Jump to content

Sayyid Mujtaba Khamna'i

Daga wikishia
Sayyid Mujtaba Khamna'i
Na uku cikin jerin Jagororin jamhuriyar Musulunci ta Iran
Cikakken SunaSayyid Mujtaba Husaini Khamna'i
NasabaDaga dangin shirafai Afɗasi da Sulɗan Sayyid Ahmad
Tarihin Haihuwa17 Shahriwar shekara 1348Sh/8 Satumba 1969M
Wurin HaihuwaMashad. Iran
Sunan MataZahra Haddad Adil
Sanannun DangiSayyid Jawad Husaini Khamna'i (Kakansa)

Sayyid Ali Husaini Khamna'i (Mahaifinsa)

Gulam Ali Haddad Adil (Mahaifin matarSa)
MazhabaShi'a
MalamaiSayyid Ali Khamna'i

Sayyid Mahmud Hashimi Shahrudi Muhammad Taƙiyyu Misbahu Yazdi Muhsin Kharrazi

Luɗfullahi Safi Gulfaigani
Sa Hannuبندانگشتی



Sayyid Mujtaba Husaiini Khamna'i (Haihuwa:1969M) shine jagora na uku na gwamnatin jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma ɗa ga Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i ne. Bayan shahadar mahaifinsa a hannun Amurka da kuma haramtacciyar gwamnatin Sahayoniya, Majalisar ƙwararru ta jagoranci a ranar 17 ga watan Isfand shekara ta 1404Sh/8 ga watan Maris 2026M, ta zaɓe shi a matsayin jagoran gwamnatin jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Tarihin Rayuwa

An haifi Sayyid Mujtaba a shekara ta 1348Sh (1969M,) a birnin Mashad. Ya yi makarantar sakandare a makarantar Alawi da ke Tehran, Ya yi karatu addini a wurin mahaifinsa da kuma Sayyid Mahmud Hashimi Shahrudi, kuma a shekara ta 1378Sh, ya tafi birnin Qom don ci gaba da karatu, ya halarci darussan malamai irin su Muhammad Taƙiyyu Misbahu Yazdi, Muhsin Kharrazi, Luɗfullahi Safi Gulfaigani, da kuma darussa na keɓance a gaban Ali Andlibi.

Daga shekara ta 2011M, har zuwa shekara ta 2024M,ya kasance yana koyar da Fiƙhu da Usul a matakin kammala karatu (Bahasul Kharij) a hauzar ilimi ta Qom. Wannan darasin da ake cewa ya ɗauki kusan shekaru 13 kuma kusan mutane 700 ne ke halarta, ya dakatar ci gaba da ba da darasi a watan Oktoba na shekara ta 2024M, bisa nuradin kansa.[1]

Sayyid Mujtaba Khamna'i ya auri Zahra Haddad Adil, ƴar Gulam Ali Haddad Adil, a shekara ta 1999M, Allah ya azurta su da samun haihuwar ƴaƴa maza biyu da mace guda ɗaya. Matarsa tare da mahaifinsa Ayatullahii Sayyid Ali Khamna'i sun yi shahada a ranar 9 28 Fabarairu 2026M, a harin haɗin gwiwa da Isra'ila da Amurka suka kai wa gidan jagoranci, shi kuma ya ji rauni.

A lokacin kallafaffen yaƙin Iraki kan Iran, a shekara ta 1987M, yana da shekaru 17, an tura shi gaba, kuma ya kasance memba na rundunar Habib Bin Muzahir na rundunar ta 27 Muhammad Rasulullah, inda ya halarci ofireshin irin su Baitul Maƙaddas 2, 3 da 4, da Fajar 10 da Mirsad.

A watan Nuwamba na shekara ta 2020M, Ma'aikatar Baitulmali ta Amurka ta sanya takunkumi a kansa tare da wasu mutane takwas masu alaƙa da gidan jagoranci.

