Fatawar Haramcin Ƙirƙirar Makamin Ƙaredangi da Yin Amfani da shi
Fatawar haramcin ƙirƙirar makamin ƙare dangi da yin anfani da shi (Larabci: فتوى تحريم صناعة واستخدام الأسلحة النووية) fatawa ce ta fiƙihu wace Assayid Ayatullahi Ali Alkhamna'i ya fitar da ita a matsayin raddi kan ƙasar Isra'ila lokacin da ta yi iƙrarin cewa Iran tana yunƙurin ƙirƙirar makamin ƙare dangi, Assayid Ali Alkhamna'i yana ganin cewa makamin ƙare dangi barazana ce ga ɗan adam kuma ya haramta.
Wasu daga cikin malamai sun kafa hujja da ayoyin kur'ani da hadisai kan haramcin mallakar makamin ƙare dangi, sabo da haramcin aikata ta'addanci kan mutane, bisa abin da Abu ƙasim Ali Dusti ya faɗa, haƙiƙa malaman Shi'a sun yi fatawar haramta makamin ƙare dangi tin ƙarni goma da suka gabata.
wannan fatawa tana da tasiri mai ƙarfi a siyasance a cibiyioyin masu fashin baƙi na siyasa da na masu tunani a duniya, kuma ita wannan fatawa an rubutata a majalisar ɗankin duniya a matsayin wani ƙuduri abin dogara a hukumance. A cikin wani littafi na haɗin gwiwar marubuta mai suna "Fiƙhu Haste'i" da kuma littafi mai suna "Fatawa Annawawi min manzruil al-ƙanun ad-duwali" na jabir Saifani Zade.
Muhimmanci
Sayyid Ali Khamna'i jagoran jamhuriyar musulinci ta ƙasar Iran ya yi fatawar haramta ƙirƙira makamin ƙare dangi da kuma yin anfani da shi, wannan ya zo ne sakamakon raddi da ya yi wa kafar yaɗa labarai ta haramtacciyar ƙasar Isra'il, a lokacin da suka bayyana cewa Iran tana da aniyar ƙirƙirar makamin ƙare dangi،[1] wannan fatawa an karantata a taro da aka yi na ƙasa da ƙasa domin lalata makamin gare daangi da kuma hana yaɗuwar shi a shekara ta 2010 miladiya.[2]
Ali Akbar Salihi shugaban tashar makamashi na Iran a lokacin da yake bada amsar wata tambaya kan aniyar ƙasar Iran ta ƙirƙirar makamin ƙare dangi, ya ce abin da ya fi ga ƙasar Iran shi ne kulawa da bin fatawar haramcin anfani da shi..[3]
Tasiri
Fatawar haramta makamin ƙare dangi ta Sayyid Ali Alkhamna'i ta samu karɓuwa a duniya[4] kuma ta ya ɗu da tasiri a guraren da suke fashin baƙi irin na siyasa[5] bisa abin da kamfanin dillancin labarai ya tabbatar da cewa wannan wasiƙa ta Ayatullahi khamna'i an rubutata a ƙudirin hana ya ɗuwar makamin ƙare dangi kuma a cikinta akwai fatawar haramcin ƙirƙira makamin ƙare dangi da kuma yin anfani da shi, a matsayin wani dalili a hukumance na majalisar ɗinkin duniya.[6] kuma Jonasan Jara'if shugaban cibiyar tsaro ta duniya a ƙasar America, ya buƙaci da Sayyid Alkhamna'i ya yin da yake yi mishi tambayoyi cewa ya rubuta wasiƙa zuwa ga malaman addini domin su mara mishi baya kan haramcin anfani da makamin ƙare dangi ta fuskar kowanne dalili..[7]
