Jerin Ayyukan Sayyid Ali Husaini Khamna'i
- Wannan maƙala tana magana ne game da ayyukan ilimi, rubuce-rubuce, da kuma jawaban Sayyid Ali Husaini Khamna'i, babban jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran.

Jerin ayyukan Sayyid Ali Husaini Khamna'i wasu adadin jerin ayyuka ne da suka haɗa da rubuce-rubuce da jawaban Sayyid Ali Khamna'i , ɗaya daga cikin maraji'an taƙlidi na Shi'a (Manyan malaman fikihu na Shi'a) .kuma jagoran jamhuriyar Musulunci ta Iran. Tun daga shekarar 2010M (1389 Sh), cibiyar wallafa ayyukan juyin juya halin Musulunci take gudanar da aikin tsarawa da fassara tunaninsa zuwa harsuna daban-daban. Haka kuma, an samar da manhajar kwamfuta mai suna "Hadise Welayat" wadda ta ƙunshi dukkan jawaban sa da littattafai sama da 120.[1]
Cibiyar Binciken Kimiyyar Musulunci ta Kwamfuta ta wallafa tarin ayyukan sa a cikin manhajar kwamfuta mai suna "Hadise Welayat". Wannan manhaja ta ƙunshi jawabai da saƙonni daga shekarar 1979M. (1357Sh) zuwa 2020M (1399Sh), tare da rubutun littattafai 121 a cikin juzu'i 208 daga ayyukan da Gidan Buga Littattafan Juyin Juya Halin Musulunci ya wallafa.[2]
Talifi Da Tarjama
- Sulhun Imam Hasan shi ne mafi girman sassaucin jarumta a tarihin duniya
Wannan littafi na Sulhul Hassan littafi ne da Sayyid Ali Husaini Khamna'i ya fassara daga Larabci zuwa Farisanci a shekarar 1969M. Littafin na Shaikh Radi Alu Yasin ne, wanda ya kasance mai bincike kuma malamin Shi'a (Rasuwa:1372Sh), littafi ne da yake bayyana dalilan siyasa da na addini da suka sa Imam Hassan ya yi sulhu da Mu'awiya.[3]

- Littattafai Huɗu na Ilimin Rijal
Littafin "Cehar Kitabe Asli Ilme Rijal" Bayan ya yi kallon gaba ɗaya kan ilimin Rijal (ma'anarsa, tarihinsa, da kuma taƙaitaccen ci gabansa), sai ya fara gabatarwa da kuma tantance littattafan Rijal da ake nufi. Amma ya gabatar da littattafai biyu kawai daga cikin manyan littattafan Rijal guda huɗu, wato "Ikhtiyaru Ma'arifatil Rijal da Al-Fihrist Shaikh Ɗusi. Gabatarwar sauran littattafan biyu Rijal Al-Ɗusi da Al-Fihristu Najashi) ya bar su zuwa ci gaban littafin (ƙarshen sa).[4] An wallafa wannan littafi a shekarar 1377Sh (1998M) ta hannun Ofishin Wallafa Al'adun Musulunci.[5]
- Makalar Jihadi (Thalath Rasa'il fi al-Jihad)
Ya ƙunshi darussan fikihu da ya bayar kan batutuwan da suka shafi amana a lokacin yaƙi, matsayin mabiya Annabi Yahaya (Sabina), da yarjejeniyar tsagaita wuta. Salasu Rasa'il Fil Jihad (Wasiƙu Uku Game da Jihadi) Littafin "Salasu Rasa'il Fil Jihad " ya ƙunshi "darussan kharijul fikhi na Sayyid Ali Khamnai da ya gabatar tsakanin shekarun 1991M zuwa 1995M, kan batun jihadi.

Littafin ya ƙunshi maƙaloli uku da ya rubuta wani lokaci bayan gabatar da darussan, kuma batutuwansu su ne: "Aman" – ba da kariya ko aminci a lokacin yaƙi,"Al‑Sabi'a" – mabiyan Annabi Yahaya (A.S), "Al‑Muhadana" yarjejeniyar daina yaƙi ko tsagaita wuta. An wallafa wannan aiki a shekarar 1396Sh (2017M) ta gidan bugawa na Juyin Juya Halin Musulunci.[6]
- Bincike kan Rayuwar Imam Sajjad (AS)
Littafin "Bincike kan Rayuwar Imam Sajjad (A.S)" yana daga cikin ayyukan da Sayyid Ali Khamna'i ya rubuta domin gabatar da halayen Imam Sajjad (A.S) da kuma zamaninsa. An wallafa shi a shekarar 1361Sh (1982M) ta gidan bugawa na Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci.[7]
A shekarar 1399Sh (2020M) an sake buga wannan littafi da sabon suna "Hamase Imam Sajjad", inda aka ƙara wasu sassa, ciki har da:
Jawabansa ga matasa a shekarar 1352Sh (1973M) a Masallacin Karama Masshad. Tarin hirarraki da mujallar Pasidare Islam ta yi da shi a shekarar 1361Sh (1982M), tare da wasu ƙarin bayanai da kuma nassoshi.[8]
- Ayande Dar Islam (Makoma A Yankin Mulkin Musulunci)
Littafin "Makoma a Yankin Mulkin Musulunci" fassara ce ta littafin Al‑Mustaƙbal Li Hazad-Din wanda Sayyid Ƙuɗub (1867–1925 M), wani mashahurin masanin tunanin Musulunci daga Masar, ya rubuta. Littafin yana magana ne game da raunin da koma bayan wayewar Yamma, da kuma yadda Musulunci zai mamaye ko ya jagoranci duniya a nan gaba.
An buga wannan aiki a shekarar 1386Sh (2007M) ta Ofishin Wallafa Littattafan Juyin Juya Halin Musulunci.[9]

- Musulmai A Gwagwarmayar Ƴancin Indiya
Littafin "Musulmai a Gwagwarmayar Ƴancin Indiya" an rubuta kuma aka fassara shi a farkon shekarar 1347Sh (1968M), sannan aka wallafa shi a watan Tir (Yuli) na wannan shekarar.
Asalin wannan littafi shi ne Kifaḥu al‑Muslimin fi Taḥrir al‑Hindi, wanda Abdul‑Mun'im al‑Nimri, ɗaya daga cikin malaman jami'ar Al‑Azhar (Masar), ya rubuta.
Sayyid Ali Khamna'i ya yi fassara tare da ƙarin bincike da bayanin tarihi domin ƙara inganci da fahimta ga rubutun, saboda haka a murfin littafin, sunansa ya bayyana a matsayin marubuci da kuma mai fassara. Wannan littafi ne da ya haɗa fassara da bincike akai game da rawar da Musulmi suka taka wajen ƴantar da Indiya daga hannun Turawan Mulkin Mallaka. Fikihu da Hukunce-hukunce. [10]

- Littafin "Rahoto Kan Tarihin Da Halin Da Hauzar Ilimi Ta Masshad Ke Ciki A Yanzu
yana daga cikin rubuce‑rubucen Sayyid Ali Khamna'i kafin juyin juya hali, wanda aka rubuta a shekarar 1346Sh (1967M). Batutuwa cikin littafin an tsara su a sassa huɗu: Matsayin tarihi da na ƙasa da kuma tarihin Hauzar Ilimi ta Masshad, Tsarin gudanarwa da yanayin karatu, Malaman makarantar da dalibai, Ayyuka da harkokin hauzar. Bayan juyin juya hali, an sake wallafa littafin a watan Tir 1365Sh (Yuli 1986M) ta hannun babban Taron Duniya na Imam Rida (A.S) tare da cibiyar bugawa da wallafa ta Astan Ƙudus Radawi (Ma'aikata kula da harami Imam Rida).[11]
- Manasik al‑Hajj
Ma'ana Ayyukan Hajji ya ƙunshi fatawowin Sayyid Ali Khamna'i game da hukunce-hukunce da ayyukan Hajji. An tsara littafin cikin sassa uku: Sashe na farko: yana bayani kan Umara Mufrada, da kuma hukunce‑hukuncen Istiɗa'a (ikon yin Hajji) da wakilci a Hajji (niyaba). Sashe na biyu: yana bayani kan manasik na Umara Tamattu'i. Sashe na uku: yana bayani kan manasik na Hajjin Tamattu'i[12]
- Ajwiba Istifta'at (Farsi)

