Jump to content

Daƙiƙa:Kisan Gillar Ayatullahi Khamna'i

Daga wikishia
Kisan Gillar Ayatullahi Khamna'i
Hoton sama (na jirgin sama) na gidan Jagoranci bayan harin makami mai linzami a lokacin Yaƙin Ramadan.
Hoton sama (na jirgin sama) na gidan Jagoranci bayan harin makami mai linzami a lokacin Yaƙin Ramadan.
Lokaci28 Fabrairu Shekara 2026M
WuriTehran
Mutanen da suka kai harinHaramtacciyar gwamnatin Sahayoniya da Amurka
SakamakoShahadantar da Sayyid Ali Husaini Khamna'i, Sayyid Abdur-Rahim Musawi, Muhammad Fakfur
SaƙonniƘungiyoyin gwagwarmaya sun shelanta jihadi tare da kai hare-hare kan Isra'ila, Fatawar jihadi daga wasu maraji'an taƙlidi.
MartaniAllah wadai da haramtacciyar gwamnatin Sahayoniya da goyan bayan Iran daga ɓangaren wasu ƙasashe da ƙungiyoyin gwagwarmaya da kuma shiya zanga-zanga da makoki


Kisan gillar Ayatullah Khamna'i na nuni ne ga shahadar Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i, jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran a wannan lokaci, wanda ya faru ne sakamakon harin haɗin gwiwa da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar a ranar 28 ga watan Fabrairu 2026 miladiyya (wanda yayi daidai da 10 ga watan Ramadan, 1447 Hijra) a harabar gidan jagoran ƙasar da ke Tehran. An sanar da labarin shahadarsa da asubar ranar 1 watan Maris wanda ya yi daidai da 10 ga Ramadan

A cikin hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra'ila, wasu daga cikin mutanen gidan jagoran Iran da kuma wasu manyan kwamandojin tsaro na Iran suma sun yi shahada, kamar Sayyid Abdur-Rahim Musawi (Babban kwamandan hafsan sojoji) Muhammad Fakfur (Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musukunci) Ali Shamakhani (Babban sakataren majalisar tsaro ta ƙoli) da Aziz Nasir Zade (Ministan tsaro)

An bayyana maƙasudin aikata kisan gilla da shahadantar jagoran Iran, shi ne yunƙurin karya ƙudurin al'ummar Iran, da kuma baiwa haramtacciyar gwamnatin Sahayoniya damar mamaye yankin Asiya ta Yamma (Gabas ta tsakiya) da canja gwamnatin Iran

Menene Dalili Kuma Yaya Suka Aikata Kisan Gilla Kan Jagoran Iran Da Duniyar Shi'a

Ayatullahi Sayyid Ali Husaini Khamna'i, jagoran jamhuriyar Musulunci ta Iran (Jagoranci: 1989-2026M) da duniyar Shi'a, a safiyar ranar Asabar 28 ga watan Fabrairu 2026 miladiyya wanda ya yi daidai da 10 Ramadan 1447 hijira, sakamakon hare-haren da haɗin gwiwar Amurka da Isra'ila suka kai kan gidan jagoranci jagoran Musulunci ya samu rabauta da shahada.[1]

'Wani ɓangare daga jawaban Ayatullahi Khamna'i (17 Fabrairu 2026M)'
Sayyid Ali Khamna'i ya ce: Al’ummar Iran sun san darussan addinin Musulunci da na Shi’a sosai; sun san abin da ya kamata su yi. Imam Husaini (A.S) ya ce: "Mutum irina ba zai yi mubaya'a ga mutum irin Yazid Bin Muawiya ba." Wato, mutum kamar ni ba zai yi mubaya’a ga mutum kamar Yazid ba.[2]