Jagorancin Jamhuriyar Musulunci

Sayyid Mujtaba Khamna'i shi ne mutum na uku daga hannun hagu a cikin wannan hoto

A ranar 8 Maris shekara ta 2026M, majalisar ƙwararru ta jagoranci, bayan wucewar kwanaki takwas daga shahadar Sayyid Ali Khamna'i, ta zaɓi Sayyid Mujtaba Khamna'i a matsayin jagora na uku na jamhuriyar Musulunci ta Iran.[2] An bayyana dalilin wannan jinkiri da cewa barazanar tsaro ce ga taron majalisar da kuma kin amincewar da ya yi tun farko na karɓar wannan nauyi.

Dangane da haka, Amurka da haramtacciyar gwamnatin Sahayoniya sun kai hari tare da lalata gine-ginen Majalisar ƙwararru a Qom da Tehran. Kafin wannan zaɓen, manyan mutane irin su Ayatullahii Makarim Shirazi, Ayatullahii Nuri Hamadani daga maraji'an taƙlidi da kuma ƙungiyoyi daban-daban sun jaddada wajabcin gaggawar aiwatar da tsarin naɗa sabon jagora.

An yi mubaya'a ga Ayatullahi Sayyid Mujtaba Khamna'i sabon jagoran Iran (Tehran 9 ga watan Maris shekara ta 2026M). [3]

Martani

Halartar Sayyid Mujtaba Khamna'i a muzaharar ranar ƙudus tare da iyalansa (2014–2015M).

Zaɓen sabon shugaban Iran ya gamu da martani da tashe-tashen hankula masu yawa a ciki da wajen ƙasar. Jami'an siyasa na ƙasashe daban-daban, ƙungiyoyin gwagwarmayar Musulunci da manyan jami'an jamhuriyar Musulunci sun taya murnan wannan zaɓe.[4] A Iran, ban da ta murna na mutane, cibiyoyi da ƙungiyoyi daban-daban, an jaddada mubaya'a ga sabon shugaba da bin umurninsa, kuma an gudanar da bukukuwan mubaya'a na jama'a tare da halartar jama'a masu yawa a duk faɗin ƙasar.[5]

Ayatullahii Nuri Hamadani daga maraji'an taƙlidi ya kira zaɓen Sayyid Mujtaba Khamna'i da cancanta da hikima, kuma ya ce yana da dukkan sharuɗɗan da ake buƙata don jagoranci, gami da ijtihadi a fagen fiƙihu, jajircewa, taƙawa, sanin lokaci, gudanarwa da tsarawa. Ayatullahii Makarim Shirazi shi ma ya yi la'akari da zaɓen majalisar a matsayin mafi dacewa, kuma ya yi kira ga jama'a da ƙusoshin gwamnati da su yi mubaya'a ga sabon shugaba kuma su ci gaba da tafiyar juyin juya halin Musulunci tare da haɗin kai da juriya.[6]

Biladmiya Putin, shugaban ƙasar Rasha, ya bayyana fatansa cewa Sayyid Mujtaba Khamna'i zai ci gaba da tafiyar mahaifinsa cikin mutunci kuma ya haɗa kan al'ummar Iran wajen fuskantar matsaloli.

Akasin haka, Amurka da haramtacciyar gwamnatin Sahayoniya sun nuna damuwa game da wannan zaɓen kuma sun yi barazanar kashe sabon shugaban Iran. A baya ma waɗannan ƙasashe biyu sun yi gargaɗi game da zaɓen Sayyid Mujtaba Khamna'i a matsayin jagoran Iran.

Matsayai A Lokacin Jagoranci

A ranar 11 ga watan Maris 2026M, Sayyid Mujtaba Khamna'i ya fitar da saƙonsa na farko a hukumance a matsayin sabon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci. Wannan saƙo, wanda aka wallafa a yayin Yaƙin Ramadan, an tsara shi a cikin manyan sassa bakwai, kuma ya ƙunshi bayanai game da: Matsayin da rawar Ayatullahii Sayyid Ali Khamna'i, nauyin da ya rataya a wuyan al'umma, rundunonin soji, hukumomin zartarwa, Ƙawancen Ƴan Gwagwarmaya, ƙasashen yankin, da kuma hanyoyin fuskantar maƙiyan waje. Haka kuma, a cikin saƙon an jaddada buƙatar ƙasashen yankin Yammacin Asiya su bayyana matsayinsu game da abin da aka kira masu kai hari kan Iran, tare da kiran rufe sansanonin soji da na kuɗi na baƙin ƙasashe a yankin.