Littafin Ajwibat al‑Istifta'at (Amsoshin Tambayoyin Shari'a) ya ƙunshi tambayoyi da amsoshi 2118 kan batutuwa daban‑daban na fikihu (shari'ar Musulunci), waɗanda aka tattara bisa fatawowin Sayyid Ali Khamna'i. Bugu na 13 na wannan littafi, tare da sabunta wasu fatawowi, an wallafa shi a shekarar 1400 Sh (2021M) ta gidan bugawa na Juyin Juya Halin Musulunci.[13]
Matanin Darasussuka Da Jawabai
Sayyid Ali Khamna'i, a tsawon ayyukansa na al'adu, zamantakewa, da siyasa, kafin da kuma bayan Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, ya gabatar da darussa da jawabai da dama ga ɓangarori daban‑daban na al'umma. An tattara waɗannan bayanai (jawabai) cikin littattafai masu yawa kuma aka buga su, waɗanda aka tsara su a wasu manyan fannoni, kamar yadda za a bayyana a ƙasa:
Ibada Da Ɗabi'a
- Khalwat‑e Uns

Littafin Khalwat‑e Uns (خلوت اُنس) an shirya shi ne domin sanin tunani da ra'ayoyin Sayyid Ali Khamna'i game da salla. Littafin ya ƙunshi fuskoki takwas, inda yake tattauna batutuwa kamar: muhimmancin sallah, ladubban sallah, tasirin sallah, da kuma matsayin sallar Juma'a da sallar jam'i.[14]
- Az Zharfa‑ye Namaz (Daga Zurfafan Ma'anonin Salla)

Wannan littafi ya tattaro wasu jawabai ne da Sayyid Ali Khamna'i ya gabatar a shekarar 1351Sh (1972M) a Masallacin Karama Masshad. A cikin waɗannan jawabai an yi tarjama da tafsirin Suratul Fatiha, tare da tattauna batutuwa kamar: Tauhidi, Tasbihatul Arba'a, rukunai da wajiban sallah.[15] Bugun na 12 na littafin ya fito a shekarar 1372Sh (1993M) ta Daftar Nashr‑e Farhang‑e Islami (Ofishin Buga Al'adun Musulunci)..[16]
- Darasin Aklaƙ (Gyaran Ɗabi'a)
Wannan aiki wasu jerin jawabai ne da darasussuka daga Sayyid Ali Khamna'i da ya yi wa Dakaraun kare da juyin juya halin Musulunci (IRGC), watan Khordad shekarar 1371Sh, Yuni An wallafa littafin a khordad 1371Sh (Yuni 1992M) ta Ofishin Wakilin Jagoran Addini a cikin Dakaraun kula da juyi..[17]

- Littafin Bedan Ayyadakallahu (Ka Sani Allah Ya Ƙarfafeka)
Littafi ne da ya ƙunshi nasihohin Sayyid Ali Khamna'i ga ɗaliban hauza (Ɗalibai na ilimin addini).Littafin ya kasu zuwa babuka uku: Kulliyat (Gaba ɗayan batun), Matsayi da ayyukan ɗaliban hauza manya-manyan ayyuka da ke kan malamai.[18]
- Guftari Dar Babe Sabr (Jawabi game da Haƙuri)
Wannan littafi ya ƙunshi zaman jawabai guda biyar daga cikin jawabai da Sayyid Ali Khamna'i ya gabatar a Masallacin Karama Masshad a shekarar 1352Sh (1973M).
A cikin waɗannan jawabai, yayin bayani kan hadisin Makarimul Akhlaƙ da siffofin annabawa, marubucin ya yi bayani kan ma'anar haƙuri (Sabru) da rabe-rabensa.[19] An rubuta (a rubuce) kuma an sake tsarawa daga waɗannan darussan a shekarar 1354Sh (1975M), sannan Nashre Ghadir ta buga shi. Bayan nasarar Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, ofishin yaɗaal'adun Musulunci ya sake wallafa littafin a lokuta daban-daban.[20][20]
- Ma'ishat‑e Mu'minaneh (Rayuwar Arzikin Mumini) ko ace Tsarin Rayuwar Mumini
Wannan littafi ya ƙunshi jawaban Sayyid Ali Khamna'i game da ma'anoni huɗu: zuhudu, walwala/yalwar rayuwa, son jin daɗi da ƙawata rayuwa, da rayuwar masu alfarma ko masu mulki. Abul Ƙasim Karimi ne ya tattara waɗannan bayanai cikin littafi.[21]
- Ma'ishate Parhizkaran (Rayuwar Masu Taƙawa).

Wannan littafi mai shafuka 150 ya kasu zuwa fuskoki biyar, inda yake tattauna batutuwa kamar:Fahimtar ma'anar taƙawa (Tsoran Allah) Muhimmanci da darajar taƙawa. Tasiri da illolin rashin taƙawa, rabe-raben taƙawa, Muhimmancin taƙawaga manyan mutane ko masu jagoranci..[22]
Ayyukan Fiƙihu, Ilimin Kalam Da Tafsiri
- Tafsirin Alƙur'ani

Wannan aiki ya ƙunshi rubutaccen tsari da aka gyara daga zaman tafsirin Kur'ani da Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i ya gabatar a lokacin yana shugaban ƙasa da kuma lokacin jagorancinsa. An wallafa wannan tafsiri a cikin mujalladi da dama, inda kowanne mujalladi yake ɗauke da tafsirin wata sura ta Kur'ani, kuma ana buga shi da sunan wannan surar. Har zuwa yanzu, tafsirin surori kamar Baƙara, Jumu'a, Hashri, Al‑Hamd (Al‑Fatiha), Mujadila, Tagabun, Mumtahana, da Bara'a (At‑Tawbah) daga Sayyid Ali Khamna'i an wallafa su ta hannun Intisharate Inqilabe Islami (Gidan Bugawa na Juyin Juya Halin Musulunci).[23]
- Risalahye Amuzeshi (Risalar Koyarwa)
Wannan mujalladi biyu ya ƙunshi mas'aloli na shari'a da mutane ke yawan fuskanta a babukan ibada da mu'amaloli, kuma an tsara shi bisa fatawowin Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i. Intisharate Inƙilabe Islami (Gidan Bugawa na Juyin Juya Halin Musulunci) ne ya wallafa littafin.[24]

