Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci
| Suna | Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci |
|---|---|
| Assasawa | 1357 Shamsi (1979 Miladiyya) |
| Jarida | Jaridar Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci |
| Aƙida | Isar da sahihan tunanin addini ga al'umma.
Isar da sahihan nazarce‑nazarce na siyasa zuwa zurfin al'umma. Bayyana juyin juya hali da ma'anarsa. Bayyana yadda ake kafa tsarin gwamnati na Musulunci. |
| Mazhaba | Shi'a |
| Ƙasa | Iran |
Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci ita ce jam'iyya mafi muhimmanci a Iran bayan nasarar Juyin Juya Halin Musulunci. Wasu fitattun mutane ma'abota ilimi, addini da siyasa a Iran, waɗanda suka taka rawa a nasarar juyin juya halin kuma suka kasance daga cikin mataimaka Imam Khomaini, sun kafa Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci a shekarar 1979 miladiyya (1357 Shamsi).
Saboda kyakkyawan suna da martabar malamai na addini da suka kafa jam'iyyar, al'ummar Iran masu goyon bayan juyin juya hali sun karɓe ta hannu biyu-biyu da kuma matuƙar farin ciki da gagarumar maraba. Sayyid Muhammad Husaini Beheshti ya zama babban Sakatare na farko na Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci.
Manufar kafa wannan jam'iyya ita ce samar da tsari na siyasa mai faɗi kuma mai inganci bayan nasarar juyin juya hali, domin kada juyin juya halin Musulunci ya faɗa cikin irin ƙaddarar da Juyin Juya Halin Mashruɗiyya (Gwagwarmayar tabbatar da tsarin mulki) ya fuskanta a baya. Jam'iyyar ta gudanar da ayyuka da dama domin cimma manufofinta, kuma ta samu manyan nasarori a fannoni daban‑daban.
Sai dai daga baya, saboda wasu dalilai, ciki har da saɓani tsakanin mambobin Majalisar Tsakiya ta jam'iyyar da kuma shagaltar shugabanninta da manyan ayyukan gudanar da ƙasa, tare da amincewar Imam Khomaini, an rushe jam'iyyar a shekarar 1987 Miladiyya (1366 Shamsi).
Falsafar Kafuwar Jam'iyya
Dangane da abin da wasu 'yan siyasa suka naƙalto, buƙatar samar da tsari na ƙungiya da kuma daidaituwar aiki tsakanin ƙungiyoyin siyasa da masu gwagwarmayar addini na daga cikin abubuwan da suka fara damun tunanin wasu ƴan siyasa masu kishin addini tun bayan Satumba 1941 Miladiyya (Shahriwar 1320 Shamsi), musamman bayan juyin mulkin 19 Agusta 1953.[1]
Masu kafa jam'iyyar sun yi nazari kan yanayin tarihi da siyasar ƙasar a lokacin, kuma suka fahimci cewa bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, yayin da nauyin gudanar da ƙasa zai hau kan ƴan juyin juya hali, kuma dole ne a tafiyar da gwamnati bisa ƙa'idoji da manufofin juyin juya halin Musulunci, to akwai matuƙar bukatar ƙungiyar siyasa mai faɗi kuma mai ingantaccen tsari.
Sun yi imanin cewa idan ba a sami irin wannan tsari ba, akwai yiwuwar juyin juya halin Musulunci ya fuskanci irin ƙaddarar da Juyin Juya Halin Mashruɗiyya ya fuskanta a baya, ko wasu irin makamantansu.[Akwai buƙatar kawo madogara]
Taƙaitaccen Tarihi
Tun daga shekarar 1341 hijirar Shamsi (1962 Miladiyya), a tsakanin wasu malamai na addini da suke da ra'ayi iri ɗaya da Imam Khomaini, an fara tunanin kafa wata jam'iyya. Wannan tunani ya ƙara ƙarfi a 1356 hijirar Shamsi (1978 Miladiyya), a lokacin da sauye‑sauyen siyasa a Iran suka fara ƙaruwa sosai. Sai dai saboda tura wasu fitattun mutane zuwa gudun hijira da kuma matsin lamba da aka yi musu, ciki har da Sayyid Ali Khamna'i, wannan shiri ya tsaya na wani lokaci.
