Jump to content

Abdullahi Ɗan Afif Azdi

Daga wikishia
Cikakken SunaAbdullahi Ɗan Afif Azdi
Nasaba/ƘabilaƘabila Azdi
Mahallin RayuwaKufa
Dalilin RasuwaIbn Ziyad ya sa aka kashe shi
ƘabariKufa
AyyukaYa je yakin jamal. siffin sannan ya nuna rashin amincewa da kalaman cin mutunci da Ibn Ziyad ya yi kan Ahlul-baiti (A.S)


Abdullahi Ɗan Afif Azdi (Larabci: عبد الله بن عفيف ازدي) wanda ya yi shahada shekara ta 61 hijra ƙamari, ya kasance sahabin Imam Ali (A.S) wanda bayan waƙi'ar karbala aka kashe shi bisa umarnin Ibn Ziyad.

Abdullahi Ɗan Afif ya kasance daga mataimakan Imam Ali (A.S) wanda a lokacin yaƙin Jamal ya rasa idonsa na hagu a lokacin yaƙin Siffin kuma ya ƙara rasa idonsa na dama yana yaƙi cikin rudunar Imam Ali (A.S).[1] bayan waƙi'ar karbala, lokacin da Ibn Ziyad yake huɗuba a masallacin kufa yana suka da cin mutuncin Ahlul-baiti (A.S) sai ya miƙe ya nuna rashin amincewarsa kan haka, daga ƙarshe Ibn Ziyad ya sa aka kama shi tare da sare kansa daga gangar jikinsa. A rahotan Tarikh Ɗabari lokacin da Ibn Ziyad ya ce: muna godiya ga Allah wanda ya bayyanar da gaskiya da ahalinta, ya taimaki Yazid Ɗan Mu'awiya da rundunarsa, ya halakar da maƙaryaci Ɗan maƙaryaci (Husaini Ɗan Ali) sai Abdullahi ya katse maganarsa ya bayyanar nuna rashin amincewa kan wannan surutai na Ibn Ziyad, ya ce: Ya kai ɗan Murjana! Kai da babanka ne maƙaryaci ɗan maƙaryaci, da kuma wanda ya naɗaka gwamnan kufa da babanshi wanda ya naɗaka ɗin. Ya kai ɗan Murjana! Ka kashe ƴaƴan Annabawa ka zo ka na maganar masu gaskiya?![2]

Sai Ibn Ziyad ya ba da umarni a kama shi.[3] sai suka kama shi suka fitar da shi daga masallaci yana ɗaga murya yana faɗin ya mabrur ya mabrur (ma'ana lamari ya kyawunta ya samu karɓuwa) wani take ne na mutanensa da danginsa[4] domin su kawo masa ɗauki su zo su taimake shi. Cikin dare lokacin da yaran Ibn Ziyad suke kewaye da gidansa.[5] Abdullahi Ɗan Afif wanda ya kasance makaho baya gani amma ƴarsa Safiyya ta dinga taimaka masa cikin yaƙar yaran Ibn Ziyad[6] daga ƙarshe dai sun cimmasa suka kama shi suka kai shi wurin Ibn Ziyad aka sare wuyansa bisa umarnin Ibn Ziyad suka rataye jikinsa a Kunasatu Kufa.[7] kafin shahadarsa ya gayawa Ibn Ziyad ni dama tuni tun kafin a haifeka na roƙi Allah da ya sanya na yi shahada a hannun mafi tsinewar halittun Allah.[8] Abdullahi Ɗan Afif Azadi ya rera waƙar jarumta gaban dakarun Ibn Ziyad:

والله لو فُـرّج لي عن بصـري ضاق عليكم موردي ومصدري

Wallahi da za a yaye min makanta na dawo ina gani da filin gidan nan ya ƙuntata kanku da kun yi kaɗan ku tunkare ni ku yi gaba da gaba da ni.[9]

Bayanin Kula

  1. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1977, juzu'i na 3, shafi na 210; Al-Tabari, Tarikh al-Unulum da al-Muluk, 1967, juzu'i na 5, shafi na 458.
  2. Ibn Kathir Damaschi, al-Bidaiya wa al-Nihaya, 1407 AH, juzu'i na 8, shafi na 191; Al-Tabari, Tarikh al-umam wa al-Muluk, 1967, juzu'i na 5, shafi na 459.
  3. Ibn Kathir Damaschi, al-Bidaya wa al-Nihaya, 1407 AH, juzu'i na 8, shafi na 191; Al-Tabari, Tarikh al-umam wa al-Muluk, 1967, juzu'i na 5, shafi na 459.
  4. Muhaddith, Farhang Ashura, shafi na 480.
  5. Al-Tabari, Tarikh al-umam wa al-Muluk, 1967, juzu'i na 5, shafi na 459.
  6. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1977, juzu'i na 3, shafi na 210.
  7. Al-Tabari, Tarikh al-umam wa al-Muluk, 1967, juzu'i na 5, shafi na 459.
  8. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 45, shafi na 120.
  9. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 45, shafi na 120.

Nassoshi

  • Ibn Kathir Damaschi, Ismail Ibn Omar, al-Bidaiya wa al-Nihaya, Beirut, Darul Fikr, 1407 AH/1986 Miladiyya.
  • Balazri, Ahmed bin Yahya, Ansab al-Ashraf, bincike: Mohammad Baqer Mahmoudi, Beirut, Dar al-Taarif na jarida, 1977 AD/1397 AH.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarihin Al-umam wa Al-Muluk, wanda Muhammad Abolfazl Ibrahim ya yi bincike a Beirut, Darul Trath, bugu na biyu, 1387H/1967 Miladiyya.
  • Mohaddisi, Jawad, Farhang Ashura, Qum, shahararren bugu, 1376/1417 AH.