- Gina (Waƙa)
Darsenamahaye Gina littafi ne da aka tsara daga darussa 75 na "Darasul Kharijil Fiƙhi" da Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i ya koyar. An gabatar da waɗannan darussa daga 4 Azer 1387Sh (24 Nuwamba 2008M) zuwa 6 Bahman 1388 Sh (26 Janairu 2010M).[25]
Littafin yana nazarin hukuncin gina (Waƙa ko sautukan nishaɗi) a shari'ar Musulunci, yana tattauna: ma'anar gina a fiƙihu bambanci tsakanin gina da sauran sautuka hujjojin Alƙur'ani da hadisi ra'ayoyin malamai kan hukuncinsa Bugawa: An wallafa littafin a shekarar 1398Sh (2019M) ta hannun Cibiyar bincike da al'adu na juyin juya halin Musulunci. Girman littafin: Shafuka: 560.[26]
- Haka kuma ku duba Littafi Gina (Littafi)
- Darasussuka Daga Nahjul Balaga
Wannan littafi yana ƙunshe da jerin darussa daga Nahjul‑Balagha da Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i ya gabatar. A cikin waɗannan darussan, an tattauna batutuwa daban‑daban, musamman: Annabci yadda saƙon annabci yake ci gaba bayan Annabi, kamar yadda Nahjul‑Balaga ya bayyana. An buga bugu na biyu na littafin a shekarar 1361Sh (1982M).[27]
- Tsarin Gaba ɗaya na Tunanin Musulunci a cikin Al‑ƙur'ani
Wannan littafi rubutaccen tsari ne na jerin jawabai da Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i ya gabatar game da bayyana aƙidojin Musulunci bisa tushen Al‑ƙur'ani. An gabatar da waɗannan jawabai a watan Ramadan na shekarar 1353Sh (1974M), wato shekaru huɗu kafin Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, a Masallacin Imam Hassan Mujtaba (A.S) a birnin Masshad[28]

Ku duba:Tsarin Gaba ɗaya Na Tunanin Musulunci A Cikin Alƙur'ani
- Annabta A Cikin Nahjul‑Balaga
A lokacin bazarar shekarar 1359Sh (1980M), reshen ɗalibai na Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci ya shirya wa Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i jerin darussan Nahjul‑Balagha kan batun Nubuwwa a cikin Nahjul‑Balagha, wanda ya gudana na tsawon watanni uku.
Dalilin zaɓar wannan batu shi ne cewa Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ana kallonsa a matsayin ci gaba na manufofin annabawa da kuma aiwatar da burinsu. Saboda haka, batun nubuwwa da sakon annabawa ya zama ginshiƙin tattaunawar waɗannan darussa.[29]
Tsarin Rayuwar Ahlul-Baiti
- Pishwaye Sadiƙ
Wannan littafi ya samo asali ne daga jerin jawabai da Sayyid Ali Khamna'i ya gabatar tsakanin shekarun 1345Sh zuwa 1350Sh (1966–1971M) game da tsarin rayuwar Imam Jafar Sadiƙ (A.S).[30] Da farko, waɗannan jawabai an buga su ne a matsayin jerin rubuce‑rubuce daga bayanan marubucin, a watan Khordad 1358Sh (Yuni 1979M), inda aka wallafa su a cikin jaridar Jamhuriyar Musulunci a sassa 17. Daga baya kuma, tsakanin shekarun 1358 zuwa 1360Sh (1979–1981M), an tattara su kuma aka buga su a matsayin littafi mai taken "Pishwaye Sadiƙ" (Jagora Mai Gaskiya)..[31]
- Haka kuma ku duba: Jagora Mai Gaskiya
- Aftab Dar Mosaf (Rana A Fagen Gwabzawa)

Wannan littafi rubutaccen tsari ne na jerin jawabai da Sayyid Ali Khamna'i ya gabatar game da Imam Husaini (A.S) da kuma nazarin abubuwan da suka faru kafin da bayan Waki'ar Ashura a shekarar 61H. An gabatar da waɗannan jawabai tsakanin shekarar 1357Sh zuwa 1390Sh (1978–2011M).[32] Cibiyar tattarawa: Cibiyar Al'adu ta Hadis Lawhi wa Ƙalam. Mai bugawa: Intisharate Inƙelabe Islami. Gidan bugawa na Juyin Juya Halin Musulunci. Shekarar bugawa: 1392Sh (2013M).[33]
- Kuma ku duba: Aftbab Dar Mosaf (Littafi)
- Yawo A Cikin Rayuwar Imam Jafar Sadiƙ (A.S.)
Wannan littafi rubutaccen tsari ne na huɗubar sallar Juma'a da Sayyid Ali Khamna'i ya gabatar a ranar tunawa da shahadar Imam Sadiƙ (A.S), wato 14 Shahriwar 1359Sh (5 Satumba 1980M).[34] A cikin wannan huɗuba, an yi nazari kan rayuwa da rawar da Imam Sadiƙ (A.S.) ya taka a tarihin Musulunci, musamman: yanayin siyasa da zamantakewa na zamaninsa, rawar da ya taka wajen yaɗa ilimin Ahlul‑Baiti tasirin makarantar fiƙihu da iliminsa ga al'ummar Musulmi. Bugawa: An buga wannan aiki a shekarar 1360Sh (1981M) ta hannun Gidan bugawa na ofishin tsakiya na Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci.[35]
- Mutum Mai Shekaru 250

Wannan littafi yana magana ne game da tsawon lokacin imamancin Imaman Shi'a na shekaru kusan 250, daga wafatin Annabi Muhammad (S.A.W) a shekarar 11H har zuwa farkon Gaiba Sugra (Ƙaramar ɓoyuwa) ta Imam Mahadi (A.S) a shekarar 260H. A cikin wannan littafi, Sayyid Ali Khamna'i ya gabatar da wannan tarihin kamar mutum guda mai rayuwar shekaru 250, wato yana kallon dukkan Imamai a matsayin wani tsari guda na gwagwarmaya da jagoranci, inda kowanne Imam yake ci gaba da aikin wanda ya gabace shi.[36]
Littafin ya samo asali ne daga jawabansa da ya gabatar a shekarun kafin Juyin Juya Halin Musulunci na Iran.[37] An tsara shi cikin rukuni uku, domin masu karatu daban‑daban: Na matasa ƙanana (matakin matasa) Na matasa manya samari da ƴan jami'a.
- Haka kuma ku duba: Mutum Mai Shekaru 250 (Littafi)
- Abokan Gwagwarmayar Husaini (A.S)
Abokan Gwagwarmayar Husaini (A.S), wannan littafi tarin jawabai ne na Sayyid Ali Khamna'i da ya gabatar a shekarar 1351Sh (1972M) a Hay'at Ansar al‑Husain a Tehran. A cikin waɗannan jawabai, an yi nazari kan manufa (risala) da gwagwarmayar siyasa ta Imamai (A.S), tare da bayyana yadda suka jagoranci al'umma a lokutan zalunci da ƙalubale.

An buga littafin a lokacin kaka na shekarar 1396 Sh (2017M) ta hannun mawallafar Inƙilabe Islami, Gidan bugawa na Juyin Juya Halin Musulunci.[38]
- Ƙabsatun Nur (Tsono Daga Haske)
Littafi ne da ya ƙunshi zaɓaɓɓun maganganun Sayyid Ali Khamna'i game da Ahlul‑Baiti (A.S) da kuma bayyanar Mai Ceto (Imam Mahdi A.S.). A cikin littafin an tattara jawabai da bayanai na addini da ke bayyana:,matsayin Ahlul‑Baiti a Musulunci, rawar da suke takawa wajen shiryar da al'umma imanin Musulmi game da bayyanar Imam Mahadi, Mai ceto na ƙarshe.
An wallafa wannan littafi a shekarar 1369 Sh (1990M) ta hannun Taron Duniya na Ahlul‑Baiti (A.S).[39]
- Imamai Biyu Masu Jihadi
Imamai Biyu Masu Jihadi. Wannan littafi ya ƙunshi jawabai shida na Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i waɗanda ya gabatar a shekarun 1351Sh da 1352 Sh (1972–1973M).