A daidai lokacin da nasarar Juyin Juya Halin Musulunci ta kusa, tare da sakin masu fafutukar addini daga takura, an sake jin buƙatar kafa ƙungiya mai tsari da haɗin kai.
A lokacin kakar da hunturun shekarar 1357 hijira Shamsi (1979 Miladiyya) wannan rukuni na malamai da ke kusa da Imam Khomaini suka tsara kundin tsarin aiki da manufofin Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci.
Ko da yake an ce Imam Khomaini ba ya da cikakkiyar sha'awa ga tsarin jam'iyyun siyasa, bayan nasarar juyin juya hali sai ya sanar da al'umma samuwar wannan jam'iyya.[2]
Waɗanda Suka Kafa Jam'iyyar

Mutanen da suka kafa Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci sun haɗa da:
- .Sayyid Muhammad Husaini Beheshti
- .Sayyid Abdul-Karim Musawi Ardabili
- .Akbar Hashimi Rafsanjani
- .Sayyid Ali Khamna'i
- .Muhammad Jawad Bahonar
A lokaci guda da kafa jam'iyyar, sun kasance mambobi na Majalisar Juyin Juya Hali. Haka kuma yawancin manyan shugabannin jam'iyyar, kamar Beheshti, Khamna'i, Hashimi Rafsanjani da Natiƙ Nuri, sun kasance mambobi na ƙungiyar malaman addini masu gwagwarmaya ta Tehran.[3]
Sayyid Ali Khamna'i ne ya rubuta sanarwar kafa jam'iyyar, kuma taron farko na Majalisar Tsakiya ya gudana a ranar 29 Bahman 1357 hijira Shamsi ( 18 Fabrairu 1979 Miladiyya) a Cibiyar Kanune Tauhid a Tehran.
Majalisar tana da membobi 30; ban da waɗanda suka kafa jam'iyyar, akwai wasu mutane 25 da suka kasance fitattun mutane masu taka rawa a juyin juya hali, daga cikin malamai, ƴan kasuwa da kuma malamai na jami'a.[4]
A wannan lokaci kuma, an zaɓi Sayyid Muhammad Beheshti a matsayin babban Sakatare na farko na jam'iyyar.
Tsarin Doka Da Tsarin Gudanarwa
Kundin tsarin Jam'iyyar ya ƙunshi maddodi 44 tare da ƙarin bayanai guda biyar, kuma an amince da shi a taron farko na babban taron jam'iyyar.
Tsarin jam'iyyar ya ƙunshi waɗannan sassa: Mamba (ɗan jam'iyya) ƙungiyar reshe, rukunin shiri ko horo, Majalisar sashe da ta gunduma da kuma ta jiha, Kwamitin zartarwa, Majalisar tsakiya Majalisar sulhu/daidaitawa (Shawarar warware sabani), Majalisar aƙida, Majalisar fatawa Babban taro, wanda shi ne mafi girman hukuma a jam'iyyar, Majalisar Tsakiya ita ce ke da alhakin tsarawa da shirya manufofi da ayyukan jam'iyyar.
Aikin majalisar aƙida da Majalisar Fatawa shi ne sa ido kan tafiyar jam'iyyar, tare da nazari da yanke hukunci kan shawarwarin da Majalisar Tsakiya ta amince da su.
