Nazariyar Mutum Mai Shekara 250
- Wannan labarin yana game da Mahangar mutum mai shekaru 250. Don ƙarin koyo game da littafi mai taken iri ɗaya, duba shafin Mutum Mai Shekara 250 (littafi).
Mutum Mai shekara 250 (Larabci: نظرية إنسان بعمر 250 سنة) Wata mahanga ce data dogara kan tarihi da siyasa da gwargwarmayar Imaman Shi'a a lokacin Banu Ummaya da Banul Abbas a matsayin wani abu cikakke kuma abin koyi, ita wannan mahanga ana kwatantata da misalin wani mutum ɗan kimanin shekara 250. Wanda ya bijiro da wannan mahanga shi ne jagoran muslunci na ƙasar Iran Sayyid Ali Khamna'i kafin nasarar juyin-juya halin ƙasar, ya yi la'akari rayuwar siyasa ta Imamai duk da bambanci na zahiri da yake tsakaninsu a matsayin wani motsi guda ɗaya mai tsayi wanda ya ci gaba har zuwan shekara 250, gaba ɗayansu (A.S) sun zo ne domin tabbatar da hadafi guda ɗaya wannan hadafi shi kamalar da ɗaukakar ɗan Adam da samar da tsayayyar al'ummar muslunci, saboda tabbatar da wannan hadafin suka bi wani tsari da uslubi mabambanta wajan yaƙar maƙiya a lokacinsu.
Bisa wannan mahanga rayuwar Imamai cikin shekara 250 ta kasu zuwa gida huɗu: lokacin haƙuri da yin shiru cikin shekara 25 na farko, sai wani gajeran lokacin na gwamnatinsu, da lokacin yin ayyuka a sirri da tsara abubuwa har zuwan shekara 20, a ƙarshe sai lokacin raya tinanin da rukunan musulinci a farkon imamancin Imam Sajjad (A.S).
Bayanin Wannan Mahanga
Bisa wannan mahanga ta mutum ɗan shekara 250, an ɗauki Imamai a matsayin wani mutum ɗaya tilo ɗan shekara 250, tin daga shekara ta 11 har zuwa 260 hijira Imamai sun kasance cikin gwagwarmaya ta siyasa ta yaƙar azzalumai da karkacewar azzaluman sarakunan lokacinsu.[1]
Bisa wannan mahanga dukkanin Imamai (A.S) suna matsayin mutum ɗaya, wanda ya yi ƙoƙari a wani lokacin da ya kai shekara 250 cikin tinani da hadafi da yaƙar zalinci domin tabbatar da hadafinshi, wanda ya yi amfani da abubuwa daban-daban domin isar da al'umma zuwa ga muslunci na gaskiya, daga cikin abubuwan da ya yi amfani da su akwai Isma wato katanguwa daga aikata saɓo da amfani da ƙur'ani da maganar Annabi (S.A.W) da masaniyarshi mai zurfi kan al'umma da addinin musulunci, saboda haka ba su karkace daga kan hadafinsu ba, kai ba zai yi wu ba ayi tinanin za su karkace daga kan hadafinsu ba, wannan kuma ya faru ne sakamakon shiryar da al'umma zuwa ga musulunci na gaskiya kuma ingantacce.[2]
Gwagwarmaya ta siyasa mai tsanani tana daga cikin abubuwa masu muhimmanci da suka bambanta rayuwar jagororin Shia cikin zuwan wannan Shekaru na 250,[3] inda cikin wannan shekaru ta bayyana cewa wane ne Imami Ma'asumi wanda baya saɓo wajan bayyana gaskiya ga mutane,[4] bisa wannan mahanga dukkan Imaman da suka zo bayan Imam Husaini (A.S) suna ɗauke da wannan tsari da uslubin yaƙar maƙiyi wanda Imam Husaini (A.S) ya yi yaƙi har ya yi shahada, amma tsarinsu na gwagwarmaya ya canza ne sakamakon canjin yanayi.[5]
Dalilai Kan wannan mahanga
