Aftab Dar Mosaf (Littafi)
![]() | |
| Marubuci | Sayyid Ali Husaini Khamna'i |
|---|---|
| Maudu'i | Imam Husaini (A.S), bincike game da Waƙi'ar Karbala |
| Harshe | Farsi |
| Adadin Jildi | 1 |
| Adadin shafuka | 1040 |
| Mai bugawa | Mawallafar juyin juya halin Musulunci |
| Wurin da aka buga shi | Tehran |
| Tarihin bugawa | 2013 miladiyya |
| Lambar littafi | 30-70-2951-964-978 |
| Kwafin PDF | kwafi na yanar gizo |
'Aftab dar Mosaf' (ma'ana: Rana a cikin fafatawa), mai ɗauke da ƙaramin take Dalilai da sasanni na waƙi'ar Ashura, littafi da aka aka samar da shi daga ne jawaban Sayyid Ali Khamna'i, jagoran jamhuriyar Musulunci ta Iran, game da Imam Husaini(A.S) da kuma nazarin abubuwan da suka shafi Waƙi'ar Karbala wadda ta faru a shekara ta 680 miladiyya (61 Hijira). An gabatar da waɗannan jawaban ne tsakanin 1979 miladiyya (1357 Shamsi) zuwa 2011 miladiyya (1390 Shamsi).
An tsara littafin Aftab Dar Mosaf zuwa babuka shida, inda yake bayani kan: halayen Imam Husaini (A.S), yanayi da dalilan da suka kai ga miƙewarsa manufofin da haduffan wannan miƙewa, sahabban Imam Husaini da maƙiyansa a Karbala, da kuma wasu daga cikin addu'o'i da aka rawaito daga gare shi ko kuma ziyarorin da suka zo game da shi.
An fara buga wannan littafi a shekarar 2013 miladiyya, kuma zuwa shekarar 2022 miladiyya (1401 Shamsiyya) an sake buga shi sau goma. Haka kuma, an fitar da wani littafi daga cikinsa mai suna Darsehaye Ashura (Darussan Ashura), wanda aka ciro shi daga wannan littafi sannan aka wallafa shi daban.
Marubuci
ُSayyid Ali Khamna'i shi ne jagora na biyu na jamhuriyar Musulunci ta Iran. A cikin jawaban sa da rubuce-rubucensa, ya kuma yi nazari kan tarihi; wasu daga cikin waɗannan nazarce-nazarce daga baya an tattara su sannan aka mayar da su zuwa littattafai, kamar Insane 250 Sale (Mutum Mai Shekaru 250), Pishwaye Sadiƙ (Jagora Mai Gaskiya) da kuma Do Imam Mujahid (Imamai Biyu Masu Jihadi).[1]
Bayan littafin Aftab Dar Mosaf, an kuma wallafa wasu littattafai guda uku da suka shafi Imam Husaini (A.S) da kuma Ashura, waɗanda aka tattara daga jawaban Sayyid Ali Khamna'i. Taken littattafan su ne: Chahar Goftar (Jawabai Guda Huɗu), Darsehaye Ashura (Darussan Ashura) da kuma 72 Sokhane Ashurayi (Maganganu 72 na Ashura).[2]
Tsari Da Kuma Abin da Yake Ciki
Batutuwan da littafin Aftab Dar Mosaf:Rana a cikin fafatawa: Dalilai da sasannin Waƙi'ar Ashura, ya ƙunsa an tsara su ne bisa jerin lokaci na jawaban Sayyid Ali Khamna'i daga shekarar 1979 miladiyya (1357 Shamsi) zuwa 2011 miladiyya.[3] An rarraba littafin zuwa babuka shida. Taƙaitaccen jerin abubuwan da littafin ya ƙunsa su kasance kamar haka:
- . Gabatarwa (Baki ɗaya):
Ya ƙunshi batutuwa na farko-farko kamar makarantar Musulunci, ilimin koyarwar Musulunci, al’ummar Musulmi, Manzon Allah (S.A.W), Imaman Shi'a, da kuma wasu batutuwa na nazarin zamantakewa.[4]
- . Imam Husaini (A.S): Ya tattaro batutuwa kamar bikin ranar haihuwarsa, halayensa da matsayinsa, da kuma darussan da ake iya koya daga rayuwarsa.[5]
- . Ashura: A wannan sashe an tattauna batutuwa kamar fahimtar miƙewar Imam Husaini (A.S), yanayin da ya haifar da miƙewar da manufofinsa, hanyoyin gwagwarmaya, siffofin wannan tashi, sirrin da ya sa miƙewarWaƙi'ar Karbala ya dawwama a tarihi, da kuma nauyin da ya rataya a wuyan al’umma da kuma gurɓatawar da aka yi wa labarin Ashura.[6]
- . Sahabban Ashura (Mataimakan Imam Husaini A Filin Ashura): Gabatar da wasu fitattun mutane na al’amarin Karbala, kamar Zainabul Kubra (A.S), Sayyidina Abbas (A.S), Ali Akbar (A.S), Muslim Bin Aƙil, Ƙasim Bin Hassan, da Abdullahi Bin Hassan.[7]
- . Maƙiyan Ashura:A nan an yi bayani kan halaye da siffofin waɗanda suka taka rawa wajen haifar Waƙi'ar Ashura kamar Mu'awiya Bin Abi Sufyan da Yazid Bin Mu'awiya.[8]
- .Ziyarori da Addu’o’i: A wannan ɓangaren an gabatar da kuma bayyana wasu daga cikin addu’o’i da aka ruwaito daga Imam Husaini (A.S) ko kuma ziyarorin da aka danganta su da shi; kamar Du'a Arafah, Ziyaratu Ashura, da Ziyaratu Arba'in.[9]