Babban taro kuwa shi ne ke da alhakin: Amincewa da kundin tsarin jam'iyyar ko yin gyara a cikinsa, Zaɓen mambobin Majalisar Tsakiya da Majalisar sulhu Nazari da duba yadda jam'iyyar ke gudanar da ayyukanta.[5]
Matsayai Da Manufofin Jam'iyyar
Manyan ginshiƙan manufofin Jam'iyyar game da duniya da aƙida, gina al'umma, shirye‑shiryen al'adu da fasaha, gudanar da ƙasa, manufofin tattalin arziƙi da kuma manufofin harkokin waje, an bayyana su dalla‑dalla a cikin sanarwa da hirarraki na masu kafa jam'iyyar da kuma manyan mambobinta.
Dangane da manufofin harkokin waje, ra'ayoyin jam'iyyar sun haɗa da:
- .Imani da ƙa'idar "Ba Gabas ba, ba Yamma ba" (Wato rashin karkata ga kowanne daga manyan ƙasashen duniya).
- .Kafa dangantaka ta ƴan uwa da dukkan Musulmi a duniya.
- .Yanke duk wata alaƙar tattalin arziƙi da za ta iya haifar da mamayar manyan ƙasashe kan ƙasar Iran.
- .Bayyana makirce‑makircen manyan ƙasashen masu neman rinjaye, musamman gwamnatin Amurka.
- .Taimakawa ƙungiyoyin gwagwarmayar ƴanci a duniya a matsayin ɗaya daga cikin nauyin da ya rataya a wuyan gwamnatin Musulunci.[6]
Manufofin Kafa Jam'iyyar
Mutanen da suka kafa Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci sun sha bayyana cewa manufar kafa jam'iyyar ba ita ce shiga fafatawar neman mulki ko korar abokan hamayya na siyasa daga fagen siyasa ba. A maimakon haka, manufar ita ce:
- .Isar da sahihin tunanin addini ga al'umma.
- .Isar da ingantattun nazarce‑nazarce na siyasa zuwa zurfin al'umma.
- .Bayyana juyin juya hali da kuma fayace yadda ake kafa tsarin gwamnati na Musulunci.
- .Ci gaba da raya ruhin gwagwarmaya a cikin mutane tare da kare haɗin kansu.
- .Koyar da waɗannan manufofi ga matasa.
- .Ƙarfafa matasa su rungumi tsari da ladabin jam'iyya, tare da shirya su domin shiga fannoni daban‑daban na shugabanci da gudanarwa.[7]
Shigar Mambobi Miliyan Biyu Cikin Wannan Jam'iyya
Bayan sanar da kafa Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci, an samu yawan masu neman shiga jam'iyyar a duk faɗin ƙasar. Lamarin ya kai matsayin da a cikin ɗan gajeren lokaci adadin masu neman zama memba ya wuce miliyan biyu.
A birnin Tehran kaɗai, yawan masu neman shiga jam'iyyar ya haura mutum dubu 400.
A lokaci guda kuma, an samu ƙaruwa mai yawa na buƙatar buɗe ofisoshin jam'iyyar a garuruwa da yankuna daban‑daban na ƙasar, domin karɓar sabbin mambobi da kuma gudanar da ayyukan jam'iyyar.
Ayyukan Jam'iyyar
A cikin shekaru biyu zuwa uku na farko bayan nasarar Juyin Juya Halin Musulunci, shugabanni da masu gudanar da Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci sun ɗauki nauyi mai wahala. Dole ne su yi abubuwa biyu a lokaci guda: A gefe guda, ƙarfafa tushen jam'iyyar, tsara ra'ayoyi da manufofi, da kuma shirya tsare‑tsaren siyasa, al'adu da tattalin arziki, tare da faɗaɗa jam'iyyar ta fuskar yawan mambobi. A gefe guda kuma, jagoranci da tsara jama'a bisa koyarwar Imam Khomaini, domin su yi aiki tare da gwamnatin da juyin juya hali ya haifar. A cikin waɗannan shekaru, jam'iyyar ta gudanar da ayyuka masu yawa domin cimma manufofinta, kuma ta samu nasarori masu muhimmanci, daga cikinsu:
- .Taimakawa wajen gudanar da kuri'ar raba gardama kan Jamhuriyar Musulunci a ranar 10 Farwardin 1358 hijira Shamsi (31 Maris 1979 Miladiyya).
