Jump to content

Bayani Mataki Na Biyu Na Juyin Juya Hali

Daga wikishia

Bayanin Mataki na Biyu na Juyin Juya Halin Musulunci ko kuma jawabi na biyu, wani bayani ne da Sayyid Ali Khamna'i, jagoran jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya fitar a ranar cika shekaru arba'in da nasarar juyin juya halin Musulunci a ranar 22 ga Bahman 1397Sh/ (2019M). A cikin wannan bayani ya yi magana kai tsaye da matasa, inda ya bayyana tarihin yadda juyin juya halin ya faru da wahalhalunsa, sannan ya yi bayani kan nasarorin da aka samu cikin shekaru arba'in na juyin juya halin Iran. Haka kuma ya fayyace hangen nesa na makomar juyin juya halin a fannoni daban-daban kamar ilimi da bincike, ruhaniya da ɗabi'a, adalci da yaƙi da cin hanci da rashawa.

Wannan bayani saƙo kai tsaye zuwa matasa, waɗanda aka bayyana a matsayin ginshiƙin tabbatar da tsarin Musulunci mai ci gaba, kuma an ɗauke su a matsayin babbar dama mai muhimmanci ga ƙasar Iran.

Nasir Makarim Shirazi, ɗaya daga cikin manyan maraji'in taƙlidi na Shi'a, da Mahadi Shabezindedar, daga malaman darasin kharijul fikihi a hauzar ilimi ta Qum, sun nuna goyon bayansu ga wannan bayani na mataki na biyu, suna mai cewa bayani ne mai zurfi da ilimi. Haka kuma Sayyid Ahmad Khatami, memba na majalisar ƙwararru ta jagoranci a Iran, ya bayyana cewa amincewar jagoran Iran ga matasa ta samo asali ne daga tarihin daga salon rayuwar Annabi (S.A.W), wanda ya ba wasu matasa uku manyan muƙamai a zamaninsa.

An gudanar gamgamin taruka da dama masu taken Mataki na Biyu na Juyin Juya Hali a Tehran da Qum. Haka kuma an buga wani littafi mai suna Bayani kan Mataki na Biyu na Juyin Juya Halin Musulunci a bazarar shekarar 2020M. domin bayyana wannan bayani ga al'umma daban-daban, musamman matasa.

Munasaba, Jigo, Wanda Ake Magana Da Su

An fitar da bayani kan mataki na biyu na juyin juya hali a ranar 22 Bahman 1397Sh, a bikin cika shekaru arba'in na nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran.[1] A farkon bayanin, an tunatar da irin nasarar da juyin juya hali ya yi da kuma wucewar shekaru arba'in, sannan aka bayyana mataki na biyu na juyin juya hali a matsayin: gyaran kai, gina al'umma, da kuma gina wayewar Musulunci.[2]

Masu sauraron wannan bayani su ne matasa, waɗanda bisa ga rubutun bayanin za su fara[3] wani sabon sashe na babban jihadi domin gina Iran ta Musulunci mai girma. A cikin bayanin, an bayyana matasa a matsayin ginshiƙin tabbatar da tsarin Musulunci mai ci gaba, kuma ci gaban juyin juya halin zai ci gaba ne da ƙoƙari da wayewar matasa.[4] Har ila yau, bayanin ya bayyana cewa babbar damar da ke ba ƙasa fata ita ce ƙarfin ɗan Adam mai basira da ƙwarewa tare da tushe mai ƙarfi na imani da addini, kuma yawan matasan da shekarunsu ke ƙasa da arba'in wata babbar dama ce ga ƙasar.[5]

Abin da Yake Cikin Bayanin

Infogirafi na Bayani na mataki na biyu tare da suranta mutane

Bayani na mataki nabiyu na juyin juya hali ya fara da magana kan nasarar juyin juya hali Musulunci na Iran a shekarar 1978M. da kuma wahalhalun kafa jamhuriyar Musulunci ta Iran. A cikin bayanin an bayyana cewa burin juyin juya halin shi ne gina sabuwar wayewar Musulunci da kuma shirya duniya domin bullowar Hasken Ranar bayyanar wilaya ma'ana Imam Mahadi (A.F) Rayukanmu fansarsa.[6]

A wani sashe na daban daga bayanin mataki na biyu, an yi bayanin manyan nasarorin juyin juya halin Musulunci, kamar: Tabbatuwar zaman lafiya da tsaro da kuma kare baki ɗayan Iran, samar da manyan ginshiƙan rayuwa da tattalin arziki da gine-gine, ƙarfafa halartar jama'a a harkokin ƙasa, ƙara wayewar siyasa a cikin al'umma, kula da adalci wajen rabon damammakin ga jama'a, ƙaruwa a ruhi da ɗabi'a a cikin al'umma, da kuma tsayawa tsayin daka a gaban manyan masu girman kai na duniya.[7]