A cikin waɗannan jawabai, ya yi nazari kan gwagwarmayar siyasa ta Hasanaini ma'ana Imam Hasan (A.S.) da Imam Husaini (A.S.), wato Hassanain (A.S.), yana bayyana yadda kowannensu ya gudanar da gwagwarmaya bisa yanayin zamansa. Littafin yana ƙoƙarin nuna cewa: gwagwarmayar Imam Hassan (A.S.) ta hanyar sulhu da gwagwarmayar Imam Husaini (A.S.) ta hanyar tashi da yaƙi a Karbala dukansu manufa ɗaya suke da ita, wato kare Musulunci da yaƙi da zaluncin mulki.[40]
- Haka kuma ku duba: Imamai Biyu Masu Jihadi (Littafi)
- Ɓangaren Gwagwarmaya A Rayuwar Imamai (A.S)
Wannan littafi yana bayyana ɓangaren gwagwarmaya da juriya a rayuwar Imaman Shi'a, tare da nuna irin ƙalubale da matsalolin da suka fuskanta a lokutan mulkin zalunci.
Asalin littafin jawabi ne na Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i da ya gabatar a shekarar 1365Sh (1986M) a Taro na Biyu na Duniya na Imam Ali al‑Rida (A.S.) da aka gudanar a Masshad.[41]
- Komawa Ga Nahjul Balaga
Wannan littafi ya ƙunshi rubutaccen jawabi na Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i da ya gabatar a watan Farwardin 1363Sh (1984M) a taron Nahjul Balaga.[42] Ko da yake an shirya wannan rubutu ne domin jawabi a taro, amma ana ɗaukarsa aiki mai zurfin bincike da daraja, domin marubucin ya yi bayani a ciki kan: tsarin mulki daga mahangar Imam Ali (A.S) halayen shugabanci da salon mulkinsa[43] yadda Imam Ali (A.S.) ya gudanar da gwamnati bisa adalci da ka'idojin Musulunci. An buga wannan littafi a shekarar 1372Sh (1993M) ta hannun Gidauniyar Nahjul Balaga.[44]

- Jawabai Game da Gwamnatin Alawi
Wannan littafi tarin jawabai uku ne na Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i da ya gabatar a huɗubobin sallar Juma'a a Tehran a watan Ramadan na shekarar 1358Sh (1979M).[45] Jawaban sun mayar da hankali ne kan ma'anar Gwamnatin Alawi, wato tsarin mulki da ya dogara da misalin mulkin Imam Ali (A.S), tare da bayyana muhimman sifofinta kamar: adalci a shugabanci, kare hakkokin talakawa, tsayayya da zalunci da cin hanci tsoron Allah da gaskiya a mulki An buga littafin a shekarar 1360Sh (1981M) ta hannun Gidan Bugawa na Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunc[46]
Zamantakewa

- Khune Deli Ke Lu'lu Shod
Wannan littafi an tattara ta hannun Muhammad Ali Azarshab, kuma shi ne fassarar Farsi ta littafin Larabci "إنّ مع الصبر نصراً" (Lallai tare da haƙuri akwai nasara). Littafin yana ɗauke da tunawa da tarihin rayuwar Sayyid Ali Khamna'i game da: lokutan da aka tsare shi a gidan yari lokutan da aka tura shi gudun hijira abubuwan da ya fuskanta a lokacin gwagwarmayar Juyin Juya Halin Musulunci na Iran kafin nasarar juyin juya hali. A cikin wannan aiki, an bayyana wahala, tsanani, da ƙalubalen da ya sha, tare da nuna yadda haƙuri da tsayuwa kan manufa suka zama hanyar samun nasara.
An buga littafin a shekarar 1399Sh (2020M) ta Gidan bugawa na Juyin Juya Halin Musulunci.[47]
- Porsesh Wa Pasokh
Wannan littafi ya ƙunshi amsoshin Sayyid Ali Khamna'i ga tambayoyi daban‑daban na matasa da ɗaliban jami'a. An tattara waɗannan tambayoyi ne daga lokuta da hanyoyi mabambanta da aka gabatar masa. An tattara amsoshin sannan aka tsara su cikin babi takwas, bisa batutuwa daban‑daban domin sauƙaƙa fahimta da karatu. An buga littafin karo na farko a shekarar 1380Sh (2001M) ta hannun Cibiyar Al'adu ta Ƙadre Welayat.[48]
- Jihade Tabyin

Wannan littafi yana magana ne game da muhimmanci da abubuwan da suka wajaba a fannin Jihade Tabyin (jihadin bayyana gaskiya), kuma ya ta'allaka ne kan jawabai da bayanan Sayyid Ali Khamna'i. Hujjatul‑Islam Sa'id Solhe Mirza'i ne ya tattara waɗannan bayanai daga jawabansa, sannan Gidan buga littattafan Juyin Juya Halin Musulunci, ta wallafa littafin.[49]
- Marge Tajirane

Wannan littafi ya ƙunshi jawabai da bayanan Sayyid Ali Khamna'i game da shahidai da kuma shahada. Haka kuma yana ɗauke da shawarwari da jagorori da ya bayar ga jami'ai, iyalan shahidai, da kuma sassa daban‑daban na al'umma dangane da wannan batu.[50]
- Hadise Wilayat
Littafin Hadise Wilayat (A juzu'i da dama) tarin jawabai da rubuce‑rubucen Sayyid Ali Khamna'i ne. An tsara abubuwan littafin cikin sassa huɗu: Kafin Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (1979M / 1357Sh). Bayan juyin juya hali har zuwa lokacin da ya zama shugaban ƙasa. Lokacin shugabancinsa na ƙasa (1360–1368Sh / 1981–1989M). Lokacin jagorancinsa (rahbari).[51] An wallafa littafin a shekarar 1398 Sh (2019M) ta hannun Gidan bugawa na juyin juya halin Musulunci.[52] Haka kuma an samar da sigar dijital ta wannan tarin a shekarar 1399Sh (2020M) ta Cibiyar Binciken Kimiyyar Kwamfuta Ta Ilimin Musulunci a birnin Qum, inda aka fitar da ita domin amfani na lantarki..[53]
- Atre Shahdat
Wannan littafi ne da ya ƙunshi saƙonni da gajerun jawabai na Sayyid Ali Khamna'i game da batun shahidai da shahada. Yawancin waɗannan maganganu an yi su ne a lokacin ganawarsa da wasu daga cikin iyalan shahidai. An tattara wannan kundin gwargwadon jerin lokaci daga shekarar 1361Sh zuwa shekarar 1379Sh. An buga littafin a shekarar 1380Sh ta hanyar mawallafar Nashr‑e Shahid.[54]
- Littafin Hauze Wa Ruhaniyat

Wannan littafi ya samo asali ne daga jawabai da bayanan Sayyid Ali Khamna'i. Daga cikin muhimman batutuwan da littafin ya tattauna akwai: Muhimmancin hauza (makarantun ilimin addini) da kuma rawar malaman da aka tarbiyyantar a cikinta a cikin al'ummar Musulunci. Bukatar ci gaba da bunƙasar hauza. Tsarin hauza da kuma sauye‑sauyen da ake buƙata a cikinta. Sa'id Solhi‑Mirza'i ne ya tattara littafin, sannan Cibiyar Buga Takardun Juyin Juya Halin Musulunci.[55]
- Fasaha Daga Mahangar Jagora Mai Girma
Wannan littafi saƙonni da ra'ayoyin Sayyid Ali Khamna'i ne. A farkon littafin an tattauna muhimmanci da kuma tsarin fasaha (Art), sannan a sassan da suka biyo baya kowanne yana magana ne kan batutuwa daban‑daban na fasaha, kamar waƙa, wasan kwaikwayo (theatre), kiɗa, madahi/waƙoƙin yabon Ahlul‑Baiti (A.S), da sauransu. Bugun na shida na wannan littafi an wallafa shi a shekarar 1377Sh (1998M) ta hannun Ofishin Buga Al'adun Musulunci.[56]