- .Gabatar da ƴan takara masu cancanta ga jama'a a zaɓen Majalisar ƙwararru wadda ta duba tare da amincewa da kundin tsarin mulki, tare da jaddada sashe na 110 (wanda ya shafi Wilayatul Faƙihi, (Iko da alhakin jagoran addini)
- .Taimakawa wajen gudanar da ƙuri'ar raba gardama kan kundin tsarin mulki.
- .Shiga mai ƙarfi a zaɓen shugaban ƙasa da kuma zaɓen Majalisar Shura ta Musulunci.
- .Tinkarar masu adawa da juyin juya hali, tare da shiga a fagen yaƙin da aka kallafa wa ƙasar.[8]
Bugu da ƙari, saboda yanayin tarihi na musamman da ƙasar ke ciki, jam'iyyar ta kuma yi wasu ayyukan raya ƙasa, kamar:
- .Kafa ɗakunan karatu (Laburare).
- .Buɗe ko kafa masana'antu.
- .Gina gidaje.
- .Shigar da bututun ruwa a ƙauyuka da yankuna masu ƙarancin ci gaba ko yankunan marasa galihu.[9]
Wallafe‑wallafe Na Hukuma
Bayan kafuwar Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci, jam'iyyar ta yi ƙoƙarin fitar da wata mujalla ko jarida da za ta zama muryarta a hukumance. An yi rijistar lasisin jaridar da sunan Sayyid Ali Khamna'i, kuma fitowar farko ta jaridar ta fito a ranar 9 Khordad 1358 hijira Shamsi (30 Mayu 1979 Miladiyya) da sunan Jaridar Jamhuriyar Musulunci. Jaridar ta fara aikinta ne da manufar: fahimtar abubuwan da ke faruwa yadda ya kamata, gano dangantakar da ke tsakanin su, da kuma watsa gaskiya cikin tsarin aƙidar Musulunci.
Babban abin da jaridar ta fi mayar da hankali a kai shi ne: Al'amuran duniyar Musulmi, goyon bayan masu rauni da zalunci ya shafa (mustad‘afun), da kuma kula da bukatun marasa galihu. Jaridar ta kuma rika wallafa jerin bayanai na musamman kamar “Mataki‑zuwa‑Mataki tare da Juyin Juya Hali”, inda take ruwaito da bayanin abubuwan da suka shafi juyin juya hali. Haka kuma ta jaddada gaggauta isar da labarai, gaskiya, da kuma ɗaukar matsayi mai dacewa wajen ba da rahoto.
Bayan rushewar jam'iyyar, jaridar ta ci gaba da aiki a matsayin mai zaman kanta, ƙarƙashin jagorancin Masiḥu Muhajiri a matsayin babban editan ta. Jam'iyyar ta kuma rika fitar da mujallar ɗaliban makaranta mai suna "Urwatul Wusƙa".
Ƙalubalen da Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci Ta Fuskanta
Duk da faɗaɗa da nasarorin da Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci ta samu, ta kuma fuskanci ƙalubale da matsaloli masu yawa. Tun daga farko, kafuwar jam'iyyar ta haifar wa da kanta wasu ƙorafe‑ƙorafe da rashin jin daɗi, domin wasu suna ganin cewa an ba wani rukuni na masu gwagwarmayar juyin juya hali fifiko a kan wasu. Wannan ya sa aka samu adawa da suka daga wasu ɓangarori.
Haka kuma abokan adawar juyin juya hali sun mai da suka da matsin lamba ga jam'iyyar da shugabanninta, musamman daga waɗanda ba su da ƙarfin halin su yi adawa kai tsaye da Imam Khomaini.
