Jump to content

Fatawar haramcin cin mutuncin jagorori masu alfarma na Ahlus Sunna

Daga wikishia

Fatawar Haramcin Cin Mutuncin Jagorori Masu Alfarma Na Ahlus Sunna (Larabci: فتوى تحريم الإساءة لمقدسات أهل السنة ) ita ce fatawar Ayatullahi Khamna'i Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran game da Haramcin Zagi da cin mutuncin Ramzin Ahlus-Sunna da matan Annabin Muslunci (S.A.W) An fitar da wannan fatawa ne a matsayin martani ga cin mutuncin da Yasir Al-Habib, Malamin Shi'a dan kasar Kuwait da yake yi ga A'isha Matar Annabi (S.A.W) da fatawar adadin malaman Shi'a na Saudiyya kan wannan batu. Fatawar haramcin zagi da cin mutuncin Ahlus-Sunnah ta yadu da yawa a kafafen yada labarai na Larabawa. ta kuma yi tasiri na gaske, Har ila yau wannan fatawa ta bada gudummawa cikin hadin kan Musulmai.

Fage

An fitar da fatawar domin kare alfarmar Ahlus-Sunna ne biyo bayan zagin da wani malamin Shi'a daga Kuwait ya yi ga A'isha matar Annabi (S.A.W), wanda ake kira da Yasir al-Habib, Yasir Habib ya sha magana a kan A'isha da Umar bin Khaddab, wadanda su ke da matsayi na musamman a wajen Ahlus-Sunna.[1] Kuma a shekara ta 2010, Yasir Habib ya gudanar da wani bikin murnar ranar mutuwar A'isha Matar Annabi (S.A.W) a birnin Landan tare da yi mata kalaman batanci [2] An watsa wannan biki na Yassir. a Tashar tauraron dan Adam ta Yaisr Al-Habib mai suna Fadak [3] A ranar tunawa da rasuwar halifa na biyu ne aka yi bikin. An kuma watsa wannan shirin ta hanyar sadarwar tauraron dan adam.[4]

yaduwar kalaman Yasir Al-Habib ya haifar da fushi da nuna rashin amincewar Ahlus-Sunna da kuma haifar da martani a duniyar Musulunci, musamman daga kasashen Ahlu-Sunna, kuma ya haifar da matsaloli da dama ga mabiya Shi'ar Kuwait da Saudiyya,[5] Babban malamin kasar Saudiyya Shailk Abdul Aziz Alu Shaik ya ce wannan kalaman batanci na Yasir Habib Malaman Shi'a na Saudiyya wani taimako daga Allah domin yaduwar Mazhabr Shi'anci a kasashan Larabawa da,Kasashen Musulunci ya samu cikas duka sakamakon wannan kalaman batanci[6]

Bayan afkuwar wadannan abubuwa marasa dadi malaman Shi'a daga kasar Saudiyya sun aiko da neman Fatawa zuwa ga Jagoran juyin juya halin muslunci na Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da bukatar ya bayyana ra'ayin sa na shari'a game da " zagin A'isha da kuma yin kalaman batanci kanta ta"[7]

Nassin Fatawa

Ayatullahi Khamna'i cikin amsarsa da yabar kan neman fatawa da malaman Shi'a a yankin Al-Ahsa na kasar Saudiyya suka aiko gare shi a ranar 30 ga watana Satumba 2010 game da zagin A'isha matar Annabi (S.A.W), ya bada fatawa "Zagin jagororin ‘yan’uwa Ahlus-Sunna da suka hada da zargin matar Manzon Allah A’isha haramun ne. Wannan mas’alar ta hada da matan annabawa baki daya musamman matan shugaban annabawan Allah wato Annabi Muhammad (SAW)."[8]

Fatawar Ayatullah Khamna'i:
'“Zagin Jagororin ‘yan’uwa Ahlus-Sunnah da suka hada da zargin matar Manzon Allah A’isha haramun ne. Wannan al’amari ya hada da matan annabawa baki daya musamman Annabinmu Annabi Muhammad (S.A.W).

