Jump to content

Karimu Ahlul-Baiti (Laƙabi)

Daga wikishia
(an turo daga Karimu Ahlul-baiti)
Ka da a yi kuskure daukar wannan kasida da kasidar Karimatu Ahlil-Baiti
Error creating thumbnail:
Talifin Sayyid Muhammad Taƙi Mudarrasi. littafi ne mai suna Karimu Ahlul-Baiti, kan tarihin rayuwar Imam Hassan (A.S)

Karimu Ahlul-Baiti (Larabci: كريم أهل البيت (لقب)) ma'anarsa shi ne Mai kyautar cikin Ahlul-Baiti, yana daga cikin laƙubban Imam Hassan Mujtaba (A.S)[1] An yi masa wannan laƙabi ne sakamakon yawan kyautarsa da karamcinsa,[2] kalmar (Karim) duk da cewa cikin tsofaffin masadir na farko-farko an yi amfani da ita[3] kan Hassan Bin Ali (A.S) amma cikin tarihin rayuwarsa babu littafin tarihi da ya rawaito ana masa laƙabi da wannan Kalmar in banda litattafan da suka zo daga baya-bayan nan.[4]

Shaharar Imam Hassan (A.S) da laƙabin Karimu Ahlul-Baiti ta samu sakamakon wasu ƙissoshi da masu nazarin tarihi suka naƙalto su dangane da karamcinsa da kyautarsa,[5] an ce Imam Hassan (A.S) ba a taɓa ganin wani mutum daga babban gida yana kyauta ga talakawa da mabuƙata kamar yanda yake yi ba,[6] Imam Mujtaba (A.S) ya kasance mutum mafi kyauta a zamaninsa, ya kasance wanda ake buga misali da shi cikin yawan kyauta da karamci, shi kaɗai ne ake masa laƙabi da Karimu Ahlul-Baiti.[7]

Ibn Jauzi wanda ya rasu shekara ta 654 h ƙamari, daga malaman Ahlus-Sunna cikin littafinsa Tazkiratul Khawas, ya kasance yana ganin Imamin ƴan Shi'a na biyu cikin manyan mutane da suke da ƙima a idanunsa, cikin ambaton falalolinsa ya rubuta cewa Imam Hassan Bn Ali cikin rayuwarsa karo biyu ya kyautar da bakiɗayan abin da ya mallaka cikin tafarkin Allah, sannan karo uku yana raba dukiyarsa gida biyu ya bada rabinta kyauta ga Talakawa,[8] ta kai ga an naƙalto cewa lokacin da wani Talaka ya roƙe shi taimako sai ya bashi kyautar Dirhami dubu ashirin.[9]

Baƙir Sharif Ƙarashi wanda ya mutu shekara ta 1433 h ƙamari, daga Malaman Shi'a, dangane da laƙabin Karimu Ahlul-Baiti ya naƙalto wata riwaya daga Imam Mujtaba (A.S) da aka tambaye shi me yasa ba a taɓa samu ka bawa Mai roƙon taimako daga gareka haƙuri ba? Sai Imam ya bada amsa ya ce: nima a gaban Allah mutum ne Mabuƙaci talaka da yake neman kada Allah ya haramta masa ni'omominsa, ina jin kunya in cira fata da tsammani daga Talakawa, sannan Allah da ya ƙarfafe ni da taimakonsa yana so na taimaki mutane.[10]

A cewar Sayyid Baharul Ulum wanda ya rasu shekara ta 1380 h ƙamari, wanda ya yi tahƙiƙi kan littafin Talkhisul Ash-Shafi, ya bayyana cewa Maudu'in laƙabin Imam Hassan (A.S) ya yaɗu ya faɗaɗa matuƙar gaske fiye da iya Magana a kansa.[11]

Shaik Hadi Alu Kashiful Giɗa wanda ya rasu shekara ta 1361 h ƙamari, daga Malaman Shi'a a cikin ƙasidarsa da yake siffanta Imam Hassan (A.S) ya rerawa Imam Hassan Mujtaba (A.S) waƙa tare da ishara zuwa ga laƙabin Karimu Ahlul-Baiti

ان الامام الحسن مُهذّبا
خَیرُ الوَری جَدّاً و اُمّاً و اَبا
کریمُ اهل البیت اهلُ الکَرَم
علیهم بَعد الصَّلاة سلم

Tarjama: Haƙiƙa Imam Hassan ya kasance tsarkakakke* mafi alherin mutane ta fuskani Kaka da Uba da Uwa. Karimu Ahlul-Baiti Ahlin Karamci* ku yi salati gare su bayan sallah.[12]


A ƙasar Iran wasu Cibiyoyin taimako da jin ƙai an sanya musu sunan Karimu Ahlul-Baiti.[13]