Ali Rida A'arafi ɗaya daga cikin shugabannin Hauza a Iran, ya ce za a iya fahimtar rukuni na wannan mahanga a ra'ayi irin na Shi'a, wanda yake cewa Imamai na Shia duk haske ɗaya ne, kuma akwai wata riwaya da aka rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) ya zo a cikinta cewa su Imamai kamar wani abu ne guda ɗaya a ilimunsu da ɗaukakarsu.[6]
Wanda Ya Ƙirƙiri Wannan Mahanga Da Tarihinta
Jagoran juyin-juya halin muslunci na ƙasar Iran Sayyid Ali Khamna'i kafin nasarar juyin muslunci.[7] Sayyid Ali Allah ya tsareshi ya yi imani cewa akwai tsare na siyasa mai ci gaban cikin yanayi mabanbanci wanda za a iya fahimtar hakan cikin koyarwar da ayyukan Ahlil-Bait (A.S) A zuwan shekaru 250,[8] motsinshi da rayuwarshi cikin wannan lokaci suna fuskantar abu guda ɗaya, da amfani da ƙur'ani da Sunna,[9] amma duk da haka akwai wanda yake ganin cewa wannan mai tinanin ɗanƙasar Iraƙi Sayayid Muhammad Baƙir Sadar wanda yar ayu daga 1313-1359 hijira yana da wannan mahanga kan rayuwar Imamai (A.S) amma bisa wannan mahanga ta Sayyid Ali Khamna'i ta fuskacin abin da ta ƙunsa tafi zama sabuwa da kuma siyasa.[10]
Kazalika Ali Rida A'arafi shugaban Hauza a Iran ya gabatar da wannan mahanga mai ɗauke da sunan Imamai wani mutum ne guda ɗaya, kuma yana ganin wannan imani ne daga cikin rukunai na Ijtihadi gun `Yanshia, kuma wannan abu yana cikin rukuni da asasi na fiƙihu gun `Yanshia.[11]
Abubuwan Da suka Keɓanta Da wannan Lokaci Na Shekara 250
Wannan shekaru 250 suna da wasu abubuwa da suka keɓanta da su, waɗanda zai yi wu a yi bayaninsu kamar haka;
Fitattu Da Sanannun Ayyukan Da Imaman Shi'a
Bisa wannan mahanga da take cewa imamai kamar wani mutum ne guda ɗaya ne, zai yi wu a taƙaita ayyuka da matakai da Imamai (A.S) suka ɗauka zuwa gida huɗu:
- Gwagwarmaya a fagen tinani da ilimi da al'adu a gaban Mulhidanci.[12]
- Fuskantar abin da ya shafi aƙida da fiƙihu na sauran mazhabobi,[13] tare da la'akari abu biyu haɗin kan musulinci a gaban waɗanda ba musulmi ba, da kiyaye aƙidar shi'anci domin ita ce Muslunci na gaskiya.[14]
- Yaƙar ɓata cikin mazhabar shi'a.[15]
- Fuskanta da hamayyar siyasa da yanayin zamantakewa Halifofin Umayyawa da Abbasiyawa.[16]
Raba Wannan Mahanga Zuwa Gida 4
Wannan mahanga mai ɗauke da sunan mutum ɗanshekara 250 ta raba rayuwar Imamai a siyasa zuwa gida huɗu tare da bambanci na zahiri, sune kamar haka;[17]
- . Lokaci na farko: Shi ne shekara 25 wanda ya fara da lokacin halifanci bayan manzon Allah (S.A.W), kuma wannan shi ne lokacin da Imam Ali (A.S) ya rayu a lokacin halifanci bayan Annabi kuma ana kiranta lokacin haƙuri.[18]
- . Lokaci na biyu: wannan shi ne lokacin da imamai suka yi mulki, ta fara daga lokacin da Imam Ali (A.S) ya fara mulki shekara (35-40) da gajeran lokaci wanda Imam Husaini (A.S) ya yi mulki, daga cikin abin da ya bambanta wannan lokacin da sauran lokuta shi ne a cikinshi ne haƙƙi (Halifanci) ya dawo zuwa ga masu shi, kuma a cikinshi ne suka samar da daula wacca ta yi kama da ta Annabi (S.A.W)[19]