Manufar wannan kisan gilla shi ne karya ƙuduri da ƙarfin zuciyar al'ummar Iran , da kuma baiwa haramtacciyar gwamnatin Isra'ila damar mamaye wannan yanki na Asiya ta Yamma[3] canja gwamnatin Iran mai mulki, haka nan an ce da cikin uzurin kisan gillar Ayatullahi Khamna'i, wai shi ne hana Iran mallakar makamin nukiliya.[4] Daidai lokacin da Ayatullahi Khamna'i shi da kansa ya yi fatawar haramta ƙera makamin nukiliya da amfani da shi, har ila yau, daidai wannan lokaci dai Amurka da Iran suna cikin halin tattaunawa game da batun shirin makamashin nukiliya. Haka kuma. shugaban ƙasar Amurka ya yi da'awar cewa a watan Yuni shekarar 2025 ya kai hari tashoshin makamashin nukliya na Iran tare da lalaa baki ɗayansu. Amurka da Isra'ila a watan Janairu na shekarar 2026 miladiyya a lokacin tashin hankali da kawo hargitsi sun jaddada goyan bayansu ga masu tayar da zaune tsaye domin kifar da gwamnatin jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Kafin wannan hare-hare, Sayyid Ali Khamna'i a gaban shugaban jamhuriyar Amurka ya kawo wata magana ta Imam Husaini (A.S) Imami na uku ga ƴanShi'a, inda yake cewa mutum irina ba zai taɓa mubaya'a ga mutum irinsa ba (Irina Husaini ba zai yi mubaya'a ga Yazid ba) an ce ya ce idan Amurka ta yi kuskure kai hari kan Iran lallai za mu yi yaƙi kamar Ashura.

A sakamakon hare-haren Amurka, wasu adadi daga iyalan jagoran Iran da wasu kwamandoji masu manyan muƙamai na Iran kamar Sayyid Abdur-Rahim Musawi, babban kwamandan hafsan sojoji, Muhammad Fakfur babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci da Ali Shamakhani, babban sakataren majalisar tsaro ta ƙoli da Aziz Nasir Zade ministan tsaro.

Jagora Da Goyan Bayan Ƙawancen Ƙungiyoyin Gwagwarmaya

Sayyid Ali Khamna'i, mutum ne da aka san shi a matsayin shugaba kuma mai taimakawa ƙawancen ƙungiyoyin gwagwarmaya. Haka kuma mutum ne mai tsananin adawa da mamayar haramtacciyar gwamnatin sahayoniya da kuma tasirin yammaci musamman Amurka a wannan yanki na yammacin Asiya.

Barazanar Kisan Gilla Kan Jagoran Iran

Kafin shahadar jagoran Iran, Amurka da Isra'ila a lokuta daban-daban sun yi barazarar kashe shi, ciki har da lokacin yaƙin kwanaki goma sha biyu tsakanin Isra'ila da Iran, shugaban Amurka, firaministan haramtacciyar gwamnatin sahayoniya ta Isra'ila da ministan yaƙi na Isra'ila[5] sun masa barazanar kashe shi[akwai buƙatar kawo madogara]

Maraji'an taƙlidi na Shi'a da makarantun addini na Najaf da Qum da malamai masu yawa da ƙungiyoyin Musulmi cikin Allah wadai da barazanar kashe jagora, sun nuna goyan bayansu ga Iran.[6] Cikin jawabi da makarantar addini ta Najaf ta fitar an bayyana Sayyid Ali Khamna'i matsayin wata alama ta gwagwarmaya da haɗin kai na da ƙarfi na al'ummar Musulmi kuma duk wani yunƙurin barazanar hallaka shi za a yi la'akari da shi matsayin ha'inci ga baki ɗayan al'ummar Musulmi da darajojin tauhidi.[7] Wasu daga cikin maraji'an taƙlidi kamar Ayatullahi Makarim Shirazi[8] Nuri Hamadani[9] sun bayyana duk wani nau'in barazana kan jagora da marja'iyyar Shi'a yana matsayin hukuncin muharaba.

Tarin jama’a a Yemen domin nuna martani ga shahadar Ayatullahi Khamna'i

Ta'asa Ta Siyasa Da Addini

Aikata kisan gilla kan jagororin na ƙasashe a mahangar haƙƙoƙi na duniya ana la'akari da shi matsayin babban lefi da ba za a yarda da shi ba[10] Kashe jagoran siyasa da addini na Iran jagoran ƴanShi'a na duniya, ya wuce lefi na siyasa, ana ɗaukarsa lefi na addini.[11]

Martanoni

“Khodaƙowat” aikin Hassan Ruhul Amin.

