Hauza Jagora Abin Koyi
Hauza jagora abin koyi wani taken saƙo ne da Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i, Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya fitar domin tunawa da cika shekaru 100 da sake farfado da Hauzar Ilimi ta Ƙum.[1] An rubuta wannan saƙo a ranar 28 ga Afrilu shekarar 2025 M, kuma Ali Rida A'arafi, shugaban cibiyoyin hauza a Iran, ya karanta shi a taron ƙasa da ƙasa na tunawa da cika shekaru ɗari na sake farfaɗo da Hauzar Ƙum a ranar 7 Mayu.[2] A cikin wannan saƙo, Ayatullah Khamna'i ya yi bayani kan ginshiƙai da ayyukan da ake sa ran hauza ta ilimi za ta gudanar. Haka kuma ya bayyana abubuwan da ake buƙata domin a samu "hauza mai jagoranci kuma abin koyi". Ya jaddada cewa hauza ya kamata ta kasance:
- Mai kirkire-kirkire da samar da sabbin hanyoyi,
- Mai ci gaba da sabuntawa domin amsa sabbin matsalolin zamani,
- Mai tarbiyya mai kyau da ruhin ci gaba da jihadi
- Mai ruhin juyin juya hali, Kuma mai ikon tsara tsarin gudanar da al'umma.[3]
A cewarsa, mafi muhimmancin aikin hauza shi ne isar da bayyanannan saƙon addini, wato bayyana manyan da ƙananan ginshiƙan sabuwar wayewar Musulunci, da kuma bayyana, yaɗa, da kafa al'adunta a cikin al'umma.[4] A farkon saƙon, an yi magana kan tarihin kafa hauzar Ilimi ta Ƙum. tare kuma da nuna irin muhimmiyar rawar da Shaikh Abdul-Karim Ha'iri Yazdi (Rasuwa: 1936 M) ya taka wajen kafa da bunƙasa wannan hauza.[5] Haka kuma an bayyana cewa daga cikin manyan alfaharin wannan hauza a cikin wannan ƙarni akwai bayyanar Imam Khomaini.[6]
Ayatullah Khamna'i ya yi imani cewa Hauzar Qum a cikin ƙasa da shekaru sittin ta hanyar ƙarfin ruhaniya da kuma karɓuwar da take da shi a tsakanin mutane ta samu damar tayar da jama'a su kifar da mulkin sarauta, sannan bayan ƙarnoni da dama Musulunci ya sake komawa matsayin jagorancin siyasa a ƙasar.[7] A cikin wannan saƙon, an bayyana cewa hauza ba kawai makarantar karatun addini ba ce. A haƙiƙanin gaskiya ita ce tsarin da ya haɗa ilimi, tarbiyya, da ayyukan zamantakewa da siyasa. Daga cikin manyan ɓangarorin hauza mai jagoranci akwai:[8]
- Cibiyar ilimi mai fannoni na ƙwarewa daban-daban.
- Cibiyar tarbiyyar mutane masu nagarta da ƙwarewa domin jagorantar al'umma a *addini da ɗabi'a.
- Gaba-gaban sahun kare al'umma a fagen yaƙi da barazanar maƙiya.
- Cibiyar samar da tunanin Musulunci game da tsarin rayuwar al'umma, kamar:
tsarin siyasa, tsarin tafiyar da ƙasa, tsarin iyali da dangantakar jama'a bisa tsari fiƙihu da falsafa
- Cibiyar kirkire-kirkire na wayewa da hangen nesa na gaba, a cikin tsarin saƙon Musulunci na duniya.
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, kuma mafi alherin salati da sallama su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad Al-Mustafa da iyalansa tsarkaka, musamman ga Baƙiyyatullah a cikin duniya.
Bayyanar Hauzar Ilimi mai albarka ta Qum a farkon ƙarni na goma sha huɗu na hijirar shamsiyya wata gagarumar al'amari ce ta musamman, wacce ta faru a cikin wani lokaci mai cike da manyan bala'o'i da rikice-rikice. Wadannan abubuwa sun jefa yankin Yammacin Asiya cikin duhu da rikici, kuma rayuwar al'ummomin yankin ta fada cikin rudani da lalacewa.
