Imamai Biyu Masu Jihadi (Littafi)
| Marubuci | Sayyid Ali Khamna'i |
|---|---|
| Tarihin rubutu | 2017M |
| Maudu'i | Tarihi na nazari |
| Harshe | Farsi |
| Da taimakon | Cibiyar binciken al’adu ta Juyin Juya Halin Musulunci. |
| Adadin Jildi | 1 |
| Mai bugawa | Cibiyar binciken al’adu ta Juyin Juya Halin Musulunci. |
| Wurin da aka buga shi | Tehran |
Imamai Guda Biyu Masu Jihadi suna ne na wani littafi na Sayyid Ali Khamna'i, wanda a cikinsa ya yi nazari kan rayuwar Imam Hassan Mujtaba (A.S) da Imam Husaini (A.S) ta hanyar salon tarihin nazari.
A cikin wannan rubutu, wanda aka tattaro daga jawaban Ayatullah Khamna'i da ya gabatar tsakanin shekarun 1972 zuwa 1973 M, an yi ƙoƙari a bayyana dalilin bambancin matakan da waɗannan Imamai biyu suka ɗauka wajen mu'amala da gwamnatin Banu Umayya a zamaninsu.
Matsayi Da Muhimmanci
Littafin Imamai Guda Biyu Masu Jihadi ya ƙunshi wasu jawabai na Sayyid Ali Khamna'i da suka mayar da hankali kan gabatarwa da bayanin matsayin Imam Hassan Mujtaba (A.S) da Imam Husaini (A.S). Ɗaya daga cikin muhimman manufofin littafin shi ne kawar da shubhar da ake yi cewa akwai saɓani tsakanin halayen wadannan Imamai biyu wajen mu'amalarsu da sarakuna guda na Banu Umayya. Saboda haka, a cikin littafin an yi ƙoƙari a bayyana cewa miƙewa da gwagwarmayar Imam Husaini (A.S) da kuma sulhun Imam Hassan (A.S) duk sun kasance daidai da yanayin zamani da halin da al’umma ke ciki a lokacin su.
A ƙarshe, an nuna cewa manufar Imaman biyu ɗaya ce, wato farfaɗo da addinin Musulunci da kuma yaƙar zalunci da mulkin Ɗawagitai.[1] Haka kuma, an taɓa amfani da wannan littafi a matsayin tushen karatu a wata gasar karanta littattafai da aka gudanar.[2]
Abubuwan Da Littafin Ya Ƙunsa
Littafin "Imamai Guda Biyu Masu Jihadi" ya ƙunshi zance guda shida. Zance na farko da na biyu sun samo asali ne daga jawabai biyu na Sayyid Ali Khamna'i da ya gabatar a watan Afrilu 1972M, a Husainiyar Irshad. A wannan ɓangare, an yi bayanin nazariyar mutum mai shekaru 250 (wato ra’ayin da ke kallon rayuwar Imaman Ahlul-Baiti a matsayin gwagwarmaya guda ɗaya mai ci gaba), sannan kuma an yi bayani kan bambancin yanayin zamanin Imam Hassan (A.S) da na Imam Husaini (A.S). Zance na uku zuwa na biyar kuwa sun samo asali ne daga jawaban Muharram na shekarar 1973M, inda aka mayar da hankali kan nazarin tashin gwagwarmayar Imam Husaini (A.S) da dalilan da suka haifar da ita. Zance na ƙarshe kuma ya samo asali ne daga wani jawabi da marubucin ya gabatar a Muharram 1973 a taron Haidar Ansar al-Husain a Tehran. A cikin wannan zance, an yi bayanin manufar Imam Husaini (A.S) cikin miƙewarsa da gwagwarmaya, sannan a wani ɓangare an duba ra’ayoyi daban-daban da aka gabatar game da dalilan wannan miƙewar da gwagwarmaya.[3]
Wallafawa
Littafin Imamai Guda Biyu Masu Jihadi an buga shi a karon farko a lokacin hunturun shekarar 2018M, ta hannun Cibiyar Kula da Adanawa da Wallafa Ayyukan Ayatullah Khamna’i (Cibiyar Bincike da Al’adun Juyin Juya Halin Musulunci), inda aka fara buga kwafi 3000.[4] Har zuwa Oktoba 2022M, littafin ya kai bugu na goma sha biyu.[5] Haka kuma, Gidan wallafa littattafan Juyin Juya Halin Musulunci ya fitar da wannan aiki a matsayin littafin murya (Audio book). Sigar sa ta murya tana da fayilolin sauti masu tsawon mintuna 178.[6]
Bayanin kula
- ↑ Khamna'i Do Imam Mujahid, sh 6
- ↑ Chap-e Davazdahom-e Kitab-e «Do Imam Mojahid» Montasher Shod, Isna
- ↑ Khamna'i, Do Imam Mujahid, sh 6-8
- ↑ Chap-e Davazdahom-e Kitab-e «Do Imam Mojahid» Montasher Shod, Khabar Online."
- ↑ Chap-e Davazdahom-e Kitab-e «Do Imam Mojahid» Montasher Shod, Khabar Online
- ↑ Kitab-e Guya-ye «Do Imam Mojahid», Wallafe‑wallafen Juyin Juya Halin Musulunci
Nassoshi
- Khamna'i , Sayyid Ali, Do Imama Mujahid, Tehran, Cibiyar Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah al‑Uzma Sayyid Ali Khamna'i , 2017M.
- کتاب گویای دو امام مجاهد, (Littafin sauti na "Imamai Biyu Mujahida), Gidan Bugawa na Juyin Juya Halin Musulunci, ranar wallafa: ba a ambata ba, ranar ziyarta: 29 Afrilu 2024M.
- «برگزاری پویش کتابخوانی «دو امام مجاهد , (Gudanar da kamfen na karanta littafin Imamai Biyu Mujahidai.»), ISNA (Kamfanin Labarai na Daliban Iran), ranar wallafa: 14 Satumba 2022M, ranar ziyarta: 29 Afrilu 2024M.
- «چاپ-دوازدهم-کتاب-دو-امام-مجاهد-منتشر-شد چاپ دوازدهم کتاب «دو امام مجاهد» منتشر شد, (An fitar da bugun na goma sha biyu na littafin Imamai Biyu Mujahida), Khabar Online, ranar wallafa: 26 Satumba 2022M, ranar ziyarta: 29 Afrilu 2024M.