Bayan shahadar Ayatullah Khamna'i, maraji'an taƙlidi irisu Sayyid Ali Sistani, Wahid Khurasani,[12] Nasir Makarim Shirazi, Husaini Nuri Hamadani, Jafar Subhani, Abdullah Jawadi Amoli, Husaini Mazahiri da kuma daraktan hauzozin ilimi na Iran sun fitar da saƙonnin ta'aziyya.

Wasu daga maraji'an taƙlidi da malaman Shi'a da Ahlus-Sunna[13] Kamar Jawadi Amoli[14] Nuri Hamadani[15] Sun shelanta jihadi, Husaini Nuri Hamadani cikin amsar tambaya ya ce ya zama wajibi a ɗauki fansar jinin jagora shahidi daga waɗanda suka aikata ta'asar kashe shi[16] Nasir Makarim Shirazi ya kira shahadar jagora a mastayin share fage ce na gab da bayyanar Imam Mahadi (A.S).

Shugaban ƙungiyar malaman Ahlus-Sunna ta Iraƙi shi ma cikin bayani game da shahadar Ayatullahi Khamna'i ya buƙaci maraji'ai da malaman Shi'a su fitar da hukuncin jihadi kan Amurka da Isra'ila[17]

Wasiƙar Ayatullahi A'arafi

Ali Rida A'arafi, shugaban makarantu na addinin Musulunci (Huazar Ilimi), a cikin wata wasiƙa da ya rubuta wa Paparoma Leo na goma sha huɗu, ya bayyana kisan Jagoran Iran a matsayin laifi marar misali a tarihin addinai da kuma wani bayyannen cin mutunci ga duk mabiyan addinan samaniya. Ya roƙi Paparoman da ya la'anci wannan kisan tare da musanta cewa yana da alaƙa da koyarwar Kiristanci.

A'arafi ya nuna cewa Ayatullah Khamna'i yana daga cikin masu goyon bayan haƙƙoƙin addinai marasa rinjaye, musamman Kiristocin Iran, kuma barazanar da ta taso kan rayuwarsa ta samo asali ne daga tsayuwarsa wajen kare al'ummar Falasɗinu a gaban kisan kiyashi da mamaya.[18]

Jami'an Siyasa Da Addini. Shugabannin ƙasashen Rasha, Tajikistan, Uzbekistan, Iraƙ, da Malesiya,[19] da Labanun, sun yi ta'aziyyar shahadar Ayatullah Khamna'i tare da yin Allah wadai da matakin Amurka da Isra'ila. Putin ya bayyana kisan gillar jagoran Iran a matsayin wani abin kunya na karya dukkan ƙa'idojin ɗa'a na ɗan Adam da dokokin ƙasa da ƙasa.

Ƙungiyoyin gwagwarmaya kamar su Kungiyoyin gwagwarmaya na yankin, ciki har da Hizbullahi Lubnan, Ansarullahi Yaman, Hamas, Jihadul Islam Falasɗinu, da ƙungiyoyin Shi'a na Iraƙi, sun fitar da sanarwa suna Allah wadai da kisan tare da bayyana goyon bayansu. [20] Wasu shugabannin addinai da mazhabobi daban-daban kamar shugaban Cocin Ortodoks (Orthodox) na Rasha[21]

Taron Jama'a A Ƙasashe Daban-daban

Taron tunawa da Ayatullahi Khamna'i A Lucknow Indiya

Kafofin watsa labarai na duniya sun yaɗa labarin wannan lamari sosai. Gwamnatin Iran ta ayyana kwanaki bakwai na hutu na hukuma da kuma kwanaki arba'in na makoki na jama'a [22] Gwamnatin Iraki kuma ta ayyana zaman makoki na kwana uku tare da sanya jihohin Karbala da Najaf hutun kwana daya. ƴanShi'a a biranen Iran daban-daban da kuma ƙasashe da dama na duniya ciki har da Iraƙ, Fakistan, Indiya, Labanun, Yaman, Astiraliya, Najeriya da Turkiyya sun gudanar da zanga-zanga da makoki tare da yin Allah wadai da kisan gillar jagoran Iran. A birnin Bairut, Bagadaza da Karaci, ƴanShi'a sun kai hari kan ofishin jakadancin Amurka. A Karaci, an shahadantar da mutane 34 da harbin bindiga. A Kashmir kuma ƴansanda sun yi musgunawa da rashin tausayi ga masu zanga-zanga.