- Rahe Roshan Mudiran'
Littafin Rahe Roshane Modiran tarin jawaban Sayyid Ali Khamna'i ne inda yake bayani da sharhi kan wasu sassa na Nahjul Balagha. Waɗannan jawabai ya gabatar da su ne a ganawarsa da majalisar ministoci (Hai'ate Daulat) a watan Ramadan, a cikin shekarun 1372Sh zuwa 1395Sh (1993–2016M).[57]
- Marde Amal, Jihad Wa Shahadat: Doktor Mostafa Chamran
Wannan littafi ya ƙunshi rubutun jawabin Sayyid Ali Khamna'i da ya gabatar a ranar cikar kwanaki arba'in bayan shahadar Dr. Musɗafa Chamran. An buga littafin a shekarar 1360Sh (1981) ta mawallafin Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci.[58]
Siyasa

Littafin Falasɗin ya ƙunshi jawabai da hudubobin sallar Juma'a na Sayyid Ali Khamna'i game da batun Falasɗinu. Jawaban sun fito ne daga shekaru 1359Sh zuwa 1390Sh (1980–2011M).
Sa'id Solhi Mirza'i ne ya tattara su, kuma Ofishin Kiyaye da Wallafa Ayyukan Ayatullah Khamna'i ne ya buga littafin a shekarar 1390Sh (2011M).[59]
- Ƙungiyoyin Adawa A Cikin Gwagwarmayar Annabawa Da Kuma A Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran.
Wannan aiki ƙaramin littafi (Juzwe / risala) ne da ya ƙunshi rubutun jawabin Sayyid Ali Khamna'i da ya gabatar a Jami'ar Tehran a ranar 3 De 1358Sh (24 Disamba 1979M). An gabatar da jawabin da taken "Ƙungiyoyin adawa a gwagwarmayar annabawa da kuma a Juyin Juya Halin Musulunci na Iran", sannan mawallafin Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci ne ya buga shi.[60]

- Guftare Dar Wahdat Wa Tahazzub
Wannan littafi ya ƙunshi rubutun jawabai biyu na Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i: Na farko: an gabatar da shi a ranar 15 Khordad 1358Sh (1979M) a taron ƙungiyoyin Musulunci na birnin Ahwaz. Na biyu: an gabatar da shi daga baya a ofishin Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci. Littafin yana tattauna batun haɗin kai a cikin al'umma da kuma rawar da jam'iyyun siyasa ko ƙungiyoyi ke takawa.[61]
- Dorust Famidane Islam
Wannan aiki ya ƙunshi jawabin Sayyid Ali Khamna'i da ya gabatar a watan Khordad 1358Sh (1979M) ga matasa na Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci a Cibiyar Al'adu ta Musulunci a birnin Ahwaz. Rubutun ya ƙunshi bayanan tarihi da nazari kan farkon lokacin Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, ciki har da: yanayin gwamnatin wucin gadi ta injiniya Mahadi Bazargan, matsayin ƙungiyar Munafiqun (MEK), ƙungiyar Furqan, da kuma shakku da ra'ayoyin Marxism. An buga littafin a shekarar 1360Sh (1981M) ta hannun mawallafar Jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci.[62]

- Doshman Shinasi
Wannan littafi ya ƙunshi bayanai da jawaban Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i game da yadda ake gane maƙiyi da kuma hanyoyin fuskantar sa. An tsara littafin cikin babi goma sha huɗu, inda yake bayani kan ma'anar maƙiyi, dabarunsa, da hanyoyin kare al'umma daga makircinsa daga mahangar Khamna'i..[63]
- Daurane Jadid A'lam
Wannan littafi ya ƙunshi babban sassa biyu: "Juyin Juya Halin Musulunci da Yammacin zamani" "Sanin Yamma da nazarin zamanintarsa ta fuskar bincike mai suka." An tsara littafin ne bisa jawabai da ra'ayoyin Sayyid Ali Khamna'i, inda yake bayyana yadda Juyin Juya Halin Musulunci yake kallon duniyar Yamma ta zamani da kuma nazarin al'adunta da tsarin zamantakewarta.[64]
- Andishe Muƙawamat