A ƙarshen bayanin Ali Khamna'i ya bayyana hangen nesa na makomar juyin juya halin Musulunci tare da shawarwari a fannoni bakwai: Ilimi da bincike: (Binciken kimiyya a fannoni daban-daban) An nuna ci gaban kimiyya na Iran, inda aka ce ƙasar ta kai matsayi na 16 cikin ƙasashe 200 na duniya. An buƙaci matasa su ci gaba da wannan tafiya tare da ƙarin jin nauyin alhaki.[8]

Ruhi da ɗabi’a An bayyana cewa ci gaban ruhi da ɗabi’a yana bukatar goyon bayan gwamnati, amma ba zai samu ta hanyar umarni kawai ba. Haka kuma an jaddada cewa hukumomi da cibiyoyi na gwamnati da na al’umma su tsara shirye-shirye na gajeren lokaci da matsakaicin lokaci domin hana ayyukan da ke yaƙi da ruhi da ɗabi’a[9] A farkon bayanin, an tunatar da irin nasarar da juyin juya hali ya yi da kuma wucewar shekaru arba'in, sannan aka bayyana mataki na biyu na juyin juya hali a matsayin: gyaran kai, gina al'umma, da kuma gina wayewar Musulunci.[10]

Tattalin arziki A cewar bayanin, mafitar matsalolin tattalin arziki ita ce manufofin tattalin arziƙin juriya shi kasancewa ya shafi kowane sashe[11] tattalin arziki mai dogaro da cikin gida, tattalin arziki mai samarwa da tushen ilimi, bai wa jama’a damar shiga harkar tattalin arziki, rage tsoma bakin gwamnati kai tsaye, da kuma bude tattalin arziki ga hulɗa da waje.[12] Adalci da yaƙi da cin hanci: An ce duk da cewa cin hanci a cikin jami’an gwamnatin Iran ya fi ƙasa da wasu ƙasashe musamman zamanin Muhammad Riza Pahlavi, amma duk da haka an bukaci dukkan jami’ai su guji dukiyar haram, kuma hukumomin sa ido su yi aiki wajen hana yaduwar cin hanci.[13] Ƴanci da cin gashin kai: An bayyana cewa ‘yanci da cin gashin kai duka ƙimomin Musulunci ne kuma baiwa ce daga Allah ga mutane, don haka kowa musamman gwamnatin Iran tana da alhakin kare su.[14] Amma an jaddada cewa cin gashin kai ba yana nufin kulle siyasa da tattalin arzikin ƙasa a cikin iyakokinta ba, kuma ‘yanci ba zai zama sabani da ɗabi’a, doka da ƙa’idodin addini ba. Martabar ƙasa da hulɗar waje: An bayyana cewa martabar ƙasa, hikima da maslaha su ne ginshiƙan hulɗar ƙasa da ƙasa. Don haka gwamnatin Iran ta kiyaye bambanci tsakaninta da shugabannin tsarin danniya na duniya, tare da kare martabar ƙasa da al’umma. [15]

Salon rayuwa: A cikin bayanin an ce ƙoƙarin ƙasashen yamma wajen yaɗa salon rayuwar yammacin duniya a Iran ya jawo matsaloli na ɗabi’a, tattalin arziki, addini da siyasa. Don haka an ce ya zama dole a yi jihadi mai faɗi da hikima domin fuskantar wannan al’amari.[16]

Zanen Hotuna Da Surori

A daidai lokacin da aka wallafa Sanarwar mataki na biyu na juyin juya halin a shafin ofishin kula da wallafa ayyukan Ali Khamna'i, jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, an fitar da wani hoto tare da rubutun sanarwar. A cikin hoton ana iya ganin ɓangarori daban-daban na al'umma suna tare da Sayyid Ali Khamna'i, kamar malamai na addini, dakaraun sa kai, ma'aikata, likitoci da ma'aikatan jinya, injiniyoyi, ƴan wasa, malamai na makarantu, masu fasaha da kuma ɗaliban jami'ai.[17] A wannan hoton kuma, tutar wannan tawaga tana hannun wata mace.[18]

Martani

Bayan fitar da sanarwar mataki na biyu daga jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, an samu martani masu kyau da dama daga masana, malamai na addini da kuma mutane na ɓangaren zamantakewa.[19]Daga cikinsu akwai Nasir Makarim Shirazi, ɗaya daga cikin manyan maraji'an taƙlidi na Shi'a mazauna birnin Qum, wanda a darasin kharijul fiƙihu da yake yi na matakin ƙoli ya bayyana sanarwar a matsayin mai matuƙar daidaito da cika, kuma ya ce tana ɗauke da wani shiri mai karfi da amfani domin shekaru arba'in masu zuwa na juyin juya halin Musulunci.[20]

