Hamase Imam Sajjad (Littafi)
![]() | |
| Marubuci | Sayyid Ali Khamna'i |
|---|---|
| Maudu'i | Tsarin rayuwar siyasa, al'ada da zamantakewa na Imam Sajjad (A.S) |
| Salo | Tarihi-Bincike |
| Harshe | Farsi |
| Da taimakon | Mawallafar Inƙilabe Islami |
| Adadin Jildi | 1 |
| Wurin da aka buga shi | Tehran |
Hamase Imam Sajjad (A.S), ma'ana Jarumtar Imam Sajjad (A.S) wani littafi ne da ya tattara wasu daga cikin jawabai da ra'ayoyin Sayyid Ali Khamna'i game da rayuwar siyasa, al'adu da zamantakewar Imam Sajjad (A.S). A cikin wannan littafi an tattauna batutuwa kamar nazariyar Mutum Mai Shekara 250, bayanin halin da mutane da ƴan Shi'a suka shiga bayan Waƙi'ar Karbala, da kuma nazarin marubucin game da rayuwar Imam Sajjad (A.S).
Muhimmanci Da Matsayi
Wannan littafi mai shafuka 282 yana bayani ne kan rayuwar al'adu da siyasar Imam Sajjad (A.S) daga hangen nesa na Sayyid Ali Khamna'i. A rahotan jaridar Khurasan, tsarin da aka tsara abubuwan cikin littafin yana da alaƙa da juna sosai, ta yadda mai karatu zai iya ƙara fahimta a hankali daga babi zuwa babi game da rayuwar Imam Sajjad (A.S), tare da warware duk wani ruɗani da zai iya tasowa a wasu sassa na littafin.[1] Binciken jaridar ya kuma nuna cewa masu tsara littafin sun shirya shi ne ta hanya da ke ba wa mai karatu damar bin tsarin karatu cikin sauƙi, musamman game da tarihin gwagwarmayar Imam Sajjad (A.S) tare da nazarin rayuwarsa ta siyasa da al'adu, ba tare da ya rikice ba.[2] Daga cikin siffofin wannan littafi akwai: Sauƙin bayani, Nazari mai zurfi, Da kuma amfani da salo na zamani wajen fahimtar abubuwan tarihi.[3]
Abubuwan Da Suke Cikin Littafin
Littafin ya kasu kashi uku:
- Kashi na Farko:Ya yi bayani kan nazariyar Mutum mai Shekara 250, tare da sharhin jawaban Sayyid Ali Khamna'i da ya gabatar a shekarar 1986 M. a babban taro na duniya na Imam Rida (A.S).[4]
- Kashi na Biyu:Wannan sashe ya ƙunshi jawabai huɗu da marubucin ya gabatar a Masallacin Karama na Mashhad a watan Fabrairu na shekarar 1974 M. A ciki an tattauna batutuwa kamar: Halin aƙidu da imanin mutane da ƴan Shi'a bayan Waƙi'ar Karbala, bayanin nauyin da ya rataya a wuyan Imam Sajjad (A.S) da himmar Imam wajen sauke wannan nauyi, makirci da kuma karkatar da gaskiya da Banu Umayya suka yi, ishara da nuni kan irin rawar da Imam ya taka wajen jagoranci da saita tunani, bayani game da dangantakar Imam da keɓantattun ƴan Shi'arsa, tarbiyya da tsara ƴan Shi'a da tura su zuwa sassa daban-daban na duniyar Musulunci,
tsauraran matakan Imam kan malaman fada, amfani da salon addu'a wajen isar da sahihiyar koyarwar Musulunci.[5]
- Kashi na Uku: Ya ƙunshi hirarraki da marubucin ya yi da mujallar Pasidare Islam a shekarar 1982 M, inda ya bayyana ra'ayinsa game da rayuwar Imam Sajjad (A.S).[6]
Buga Littafin
An gabatar da bikin ƙaddamar da littafin “Hamase Imam Sajjad (A.S)” a ranar 3 ga watan Maris 2021 M. a Jami'ar Ilimin Musulunci ta Ridawi a birnin Masshad.[7] Kamfanin wallafar Inƙilabe Islami, wanda yake ƙarƙashin ofishin kula da wallafawa da yaɗa ayyukan Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i, [8]shi ne ya buga littafin. An wallafa littafin a shekarar 2021 M, kuma zuwa watan Satumba 2021 M, ya kai bugu na shida, inda aka buga sama da kwafi 10,000.[9]
Bayanin kula
- ↑ Rawayati Motafawit az, Hamase-ye Imam Sajjad (A.S) Jaridar Khurasan.
- ↑ Rawayati Motafawit az Hamase-ye Imam Sajjad (A.S) Jaridar Khurasan.
- ↑ Rawayati Motafawit az Hamase-ye Imam Sajjad (A.S), Jaridar Khurasan.
- ↑ Kitab-e Hamase-ye Imam Sajjad (A.S) Tajdid-e Chap Shod, Kamfanin Labarai na ABNA.
- ↑ Kitab-e Hamase-ye Imam Sajjad (A.S), Kamfanin Labarai na ABNA.
- ↑ Kitab-e Hamase-ye Imam Sajjad (A.S), Kamfanin Labarai na ABNA.
- ↑ Hamase-ye Imam Sajjad (A.S) az Manẓar-e Rahbar-e Mo'aẓẓam-e Enqelab, Kamfanin Labarai na Tasnim Ali Khamenei.
- ↑ Kitab-e Hamase-ye Imam Sajjad (A.S) Tajdid-e Chap Shod, Kamfanin Labarai na ABNA.
- ↑ Kitab-e «Hamase-ye Imam Sajjad (A.S)» be Chap-e Sheshom Resid, Kamfanin Labarai na Littattafai na Iran.
Nassoshi
- کتاب حماسه امام سجاد(ع) تجدید چاپ شد., (An sake buga littafin Gwarzantakar Imam Sajjad (A)), Kamfanin Labarai na ABNA, ranar wallafa labari: 11 Maris 2023M, ranar ziyara: 1 Yuli 2023M.
- «کتاب «حماسه امام سجاد (ع)» به چاپ ششم رسید.، (Littafin Gwarzantakar Imam Sajjad (A) ya kai bugu na shida), Kamfanin Labarai na Littattafai na Iran, ranar wallafa labari: 31 Agusta 2022M, ranar ziyara: 1 Yuli 2023M.
- «روایتی متفاوت از «حماسه امام سجاد(ع).»، (Wani Labari na Musamman daga Gwarzuwar Imam Sajjad (A), Jaridar Khorasan, ranar wallafa labari: 10 Agusta 2022M, ranar ziyara: 1 Yuli 2023M.
- ««حماسه امام سجاد (ع)» از منظر رهبر معظم انقلاب»، (Gwarzantakar Imam Sajjad (A.S) daga hangen nesa na Babban Jagoran Juyin Juya Hali Ali Khamna'i.), Kamfanin Labarai na Tasnim, ranar wallafa labari: 1 Maris 2021M, ranar ziyara: 1 Yuli 2023M.