Daga cikin ƙungiyoyi da mutane da suka fi adawa da jam'iyyar akwai: Ƙungiyar Mujahidin Khalƙi, Abul-Hassan Bani Sadar, da kuma Jam'iyyar Khalƙi Musulman. Waɗannan sun zargi jam'iyyar da ƙoƙarin mamaye iko da kuma son rinjaye siyasa (Monopolizing power). Wannan adawa ta fara ne da: Yaɗa jita‑jita da farfaganda a kan shugabannin jam'iyyar, daga baya ta koma kisan mutunci (Character assassination), sannan ta kai ga yunƙurin kisan kai a zahiri. Misalai daga cikin waɗannan hare‑haren sun haɗa da: Yunƙurin kisan Hashemi Rafsanjani a bazaran shekarar 1979. Harinsa kan Sayyid Ali Khamna'i a ranar 6 Tir 1360 (27 Yuni 1981 Miladiyya), lokacin da bam ya fashe a wajen da yake gabatar da jawabi, wanda ya jikkata shi sosai a hannunsa.
Fashewar Ofishin Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci
A ranar 7 Tir 1360 hijira Shamsi (28 Yuni 1981) wani mummunan fashewar bam ya faru a hedikwatar Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci a Tehran. Wannan taron ya kasance na shugabannin jam'iyyar da jami'an gwamnati. A sakamakon fashewar: Sayyid Muhammad Beheshti, ɗaya daga cikin manyan shugabannin juyin juya hali kuma shugaban jam'iyyar, ya yi shahada. Fiye da mutane 80 daga manyan jami'an gwamnati da ƴan majalisa ma sun yi shahada. Saboda haka ana yawan kiran wannan lamari a tarihin Iran da suna “Hatsarin Shahidai 72” (Haftad‑o‑Do Shahid).
Bayan ɗan lokaci, a ranar 8 Shahrivar 1360 (30 Agusta 1981), wani fashewar bam ya faru a ofishin aikin shugaban gwamnati. A wannan harin: Muhammad Jawad Bahonar, wanda shi ne Sakataren Janar na biyu na Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci kuma Firaministan ƙasar Iran a lokacin, tare da Muhammad Ali Raja'i, Shugaban Ƙasar Iran a wancan lokaci, dukkansu sun yi shahada sakamakon fashewar bam a cikin ofishinsu. Rahotanni daga gwamnatin Iran sun danganta wannan hari da kuma fashewar ofishin jam'iyyar da Ƙungiyar Mujahidin Khalƙi ta Iran (MEK).
Bugu da ƙari, mutane biyu daga cikin mambobin Majalisar Tsakiyar Jam'iyyar ma sun rasa rayukansu a wasu hare‑haren ta'addanci da suka biyo baya. Rahotanni daga gwamnatin Iran sun danganta wannan hari da Ƙungiyar Mujahidin Khalƙi, wadda a wancan lokaci ta shiga rikici da gwamnatin juyin juya hali.
Wannan fashewa ta kasance ɗaya daga cikin manyan hare‑haren ta'addanci mafi girma a farkon shekarun bayan Juyin Juya Halin Musulunci na 1979 Miladiyya, kuma ta yi tasiri sosai a siyasar ƙasar da tsarin shugabancinta.
Duk da ƙarfi da nasarorin da Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci ta samu, akwai kuma raunuka a cikin tsarin ayyukanta. Jam'iyyar ta fuskanci matsaloli daga waje da kuma daga cikin gida, waɗanda suka haifar da ƙalubale ga aikinta. Daga cikin waɗannan raunuka akwai:
- .Saurin faɗaɗar jam'iyyar a fadin ƙasa ta fuskar yawan mambobi. Wannan ƙaruwa ta fi ƙarfin iyawar tsarin horo da gudanarwa na jam'iyyar, wanda ya sa ya zama da wuya a tsara dukkan mambobin yadda ya kamata.