Littafin "unani Na Gwagwarmaya" ya ƙunshi jawabai da bayanan Sayyid Ali Khamna'i game da tsayuwa da juriya a gaban barazana. Littafin yana tattauna batutuwa kamar: Ƙa'idoji da ginshiƙan Gwagwarmaya, Imanai da tushen tunanin Gwagwarmaya, muhimmancin Gwagwarmaya, da kuma fannonin da ake aiwatar da Gwagwarmaya[65]
- Mashurate Hukumate Alawi
Wannan littafi ya ƙunshi jawabai goma sha biyu (12) da suke sharhi kan wasu sassa na Nahjul Balagha. An gabatar da waɗannan jawaban ne a shekarun 1352 da 1353Sh (1973–1974M) a Masallacin Imam Hasan Mujtaba (A.S) da kuma Masallacin Karama.[66]
Sauran Ayyuka
An fitar da wannan jawabai 22 Bahman 1397Sh (11 Fabrairu 2019M), wanda ya zo daidai da cika shekaru 40 na nasarar Juyin Juya‑Halin Musulunci na Iran.[67] Wannan jawabai sun ƙunshi sassa uku masu muhimmanci: Farkon sashi: yana magana ne kan nasarar juyin juya‑halin Musulunci a shekarar 1357SH (1979M) da kuma wahalar da aka sha wajen kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Sashi na gaba: Yana bayyana manyan nasarori da abubuwan da juyin juya‑halin ya cimma a fannoni daban‑daban. Sashi na ƙarshe: Yana bayani kan hasashen gaba da shawarwari game da makomar juyin juya‑halin Musulunci, musamman ga matasa da al'ummar Iran.[68]
Wannan suna ne da aka fi sanin wasiƙu biyu da Sayyid Ali Khamna'i ya rubuta zuwa ga matasa na Turai da Arewacin Amurka.An fitar da wasiƙar ta farko a Bahman 1393SH (Janairu 2015M). An fitar da ta biyu a Azar 1394SH (Nuwamba 2015M). An rubuta waɗannan wasiƙu ne bayan ƙaruwa sabuwar guguwar tsoron Musulunci (Islamophobia) a ƙasashen Yamma, wadda ta biyo bayan ayyukan ta'addanci na ƙungiyoyin takfiri kamar Da'ish (ISIS).[69] An gabatar da tambayoyi da bayanai da ke nazari da sukar yadda wasu ƴan siyasar Yamma ke yada tsoron Musulunci, kuma an roƙi matasan Turai da Arewacin Amurka su koyi Musulunci daga ainihin tushensa, kamar Alƙur'ani da tarihin Annabi Muhammad (S.A.W), tare da kauce wa yanke hukunci tun kafin bincike (Prejudice) game da addinin Musulunci.[70]
- Hanyar Imam Ita Ce Hanyarmu
Wannan littafi ya ƙunshi rubutaccen saƙon Sayyid Ali Khamna'i da ya gabatar a bikin tunawa da rasuwar Imam Ruhullah Khomaini a shekarar 1369Sh (1990M). An wallafa littafin ne ta Cibiyar Tsara da Buga Ayyukan Imam Khomaini.[71]
- Hirarraki
Wannan littafi tarin hirarraki da aka yi da Sayyid Ali Khamna'i ne a lokacin da yake Shugaban ƙasa na Iran, musamman daga shekarun 1363 zuwa 1364Sh (1984–1985M). Cibiyar Takardun Al'adu ta Juyin Juya‑Halinsu na Musulunci ce ta tattara wannan aiki Bugu na farko na littafin ya fito a shekarar 1366SH (1987M) ta Nashr‑e Sorush.[72]
Bayanin kula
- ↑ «درباره انتشارات انقلاب اسلامی»،Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ حدیث ولایت؛ مجموعه بیانات و پیامهای رهبر معظم انقلاب اسلامی حضرت آیتالله العظمی خامنهای (مد ظله العالی) و آثار انتشارات انقلاب اسلامی، Cibiyar Binciken Kwamfuta ta Ilimomin Musulunci.
- ↑ Golizavareh, Muj'arrifi, Nakze Wa Barrasi Kitabe Sulhe Imam Hassan (A.S), lamba 51 da 52.
- ↑ «چهار کتاب اصلی علم رجال»، Kundin Ilimin Musulunci.
- ↑ «چهار کتاب اصلی علم رجال»، Dakin Karatu na Makarantar Fiƙihu.
- ↑ «ثلاث رسائل فیالجهاد»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ «پژوهشی در زندگی امام سجاد(ع)»، Ɗakin Karatu na Makarantar Faqaha..
- ↑ Khamna'i, Hamase Imam Sajjad (A.S), Muqaddime
- ↑ «کتاب آینده در قلمرو اسلام»، Dandalin Littafin Gobe
- ↑ «معرفی کتاب مسلمانان در نهضت آزادی هندوستان»،Shafin Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Mayakan Musulunci.
- ↑ «کتابشناسی تألیفات آیتالله العظمی خامنهای»، Quds ta Yanar Gizo.
- ↑ «معرفی کتاب مناسک حج»، Shafin Intanet na Taqcheh.
- ↑ «درباره کتاب رساله اجوبة الإستفتائات»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci..
- ↑ «خلوت اُنس»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ «از ژرفای نماز»، Wurin Taro na Littafin Gobe
- ↑ «از ژرفای نماز»، Ɗakin Karatu na Makarantar Faqahat..
- ↑ Khamna'i، Darse Akhlaƙ، Sh 6.
- ↑ «بدان ایدک الله»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci..
- ↑ «گفتاری در باب صبر»، Wurin Taro na Littafin Gobe.
- ↑ «گفتاری در باب صبر»، Dandalin Littafin Gobe.
- ↑ «معیشت مؤمنانه»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ «معیشت پرهیزکارانه»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ «سه کتاب تفسیر از رهبر انقلاب»، Kamfanin Labarai na Mehr.
- ↑ «انتشار نسخه الکترونیکی رساله آموزشی»،Kamfanin Labarai na IQNA.
- ↑ Khamna'i, Gina, Mukaddime Kitab G
- ↑ Khamna'i, Gina, Mukaddime
- ↑ «درسهایی از نهج البلاغه»، Cikakkiyar Hanyar Sadarwar Littattafai ta Gisoom..
- ↑ Khamna'i,Tarhe Kulli Andishe Islami Dar Kur'an, sashen ishara, sh 11-15
- ↑ «نبوتها در نهج البلاغه»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ سیره فرهنگی و سیاسی «پیشوای صادق(ع)» از زبان امام خامنهای Kamfanin Labarai na ana (ANA).
- ↑ معرفی کتاب|کتاب پیشوای صادق تألیف امام خامنهایShafin Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Mayakan Musulunci.
- ↑ Khamna'i, Aftab Dar Mosaf, 1392SH, Sh 5
- ↑ «آفتاب در مصاف»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ سيري در زندگي امام صادق (ع )
- ↑ سيري در زندگي امام صادق (ع )
- ↑ Insane 250 Saleh, 16.
- ↑ Insane 250 Saleh, 15.
- ↑ «همرزمان حسین(ع)»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci
- ↑ «قبسات النور»Cikakkiyar Hanyar Sadarwar Littattafai ta Gisoom.
- ↑ «دو امام مجاهد»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ «عنصر مبارزه در زندگی ائمه(ع)»، Kasuwar Littattafai ta Qa'imiyya..
- ↑ Khamna'i, Bazgashte Be Nahjul Balaga, sh 21
- ↑ «بازگشت به نهجالبلاغه»، Ɗakin Karatu na Kama-da-wane na Alifba.
- ↑ «بازگشت به نهجالبلاغه»، Cibiyar Haɗaɗɗiyar Littattafai ta Gisoom..
- ↑ «گفتاری دربارهٔ حکومت علوی»،Shafin Intanet na Ƙungiyar Injiniyoyi Musulmi.
- ↑ «گفتاری دربارهٔ حکومت علوی»، Ma'ajiyar Littattafai ta Nūsta..
- ↑ «خون دلی که لعل شد»،Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ «پرسش و پاسخ»، Cibiyar Haɗaɗɗiyar Littattafai ta Gīsūm.
- ↑ «جهاد تبیین»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci..
- ↑ «مرگ تاجرانه»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ «کتاب حدیث ولایت»،Shafin Yaɗa Labarai na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i.
- ↑ «حدیث ولایت»، Dandalin Littafin Gobe.
- ↑ «مجموعه بیانات و پیامهای رهبر معظم»، Cibiyar Binciken Kwamfuta ta Ilimomin Musulunci..
