Abokan Gwagwarmayar Husaini (Littafi)
| Marubuci | Sayyid Ali Khamna'i |
|---|---|
| Tarihin rubutu | 2017M |
| Maudu'i | Kalam da Akhlaƙ |
| Harshe | Farsi |
| Da taimakon | Cibiyar Bincike da Al'adu ta Juyin Juya Halin Musulunci. |
| Adadin Jildi | 1 |
| Mai bugawa | Cibiyar Bincike da Al'adu ta Juyin Juya Halin Musulunci. |
| Wurin da aka buga shi | Tehran |
'Abokan gwagwarmayar Husaini' wani littafi ne da ya ƙunshi rubutattun jawaban Sayyid Ali Khamna'i da ya gabatar a watan Muharram na shekarar 1972 miladiyya (wanda ya yi daidai da 1393 Hijiriyya ƙamari). A cikin wannan aiki, an tattauna batutuwa kamar nazariyar mutum mai shekaru 250, ma'anar jihadi, nazarin jihadi a cikin rayuwar Imaman Shi'a, da kuma fahimtar makircin abokan gaba wajen karkatar da hoton gwagwarmayar su.
An buga wannan littafi a shekara ta 2017 miladiyya.
Matsayi Da Muhimmanci
Littafin Abokan gwagwarmayar Husaini ya ƙunshi jerin jawaban da aka gabatar a Muharram na 1972 miladiyya (1393H), a lokacin da yanayin siyasa da addini a Iran yake da zafi kafin juyin juya halin Musulunci na 1979 miladiyya. A wancan lokaci, Sayyid Ali Khamna'i, wanda shi ne mai gabatar da jawaban, yana cikin masu gwagwarmaya da gwamnatin Pahlawi.
An gabatar da waɗannan jawaban a Hai'at Ansarul Husain a Tehran. A cikin su, Khamna'i ya yi magana kan: Muhimmancin sanin Imamai daidai, fahimtar makircin abokan gaba wajen karkatar da hoton gwagwarmayar su, da kuma ma'anar jihadi[1] A cikin wannan littafi marubucin ya gabatar da nazariyar mutum mai shekaru 250, inda ya bayyana cewa daga Imam Sajjad (A.S) zuwa Imam Hassan Askari (A.S) duk abokan gwagwarmayar Imam Husaini (AS) ne.[2]
Ɗaya daga cikin bambance‑bambancen wannan littafi da littafin Mutum Mai Shekaru 250 shi ne cewa wannan yana da tsari mai haɗin kai a cikin batutuwansa kuma yana ƙunshe da ƙarin bayanai a ɓangaren tarihi da ɗabi'a.[3]
A wajen rubuta littafin, an yi ƙoƙari kada a canza salon magana na asali sosai domin mai karatu ya fi samun kusanci da rubutun.[4]
Haka kuma, an zaɓi wannan littafi a matsayin ɗaya daga cikin darussan ilimin addinin Musulunci a jarabawar ɗaukar malaman makaranta (Primary teachers) da Ma'aikatar Ilimi ta Iran gudanarwa.[5]
Abubuwan Da Littafin Ya Ƙunsa
Littafin ya ƙunshi jawabai goma na Sayyid Ali Khamna'i, kuma dukkansu suna magana ne kan ɓangaren gwagwarmaya a rayuwar Imman Shi'a.[6]
Batutuwa goma na littafin su ne:[7]
- Nau'o'in tattaunawa kan batun Imamanci
- Muhimmancin sanin ainihin halaye da rayuwar A'imma
- Falsafa da manufar Imamanci
- Mutum mau shekaru 250 na gwagwarmaya
- Lokuta huɗu na Imamanci
- Nazarin farkon zangon lokaci na huɗu na Imamanci
- Rayuwar siyasa ta Imam Sadiƙ (A.S)
- Matakai masu tsauri na A'imma da yadda suka yi hulɗa da malamai da mawaƙan fadar sarauta
- Ƴaƴan Imamai masu juyin juya hali
- Taƙiyya
Buga Littafin
Cibiyar Bincike da Al'adun Juyin Juya Halin Musulunci (Ofishin kiyaye da wallafa ayyukan Ayatullah Khamna'i) ce ta tattara littafin daga fayilolin sauti na jawaban Sayyid Ali Khamna'i, ta shirya su sannan ta buga littafin a 2017 miladiyya.
A yayin rubuta jawaban na tara da na goma, saboda babu fayilolin sauti, an dogara ne da rubutaccen kwafin da aka riga aka sauya daga magana zuwa rubutu.[8]
Bayanin kula
- ↑ Khamna'i, Hamarzaman Husain, shafi na 7
- ↑ Hamarzaman Husain (a.s.), shafin yanar gizon Ayatullah al‑Uzma Sayyid Ali Khamna'i.
- ↑ Tafāwut-e Kitāb-hā-ye Insān-e 250 Sālah va Hamarzaman Husain (a.s.), shafin yanar gizon Aqeeq.
- ↑ Hamarzaman Husain (a.s.), shafin yanar gizon Ayatullah al‑Uzma Sayyid Ali Khamna'i.
- ↑ Manabi'-e Umumi-ye Azmun-e Estekhdami-ye Dabiri wa Honaramuz, Kamfanin Labarai na Rasta.
- ↑ Khamna'i, Hamarzaman Husain, shafi na 7
- ↑ Khamna'i, Hamarzaman Husain, shafi na 9-10
- ↑ Khamna'i, Hamarzaman Husain, shafi na 8
Nassoshi
- «تفاوت کتابهای انسان ۲۵۰ساله و همرزمان حسین(ع)، (Bambanci tsakanin littattafan Mutumin Shekara 250 da Hamarzaman Husain (A.S)),Shafin Aqiq, ranar wallafa bayani: 10 Yuli 2018 Miladiyya, ranar dubawa: 19 Agusta 2023 M.
- «همرزمان حسین (علیهالسّلام) »،(Abokan gwagwarmayar Husain (A.S)), Shafin yanar gizon Ayatollah al‑Uzma Sayyid Ali Khamna'i, ranar wallafa: 27 Nuwamba 2017, ranar ziyara: 19 Agusta 2023M.
- «منابع عمومی آزمون استخدامی دبیری و هنرآموز۱۴۰۲»،(Tushen karatu na gama‑gari – jarrabawar daukar ma'aikata ta Ma'aikatar Ilimi (Iran)), Kamfanin Labarai na Rasta,Kamfanin Dillancin Labarai na Rasta, ranar wallafa: 18 Yuni 2023 M, ranar dubawa: 19 Agusta 2023 M.
- Khamna'i, Sayyid Ali, Hamrazaman Husain (A.S), Tehran: Cibiyar Bincike da Al'adu ta Juyin Juya Halin Musulunci, 1397Sh...