A shekara ta 2013 ne mutum shida daga masu hango abin da zai faru da kwararrun masana doka na ƙasar Amurka suka haɗu da wasu daga cikin malaman shi'a domin tattauna ingancin fatawar Sayyid Ali khamna'i ta haramta ƙera makamin ƙare dangi da kuma haramcin anfani da shi, kuma sun isar da saƙon hana ƙirƙirar makamin ƙare dangi a fiƙihun shi'a da sakamakon ziyarar da suka kai ƙasar Iran ga gwamnatin ƙasar Amurka, domin shigar da su cikin tattaunar Iran da ƙasashan yammacin duniya kan makamin ƙare [8] a shekara ta 2021 gidan talbijin na BBC Farisi ya yaɗa wani fim mai ɗauke da take ko sunan Fatawar makamin ƙare dangi a wani shiri mai suna yiwar canji fatawar Ayatullahi Al-khamana'i[9] sai dai malamai sun kore yiwuwar canzawarta. sabo da rashin alaƙar wannan fatawa da wani lokacin na masamman ko wani guri daban.[10]
Tarihin Mas'alar
Makamin nukiliya shi ne wanda akafi sani da makaman kare dangi[11] A cewar Abu al-ƙasim alidust, a cikin shekarar 2014, malaman fikihu na Shi'a sun ba da fatawa da ke hana amfani da makamin ƙare dangi da kayan aikin da ke haddasa kisan kare dangi, da kashe halittu da lalata muhalli.[12] tun daga ranar 19 ga watan Fabrairun 2010 Ayatullah Khamna'i ya sha bayyana fatawa da ra'ayinshi na adawa da kera da kuma amfani da makaman nukiliya.[13]
Fatawar Da Ittifaƙin Maraji'ai

A ranar 17 ga watan Afrilu, 2010, Ali Akbar Wilayati ya karanta fatawar Ayatullahi Khamna'i a cikin wasiƙarsa ta hukuma zuwa taron farko na duniya ga ƙasashe masu ƙawance domin lalata makamin ƙare dangi[14] ga abin da yake cewa: Baya ga makaman nukiliya, mun yi imanin cewa sauran nau'o'in makaman kare dangi, irin su makamai masu guba da ƙananan makamai, suna haifar da mummunar barazana ga bil'adama, kuma muna ganin haramun ne yin amfani da waɗannan makamai .[15]
Fatawowin wasu Maraji'u na Taƙalidi, kamar Makarim Shirazi, Nuri Hamadani Jafar Subhani, da Jawadi Amoli, sun tabbatar da fatawar Ayatullah Khamna'i[16] Abu Al-ƙasim Ali Dust, darektan taron ƙasa kan harkokin shari'a na nukiliya, da Ahmed Muballigi, ɗaya daga cikin wakilan majalisar kwararru ta jagoranci, sun yi imanin cewa wannann fatawa hukunci ne na Ubangiji madawwami wanda ba za a iya canza taba.[17]
Dalilan Fatawar Haramta Makamin Ƙare Dangi
An ambaci dalilai daban-daban shari'a da suka haramta kira da amfani da makaman nukiliya, kuma a akidar Ayatullah Khamna'i, dalilin hana kerawa da amfani da makaman kare dangi shi ne cin karon amfani da makaman kare dangi tare da manufofin Musulunci. kamar yadda amfani da irin waxannan makaman yana lalata noma da tsirrai, kuma wannann shi ne abin da ya zo a cikin aya ta 205 daga cikin Suratul Baƙarah: Kuma idan ya juya sai ya yi gaggawa don yaɗa fasadi a cikinta. Kuma Ya halakar da shuka da ƴaƴan dabbobi. Kuma Allah ba ya son ɓarna.[18] Dangane da hakan, Abu Al-ƙasim Alidust ya bayyana cewa, gyara yanayin da mutane ke ciki da alakarsu da Allah da juna, yana daga cikin manufofin shari'a, kuma ba a taba samun gyara tare da fasadi da amfani da makaman kare dangi.[19]
Ayoyin Kur'ani
Ahmad Muballigi Malamin fiƙihu a shi'a ya yi imani cewa abubuwan da suka yi sanadiyyar wannan fatawa suna da yawa, da cikin su akwai ginshiƙai guda uku a kur'ani ،[20] ga su kamar haka:
- Dogaro bisa ƙa'idatul Wizri, "ولا تَزِرُ وازرةٌ وزرَ أُخرى" Kuma wani rai ba ya ɗaukar nauyin wani. wannan aya tana hana hukunta wani da laifin wani, wato yayin da ake so a hukunta masu laifi ba zai yiwu a haɗa da marasa laifi ba.