Ku Duba

Bayanin kula

  1. Aqeel, daga cikin mafi kyawun abin da Imam Hassan (a.s) ya fada, 1430 AH, shafi 7; Al-Saif, Sayyid Al-Jannah Imam Hassan (a.s), 1443 AH, shafi 164
  2. Hakim,Fishwayan Hidayat, 1385 SH, juzu'i na 4, shafi na 46
  3. Duba zuwa Ya'qubi, Tarikh Ya'qubi, Dar Sader, juzu'i na 2, shafi na 226
  4. Ku duba «چرا به امام حسن مجتبی(ع) کریم می‌گویند؟»، Kamfanin dillancin labarai na Isna.
  5. "Razavi, 'Karim Ahlul-Bayt', shafi na 46."
  6. "Muhakkik Arzagani, Fa'idodin A'imma Ahlul-Bayt (a.s) daga Duba Ahlus-Sunnah, 1395 SH, shafi na 103.">
  7. "Qurashi, Dāshināma Imam Amir al-Mu'minin (a.s), 1394 SH, juzu'i na 1, shafi na 32."
  8. "Ibn Jawzi, Tazkirat al-Khawas, 1376 SH, shafi na 176 da 178."
  9. "Nazari Munfared, Al-Sulh Al-Dami, 1429 AH, shafi na 349."
  10. "Qurashi, Al-Nizam Al-Tarbawi Fi Al-Islam, Dar Al-Kitab Al-Islami, shafi na 248; Shushtari, Ihqaq Al-Haq, 1409 AH, juzu'i na 11, shafi na 238."
  11. "Tusi, Talkhis al-Shafi, 1382 SH, juzu'i na 4, shafi na 179."
  12. "Aqa Bozorg Tehrani, Al-Dhari'ah, 1403 AH, juzu'i na 1, shafi na 497.
  13. Ku duba «پایگاه اطلاع‌رسانی خیریه‌ها و سمن‌های کشور».

Nassoshi

  • Aqa Bozorg Tehrani, Muhammad Mohsen, Al-Dhari'ah ila Tasaneef al-Shi'a, Beirut, Dar al-Adhwaa, 1403 AH.
  • Al-Seif, Fawzi, Sayyid al-Jannah Imam al-Hasan (AS), Beirut, Dar al-Mahajja al-Bayda, 1443 AH.
  • Ibn Jawzi, Yusuf bin Qazawghli, Tadhkirat al-Khawas, Qom, Sharaf Razi, 1376 SH.
  • «پایگاه اطلاع‌رسانی خیریه‌ها و سمن‌های کشور»، Ziyara: 14 ga watan Aban 1402 SH.
  • Hakim, Sayyid Munzir, Fishwayane Hidaya, Qom, Majma'in Duniya na Ahlul-Bayt, 1385 SH.
  • «چرا به امام حسن مجتبی(ع) کریم می‌گویند؟»، Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA, An buga labarin: 17 ga watan Farvardin 1402 SH, Ziyara: 7 ga watan Aban 1402 SH.
  • Sayyid Abbas Rezawi، «کریم اهل‌بیت»، Farhange Kawsar, Shafi na 55, Fall 1382 SH.
  • Shushtari, Qazi Nurullah, Ihqaq al-Haq wa Izhaq al-Batil, Gabatarwa da Sharhi daga Ayatollah al-Uzma Marashi Najafi, Maktabat Ayatollah Marashi Najafi, Qom, Bugu na Farko, 1409 AH.
  • Tusi, Muhammad bin Hasan, Talkhis al-Shafi, Qom, Muhibbin, 1382 SH.
  • Aqeel, Mohsen, Daga cikin mafi kyawun abin da Imam Hassan (AS) ya fada, Beirut, Dar al-Mahajja al-Bayda, 1430 AH.
  • Qurashi, Baqir Sharif, Al-Nizam Al-Tarbawi Fi Al-Islam, Bi-Ja, Dar Al-Kitab Al-Islami.
  • Qurashi, Baqir Sharif, Dāshināma Imam Amir al-Mu'minin Ali bin Abi Talib, Qom, Dar al-Tahdhib, 1394 SH.
  • Muhakkik Arzagani, Qurban Ali, Fa'dael A'imma Athar (A.S) Az Difgahe Ahlus-Sunnah, Qom, Majma'in Duniya na Shi'a, 1395 SH.
  • Nazari Munfared, Ali, Al-Sulh Al-Dami, Beirut, Dar al-Rasul al-Akram (SAW), 1429 AH.
  • Ya'qubi, Ahmad bin Abi Ya'qub, Tarikh al-Ya'qubi, Beirut, Dar Sader, Bi-Ta.