- .Shagaltar shugabannin jam'iyyar da manyan ayyukan gwamnati. Yawancin shugabannin jam'iyyar suna riƙe da manyan mukamai a cikin gwamnati, don haka ba su da isasshen lokaci da za su ba jam'iyyar domin tsara ta da kula da harkokinta.
- .Shahadar manyan shugabanni da muhimman jami'an jam'iyyar, wanda ya kasance babbar illa ga wannan jam'iyya da ke cikin sabon mataki na kafuwa.[10]
- .Bayan kafa gwamnati bisa kundin tsarin mulki, bambance‑bambancen ra'ayi game da yadda za a tafiyar da al'amuran ƙasa suka fara bayyana sosai, musamman a batutuwan tattalin arziƙi.
Waɗannan bambance‑bambancen sun bayyana har cikin Majalisar Tsakiyar Jam'iyyar, misali a cikin muhawara kan: faɗaɗa ko rage mallakar gwamnati a tattalin arziki, da kuma matakin mayar da tattalin arziki karkashin kulawar gwamnati. Haka kuma, wasu mutane da ƙungiyoyin siyasa daga wajen jam'iyyar sun taka rawa wajen ƙara tsananta sabani da rarrabuwar kai.[11]
Dalilan Rushe Jam'iyyar
Yayin da saɓani a cikin Majalisar Tsakiyar Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci ya ƙaru, kuma aka samu matsaloli tsakanin jami'an jam'iyyar da masu gudanar da gwamnati a wasu birane, wannan al'amari ya isa wurin Imam Khomaini. Saboda haka, Sayyid Ali Khamna'i da Hashimi Rafsanjani suka rubuta wasiƙa ga Imam Khomaini a ranar 11 Khordad 1366 hijira Shamsi (1 Yuni 1987 Miladiyya) . A cikin wasiƙar: Sun jaddada rawar da jam'iyyar ta taka wajen tabbatar da tsarin Jamhuriyar Musulunci da kuma fuskantar maƙiyan juyin juya hali. Amma suka bayyana cewa ci gaba da ayyukan jam'iyyar na iya jawo rarrabuwar kai tsakanin ƙungiyoyin juyin juya hali. Saboda haka, suka sanar da Imam cewa Majalisar Tsakiyar jam'iyyar ta amince da rufe jam'iyyar da kuma dakatar da dukkan ayyukanta.
Imam Khomaini ya amince da wannan shawara, kuma daga nan ne aka dakatar da ayyukan Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci a shekarar 1987 Miladiyya.[12]
Bayanin kula
- ↑ Beheshti, Muhammad, Rast Qamatane Javdaneye Tarikhe Islam, daftar 1, Sh 450–451.
- ↑ Khamna'i ,Mosahabe darbare-ye Hezb-e Jomhuri-ye Islami, Noskhe-ye Mojud dar Ketabkhane-ye Bonyad-e Da'irat al-Ma'arif-e Islami.
- ↑ Kamfanin Labarai na Fars, 9/12/1392, Mosahabe ba Hojjat al-Islam Ebrahimi darbare-ye Hezb-e Jomhuri-ye Islami.
- ↑ Khamna'i , Sayyid Ali: Mosahabe darbare-ye Hezb-e Jomhuri-ye Islami, Noskhe-ye Mojud dar Ketabkhane-ye Bonyad-e Da'irat al-Ma'arif-e Islami.
- ↑ Jasbi, Abdullah, Tashakkole Faragir: Moruri bar Yek Dahé Fa'aliyyat‑e Hezbe Jomhuriye Eslami, j. 1, zamayem, SH 290–394.
- ↑ Jomhuriye Eslami (Jarida),Sal 2, Sh. 500–507, 4–12 Hezbe Jomhuri‑ye Eslami, Sh 9, 23–55, 80.