kuma anfani da makamin nukiliya yana kai ga kisan kiyashi da kashe ƴan ba ruwana, kai anfani da shi yana kai ga cutar da mutaanan da za su zo a nan gaba.
- Bisa dokar hana fasadi a doran ƙasa aya ta 205 a cikin Baƙara, Allah ya hana aikata duk wani aiki wanda zai kai ga fasadi a doran ƙasa da kuma lalata shuka da ƴaƴan dabbobi.
- Ƙa'idatul Ismi, «إثمُهُما اَكْبَرُ مِنْ نَفْعِهِما» daga wannan ana fahimtar cewa, duk wani abu da sharrinshi da fasadinshi idan yafi yawa ya rinjayi anfanin shi zai zamo haramun, to a bayyane yake cewa fasadin makamin nukiliya yafi anfanin shi da ake sa rai.
Haka kuma Nasir ƙurbani niya ya kafa hujja da cewa aya ta 190 da ta 205 a cikin Suratul Baƙarah da aya ta 8 da 32 a cikin Suratul Ma'idah sun ƙunshi haramcin makaman kare dangi.[21]
Dalili Na Riwaya
A cikin binciken fikihun haramta makaman kare dangi, an kawo wasu ruwayoyi, kamar ruwayoyin da suka haramta sanya guba a cikin ruwan makiya.[22] waɗanda Abu al-ƙasim Alidust da Muhammad Jawad Fadil Lankarani suka kawo a matsayin hujja, da ruwayoyin haramta cin zarafi ga wasu kamar, yara, mata, dattijai, ƴantattu, da dabbobi).[23]

Bayanin kula
- ↑ «تسجيل رسالة قائد الثورة الإسلامية كوثيقة عند الأمم المتحدة»،Ofishin Kiwo da Wallafa Na Ayyukan Ayatollah Khamenei.
- ↑ «التعريف بالمؤتمر الدولي لنزع السلاح وعدم انتشار الأسلحة النووية»،Shafin Hamshahri Online
- ↑ «صالحي: وحده قائد الثورة يستطيع أن يعطي رأي صائب حول صناعة الأسلحة النووية»، Kamfanin dillancin labarai na Hamshahri.
- ↑ «مراجعة لفتوى تحريم الأسلحة النووية الصادرة عن قائد الثورة الإسلامية»، Shafin basira.
- ↑ «تسجيل رسالة السيد الخامنئي كوثيقة عند الأمم المتحدة»، Jaridar Kihan.
- ↑ «زعماء دينيون ينضمون إلى آية الله خامنئي»، Ofishin Kiwo da Wallafa Na Ayyukan Ayatollah Khamenei.
- ↑ «زعماء دينيون ينضمون إلى آية الله خامنئي»، Ofishin Kiwo da Wallafa Na Ayyukan Ayatollah Khamenei
- ↑ «ذهبنا إلى قم للتحقيق في فتوى النووي لآية الله الخامنئي/أرسلنا تقرير رحلتنا إلى البيت الأبيض/من المؤكد دراسة هذا التقرير من قبل الحكومة الأمريكية»،Shafin Mashraq.
- ↑ «فتوى نووية - بین السطور»، موقع BBC News الفارسي.
- ↑ «هل يمكن تغير فتوى تحريم السلاح النووي؟»، Kafanin dillancin Labarai na Fars.
- ↑ «صناعة واستخدام أسلحة الدمار الشامل من منظور الفقه الإسلامي»، Shafin cibiyar A'Immatul Athar Fikhi
- ↑ «بحث في تحريم أسلحة الجمار الشامل في تاريخ التشيع»، Shafin Ayatullahi Ali Dusti.