Asalin wannan wahala mai yawa da tsawon lokaci shi ne tsoma bakin ƙasashen mulkin mallaka da kuma ƙasashen da suka yi nasara a Yaƙin Duniya na Farko. Wadannan ƙasashe, domin su mallaki wannan yanki mai matuƙar muhimmanci da ke cike da arzikin ƙasa, sun yi amfani da duk wata hanya da za ta kai su ga burinsu: da ƙarfin soja, da makirce-makircen siyasa, da cin hanci, da ɗaukar masu cin amanar cikin gida, da kayan yaɗa farfaganda da al'adu, da kuma duk wata dabara da za su iya amfani da ita, har suka cimma manufofinsu.
A Iraƙi, sun kafa gwamnatin Ingila, sannan daga baya suka kafa wata sarauta mai biyayya gare su. A yankin Sham, Ingila da Faransa sun shimfiɗa mulkin mallakarsu ta hanyar kafa tsarin rarrabuwa na addini a wani bangare, da kuma kafa wata sarauta mai biyayya ga Ingila a wani bangare, tare da kakabawa jama'a – musamman musulmi da malamai – matsin lamba da tsanantawa. A Iran, sun ɗaga wani soja daga rundunar Ƙozzak wanda ba shi da tausayi, mai son duniya kuma marar mutunci, suka ba shi iko har ya zama firaminista sannan daga baya sarki. A Falasɗinu, kuma sun fara shigar da sahyoniyawa a hankali a hankali, suna ba su makamai, suna shimfiɗa hanya cikin nutsuwa domin kafa wata cuta mai kama da ƙari a tsakiyar duniyar Musulunci
Duk inda aka sami juriya ga shirinsu – ko a Iraƙi, ko Sham, ko Falasɗinu, ko Iran – sai su murƙushe shi. A wasu garuruwa kamar Najaf, lamarin ya kai ga kama malamai gaba ɗaya, har ma da kora da wulakanta manyan maraji'i kamar Mirza Na'ini, Sayyid Abul Hassan Isfahani, da Shaikh Mahadi Khalisi. Har ma sun fara binciken gida-gida domin kama jaruman gwagwarmaya. Al'ummomi suka shiga firgici da ruɗani, kuma makoma ta zama mai duhu da rashin fata. A Iran kuma an zubar da jinin mujahidai a Gilan, Tabriz, da Mashhad, yayin da masu aiwatar da yarjejeniyoyin cin amanar ƙasa suka hau kan madafun iko.
A cikin irin wannan yanayi na bala'o'i da kuma irin wannan dare mai duhu ne tauraron Qum ya fara haskawa. Ikon Allah ya motsa wani babban fakihi mai tsoron Allah, mai kwarewa da hikima, wanda ya yi hijira zuwa Qum domin ya sake raya hauzar da ta lalace kuma aka rufe. Ya shuka wata sabuwar bishiya mai albarka a cikin wannan zamani mai wahala, a kusa da haramin tsarkakakkiyar ƴar Imam Musa Bin Jafar (A.S), a wata ƙasa mai shirin karɓar wannan shuka. Lokacin da Ayatullah Ha'iri ya shiga Qum, garin ba ya rasa manyan malamai. Akwai mutane masu girma kamar Ayatullah Mirza Muhammad Arbab, Shaikh Abul Ƙasim Kabir, da wasu da dama. Amma fasahar kafa Hauzar Ilimi – wacce za ta zama cibiyar ilimi, malamai, addini da masu tsoron Allah – tare da dukkan dabaru da hikimomin da ake bukata, abu ne da kawai mutum mai taimakon Allah kamar Ayatullah Haj Shaikh Abdul-Karim Ha'iri zai iya yi.
Kwarewarsa ta kafa da tafiyar da wata hauza mai bunƙasa a Arak na tsawon shekaru takwas, da kuma shekaru da dama kafin haka na kusanci da babban jagoran Shi'a Mirzayi Shirazi a Samarra, da kuma lura da yadda yake kafa da tafiyar da hauzar ilimi a can – duk waɗannan sun zama masa jagora. Hikimarsa, jarumtarsa, azamarsa da fatansa suka taimaka masa ya ci gaba a wannan hanya mai wahala. A shekarun farko, hauzar ta tsira daga tsananin zaluncin Rida Shah, wanda ya yi niyyar goge dukkan alamu da ginshiƙan addini ba tare da tausayi ga babba ko yaro ba. Amma da jajircewar wannan malami mai ikhlasi da tawakkali ga Allah, hauzar ta tsira. A ƙarshe wannan azzalumi ya halaka, amma hauzar – wacce ta sha wahala mai tsanani a karkashin matsin lambar sa – ta ci gaba da wanzuwa kuma ta bunƙasa. Daga cikinta ne daga baya wani rana mai haske ya fito – Imam Khomaini.