- ↑ «عطر شهادت»، Cibiyar Haɗaɗɗiyar Littattafai ta Gisoom..
- ↑ «کتاب حوزه و روحانیت»،Shafin Intanet na Taqcheh.
- ↑ «هنر از دیدگاه مقام معظم رهبری»،Cibiyar Haɗaɗɗiyar Littattafai ta Gīsoom..
- ↑ «راه روشن مدیران»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ «نگاهی به آثار و کتابهای منتشر شده درباره شهید چمران»، Cibiyar Takardun Tarihin Juyin Juya Halin Musulunci..
- ↑ «فلسطین» Shafin Yaɗa Labarai na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i.
- ↑ معارض در نهضتهای انبیا و در انقلاب اسلامی ایران
- ↑ در وحدت و تحزب
- ↑ درست فهمیدن اسلام، Hauze News
- ↑ «دشمن شناسی»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ «دوران جدید عالم»،Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ «اندیشه مقاومت»، Wallafe-wallafen Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ حکومت علوی
- ↑ «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»، Shafin Yaɗa Labarai na Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i.
- ↑ «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»، A cikin shafin Ofishin Kiyayewa da Wallafa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i.
- ↑ نامه رهبر معظم انقلاب به جوانان اروپا و آمریکای شمالی، Shafin Yaɗa Labarai na Ofishin Jagoran Ƙoli na Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ نامه رهبر انقلاب به عموم جوانان غربی،Shafin Yaɗa Labarai na Ofishin Jagoran Ƙoli na Juyin Juya Halin Musulunci..
- ↑ «راه امام راه ما»،Cibiyar Haɗaɗɗiyar Littattafai ta Gisoom.
- ↑ «مصاحبهها»، Cibiyar Haɗaɗɗiyar Littattafai ta Gisoom..
Nassoshi
- «دوران جدید عالم»، (Sabon Zamanin Duniya), Intisharate Inƙilabe Islami, ranar ziyara: 6 Fabrairu 2023M.
- «راه روشن مدیران، (Hanya Mai Haske ga Shugabanni (Sharhin Nahjul‑Balagha).), Intisharate Inƙilabe Islami, ranar ziyara: 6 Fabrairu 2023M.
- «مرگ تاجرانه»، (Mutuwa irin ta ɗan kasuwa), Intisharate Inƙilabe Islami; ranar ziyara: 6 Fabrairu 2023M.
- «جهاد تبیین»، (Jihadin Bayyanawa a Tunani na Ayatollah al‑Uzma Sayyid Ali Khamna'i.), Intisharate Inƙilabe Islami, ranar ziyara: 6 Fabrairu 2023M.
- Ali Khamna'i, «درس اخلاق»، (Darasin gyaran dabi'a), Tehran, Ofishin Wakilin Jagoran Addini (Waliyyul‑Faƙih), a Rundunar Sepah‑e Vali‑e Amr, bugun farko, shekara (1992/1993M).
- Goli Zade Zawware Ƙomshe'i, Golam Rida. Ma'arifi, Naqd wa Barrasi-ye Kitab-e Solh-e Imam Hassan (A.S), (Gabatarwa, suka (bincike), da nazarin littafin Sulhun Imam Hassan A.S)).Cikin mujallar wata-wata littafin Mahe din, Dey Mahe wa Bahman, 2001 M.. lamba 51-52.
- Khamna'i, Sayyid Ali, Aftab Dar Mosaf, Cibiyar Pazhuheshi-ye Farhangi-ye Enqelab-e Eslami, bugu na biyu, shekarar 1392Sh.
- Khamna'i, Sayyid Ali, Gina, Tehran, Mawalafar Fiƙhu na yau. 1398Sh.
- Khamna'i, Sayyid Ali, Hamase Imam Sajjad (A.S) wani nazari ne kan gwagwarmayar siyasa da al'ada ta Imam Sajjad (A.S), Tehran, Intisharate Fiƙh Roz, 1399Sh.
- Khamna'i, Sayyid Ali, Tarhe Kulli Andishe Islami Dar Ƙur'an, Tehran, CibiyarFarhangi-ye Iman-e Jihadi (Sahba) bugu na biyu, 1392Sh.
- Khamna'i, Sayyid Ali, Bazgashte Be Nahjul Balaga, Cibiyar Pazhuheshi Farhangi Enqelab-e Eslami, bugu na daya, shekarar 1372Sh.
- «مصاحبهها»، Cibiyar Haɗaɗɗiyar Littattafai ta Gisoom; ranar ziyara: 23 Disamba 2022M..
- «معرفی کتاب پیشوای صادق تألیف امام خامنهای», (Gabatarwa ga littafin Peshwa‑ye Ṣadiq (Jagora Mai Gaskiya) wanda Imam Khamna'i ya rubuta.), Shafin Bayar da Bayanai na Ƙungiyar Mayaka (Hey’at‑e Razmandegan); ranar ziyara: 19 Disamba 2022M.
- «معرفی کتاب مسلمانان در نهضت آزادی هندوستان».»، (Gabatarwa ga littafin Musulmai a cikin Gwagwarmayar ’Yancin Kan Indiya), Shafin Bayar da Bayanai na Ƙungiyar Mayaka (Hey’at‑e Razmandegan); ranar ziyara: 21 Disamba 2022M.
- «نامه رهبر انقلاب به عموم جوانان غربی»، («Wasiƙar Jagoran Juyin Juya Hali zuwa ga dukkan matasan Yamma (Turai da Arewacin Amurka)), Shafin yada labarai na Ofishin Kiyaye da Wallafa Ayyukan Ayatعllah Sayyid Ali Khamna'i; ranar bugawa: 29 Nuwamba 2015, ranar ziyara: 20 Disamba 2022M.
- «بیانیه "گام دوم انقلاب" خطاب به ملت ایران»، (Sanarwar 'Mataki na Biyu na Juyin Juya Hali zuwa ga al’ummar Iran), A shafin Ofishin Kiyaye da Buga Ayyukan Ayatollah Khamna'i; ranar bugawa: 11 Fabrairu 2019; ranar da aka duba: 20 Disamba 2022M.
- گروههای معارض در نهضتهای انبیا و در انقلاب اسلامی ایران, ranar dubawa: 8 Agusta 2026M.
- درست فهمیدن اسلام، Hauza News, ranar ziyara: 22 Disamba 2022M.
- «گفتاری دربارهٔ حکومت علوی»، (Jawabi game da Gwamnatin Alawiyya (Gwamnatin Imam Ali).), ranar ziyara: 8 Agusta 2026M.
- «معیشت مؤمنانه»، (Rayuwar mumini (rayuwar da ta ginu bisa imani da ƙa’idodin Musulunci).), Gidan Buga Littattafan Juyin Juya Halin Musulunci; ranar ziyara: 7 Fabrairu 2023M.
- «آفتاب در مصاف»، (Rana a fagen fafatawa), Bugun Juyin Juya Halin Musulunci, ranar da aka duba: 20 Disamba 2022M.
- «خون دلی که لعل شد»، (Jinin Zuciya da ya Zama Lu’ulu’u (ko Jaƙi mai daraja).), Gidan Buga Littattafan Juyin Juya Halin Musulunci, ranar ziyara: 2 Fabrairu 2023M.
- «دو امام مجاهد»، (Imamai Biyu Masu Jihadi), Gidan Buga Littattafan Juyin Juya Halin Musulunci, ranar ziyara: 2 Fabrairu 2023M..
- «اندیشه مقاومت»، (Tunani kan Gwagwarmaya ko Akidar Gwagwarmaya), Gidan Buga Littattafan Juyin Juya Halin Musulunci, ranar da aka duba: 23 Disamba 2022M
- «درباره کتاب رساله اجوبة الإستفتائات»، (Game da littafin Risala: Amsoshin Tambayoyin Fikihu (Ajwibat al‑Istifta’at)), Gidan Buga Littattafan Juyin Juya Halin Musulunci, ranar ziyara: 23 Disamba 2022M.
- «معیشت پرهیزکارانه»، (Rayuwa mai takatsantsan da tsoron Allah (rayuwar masu taƙawa)), Gidan Buga Littattafan Juyin Juya Halin Musulunci; ranar ziyara: 7 Fabrairu 2023M.
- «پرسش و پاسخ»، (Littafin 'Saƙonni Uku Game da Jihadi’: Jawaban Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci game da batun Jihadi), Gidan Buga Littattafan Juyin Juya Halin Musulunci, ranar ziyara: 23 Disamba 2022M.
- (سيري در زندگي امام صادق (ع , ranar ziyara: 8 Agusta 2026M.
- «درباره انتشارات انقلاب اسلامی»، (Game da Mu: Game da Gidan Buga Littattafan Juyin Juya Halin Musulunci), Gidan Buga Littattafan Juyin Juya Halin Musulunci, ranar ziyara: 2 Fabrairu 2023M..
- «بازگشت به نهجالبلاغ، (Komawa zuwa Nahjul‑Balagha) Dakin karatu na intanet na Alfaba (Alefba Virtual Library), ranar da aka duba: 20 Disamba 2022M.
- «از ژرفای نماز»،(Daga zurfin salla.), Dandalin Littafi na Gobe), ranar da aka duba: 20 Disamba 2022M..