- ↑ Ku Duba«بیانات خلال لقاء مع العالمين على المدمرة جماران»، Ofishin Haƙƙoƙi da Wallafa Ayyukan Ayatullah Khamenei; «بیانات قائد الثورة الإسلامية خلال لقاء مسؤلين وعاملين في الحكومة»، Ofishin Haƙƙoƙi da Wallafa Ayyukan Ayatullah Khamenei; «الفتوى التي وصلت إلى الأمم المتحدة بعد 10 سنوات»، Kamfanin dillancin Labarai na Mehr.
- ↑ «رسالة إلى المؤتمر العالمي لنزع السلاح النووي ومنه انتشاره»، Ofishin Kiwo da Wallafa Na Ayyukan Ayatollah Khamenei.
- ↑ «رسالة إلى المؤتمر العالمي لنزع السلاح النووي ومنع انتشاره»، Ofishin Kiwo da Wallafa Na Ayyukan Ayatollah Khamenei
- ↑ «تحریم أسلحة الدمار الشامل في تاريخ التشيع»، Kamfanin dillancin labarai na ISNA.
- ↑ «لوازم فتوى قائد الثورة حول تحريم السلاح النووي»، Shafin Tasneem؛ «هل يمكن تغير الحكم بحرمة السلاح النووي؟»، Kamfanin dillancin labarai na tasneem.
- ↑ «بيانات خلال لقاء مع العاملين في بناء المدمرة جماران»، Ofishin Kiwo da Wallafa Na Ayyukan Ayatollah Khamenei.
- ↑ Rukunin marubuta, “Fiƙh Haste'i” (Fiƙh al-Nawawi), 1397 AH, shafi 113.
- ↑ «الأدلة الفقهية لتحريم السلاح النووي»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي.
- ↑ Majmu muallifin, “Fiƙhu Haste'i” (Fiƙh al-Nawawi), 1397 AH, shafi na 182-184.
- ↑ Majmu muallifin, “Fiƙhu Haste'i” (Fiƙh al-Nawawi), 1397 AH, shafi na 87-112
- ↑ Majmu muallifin, “Fiƙhu Haste'i” (Fiƙh al-Nawawi), 1397 AH, shafi na 85-87.185. 231.343
Nassoshi
- «التعريف بالمؤتمر الدولي لنزع السلاح وعدم انتشار الأسلحة النووية»، Shafin yanar gizo na Hamshehri Online, ranar wallafa: 3 ga Mayu 1389, ranar kallo: 27 ga Fabrairu 2024.
- «هل يمكن تغيير فتوى حرمة الأسلحة النووية»،Hausa News Agency, Date of publication: 16th Bashman 1400, Date of viewing: 27th February 2024..
- «مراجعة لفتوى تحريم الأسلحة النووية الصادرة عن قائد الثورة الإسلامية»، Shafin Basira, ranar wallafa: 25 ga Fabrairu 1399SH, ranar kallo: 27 ga Fabrairu 2024.
- «تحقيق في تحريم أسلحة الدمار الشامل في تاريخ الشيعة»Shafin Ayatullah Ali doust, ranar wallafa: 9 Maris 1393 SH, ranar duba: 27 Fabrairu 2024 M.
- «ذهبنا إلى قم للتحقيق في فتوى النووي لآية الله الخامنئي/أرسلنا تقرير رحلتنا إلى البيت الأبيض/من المؤكد دراسة هذا التقرير من قبل الحكومة الأمريكية»،Shafin Mashriq, ranar wallafa: 18 ga Nuwamba, 1393, ranar kallo: 27 ga Fabrairu, 2024.
- «بيانات خلال لقاء مع العاملين في بناء المدمرة جماران »،Ofishin Kula da Bada Hujja na Ayatollah Khamenei, Ranar buga: 30 Fadama 1388SH, Ranar ganin: 27 Fabrairu 2024M.