Haka kuma Mahdai Shabezindedar, daga cikin ƙwararrun malaman fiƙihu a majalisar tsaron kundin mulki, kuma malami a darasul kharij, ya bayyana sanarwar a matsayin mai zurfin ma'ana da ilimi, har ma ya ware wasu darussan karatunsa na kharij domin bayaninta.[21] Sayyid Ahmad Khatami, memba na majalisar ƙwararru ta jagoranci, ya bayyana cewa tushen amincewar jagoran Jamhuriyar Musulunci ga matasa yana samo asali ne daga salon tsarin rayuwar Annabi Muhammad (S.A.W), wanda ya taba zaɓar matasa uku domin manyan muƙamai.[22]

Muhammad Taƙiyyu Misbahu Yazdi, memba na majalisar ƙwararru ta jagoranci, ya ce manufar fitar da wannan sanarwa ita ce isar da gadon da ya gabata ga sabuwar al'umma. Ya kuma jaddada cewa ra'ayin cewa duk wani juyin juya hali yana mutuwa ba gaskiya ba ne; juyin juya halin da ke mutuwa shi ne wanda aka gina shi kan abin duniya kawai, amma juyin juya halin Musulunci zai dawwama zai wanzu saboda ƙimominsa suna da alaƙa da halittar ɗan Adam.[23]

Mahadi Golshani, memba na cibiyar kimiyya ta Iran, ya bayyana cewa dalilin da ya sa aka mai da hankali ga matasa a cikin sanarwar shi ne domin su ne fata wajen gina makomar ƙasa, kuma a mahangar Ali Khamna'i wannan tsara ta matasa ba ta cika gurbata da sha'awar amfanin duniya na gajeren lokaci ba.[24] Muhsin Isma'ili, shi ma memba na majalisar ƙwararru, ya bayyana sanarwar a matsayin ɗaya daga cikin takardun fiƙihun siyasa. Ya kuma kwatanta ta da littafin Tanbihul Umma Wa Tanzihul Milla na Muhammad Husaini Na'ini, yana mai cewa sanarwar tana da muhimman ɓangarori uku: 1-Sake bayyana manufofin juyin juya halin Musulunci. 2-Duba tarihin ayyukan juyin juya halin Musulunci. 3-Tsara hanyar da za a bi a nan gaba.[25]

Sayyid Ibrahim Ra'isi, memba a majalisar ƙwararru ta Jagoranci, ya bayyana sanarwar a matsayin wani muhimmin juyi a tarihin juyin juya halin Musulunci, wanda ke nuna ci gaban da aka samu cikin shekaru arba'in, kuma yana ba da dabarun tafiyar da tsarin gwamnati a nan gaba. Ya kuma jaddada cewa wannan sanarwa ta bayyana a sarari cewa gina wayewar Musulunci abu ne mai yiwuwa.[26] Sayyid Muhammad Mahadi Mir Baƙiri, shi ma memba a majalisar ƙwararru, ya bayyana sanarwar a matsayin wacce ta fi girma fiye da littafin Tanbihul Umma Wa Tanzihul Milla, kuma ya kwatanta ta da takardar wasiyyar siyasar Allah ta Ruhullah Khomaini. Ya ce manufarta ita ce samar da ƙa'idar tafiyar da al'umma ta Musulunci domin kaiwa ga gina wayewar Musulunci.[27]

Bayanin kula

  1. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران», A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i..
  2. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»،A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i.
  3. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»، A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i.
  4. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»،A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i.
  5. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»، A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i.
  6. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»،A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i.
  7. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»،A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i..
  8. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»،A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i..
  9. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»، A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i..
  10. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»،A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i..
  11. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»، A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i..
  12. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»،A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i..
  13. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»،A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i.
  14. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»،A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i.
  15. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»،A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i.
  16. «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»،A shafin Ofishin Kula da Adanawa da Yada Ayyukan Ayatullahi Khamna'i.
  17. «در مورد گام دوم در ویکی تابناک بیشتر بخوانید»،Shafin Intanet na Tabnāk..
  18. «در مورد گام دوم در ویکی تابناک بیشتر بخوانید»، Shafin Intanet na Tabnāk.
  19. Wasu daga cikin waɗannan kyawawan martanoni.:پرونده/ گام دوم
  20. آیت‌الله مکارم شیرازی: بیانیه رهبر انقلاب بسیار راهگشا و جامع است، A cikin Kamfanin Labarai na Ānā (ANA).
  21. آغاز تبیین و تحلیل بیانیه گام دوم انقلاب از سوی آیت الله شب زنده دار، A cikin Kamfanin Labarai na ABNA
  22. «اعتماد به جوانان بر مبنای سیره نبوی است»، Shafin Intanet na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i .
  23. «آفت‌زُدایی از انقلاب» مأموریت جوانان در گام دوم, Shafin Intanet na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i ..
  24. «تولید علم در چهارچوب جهان‌بینی توحیدی»، Shafin Intanet na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i .
  25. «بیانیه گام دوم، سند فقه سیاسی»،Shafin Intanet na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i ..
  26. «با عزم راسخ، رسیدن به قله تمدنی امکان‌پذیر است»،Shafin Intanet na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i ..
  27. «دولت‌سازی اسلامی کارِ نسل جدید است»، Shafin Intanet na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i ..

Nassoshi