Jump to content

Wasiƙar Ayatullah Khamene'i zuwa ga Ɗaliban Jami'a Masu Goyan Bayan Palasɗinawa

Daga wikishia

Wasiƙar Ayatullah Khamena'i zuwa ga ɗaliban jami'a a Amurka masu goyan bayan Gaza (Laabci: رسالة آية الله الخامنئي إلى الطلاب الداعمين لغَزَّة في أمريكا) Wata wasiƙa ce ta neman haɗin kai da nuna jin ƙai da jagoran jamhuriyar muslunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i wace cikinta ya bayyana yabawarsa da fata tare da masu goyan bayan palasɗin a Amurka da suke nuna rashin amincewarsu kan hare-haren da haramtacciyar ƙasar Isra'ila take kaiwa kan zirin Gaza tun bayan ofireshin ɗin Tufanul Al-Aksa waɗannan ɗalibai sun shirya jerin gwano a jami'o'in amurka.

Abin da Take Tattare Da Shi

Ayatullahi Khamna'i cikin wannan wasiƙa ya kira ga matasan da suke nuna goyan bayansu ga Falasɗinu matsayin wani ɓangare daga gwagwarmayar neman ƴanci saɓanin gwamnatocinsu, sun fara fito na fito mai daraja kan haramtacciyar ƙasar Isra'ila don nuna rashin amincewa da kashe fararen hula. Sun tsaya kan hanya ta daidai a cikin tarihi, haka kuma ya yi ishara kan rawar da ƙasar Birtaniya ta taka cikin samar gwamnatin sahayoniya. haka nan ya gabtar da Amurka da Ingila a matsayin mafi girman masu goyan bayan Sahayoniya, Kuma ya jaddada haƙƙin Falasdinawa na kare kansu, Ayatullahi Khamna'i cikin wannan wasiƙa ya lissafa tsayuwa ƙyam cikin hanyar gaskiya matsayin darasi da kur'ani ya koyar da dukkanin musulmi da dan Adam. haka nan ya tunatar da cewa jamhuriyar muslunci ta Iran ya faɗaɗa fagen gwagwarmaya tare da ƙarfafa shi. A ƙarshen wasiƙar ya yi wasiyya ga matasan da yake aika wannan saƙo zuwa gare su da cewa su nemi sanin kur'ani؛[1] don haka aka ce Ayatullahi Khamna'i a cikin wannan wasiƙa kamar dai sauran wasiƙu guda biyu ya buƙaci waɗannan matasa domin fahimtar addinin muslunci, su koma zuwa ga litattafan muslunci na asali, ka da su tasirantu da maganganu da fassarorin gabashi da yammacin duniya da makarantunsu daban-daban.[2]

Fitowar Wasiƙar

Wasikar Ayatullahi Khamna'i zuwa ga ɗaliban da ke goyon bayan Falasɗinu an fitar da ita a ranar 5 ga watan Khordad, shekara ta 1403 hijira shamsiyya (25 ga Mayu, 2024 Miladiyya) kuma an wallafa ta a ranar 10 ga watan Khordad.[3] Wannan wasika ta Ayatollah Khamenei an fitar da ita bayan zanga-zangar ɗaliban jami'o'in Amurka da ke adawa da kisan kiyashi da kashe-kashen da Isra'ila ke yi wa mutanen Gaza. Wannan zanga-zanga ta fara ne a ranar 17 ga Afrilu, 2024, daga wasu jami'o'in Amurka, sannan ta bazu zuwa wasu ƙasashen yamma.[4] Zanga-zangar lumana ta ɗaliban jami'o'in Amurka don goyon bayan Gaza ta fara a ranar 17 ga Afrilu, 2024 daga wasu jami'o'in Amurka, sannan ta bazu zuwa wasu ƙasashen yamma.[5] Yunƙurin ƴansanda na tarwatsa waɗannan matasa a amurka da wasu ƙasashen yammacin turai tare da korarsu daga jami'o'in da suke karatu ya fuskanci martani daban-daban daga ƙasashen duniya.[6]

Martani

Buga wannan wasiƙar ya haifar da martani daban-daban kuma kafofin watsa labaru na duniya sun nuna hakan.[7] Ba'arin kamfanonin labarai sun labarta cewa mutane miliyan goma sha biyar suka bibiyi shafin dandanlin kafar sada zumunci a shgafin dfa ake danganta shi ga Ayatullahi Khamna'i game da batun wasiƙar da ya fitar zuwa ga matasan ɗaliban jami'a na amurka a ranar 31 ga watan mayu shekara ta 2024.[8]

Wasiƙar Matasan Ƙasar Beljiyom Zuwa Ga Ayatullahi Khamna'i

Wasu jama'a daga matasan Beljiyom cikin amsar da suka bayar ga wannan wasiƙa, sun rubuta wata wasiƙa zuwa ga Sayyid Ali Khamna'i, wani sashe daga cikin wannan wasiƙa ya kasance kamar haka: Haƙiƙa mun yi matuƙar jin dadin saƙon ku na kira zuwa adalci da neman gaskiya, da kuma jajircewarku wajen kare haƙƙoƙin Falasɗinu da sauran masu zalunci a duniya.