- «بيانات قائد الثورة الإسلامية خلال لقاء مسؤولين في الحكومة»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي، تاريخ النشر: 11 آبان 1382ش، تاريخ المشاهدة: 27 فبراير 2024م.
- «رسالة إلى المؤتمر الدولي الأول لنزع السلاح النووي»،Makataf din adana da wallafa ayyukan Ayatollah Khamenei, ranar buga: 28 Fafaruddin 1389, ranar kallo: 27 Fabrairu 2024.
- «تسجيل رسالة قائد الثورة الإسلامية إلى مؤتمر طهران كوثيقة عند الأمم المتحدة »، Jaridar Kayhan, Ranar wallafa: 4 ga Mayun 1389, Ranar kallo: 27 ga Fabrairu 2024.
- «تحريم أسلحة الدمار الشامل في تاريخ الشيعة»، Hukumar Labarai ta ISNA, ranar wallafa: 27 ga Yuni, 1393 na kalandar Jamhuriyar Islamiyya, ranar dubawa: 27 ga Fabrairu, 2024.
- «صنع واستخدام أسلحة الدمار الشامل من منظور الفقه الإسلامي»،Makarantar Masarautar Imamai tsarkaka, Ranar duba: 27 Fabrairu 2024.
- «تسجيل رسالة قائد الثورة الإسلامية كوثيقة عند الأمم المتحدة»،Makataf din adana da wallafa ayyukan Ayatullah Khamenei, ranar buga: 28 Fafaruddin 1389, ranar kallo: 27 Fabrairu 2024.
- Taron marubuta, Fiqh na 'Fiqh al-Nawawi', bincike na Abu al-Qasim Alidust, Tehran, tunanin musulunci, bugu na farko, 1397.
- «الأدلة الفقهية على تحريم السلاح النووي»،Ofishin Kiyaye da Wallafa Ayyukan Ayatollah Khamenei, ranar buga: 4 ga Afrilu 1389, ranar dubawa: 26 ga Janairu 1402.
- «الزعماء الدينيون ينضمون إلى آية الله الخامنئي»، Ofishin Kula da Bada Hujjojin Ayatollah Khamenei, Ranar buga: 1 ga Afrilu 1389, Ranar duba: 26 ga Janairu 1402.
- «صالحی: تنها رهبر انقلاب میتوانند درباره ساخت سلاح هستهای نظر صائب بدهند»، Kamfanin dillancin labarai na Fars, ranar wallafa: 24 ga watan Oktoba 1401, ranar ziyara: 30 ga watan Janairu 1402.
- «عرض كتاب "فقه هستهاي" (فقه النووي) في معرض الكتاب الثاني والثلاثين)»،Shafin tunanin Musulunci, ranar wallafa: 8 ga watan Farvardin 1398, ranar ziyara: 1 ga watan Bahman 1402.
- «الفتوى التي وصلت إلى الأمم المتحدة بعد 10 سنوات»Hausa News Agency, Date of publication: 3rd of Mehr 1392, Date of viewing: 27th of Dey 1402.
- «انتشار كتاب الفتوى النووية لقائد الثورة من منظور القانون الدولي في أمريكا»، Hukumar Labarai ta Fars, ranar wallafa: 25 ga Fabrairu, 1395 na zamani, ranar da aka duba: 27 ga Jumaada al-Awwal, 1402 na zamani.
- «لوازم فتوى السيد الخامنئي حول حرمة السلاح النووي»،Shafin Tasnim, Ranar wallafa: 30 ga Fabrairu, 1392 na Hijira, Ranar da aka duba: 26 ga Juma'a, 1402 na Hijira.
- Mohammed Bour, Mohammed, "Fatwa as a Source of International Rights," in the magazine "Shahr Qanoon," Issue 13, Spring 1394 Sh.
- «فتوى نووية - بین السطور»، موقع BBC News الفارسي، تاریخ النشر: 9 بهمن 1400ش، تاريخ المشاهدة: 15 بهمن 1402ش.