Hoton bangon "Salih ba'da Salih", a dandalin Waliasr na Tehran bayan zaɓen Sayyid Mujtaba Khamna'i a matsayin Jagora. Mai zane: Muhammad Turk.

Ya kuma bayyana iƙirarin Amurka na cewa tana kawo zaman lafiya da tsaro a yankin a matsayin Ƙarya bayyananniya'. Har ila yau, ya jaddada ci gaba da amfani da matakan matsin lamba, ciki har da ci gaba da rufe mashigar Hormuz har sai masu kai hari sun janye gaba ɗaya.[7]

Shi ma, a gaban bukukuwan Sallah ƙarama da sabuwar shekara ta Noruz, ya bayyana tausayinsa ga iyalan da suka rasa ƴan uwa a yaƙin kwanaki goma sha biyu, da kuma abubuwan da suka faru watan Dey shekarar 1404 shamsi (Janairu 2026M) da Yaƙin Ramadan.

Ya kira lamuran watan Dey da yaƙi da yunƙurin juyin mulki. Haka kuma ya bayyana taken shekara ta 1405Sh (2026–2027M) a matsayin: Tattalin arziƙin juriya cikin inuwa ta haɗin kan ƙasa da tsaron ƙasa.[8]

A cikin saƙon, an jaddada mu'amala mai kyau da ƙasashen makwabta, tare da roƙon Afganistan da Pakistan su ƙara kyautata dangantaka don kiyaye haɗin kan Musulmi.

Na'im Ƙasim, babban sakataren Hizbullahi Lubnan, ya bayyana cewa manufar daular Musulunci ta Iran tana bin tafarkin Imam Khomaini da Ayatullahi Khamna'i wajen ci gaba da goyon bayan gwagwarmayar ƙin zalunci da tsayin daka gaban Amurka da Sahayoniyawa.

Bayanin kula

  1. ↑ «چرا آیت‌الله مجتبی خامنه‌ای کلاس درس خارج را تعطیل کرد؟ (فیلم)»، Asre Iran.
  2. ↑ «چرا آیت‌الله مجتبی خامنه‌ای کلاس درس خارج را تعطیل کرد؟ (فیلم)»، Asre Iran.
  3. ↑ «Marasime Bai'at ba Sebomin Rahbare Inƙilab.» ISNA. «Payamhaye Tabrike Maraje', Shakhsiyyat-ha wa Maƙamate Hauzawi wa Keshwari dar Peye Intekhabe Rahbare Jadide Inƙilabe Islami,» Shafaqna.
  4. ↑ «Jadidtarin Wakonesh-haye Bainal-melali be Intekhabe Rahbare Jadide Inƙilabe Islami,» Kamfanin Labarai na Mehr.
  5. ↑ «Payamhaye Tabrike Maraje', Shakhsiyyat-ha wa Maƙamate Hauzawi wa Keshwari dar Peye Intekhabe Rahbare Jadide Inƙilabe Islami,» Shafaqna.
  6. ↑ «Payamhaye Tabrike Intekhabe Sebomin Rahbare Inƙilabe Islami,» Shafaqna.
  7. ↑ «Awwalin Payame Hazrat Ayatullahi Sayyid Mujtaba Husaini Khamna'i, Rahbare Mu'azzame Inƙilabe Islami,» Shafin Ofishin Hifze Wa Nashre Asare Hazrat Ayatullahi al-Uzma Khamna'i.
  8. ↑ Don ganin cikakken rubutun wannan saƙo, duba::https://farsi.Khamenei .ir/news-content?id=62807

Nassoshi