Bayan shahadar jagoran Iran, an canza tutar haramin Imam Rida (A.S). A Masallacin Jamkaran kuma an ɗaga tuta ja mai taken "Ya Lasaratul Husaini" a matsayin alamar ɗaukar fansa.

A wasu biranen Iraƙi da haramin Imam Ali da haramin Kazimaini an gudanar da jana'izar misali da kwatankwaci ga Ayatullah Khamna'i, kuma a wasu biranen Fakistan an gudanar da salatul ga'ib a kansa. A Iran, ana kallon shahadar Ayatullah Khamna'i tare da wasu daga iyalansa a matsayin wani babban sadaukarwa mai girma, (Zibhul Azim) kuma ana alaƙanta shahadarsa da shahadar Imam Husaini (A.S), ana kuma ɗaukarta a matsayin wata alama ta gwagwarmaya da ɗauki babu daɗi tsakanin gaskiya da ƙarya ta wannan zamani.

Sakamako

Rundunar dakarun kare Juyin Juya halin Musulunci, a cikin martani da kuma raddi da hari kan harin haɗin gwiwar Isra'ila da Amurka da kuma shahadar jagoran Iran, ta fara ofireeshin "Wa'adus Sadiƙ 4" wanda ya ƙunshi hare-haren makamai masu linzami da na jiragen sama marasa matuka a kan yankunan da Isra'ila ta mamaye da kuma sansanonin sojin Amurka a ƙasashen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Bahrain, Qatar, Kuwait, Jordan da Saudiyya.

Hizbullahi Lubnan, ta hanyar fitar da wata sanarwa, domin daukar fansar shahadar jagoran Iran, ta kai harin makami mai linzami kan Isra'ila, tare da haɗa karfi da Iran, ta shiga yaƙi da Isra'ila. Wasu ƙungiyoyin gwagwarmaya na Iraƙi kamar "Saraya Awliya al-Dammi" suma sun shiga yaƙi da Amurka da Isra'ila. Hizbullahi ta Kurdistan ta Iraki kuma ta ayyana jihadi da Amurka da Isra'ila.

Bayan wannan lamari, Majalisar Ƙwararru Ta Jagoranci ta zaɓi Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamna'i a matsayin jagora na uku daga jagororin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Yunƙurin Kisan Da Bai Yi Nasara Ba A Shekara Ta 1981 Miladiyya

A ranar 27 ga Yuni, 1981 M. yayin da yake jawabi a masallacin Abu‌ Zar da ke Tehran, an yi ƙoƙarin kashe shi.[23] Ya ji munanan raunuka a kafaɗa, ƙirji da hannun dama.[24] Da farko, an danganta wannan harin da kungiyar Furƙan,[25] amma wasu majiyoyi sun ce Ƙungiyar Mujahidin Khalƙe ce ke da alhakin hakan.[26]