Wata rana daliban wannan hauza suna ɓoye kansu tun daga safiya a wajen gari domin su tsira daga kamuwa, suna karatu da tattaunawa, sannan da dare su dawo dakunansu masu duhu a makarantu. Amma cikin shekaru arba'in bayan haka, wannan hauza ta zama cibiyar da ta watsa wutar gwagwarmaya a duk fadin Iran, tana ƙarfafa zukatan da suka karaya, tana kuma jawo matasa masu zaman kansu su shiga cikin fagen fafutuka.
Haka kuma wannan hauza ce wacce, bayan rasuwar wanda ya kafa ta, da zuwan babban marja'i Ayatullah Burujerdi, ta zama ƙololuwar cibiyar ilimi, bincike da yaɗa Shi'anci a duniya baki ɗaya.
A ƙarshe, wannan hauza ce wacce cikin ƙasa da shekaru sittin ta kai matsayin da ƙarfin ruhaniya da karɓuwarta a wajen jama'a ya kai har ta iya kifar da gwamnatin sarauta mai cin amanar ƙasa, mai lalacewa da fasadi ta hannun jama'a. Bayan ƙarni da dama, Musulunci ya sake samun matsayi na shugabanci na siyasa a wata ƙasa mai girma, mai al'adu da kuma cike da basira da damar ci gaba.
Dalibin wannan hauza ne ya mayar da Iran abin koyi na neman Musulunci a duniyar Musulmi. Da kiransa na annabta jini ya yi nasara a kan takobi; da hikimarsa aka kafa Jamhuriyar Musulunci; da jarumtarsa jama'ar Iran suka tsaya tsayin daka a gaban barazana.
Rahamar Allah ta tabbata ga wanda ya kafa wannan hauza mai albarka – Ayatullah al-Uzma Haj Shaikh Abdul-Karim Ha'iri. Batutuwan da suka shafi makomar Hauza Yanzu ya zama dole a yi magana kan wasu muhimman batutuwa da za su taimaka wa makomar Hauzar Ilimi, domin ta zama hauza mai jagoranci kuma abin koyi. 1. Ma'anar Hauzar Ilimi Hauza ba kawai makarantar koyarwa ba ce. Ita ce: Cibiyar ilimi mai fannoni na musamman. Cibiyar tarbiyyar malamai masu tsoron Allah domin jagorantar al'umma. Gaban gaba na yaƙi da barazanar makiya. Wurin samar da tunanin Musulunci game da tsarin rayuwar al'umma – siyasa, zamantakewa, tattalin arziki, iyali da sauransu.
Cibiyar kirkire-kirkire domin gina sabuwar wayewar Musulunci. 2. Hauza a matsayin cibiyar ilimi Hauzar Qum ta gaji tarin ilimin Shi'a na shekaru fiye da dubu. Fiƙihu, kalam, falsafa, tafsiri da hadisi sun kasance ginshiƙai. Amma a yau ana bukatar fiƙihu ya iya amsa sabbin tambayoyi da matsalolin zamani. Dole ne fakihi ya san ilimin addini gaba ɗaya, kuma ya fahimci ilimin zamantakewar dan Adam na zamani domin ya iya bayar da amsa ga matsalolin yau. 3. Tarbiyyar malamai masu aiki Hauza tana da alhakin isar da saƙon addini ga al'umma (balagh mubin). Amma wannan yana bukatar: Horar da dalibai yadda za su yi muhawara da tattaunawa.