- ↑ Khamna'i , Sayyid Ali: Mosahabe darbare-ye Hezb-e Jomhuri-ye Islami, Noskhe-ye Mojud dar Ketabkhane-ye Bonyad-e Da'irat al-Ma'arif-e Islami.
- ↑ Beheshti, Rast-Qamatan-e Javidane-ye Tarikh-e Eslam, 1361 Shamsiyya, Daftar-e 3, safha 995; Khamene'i, Mosahabe darbare-ye Hezb-e Jomhuri-ye Islami, noskhe-ye mojud dar Ketabkhane-ye Bonyad-e Da'irat al-Ma'arif-e Islami."
- ↑ Beheshti, Mohammad, Amalkarde Yeksale ye Hezbe Jomhuri‑ye Eslami, Sh 48–49.
- ↑ Beheshti, Mohammad, Amalkarde Yeksaleye Hezbe Jomhuriye Eslami, Sh 14–17; Khamna'i , Sayyid Ali, Mosahabe darbare-ye Hezb-e Jomhuri-ye Islami, noskhe-ye mojūd dar Ketābkhāne-ye Bonyād-e Dā’irat al-Ma‘āref-e Eslāmi.
- ↑ Khamna'i , Sayyid Ali, Mosahabe darbare-ye Hezb-e Jomhuri-ye Islami, noskhe-ye mojūd dar Ketābkhāne-ye Bonyād-e Dā’irat al-Ma‘āref-e Eslāmi.; Jomhuriye Eslami (Jarida), sal 5, sh. 29 Bahman 1362, Sh. 10.
- ↑ Imam Khomaini, Sayyid Ruhollah, Sahifeye Nur, j. 20, Sh 93.
Nassoshi
- Hezb-e Jomhuri-ye Islami, Mavaze'-e Ma (Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci, Matsayoyinmu), ba a ambaci wurin bugawa ba, ba a ambaci shekarar bugawa ba.
- Beheshti, Mohammad, Rast Qamatane Javdaneye Tarikhe Islam, Tehran, Gidauniyar Shahidan Juyin Juya Halin Musulunci, 1361 SH.
- Beheshti, Muhammad, Amalkarde Yeksaleye Hezbe Jomhuriye Eslamii, Tehran, ba a ambaci mai wallafa ba, 1359 SH.
- Hashemi Rafsanjani, Akbar, Be Su‑ye Sarnewesht: Karnameh va Khaterat, Sale 1363 SH, bincike: Muhsin Hashimi, Tehran, ba a ambaci mawallafi ba, 1385 SH.
- Imam Khomaini, Sayyid Ruhullah, Sahifeye Nur, Tehran, Cibiyar Tsarawa da Buga Ayyuka na Imam Khomaini, 1369 SH.
- Jasbi, Abdollah, Tashakkole Faragir: Moruri bar Yek Dahé Fa'aliyyate Hezbe Jomhuriye Eslami, Tehran, ba a ambaci mai wallafa ba, 1377 SH.
- Khamna'i, Sayyid Ali, Chahar Sal ba Mardom, Tehran, Cibiyar Wallafa ta Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci, 1364 SH.
- Khamna'i, Sayyid Ali, Payam-e Dabire Kol-e Hezb-e Jomhuri-ye Islami dar Sheshomin Sālgerd-e Ta'sis-e Hezb (Saƙon Babban Sakataren Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci a bikin cika shekara ta shida da kafuwar jam'iyyar), Jaridar Jamhuriyar Musulunci, shekara ta 6, lamba ta 1662, 8 February 1985 Miladiyya.
- The Oxford encyclopedia of the modern Islamic world, ed. John L. ( Encyclopedia ta Oxford ta Duniyar Musulunci ta Zamani, wanda John L. ya shirya (Mai gyara).), Esposito, New York, 1995, ƙarƙashin taken Jam’iyyar Jamhuriyar Musulunci (Islamic Republican Party) wanda Eliz Sanasarian ya rubuta.