- . Lokaci na uku: shi ne lokacin ayyukan ɓoye da tsarin da Imamai (A.S) suka shirya, wannan marhala ta faro a tsakanin shekara ta 41-61 hajira. Abin da wannan lokaci ya shahara da shi shi ne samar da wani yanayi na yin tinani a cikin al'ummar musulmi wanda `yangwagwarmaya suka yi, da kuma tarbiyar wasu matasa waɗanda sune suka taimaki imam Husaini (A.S) wannan ya faru ne a lokacin da suke tsara abubuwa domin tabbatar da hadafin Imam Husaini (A.S).[20]
- Lokaci na huɗu, yana farawa ne da imamancin Imam Sajjad (A.S) shi wannan lokaci ya ci gaba har zuwa 250 na hijira, daga cikin abubuwan da suka faru a wannan lokaci akwai:[21]
- Raya muslunci, al'ummar musulmi a lokacin mulkin Banu Umayya da kafin nan, an samu canje-canje ta inda har abin ya kai su ga manta asalin Muslinci da koyarwar Musulinci, saboda haka sai Imamai suka fara raya asasi da rukunan Muslinci, suka yi duk mai yiyuwa domin gusar da duk wani gurɓataccan tinanin da ba na Musulinci ba wanda ya yaɗu a cikin al'umar musulmi cikin wannan shekarun.[22]
- Kafa wannan gungu na siyasar addini a ɓoye domin kiyaye Musulinci da musulmi, da samar da alaƙa a tsakanin waɗanda suke da tinani iri ɗaya, yana daga cikin abubuwa masu muhimmanci a wannan lokaci akwai batun cewa Imam Ali (A.S) tilas ya ƙalubalanci mahukunta, hakan ta sa yana buƙatar mayaƙa da masu jihadi, to daga cikin abun da ya faru a wannan lokacin samar da wannan yanayi da tabbatar da wannan hadafi.[23]
Raba Wannan Lokaci Zuwa Marhaloli Takwas
Malam A'arafi a muƙaddamar littafinshi mai suna ƙalubalantar masu mulki da Imamai suka yi, ya kasa wannan lokacin na shekarau 250 zuwa gida takwas;
- . Marhalar Imam Ali (A.S).[24]
- . Marhalar Imam Hassan (A.S)[25]
- . Marhalar Miƙewar Imam Husaini (A.S)[26]
- . Marhalar Imam Sajjad (A.S)[27]
- . Marhalar Imam Baƙir (A.S) da Imam Sadiƙ (A.S)[28]
- Marhalar Imam Musa Bin Ja'afar (A.S)[29]
- . Marhalar Imam Rida (A.S)[30]
- . Marhalar ruɗani cikin al'umma da rashin tabbas da fatan yin nasarar ma'abota gaskiya, wannan lokacin ya fara ne daga Imam Jawad (A.S) kuma ya ƙare a lokacin gaiba sugra ta Imam Mahadi (A.S).[31]
Littafin Mutum Mai Shekara 250
Littafi na wannan mahanga ta mutum mai shekara 250, yana ɗauke da laccoci kan wannan mahanga na jagoran juyin-juya halin Musulinci na ƙasar Iran Ayatullah Khamna'i, wannan littafi an buga shi a wata Mu'assasa mai suna cibiyar Sihba don buga da yaɗa littafai, littafin yana ɗauke da shafuka 375 a shekara 2011 da yaran Farisanci, an sake bugashi sau 85 a shekara 2020,[32] kuma wannan littafi an fassarashi da harshe daban-daban, kamar Larabci, Turanci, harshan Urdu, Azariyya, Kurdiyya, harshan Turkiyya, yaran Indiya, harshan Sindiyya, harshan Jamani, harshan Tayiland, harshan Hausa da Faransaci.[33]
Bayanin kula
- ↑ Khamenei, Hamrazmane Husaini, 1397 (Hijira Shamsiyya), shafi na 6
- ↑ Khamenei, Do Imam Mujahid, 1396 (Hijira Shamsiyya), shafi na 61.
- ↑ Siyahpush, Siyasa, 1398 (Hijira Shamsiyya), shafi na 483.
- ↑ Jabra'ili, Riwate Rahbari, 1398 (Hijira Shamsiyya), shafi na 319
- ↑ Khamenei, Hamrazmane Husaini, 1397 (Hijira Shamsiyya), shafuka na 5, 99, 100, da 236.