Maƙaloli Masu Alaƙa

Bayanin kula

  1. «اطلاعیه شهادت حضرت آیت‌الله العظمی سیدعلی حسینی خامنه‌ای رهبر انقلاب اسلامی»،Ofishin Kula da Adanawa da Yaɗa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i.«رهبر معظم انقلاب به شهادت رسیدند»، Kamfanin Dillancin Labarai na Jamhuriyar Musulunci (IRNA).؛ «رهبر معظم انقلاب به شهادت رسیدند»، Tashar Al-Alam.
  2. «بیانات در دیدار مردم آذربایجان شرقی»Ofishin Kula da Adanawa da Yaɗa Ayyukan Babban Ayatullahi Khamna'i.
  3. «رهبر انصارالله: هدف ترور آیت الله خامنه‌ای درهم شکستن روحیه ملت ایران است»،Tashar Al-Alam.
  4. «ایران خواستار محکومیت فوری تجاوزات آمریکا و "اسرائیل" در شورای حکام شد»، Tashar Al-Alam..
  5. Vazīr-e Jang-e Esrā’īl barāye noḥdahdan-e Rahbar-e Enqelāb tahdīd kard, kamfanin dillancin labarai na sauye-sauyen duniyar Musulunci
  6. «واکنش قاطع مراجع تقلید و علما نسبت به گستاخی ترامپ به رهبر انقلاب»Kamfanin Dillancin Labarai na Rasa..
  7. «حوزه علمیه نجف بر علیه تهدید گستاخانه «ترامپ جنایت‌کار» مبنی بر ترور امام خامنه‌ای واکنش شدید نشان داد»، Kamfanin Dillancin Labarai na Dalibai..
  8. «هر شخص یا رژیمی که رهبری و مرجعیت را تهدید کند حکم محارب دارد»، Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA..
  9. «هرگونه تعرض و تهدید به رهبری و مرجعیت شیعه حکم محارب دارد»،Kamfanin Dillancin Labarai na Jamhuriyar Musulunci
  10. «عراقچی: اقدام دشمن جنایت سیاسی-مذهبی بود / در مذاکره فریب نخوردیم»،Tashar Al-Alam..
  11. «عراقچی: اقدام دشمن جنایت سیاسی-مذهبی بود / در مذاکره فریب نخوردیم»،Tashar Al-Alam..
  12. «پیام تسلیت دفتر آیت‌الله وحید خراسانی در پی شهادت امام خامنه‌ای»، Kamfanin Dillancin Labarai na Rasa.
  13. «رئیس سازمان‌های اسلامی شورای مشورتی مالزی: جهاد اکنون بر همه مسلمانان واجب است»، Kamfanin Dillancin Labarai na Abna..
  14. «ویدیو | فتوای جهاد آیت‌الله العظمی جوادی آملی؛ امروز ریختن خون ترامپ و صهیونیست‌ها واجب است» Kamfanin Dillancin Labarai na Abna.
  15. «بر همه مسلمانان فرض است که منتقم خون رهبر شهید خود باشند»، Kamfanin Dillancin Labarai na Rasa..
  16. «بر همه مسلمانان فرض است که منتقم خون رهبر شهید خود باشند»، Kamfanin Dillancin Labarai na Rasa.
  17. «رئیس جمعیت علمای اهل سنت عراق: علما و مراجع باید فتوی جهاد بدهند»، Kamfanin Dillancin Labarai na Abna.
  18. «نامه مهم آیت الله اعرافی به پاپ رهبر کاتولیک‌های جهان / در مقابل جنایت علیه ملت ایران موضعی اصولی و هشداردهنده اتخاذ کنید»،Kamfanin Dillancin Labarai na Hauza.
  19. «مالزی شهادت آیت‌الله خامنه‌ای را تسلیت گفت»، Kamfanin Dillancin Labarai na Abna..
  20. «بازتاب شهادت رهبر معظم انقلاب در رسانه‌های جهان»، Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr..
  21. «پیام تسلیت رهبر ارتدکس روسیه به رئیس‌جمهور به مناسبت شهادت رهبر معظم انقلاب»، Kamfanin Dillancin Labarai na Abna.
  22. «اعلام ۴۰ روز عزای عمومی و ۷ روز تعطیلی در پی شهادت رهبر معظم انقلاب»، Tashar Al-Alam.
  23. Hashimi, Inƙilab Dar....Sh 176.
  24. Ƙubadi، «گزارشی از ماجرای ترور ۶ تیر ۱۳۶۰».
  25. «بازخوانی 24 ترور پس از پیروزی انقلاب اسلامی»،Cibiyar Takardun Tarihi ta Juyin Juya Halin Musulunci.
  26. «ترور نافرجام آیت الله خامنه‌ای»، Teebyan.

Nassoshi