(Taskar kwanan wata, Jaridar Resalat, 11 Mehr 1389, shafi na 3.)[9]

Yanda Wannan Fatawa Ta Haifar Da Martani Da Canjin Tunani

Fatawar haramcin cin mutuncin Ahlus-Sunna ta kasance tare da canjin tunani da martani a kafafen yada labarai da kasashen Larabawa. Misali, jaridun "Al-Anba" da "Al-Rai Al-Aam" da aka buga a Kuwait, gidan yanar gizon "Mahit", "Al-Safir" da "Al-Antaqad" na Labanon, "Al-Watan" da "Akaz". " Jaridu a Saudiyya, jaridar "Al-Hayat" da aka buga a London, jaridar "Al-Shoroq" Mirsa da gidan rediyo da talabijin na kasar da wasu tashoshin tauraron dan adam na Larabawa sun ruwaito shi.[10]

Tashar talabijin ta Aljazeera a cikin shirin "Maura'ul-Khobar" tare da halartar masana ta yi nazari kan wannan fatawa da irin rawar da take takawa wajen hadin kai da kusanci a tsakanin mabiya addinin Musulunci daban-daban.[11]

Hakazalika masana daban-daban a kasashen Larabawa sun mayar da martani kan fatawar cin mutuncin Ahlus-Sunna. Daga cikin su Sheikh Ahmad Al-Tayeb Shehin Malamin Jami'ar Azhar ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, an fitar da wannan fatawa a daidai lokacin da ya dace domin hana rarrabuwar kawuna da kuma rufe kofofin fitina,.[12] Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, ya dauki wannan fatawa a matsayin dalilin rufe hanyar da masu niyyar kawo cikas ga hadin kan al'ummar musulmi. Su ma malaman addinin kasar Labanon suna goyan bayan hakan, sun dauki fatawa wajen kawar da makirce-makircen makiya.[13] ga masu niyyar kawo cikas ga hadin kan al'ummar musulmi, bayanin su na karshe ya goyi bayan fatawar Ayatullah Khamene'i..[14]

Ba'arin wakilan Ahlus-Sunna a majalisar musulunci ta Iran a cikin wata sanarwa da suka fitar, sun dauki wannan fatawa a matsayin abin alfahari da karfafa gwiwa ga Ahlus-Sunnar kasar[15] Malaman Ahlus-Sunna na lardin Golestan, ta hanyar fitar da bayanai daban-daban, sun bayyana fatawar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei daidai da tunaninsa da aiki da shi, sun yi hakan ne wanda ke kawar da sharrin fitinar makiya.[16]

A Duba Masu Alaƙa

Bayanin kula

  1. یاسر الحبیب؛ آخوند لندن‌نشین/ دیروز در شبکه «فدک»، امروز در «صوت العترة»‌،
  2. https://www.mashreghnews.ir/news/248345
  3. https://www.mashreghnews.ir/news/248345
  4. https://tn.ai/248228
  5. https://www.khabaronline.ir/news/97531
  6. «روایت‌های جعلی شبکه‌های سلام، فدک و اهل‌بیت از شیعه»، مشرق نیوز.
  7. https://www.khabaronline.ir/news/97817
  8. «استقبال جهان اسلام از استفتای جدید آیت‌الله خامنه‌ای»Jaridar Resalat, 11 Mehr 1389 (Persian calendar), shafi na 3.
  9. https://www.magiran.com/article/2162589
  10. https://www.mashreghnews.ir/news/248345
  11. https://www.mashreghnews.ir/news/614925
  12. «استقبال شیخ الازهر از فتوای رهبر انقلاب»، سایت خبرآنلاین.
  13. «گروه‌های مذهبی لبنان از فتوای مهم رهبر انقلاب حمایت کردند»Kamfanin dillancin labarai na Mehr.
  14. «حمایت از فتوای رهبری درباره حرام بودن توهین به اهل سنت در کنفرانس تقریب لندن»، Shafin KhabarOnline...
  15. «تقدیر نماینده خاش از فتوای رهبری درباره حرمت نمادهای اهل سنت»Shafin KhabarOnline..
  16. «علمای اهل سنت استان گلستان: شیعه و سنی هر نوع توطئه دشمنان اسلام را خنثی می‌کنند مقام معظم رهبری منادی وحدت جهان اسلام است»،Kamfanin dillancin labarai na ISNA.

Nassoshi