- .Ƙoƙarin kauce wa rubutu mai rikitarwa ko mai kawo ruɗani a cikin bayanai[10] rarraba batutuwa zuwa ƙananan sassa masu ma’ana domin sauƙaƙa fahimta, da kuma rubuta taƙaitaccen muhimmin bayani a gefen shafukan littafi, domin sauƙaƙa wa mai karatu samun manyan bayanai cikin sauri.[11]
Bugawa
Littafin Aftab Dar Mosaf an tattara shi ne da ƙoƙarin Cibiyar Al'adu ta Hadis Lawhi Wa Ƙalam, sannan Maɗabba'ar Inƙilabe Islami[12]Littafin Aftab dar Misaf Tajdid-e Chap Shud, Maɗabba'ar Inƙilabe Islam An tsara littafin cikin shafuka 1040, amma a sabbin bugun littafin an cire shafuka 362[13] waɗanda suka ƙunshi sunayen mutane da kundin bayanai, sannan aka sanya su a shafin yanar gizon Maɗabba'ar Inƙilabe Islami domin masu karatu su samu sauƙin duba su.[14] Zuwa shekarar 2023 miladiyya, an sake buga littafin sau goma.[15]
Haka kuma, littafin Darsehaye Ashura (Darussan Ashura), wanda ya ƙunshi darussa da wa'azi guda hamsin da ake iya koya daga al’amarin Ashura, an fitar da shi ne daga cikin littafin Aftab dar Mosaf. Wannan littafi yana da shafuka 264, kuma Cibiyar Al'adu Hadis Lawhi Wش Ƙalam ce ta wallafa shi[16]
Bayanin kula
- ↑ «نگاهی گذرا به زندگینامه آیتالله سید علی خامنهای»، Shafin Intanet na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i..
- ↑ Kitab-e Aftab dar Misaf Runamayi Mishawad, Maɗabba'ar Inƙilabe Islami
- ↑ Khamna'i, Aftab Dar Mosaf, sh 5
- ↑ Khamna'i, Aftab Dar Mosaf, sh 7
- ↑ Khamna'i, Aftab Dar Mosaf, sh 7
- ↑ Khamna'i, Aftab Dar Mosaf, sh 8
- ↑ Khamna'i, Aftab Dar Mosaf, sh 8
- ↑ Khamna'i, Aftab Dar Mosaf, sh 8
- ↑ Khamna'i, Aftab Dar Mosaf, sh 8
- ↑ Khamna'i, Aftab Dar Mosaf, sh 6
- ↑ Khamna'i, Aftab Dar Mosaf, sh 6
- ↑ «آفتاب در مصاف»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ Kitab-e Aftab dar Misaf Tajdid-e Chap Shud, Maɗabba'ar Inƙilabe Islam
- ↑ Kitab-e Aftab dar Misaf Tajdid-e Chap Shud, Maɗabba'ar Inƙilabe Islam
- ↑ Kitab-e Aftab dar Misaf Tajdid-e Chap Shud, Maɗabba'ar Inƙilabe Islam
- ↑ «درسهای عاشورا از نگاه رهبر معظم انقلاب منتشر شد». Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
Nassoshi
- Ali Khamna'i, Aftab dar Mosaf, Tehran, ْCibiyar Bincike da Al’adu na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, bugun na biyu, 2013 Miladiyya.
- «نگاهی گذرا به زندگینامه حضرت آیتالله العظمی سیدعلی خامنهای»، (Hasashen Tarihin Rayuwar Mai Girma Ayatollah al‑Uzma Sayyid Ali Khamna'i), Shafinn ofishin kula da yada ayyukan Mai girma Ayatullahi Al-uzma Khamna'i، Ranar da aka wallafa bayanin: 21 Maris 2014, ranar da aka duba:23 Agusta 2021M.
- عاشورا از نگاه رهبر معظم انقلاب منتشر شد»، خبرگزاری فارس،»,(Darussan Ashura daga hangen nesa na Jagora Mai Girma na Jamhuriyar Musulunci an wallafa shi – wani ɓangare daga littafin Darussan Ashura daga hangen nesa na Jagora Mai Girma), Kamfanin dillancin labarai na Fars, Ranar wallafa rubutu: 18 Yuni 2012 Miladiyya, Ranar ziyara: 17 Satumba 2021 Miladiyya.
- «.«کتاب آفتاب در مصاف رونمایی میشود»، (Littafin Aftab dar Mosaf zai samu gabatarwa/fitowa), Buga Littattafai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ranar shigarwa: 29 Oktoba 2013 Miladiyya , Ranar dubawa: 27 Disamba 2025 Miladiyya.
- ««کتاب آفتاب در مصاف تجدید چاپ شد.»،(Littafin Aftab dar Mosaf an sake buga shi), Buga Littattafai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ranar shigarwa:29 Yuli 2022 Miladiyya.Ranar dubawa:27 Disamba 2025 Miladiyya.
- «Aftab dar Masaf: Dars-haye Ashura: Gozide-yi Bayanat-e Hazrat Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamenei, Rahbar-e Mu'azzam-e Enqelab-e Islami»(Darussan Ashura: Zaɓaɓɓun jawabai na Mai Girma Ayatullahi Uzma Sayyid Ali Khamna'i.),, shafin Khaneh-ye Ketab, ranar dubawa: 6 Satumba 2021.
- ««آفتاب در مصاف بر گرفته از بیانات حضرت آیتالله العظمی خامنهای (مدّظلّهالعالی) رهبر معظّم انقلاب اسلامی»»،(Aftab dar Mosaf an ciro shi ne daga jawaban Ali Khamna'i, Jagora mai girma na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.), Buga Littattafai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ranar ziyara: 12 Satumba 2021 Miladiyya.