Kokarinku na fahimtar juna, adalci da haɗin kai wajen fuskantar ƙalubalen da muke ciki yana da matukar muhimmanci, kuma mun ƙuduri aniyar zurfafa fahimtarmu game da addinin Musulunci.[9]

Wannan wasiƙa an buga tare da baza ta duniya cikin kwafin harsunan Farsi, Ingilishi, Faransanci da Larabci, cikin Hashtag Letter4Leader.[10]


Nassin Wannan Wasiƙar

بسم الله الرّحمن الرّحيم
Da sunan Allah Mai rahama Mai Jin ƙai Ina rubuta wannan wasiƙar zuwa ga matasan da farkakken lamirinsu ya motsar su don kare yara da matan Gaza da ake zalunta.

Ya ku matasa dalibai da ke Amurka! Wannan shi ne sakonmu na tausayawa da kuma goyon bayanmu gare ku. Yanzu kuna tsaye a bangaren daidai na tarihi - wanda ke gudana a halin yanzu. Yanzu kun kafa wani bangare na gwagwarmaya, kuma a ƙaraashin yin matsin lamba ga zaluncin gwamnatinku - wacce ke ba da kariya ga gwamnatin sahyoniya ta mamaya da rashin tausayi - kun fara yin gwagwarmaya mai daraja.

Babban fagen gwagwarmaya da ke a wuri mai nisa ya kasance yana fito na fito a tsawon shekaru tare da hangen nesa da jin ku na yanzu. Manufar wannan gwagwarmaya ita ce dakatar da irin zaluncin da wata Cibiyar ta'addanci da rashin tausayi da ake kira "Sahyoniyawa" ta ke yi wa al'ummar Palasɗinu tun shekaru da suka gabata tare da jefa su cikin mawuyacin hali da azabtarwa bayan mamaye ƙasarsu. Kisan gillar da gwamnatin wariyar launin fata ta Sahayoniya ta ke yi a yau ci gaba ne na muguwar halayyar da suke yi ne a cikin shekarun da suka gabata.

Falasɗinu ƙasa ce mai cin gashin kanta mai al'umma da ta kƙnshi Musulmai, Kirista da Yahudawa, kuma tana da dogon tarihi. Bayan yakin duniya, 'yan jari-hujjar cibiyar Sahayoniya tare da taimakon gwamnatin Burtaniya, sannu a hankali sun shigo da dubban 'yan ta'adda sannu a hankali cikin wannan ƙasa; Suka mamaye biranenta da ƙauyukanta; Dubun dubatar mutane ne aka kashe ko aka kore su zuwa ƙasashe makwabta; Sun kwace gidaje, kasuwanni, da gonaki daga hannunsu, suka kafa gwamnati mai suna Isra’ila a cikinƙkasar Falasɗinu da suka kwace.

Babban mai goyan bayan wannan gwamnatin kwace, bayan taimakon farko na Birtaniya, ita ce gwamnatin Amurka, wadda ta ci gaba da goyon bayanta a siyasance da tattalin arziki da makamai ga wannan gwamnatin, har ma cikin sakaci da bazai yiwu a yafe ba ta bude mata hanyar kera makaman kare dangi da makaman nukiliya ta taimaka masa ta wannan hanya.

Tun daga rana ta farko gwamnatin sahyoniyawan ta yi amfani da manufar "ƙarfin ƙarfe" a kan al'ummar Palasɗinu da ba su da kariya, tare da yin watsi da duk wata kima, ta dan Adam da ta addini, a kowacce rana tana ƙara aikata zalunci da ta'addanci da danniya.

Gwamnatin Amurka da kawayenta ba su ma nuna adawa da wannan gwamnatin ta'addanci da zalunci da ke cigaba ba. Har yau, wasu kalaman gwamnatin Amurka dangane da munanan laifuka a Gaza sun fi a munafunce fiye da na gaske.

“Fagen gwagwagwarmaya” ya taso ne daga cikin wannan yanayi mai duhu da rashin tabbas wanda kuma da kafa gwamnatin “Jamhuriyar Musulunci” a Iran ta faɗaɗa ta tare da ba shi karfin gwiwa.