- «کتاب آینده در قلمرو اسلام, (Littafin Makoma a Cikin Fagen Musulunc) Patogh‑e Ketab‑e Farda (Dandalin Littafin Gobe), ranar ziyara: 21 Disamba 2022M.
- «حدیث ولایت», Patogh‑e Ketab Farda (Taron/Lokacin Littattafan Farda), ranar ziyara: 20 Disamba 2022M.
- «گفتاری در باب صبر.»، (Jawabi game da Haƙuri (Sabr)), Patogh‑e Ketab‑e Farda (Wurin Taron Littafin Gobe); ranar ziyara: 21 Disamba 2022M.
- «فلسطین»، (Falasɗinu), Shafin Bayanan Ofishin Kiyaye da Buga Ayyukan Ayatollah Khamna'i; ranar wallafa: 1 Oktoba 2011; ranar ziyara: 19 Disamba 2022M.
- «همرزمان حسین(ع)»، (Abokan gwagwarmayar Husain (a.s.).), Gidan Buga Littattafan Juyin Juya Halin Musulunci; ranar ziyara: 2 Fabrairu 2023M..
- «کتاب حدیث ولایت»، (Littafin Hadise Wilayat), Shafin Bayanan Ofishin Kiyaye da Buga Ayyukan Ayatollah Khamna'i; ranar wallafa: 4 Mayu 2020; ranar ziyara: 20 Disamba 2022M.
- «انتشار نسخه الکترونیکی رساله آموزشی»، (Fitar da sigar lantarki (e‑book), ta risalar koyarwa ta Ayatollah Sayyid Ali Khamna'i), Kamfanin Dillancin Labarai na IQNA (International Quran News Agency), ranar bugawa: 3 Agusta 2014; ranar da aka duba: 23 Disamba 2022M.
- «نگاهی به آثار و کتابهای منتشر شده درباره شهید چمران»، (Kallo ko nazari kan ayyuka da littattafan da aka wallafa game da Shahid Chamran), Cibiyar Takardun Tarihin Juyin Juya Halin Musulunci; ranar bugawa: 22 Yuni 2022, ranar ziyara: 22 Disamba 2022M.
- «از-ژرفای-نماز «از ژرفای نماز.», (Daga zurfin salla.)Dakin karatu na Makarantar Fikihu (Madrese‑ye Feqahat), ranar da aka duba: 20 Disamba 2022M.
- «پژوهشی در زندگی امام سجاد(ع)»، (Bincike a Rayuwar Imam Sajjad (A.S).), Dakin karatu na Makarantar Fikihu (Madrese‑ye Feqahat), ranar da aka duba: 22 Disamba 2022M.
- «چهار کتاب اصلی علم رجال»، (Littattafai Huɗu na Asali a Ilimin Rijal.), Dakin karatu na Makarantar Fikihu (Madrese‑ye Feqahat), ranar ziyara: 20 Disamba 2022M.
- «نبوتها در نهج البلاغه»، (Annabce‑annabce a cikin Nahjul‑Balagha), Gidan Buga Littattafan Juyin Juya Halin Musulunci; ranar ziyara: 6 Fabrairu 2023M.
- «کتاب حوزه و روحانیت», (Hawza da Malaman Addini, an tattaro daga jawabai na Hazrat Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i (Allah Ya tsawaita inuwarsa)), Shafin Taqcheh, ranar dubawa: 22 Disamba 2022 M.
- «معرفی کتاب مناسک حج»، («Gabatarwa ga littafin Manasik‑e Ḥajj (Hanyoyin Ayyukan Hajji)), Shafin Taqcheh; ranar ziyara: 23 Disamba 2022M.
- چهار_کتاب_اصلی_علم_رجال_(کتاب) «چهار کتاب اصلی علم رجال».»، (Littattafai huɗu mafi muhimmanci da ake amfani da su a ilimin rijal (ilimin tantance amincin masu ruwaito hadisi)), Kundin Ilimi na Musulunci (Daneshnameh‑ye Eslamī), ranar ziyara: 20 Disamba 2022M.
- «سیره فرهنگی و سیاسی «پیشوای صادق(ع)» از زبان امام خامنهای», (Salon rayuwar Al’adu da Siyasa na Jagora Mai Gaskiya (Imam Ja'far al‑Ṣadiq a.s.) daga bakin Imam Khamna'i.), Kamfanin Dillancin Labarai na ANA, ranar wallafa: 29 Yuni 2019; ranar ziyara: 19 Disamba 2022M.
- «عنصر مبارزه در زندگی ائمه(ع)»، (Ka'idar Gwagwarmaya a Rayuwar Imamai (a.s.).), Kasuwar Littattafai ta Qaemiyyeh (Qaemiyyeh Book Market), ranar ziyara: 22 Disamba 2022M.
- «هنر از دیدگاه مقام معظم رهبری»، (Fasaha daga mahangar Jagoran Juyin Juya Hal), Babbar Hanyar Sadarwar Littattafai ta Gisoom; ranar ziyara: 20 Disamba 2022M.
- «پرسش و پاسخ»، (Tambaya da Amsa daga wajen Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatollah al‑Uzma Sayyid Ali Khamna'i), Shafin yanar gizo na cikakken cibiyar littattafai Gisoom’, ranar ziyara: 22 Disamba 2022M.
- «عطر شهادت»، (Littafin Ƙamshin Shahada: tarin jawabai da saƙonnin Jagora Mai Girma, Ayatollah Khamna'i, game da shahidai), Cibiyar/Shafin Littattafai na Gisoom (Gisoom Book Network), ranar ziyara: 22 Disamba 2022M.
- «درسهایی از نهج البلاغه»، (Darussa daga Nahjul Balagha), Cibiyar Sadarwar Littattafai ta Gisom, ranar ziyara: 21 Disamba 2022M.
- «بازگشت به نهجالبلاغه»، (Wannan littafi yana ɗauke da rubutun jawabai na Ayatollah Sayyid Ali Khamna'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, da ya gabatar a taron (kongare), na Nahjul‑Balagha, inda yake bayani kan muhimmancin komawa ga koyarwar Imam Ali (A.S) da ke cikin Nahjul‑Balagha wajen tafiyar da al’umma da shugabanci.), Cikakkiyar Cibiyar Littattafai ta Gisoom، Ranar da aka duba: 20 Disamba 2022M.
- «قبسات النور», (Littafin 'Qabasat al‑Nūr (Ɗigon Haske), zaɓaɓɓun maganganun Ayatullah Khamna'i game da Ahlul‑Bayt (a.s.))، Cibiyar/Shafin Littattafai na Gisoom, ranar ziyara: 22 Disamba 2022M.
- «راه امام راه ما», (Littafin Hanyar Imam ita ce Hanyarmu: Saƙon Ayatollah Sayyid Ali Khamna'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, a ranar tunawa da rasuwar Imam Khomeini (Allah ya ji ƙansaا)، Cibiyar Sadarwar Littattafai ta Gisom, ranar ziyara: 22 Disamba 2022M.
- «.نامه رهبر معظم انقلاب به جوانان اروپا و آمریکای شمالی»، (Wasiƙar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci zuwa ga matasan Turai da Arewacin Amurka), Shafin yada labarai na Ofishin Jagora; ranar bugawa: 22 Janairu 2015, ranar ziyara: 20 Disamba 2022M.
- «سه کتاب تفسیر از رهبر انقلاب»، (Littattafan Tafsiri guda uku daga Jagoran Juyin Juya Hali sun isa baje kolin littattafai.), Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr, ranar wallafa: 14 Mayu 2022; ranar ziyara: 23 Disamba 2022.
- «مجموعه بیانات و پیامهای رهبر معظم»، (Manhajar Hadith‑e Velayat: Tarin Jawabai da Saƙonnin Jagoran Babban Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatollah al‑Uzma Sayyid Ali Khamna'i. Allah ya kara masa tsawon rai-%22-%22-Tarin Jawabai da Saƙonnin Jagora Mai Girma.), Cibiyar Binciken Kimiyyar Addinin Musulunci ta Kwamfuta; ranar wallafa: 8 Maris 2021; ranar ziyara: 20 Disamba 2022M.
- «گفتاری دربارهٔ حکومت علوی»، (Jawabi game da Gwamnatin Alawiyya (Gwamnatin Imam Ali).), Taskar Littattafai ta Nosta; ranar ziyara: 22 Disamba 2022M.
- «کتابشناسی تألیفات آیتالله العظمی خامنهای»، (Jerin Littattafai da Rubuce‑rubucen Ayatollah al‑Uzma Khamna'i.), Quds Online; ranar wallafa: 21 Maris 2016; ranar ziyara: 24 Disamba 2022M.
- منشور حکومت علوی،; ranar ziyara: 6 Fabrairu 2023M.
- گفتاری در وحدت و تحزب, ranar ziyara: 21 Disamba 2022M.
- «خلوت اُنس»، (Khalwat na Kusanci (ko Keɓantacciyar Zamantakewa da Allah)), Gidan Buga Littattafan Juyin Juya Halin Musulunci, ranar ziyara: 7 Fabrairu 2023M.