- ↑ A'rafi, Khurshi Ashura, 1396 (Hijira Shamsiyya), shafuka na 24 - 25
- ↑ Ghaffari, Az Nimeh Khordad, 1398 (Hijira Shamsiyya), shafi na 74; Khamenei, Isane 250 saleh, 1391 (Hijira Shamsiyya), shafi na 15
- ↑ Ghaffari, Az Nimeh Khordad, 1398 (Hijira Shamsiyya), shafi na 75
- ↑ Khamenei, Hamrazmane Husaini, 1397 (Hijira Shamsiyya), shafi na 61.
- ↑ Najafi, Mu'allifahaye Tamaddunsazi dar Maktab Siyasi Imam Rida (A.S.), 1396 (Hijira Shamsiyya), shafi na 29
- ↑ A'rafi, Khurshid Ashura, 1396 (Hijira Shamsiyya), shafuka na 24 - 45
- ↑ A'rafi, Khurshid Ashura, 1396 (Hijira Shamsiyya), shafuka na 31.
- ↑ A'rafi, Khurshid Ashura, 1396 (Hijira Shamsiyya), shafuka na 31
- ↑ A'rafi, Khurshid Ashura, 1396 (Hijira Shamsiyya), shafuka na 31
- ↑ A'rafi, Khurshid Ashura, 1396 (Hijira Shamsiyya), shafuka na 31
- ↑ A'rafi, Khurshid Ashura, 1396 (Hijira Shamsiyya), shafuka na 33
- ↑ Khamenei, Hamraznmane Hussein, 1397, p. 61. 1
- ↑ Khamenei, Hamraznmane Hussein, 1397, p. 118.
- ↑ Khamenei, Hamraznmane Hussein, 1397, p. 124.
- ↑ Khamenei, Hamraznmane Hussein, 1397, p. 124-148
- ↑ Khamenei, Hamraznmane Hussein, 1397, p. 124-150
- ↑ Khamenei, Hamraznmane Hussein, 1397, p. 150-151
- ↑ Khamenei, Hamraznmane Hussein, 1397, p. 154
- ↑ Arafi, Khurshid Ashura, 1396, p. 34.
- ↑ Arafi, Khurshid Ashura, 1396, p. 35.
- ↑ Arafi, Khurshid Ashura, 1396, p. 35-36.
- ↑ Arafi, Khurshid Ashura, 1396, p. 36.
- ↑ Arafi, Khurshid Ashura, 1396, p. 36-37.
- ↑ Arafi, Khurshid Ashura, 1396, p. 38.
- ↑ Arafi, Khurshid Ashura, 1396, p. 38.
- ↑ Arafi, Khurshid Ashura, 1396, p. 39.
- ↑ Khamenei, Insane 250 Saleh p. 4-5 1
- ↑ «انسان 250 ساله تبیین استراتژی امامان در جریانِ مبارزه سیاسی»، Hukumar labarai Fars
Nassoshi
- Al-A’rafi, Ali Reza, Khorshid Ashura [Fassarar: Shams Ashura], Wanda ya shirya: Mohammad Azadi, Ishraq va Irfan Foundation [Fassarar Ishraq va Irfan Foundation], Qom, 1396 AH.
- «انسان 250 ساله تبیین استراتژی امامان در جریانِ مبارزه سیاسی»،Kamfanin Dillancin Labarai na Fars, fitowa ta 11, Azar 1399 AH, Dubawa: 4 Ordibehesht 1401 AH.
- Jibrili, Yasser, Labarin Jagora, Cibiyar Nazarin Al'adun Juyin Musulunci, 2010.
- Al-Khamenei, Sayyid Ali, Mutum mai Shekara 250 [Fassarar: Mutum mai Shekaru 250], Cibiyar Sahabbai,
Khamenei, Sayyid Ali,Do Imam Mujahid, Cibiyar Nazarin Al'adun Juyin Musulunci, 2017.
- Al-Khamenei, Al-Sayed Ali, Hamrazman Hussein (Al-Ta'rib: Rafaq Darb Al-Hussein), Cibiyar Nazarin Al'adun Juyin Juya Halin Musulunci, 2018.
- Siahposh, Amir, Siyasat, Cibiyar Nazarin Al'adun Juyin Musulunci, 2010.
- Al-Ghaffari, Mustafa,Az Nimeh Khordad, Cibiyar Nazarin Al'adun Juyin Musulunci.
- Al-Najafi, Musa, As-siyasa Lil Imam Riza, Arma, 1396sh.