Fahimtar kafofin watsa labarai da sararin intanet. Shirya amsoshi ga shakku da ake yadawa. Haka kuma akwai bukatar tazkiya da gyaran hali, domin wanda zai kira mutane zuwa kyawawan dabi'u dole ya kasance yana da su. 4. Gaban gaba a fagen gwagwarmaya A cikin shekaru 150 da suka wuce, kusan dukkan gwagwarmayar gyara ko juyin juya hali a Iran da Iraki malamai ne suka jagoranta. Daga haramta taba sigari na Mirza Shirazi, zuwa gwagwarmayar juyin juya halin Musulunci. Saboda haka hauza dole ta ci gaba da kasancewa tare da jama'a kuma ta tsaya kan kare adalci da yaƙar zalunci. 5. Samar da tsarin zamantakewa na Musulunci Al'ummomi suna tafiya ne da tsare-tsare: tsarin siyasa, tattalin arziki, shari'a, iyali da sauransu. A tsarin Musulunci dole wadannan su samo asali daga Kur'ani da Sunnah. Hauza tana da alhakin fitar da wadannan tsare-tsare. 6. Ginin sabuwar wayewar Musulunci Babban buri na juyin juya halin Musulunci shi ne gina sabuwar wayewar Musulunci – wayewa wacce ilimi, fasaha, gwamnati, tattalin arziki da dukkan karfin dan Adam za su yi aiki domin adalci, walwala da cigaban ruhaniya. Wannan wayewar za ta kasance akasin wayewar kayan duniya ta yau, wacce ta ginu kan mulkin mallaka, zalunci da lalacewar dabi'u. Halin Hauzar Qum a yau Hauzar Qum a yau tana da dubban malamai, masu bincike da marubuta. Akwai ci gaba a darussan tafsiri, falsafa da sauran ilimi. Dalibai daga kasashe daban-daban suna karatu a cikinta. Sai dai har yanzu akwai tazara tsakanin wannan matsayi da matsayin da ake so na hauza mai jagoranci. Don haka: Dole hauza ta rika tafiya tare da zamani. A kara kula da tarbiyyar dalibai. A kara kusanci tsakanin malamai da jama'a.
A rubuta manhajar karatu da za ta hada fiƙihu mai amsa tambayoyin zamani, falsafa mai zurfi, da kalam mai gamsarwa. A karfafa dabi'u kamar zuhudu, taƙwa, tawakkali da shirye-shirye na jihadi. Game da takardun karatu kuma, ya dace hauza ce da kanta ta rika ba da shaidar karatu ga dalibanta. A ƙarshe ina roƙon Allah Madaukaki Ya ƙara ɗaukaka Musulunci, Ya ƙarfafa al'ummar Musulmi, Ya ba wa al'ummar Iran cigaba da farin ciki, Ya kuma ƙara ɗaukaka da ƙarfafa hauzocin ilimi. Salamar Allah ta tabbata ga Imam Mahdi (a.f.), da kuma tsarkakan ruhukan shahidai da ruhin Imam Khomaini.
27 ga watan Afrilu 2025 M
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Sayyid Ali Khamna'i
Bayanin kula
- ↑ «حوزه پیشرو و سرآمد»،Shafin Yaɗa Labarai na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Uzmā Sayyid Ali Khamna'i ..
- ↑ «حوزه پیشرو و سرآمد»، Shafin Yaɗa Labarai na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Uzmā Sayyid Ali Khamna'i .
- ↑ «حوزه پیشرو و سرآمد»، Shafin Yaɗa Labarai na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Uzmā Sayyid Ali Khamna'i .
- ↑ «حوزه پیشرو و سرآمد»،Shafin Yaɗa Labarai na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Uzmā Sayyid Ali Khamna'i .
- ↑ «حوزه پیشرو و سرآمد»،Shafin Yaɗa Labarai na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Uzmā Sayyid Ali Khamna'i ..
- ↑ «حوزه پیشرو و سرآمد»، Shafin Yaɗa Labarai na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Uzmā Sayyid Ali Khamna'i ..
- ↑ «حوزه پیشرو و سرآمد»، Shafin Yaɗa Labarai na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Uzmā Sayyid Ali Khamna'i ..
- ↑ «حوزه پیشرو و سرآمد»،Shafin Yaɗa Labarai na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Uzmā Sayyid Ali Khamna'i ..
Nassoshi
- «حوزه پیشرو و سرآمد»، (Hauza Jagora Abin Koyi), Cibiyar sadarwa ta ofishin kula da buga ayyukan Mai girma Ayatullahi Al-Uzma Sayyid Ali Khamna'i، Ranar wallafawa 17ga watan Mayu 2025 M. Ranar da aka duba shafin: 25 ga watan Mayu 2025 M.