Shugabannin yahudawan sahyoniyanci na ƙasa da ƙasa, wanda ya zamo galibin kamfanonin yada labarai a Amurka da Turai nasu ne ko kuma suna ƙarƙashin tasirin kuɗaɗensu da cin hancinsu, sun gabatar da wannan gwagwarmaya ta mutuntaka da jajircewa a matsayin ta'addanci! Shin al'ummar da ta kare kanta a cikin ƙasarta daga laifukan sahyoniyawa 'yan mamaya 'yan ta'adda ne? Sannan shin taimakon ƴan Adamtaka da ake baiwa wannan al'umma da ƙarfafa makamanta ana iya ɗaukarsa a matsayin ta'addanci? Shugabannin mulkin mallaka na duniya ba sa jin tausayin ra'ayoyin ɗan adam. Suna goyon baya ga azzalumar gwamnatin ta'addanci ta Isra'ila, kuma suna kiran gwagwarmayar Palasɗinawa da ke kare 'yancinta, tsaro da 'yancin kai, a matsayin "'yan ta'adda"!

Ina so in tabbatar muku cewa a yau al'amura sun canza. Wata makoma tana jiran yankin da ke da muhimmanci na yammacin Asiya. Lamiri da yawa a duniya suna kara farkawa kuma gaskiya tana bayyana. Kuma fagen gwagwarmaya ya yi ƙarfi kuma zai ƙara yin ƙarfi sosai. Tarihi kuma yana cikin canzawa. Baya ga ku, ɗaliban jami'o'i da dama a Amurka, jami'o'i da jama'ar wasu ƙasashe ma sun tashi tsaye. Suna masu goyon baya da tallafawa malaman jami'a gare ku dalibai wani abu ne mai mahimmanci kuma mai tasiri. Wannan zai iya zama ɗan kwantar da hankali idan akai la’akari da tsananin matakan ƴan sandan da gwamnati ke yi da kuma matsin lamba da suke yi. Ina kuma tausaya muku matasa kuma ina girmama matsayinku.

Koyarwar Alkur'ani gare mu Musulmi da dukkan mutanen duniya shi ne tsayawa kan tafarkin gaskiya فَاستَقِم کَما اُمِرت” (Suratul Hud, bangare na aya ta 112) kuma koyarwar Alkurani dangane da alaƙoƙin da su ke tsakanin mutane ita ce: “kada ku yi zalunci kuma kada ku bari a zalince ku”: (لا تَظلِمونَ وَ لا تُظلَمون) (Suratul Baƙarah, aya ta 279) fagen gwagwarmaya da bin waɗannan umarni da ɗaruruwan makamantansu ta ke ci gaba kuma zata samu kaiwa ga nasara; Da yardar Allah

Ina Mai Shawarartarku Da Ku San Alkur'ani.

Sayyid Ali Khamenei 25/5/2024



(: : )


.[11]

Bayanin kula

  1. «نامه حضرت آیت‌الله خامنه‌ای به دانشجویان حامی مردم فلسطین در دانشگاه‌های ایالات متحده آمریکا»،Shafin yanar gizo na ofishin adana da wallafa ayyukan Ayatollah Ali Khamenei
  2. Ali Reza Biaban-Nord Sarvostani ya rubuta a cikin jaridar Farhikhtegan suna mai da hankali kan fahimtar Islam ba tare da wata hukunci na gaba ba
  3. «نامه حضرت آیت‌الله خامنه‌ای به دانشجویان حامی مردم فلسطین در دانشگاه‌های ایالات متحده آمریکا»Shafin yanar gizo na ofishin adana da wallafa ayyukan Ayatollah Ali Khamenei.
  4. Ku duba Azhari، « Shekeste Marefic Sukut Dar dele Amrika »، Ruznameh Farhgtan.
  5. «بازتاب نامه رهبر انقلاب به دانشجویان آمریکا در شبکه تی‌آرتی ترکیه»، Kamfanin dillancin labarai na Mehr.
  6. Alal mislai ku duba «واکنش سازمان ملل به بازداشت دانشجویان حامی فلسطین در دانشگاه‌های آمریکا»، Kamfanin dillanincin labarai na IRNA.
  7. «بازتاب نامه رهبر انقلاب به دانشجویان آمریکا در فضای بین‌المللی»، Kamfanin dillancin labarai na Mehr
  8. «بازدید ۱۵ میلیونی توییت حساب کاربری رهبر انقلاب»،Masharaq News
  9. «نامه جوانان بلژیکی خطاب به رهبر انقلاب اسلامی»Ofishin Adana da Buga Ayyukan Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.
  10. «نامه جوانان بلژیکی خطاب به رهبر انقلاب اسلامی»،Ofishin Adana da Buga Ayyukan Ayatollah Sayyid Ali Khamenei
  11. «نامه حضرت آیت‌الله خامنه‌ای به دانشجویان حامی مردم فلسطین در دانشگاه‌های ایالات متحده آمریکا»، وبگاه دفتر حفظ و نشر آثار حضرت آیت‌الله العظمی خامنه‌ای.

Nassoshi

«بازتاب نامه رهبر انقلاب به دانشجویان آمریکا در شبکه تی‌آرتی ترکیه»، Jaridar Mehr, ranar rubuta labarin: 10 ga Yuni, 1403 na Hijira, ranar ziyara: 11 ga Yuni, 1403 na Hijira.