Hadise Wilayat (Littafi)
![]() | |
| Suna na asali | Hadisi Wilayat |
|---|---|
| Marubuci | Sayyid Ali Khamna'i |
| Maudu'i | Wasu adadin jawabai da rubuce-rubucen Sayyid Ali Khamna'i |
| Mai bugawa | Maɗabba'ar Inƙilabe Islami |
| Wurin da aka buga shi | Tehran |
| Yawan bugawa | 2020 miladiyya |
Hadise Wilayat, sunan wani littafi ne da ya ƙunshi bayanai, jawabai da kuma rubuce-rubucen Sayyid Ali Khamna'i, shugaban ƙasa na biyu kuma jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda cibiyar bincike da al'adu ta Juyin Juya Halin Musulunci ta tattara domin adanawa, tabbatar da ingancinsu da kuma gabatar da su cikin tsari mai nagarta. An wallafa wannan littafi a shekara ta 2020 miladiyya.
Gabatarwa Da Muhimmanci
Hadise Wilaya, wasu tarin bayanai, jawabai da rubuce-rubuce ne na Sayyid Ali Khamna'i ne, jagora na biyu na Iran,[1] wanda aka tattara domin adanawa da kuma samar da ingantaccen kundin waɗannan ayyuka.[2] Jawabai da aka tattara na jawabe-jawabe da rubuce-rubuce an raba su zuwa lokuta huɗu na zamani:
- Daga farkon lokaci har zuwa nasarar Juyin Juya Halin Musulunci.
- Daga nasarar Juyin Juya Halin Musulunci har zuwa fara wa’adin shugabancin ƙasa (Oktoba 1981 / Mehr 1360).
- Lokacin shugabancin ƙasa.
- Lokacin Wilaya da Jagoranci (daga tsakiyar Yuni 1989 / rabin Khordad 1368 zuwa bayan haka).[3]
Bugawa
Wannan littafi an tsara shi ne ta hannun Cibiyar Nazarin Al’adu da Bincike ta Juyin Juya Halin Musulunci, sannan aka wallafa shi a shekarar 1399Sh (2020 M) a matsayin sigar dijital.[4] Abubuwan da ke cikinsa an tattara su a shafin Khamna'i .ir, haka kuma sigar lantarki ta shi mai taken "Bayanat" a cikin manhajar Hadith-e Wilayat 3, wadda ta ƙunshi mujalladi 45 daga shekarar 1357Sh (1979 M) zuwa shekarar 1402Sh (2023 Miladiyya). An tsara jawaban ne bisa shekarar da aka gabatar da su, kuma ba su da lambobin jere masu ci gaba.[5]
Hanyar Tattarawa Da Gyarawa
An shirya wannan aiki ne bisa wata ƙa'ida ta musamman da ta ginu a kan ka'idoji biyu: Kiyaye lafazin magana, Kiyaye salon lafazin magana A cikin wannan tsari, an rubuta kalmomin jawaban daidai kamar yadda aka faɗar su, sannan ankiyaye salon maganar ta hanyar sake dubawa akai-akai da fayilolin sauti. Haka kuma an yi gyaran rubutun tare da kiyaye salon magana na Sayyid Ali Khamna'i, kuma an rubuta shi bisa ƙa'idar rubutun da Cibiyar Harshe da Adabin Farsi ta amince da ita.[6] Kowane juzu'i yana ƙunshe da: Jadawalin manyan abubuwan da suka faru a shekarar Fihirisan batutuwa da sunaye Bayanan ƙarin sharhi (footnotes) don bayani kan kalmomi, sunaye, abubuwan tarihi da kuma tushe Waɗannan kayan bincike suna taimaka wa masu bincike da masu karatu su sami bayanai cikin sauƙi da daidaito daga cikin wannan littafi.[7]
Waɗanne Jawabai Ne Ba A Wallafa A Cikin Wannan Aiki Ba?
Wasu daga cikin jawabai da bayanan da aka gabatar ba a tattara su a cikin wannan kundin ba, saboda ba a fitar da su ga jama’a ba, ko kuma saboda kasancewarsu na sirri, ko kuma an riga an buga su a matsayin littafi na daban.[8] Waɗannan sun haɗa da:
- Rubuce-rubucen kansa ko fassarori.
- Zaman darussan fikihu na musamman (bahsin kharij).
- Zaman darussa na musamman kan tafsirin Alƙur’ani.
- Bayanan da aka gabatar a tarurrukan sirri.
- Bayanan da aka gabatar yayin ganawa da iyalan shahidai.
- Bayanan ganawa na gama-gari da ƙungiyoyi da mutane daban-daban.
- Wasiƙu da ƙarin bayanai da aka rubuta a gefen takardu (Footnotes).[9]
Bayanin kula
- ↑ Hadith-e Wilayat, Mawallafar Inƙilabe Islami
- ↑ Kitab-e Hadith-e Velayat Montasher Shod, ofishin kula da adanawa da wallafa ayyukan Ali Khamna'i.
- ↑ Kitab-e Hadith-e Velayat Montasher Shod, ofishin kula da adanawa da wallafa ayyukan Ali Khamna'i.
- ↑ Hadith-e Wilayat, Nashriyyar Enqelab-e Eslami; Kitabe Hadise Wilayat Muntashir Shode, Ofishin Kiyaye da Yada Ayyukan Ayatullah Khamna'i .
- ↑ Kitabe Hadith-e Wilayat Muntashir Shod, Ofishin Kiyaye da Yada Ayyukan Ayatullah Khamna'i, Bayanat, Manhajar Wilayat.
- ↑ Hadith-e Wilayat, Nashriyyar Juyin Juya Halin Musulunci; Hadith-e Wilayat, Ofishin Kiyaye da Yada Ayyukan Ayatullah Khamna'i .
- ↑ Hadith-e Wilayat, Mawallafar Inƙilabe Islami
- ↑ Hadith-e Wilayat, Nashriyyar Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ Kitabe Hadith-e Wilayat Muntashir Shod, Mashriq News; Kitabe Hadith-e Wilayat Muntashir Shod, Ofishin Kiyaye da Yada Ayyukan Ayatullah Khamna'i .
Nassoshi
- «کتاب حدیث ولایت منتشر شد»،(An wallafa littafin Hadisul Wilaya.), Ofishin Kula da Yaɗa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i, ranar wallafa labarin: 4 Mayu 2020 M, ranar dubawa: 16 Disamba 2025 M.
- «کتاب "حدیث ولایت" منتشر شد»، (An wallafa littafin Hadisul Wilaya.), Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA, ranar wallafa labarin: 5 Mayu 2020 M, ranar dubawa: 16 Disamba 2025 M.
- «کتاب حدیث ولایت منتشر شد»، (An wallafa littafin “Hadisul Wilaya”.), Mashregh News, ranar wallafa labarin: 4 Mayu 2020 M, ranar dubawa: 28 Disamba 2025 M.
- «حدیث ولایت»، (Hadisul Wilaya.), Cibiyar Bugawa ta Juyin Juya Halin Musulunci, ranar dubawa: 23 Disamba 2025 M.
