyyed Hashim Rasouli Mahalati, Al-Maktab Al-Ilamiya al-Islamiyyah.
- Ghazali, Muhammad bin Muhammad, Ehya Ulum al-Din, bincike na Abdur Rahim bin Hossein Hafiz Ira ƙi, gabatarwar Muhammad Khizr Hossein, Bija, Dar Al Kitab Al Arabi, Beta.
- "Gaslahaye ke aza wudu kifayat mikonad", ofishin Ayatullahi Makarem Shirazi, Jame' Al-Masal, Cibiyar amsa hukunce-hukuncen shari'a da lamurra na shari'a, wanda aka duba a ranar 10 ga Agusta 1402.
- Fazil Mo ƙdad, Mo ƙdad bin Abdullah, Kanz al-Irfan Fi Fi ƙh al- ƙur'an, bincike na Seyyed Mohammad Ghazi, Bija, Majma jahani takreeb baina mazahib islami Duniya 1419 AH.
- Fallahzadeh, Mohammad Hossein, Ahkam Addini: Kamar yadda fatawowin Manyan Masu koyi, Tehran, Mashaar, 2006.
- Fallahzadeh, Mohammad Hossein, Ahkam mubtala be Hujjaj hukunce-hukuncen, Tehran, Mashaar, 2009.
- Faiz Kashani, Mohammad Mohsen, Rasael Faiz Kashani, Binciken Behzad Jafari, Tehran, Makarantar Shahid Motahari, 1429 AH.
- Faiz Kashani, Mohammad Mohsen, Moatasim al-Shia fi Hakam al-Sharia, edited by Masih Tawhidi, Tehran, Shahid Motahari High School, 1429 AH.
- ƙomi, Ali, “cegunagi anjam wudu baina farikaini (1)”, a cikin mujallar Mi ƙat Hajj, shafi na 87-88, bazara da lokacin rani 2013.
- ƙomi, Ali, “cegunagi anjam wudu baina farikaini (3) (Masahu)”, a cikin Mujallar Mi ƙat Hajj, shafi na 90, hunturu 2013.
- Kashshi, Mohammad bin Omar,Rizal Kashi,Mashhad,Mashad University Publishing House,1409AH.
- Cibiyar Ilimin Fikihu ta Musulunci, al'adun fikihu bisa addinin ahlul-baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, karkashin kulawar Sayyid Mahmoud Hashemi Shahroudi, ƙum, Cibiyar Fikihu ta Musulunci, 1426H.
- Motaghi Handi, Ali bin Hasam al-Din, Kenz al-Ammal fi Sunan al-A ƙwal wa al-Afeal, Tafsir da Sahih Bakri Hayyani da Safwa al-Sa ƙ ƙah, Beirut, Al-Risalah Foundation, 1405 AH.
- Muhaddith Nouri, Hossein, Mostadrak al-Wasail, ƙum, Al-Baiti Foundation for Revival of Tradition, [1407 AH].
- Cibiyar Al'adu da Ilimin Kur'ani, Encyclopedia of Al ƙur'ani Mai Girma, ƙum, Cibiyar Lambun Littafin Kum, 1382.
- Maghrib, ƙazi Noman, Da'aim al-Islam, ƙum, Al-Bait Institute, 1385H.
- Makarem Shirazi, Nasser, sharhi Ahkam Jawanan hukunce, 1390.
- Mousavi Khomeini, Sayyid Ruhollah, Tauzihul Masa'il (Masahu), bincike na Sayyid Mohammad Hossein Bani Hashemi, ƙum, ofishin da'a na Musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta ƙum Seminary Society, 1424H.
- Najafi, Mohammad Hasan bin Ba ƙir, Jawaher al-Kalam fi Sharh Shar'e al-Islam, Abbas ƙuchani, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na 7, 1362.