Jump to content

Tsarin Gaba ɗaya Na Tunanin Musulunci A Cikin Alƙur'ani (Littafi)

Daga wikishia
Tsarin Gaba ɗaya Na Tunanin Musulunci A Cikin Alƙur'ani
MarubuciSayyid Ali Khamna'i
Tarihin rubutu1974 miladiyya
Maudu'iAƙidun Musulunci
SaloTafsirul Maudu'i
HarsheFarsi
Adadin JildiGuda ɗaya
Tarjama zuwa sauran harsunaLarabci, Ingilishi, Jamusanci, Azeri, Italiyanci, Sinanci
Mai bugawaOfishin yaɗa al'aun Musulunci da cibiyar Sahba cibiya ta jihadi
Wurin da aka buga shiTehran
Tarihin bugawaBugu na farko ta hannun ofishin yaɗa al'adun Musulunci: a shekarar 1975 miladiyya da cibiyar Sahba a shekarar 2013 miladiyya
Yawan bugawafiye da kwafi duba ɗari

Tsarin Gaba ɗaya na Tunanin Musulunci a cikin Alƙur'ani (Larabci: مشروع الفکر الإسلامی فی القرآن) littafi ne na Sayyid Ali Husaini Khamna'i , jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Littafin yana bayani ne kan ginshiƙan aƙidun Musulunci kan asasin Kur'ani, kuma marubucin ya gabatar da shi a matsayin tushen tunani na kafa tsarin gwamnatin Musulunci. Wannan littafi a haƙiƙanin gaskiya rubutaccen tsari ne na jerin laccocinsa da ya gabatar a watan Ramadan na shekara ta 1974 miladiyya a birnin Masshad, wato shekaru huɗu kafin juyin juya halin Musulunci na Iran na 1979.

Littafin ya bi hanya mai tsari wadda ta dogara da Kur'ani, inda yake nazartar batutuwan Musulunci a matsayin wani tsari guda mai haɗin kai. Haka kuma yana ƙoƙarin kauce wa gabatar da ra'ayoyin mutum ɗaya, yana mai ƙoƙarin fitar da muhimman ƙa'idojin Musulunci daga nassosin Kur'ani. Ɗaya daga cikin siffofinsa shi ne gabatar da sabon hangen nesa game da wasu muhimman ma'anonin addini kamar wilaya (Jagoranci).

An tsara wannan littafin cikin manyan sassa huɗu: Imani, Tauhidi, Annabta (Nubuwwa), da Wilaya, kuma kowane sashe yana ɗauke da zaman laccoci da dama.

Muhimmanci

An ɗauki littafin "Tsarin Gaba ɗaya na Tunanin Musulunci a cikin Alƙur'ani" a matsayin ɗaya daga cikin ayyukan Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i wajen farfaɗo da tunanin Musulunci.[1] Haka kuma ana la'akari da shi a matsayin littafin da ke bayyana tsarin tunaninsa gaba ɗaya.[2] A cewar Ayatullah Khamna'i da kansa, abubuwan da ke cikin wannan littafi sun kasance tushen tunani na kafa tsarin gwamnatin Musulunci.[3] An shirya darussa da shirye-shirye daban-daban a hauzozin ilimi (Makarantu na addini ) da kuma jami'o'i dangane da wannan littafi. Daga cikin su akwai: Shirin horas da malamai (Tarbiyyar masu koyarwa),[4] Darussan nazari kan littafin,[5] Gasar karanta littafin,[6] Da kuma karatun littafin tare a rukuni (karatun haɗin gwiwa)[7] Bugu da ƙari, ana koyar da littafin Tsari na Gaba ɗaya na Tunanin Musulunci a cikin Alƙur'ani a wasu jami'o'i a matsayin darasi.[8]

Jerin Zaman Laccocin Tsarin Gaba ɗaya na Tunanin Musulunci a cikin Alƙur'ani

Tsarin Gaba ɗaya na Tunanin Musulunci a cikin Alƙur'ani sakamako ne na laccoci 28 da Sayyid Ali Husaini Khamna'i ya gabatar a lokacin bazarar shekara ta 1974 miladiyya a Masallacin Imam Hassan Mujtaba (A.S) da ke birnin Masshad (A ƙarshen kasuwar Sarshur).[9]A lokacin yana da shekara 35 da haihuwa, kuma a watan Ramadan yana gabatar da lacca kowace rana bayan sallar azahar da la'asar kan batun tsarin Gaba ɗaya na tunanin Musulunci a cikin Alƙur'ani. A cikin waɗannan laccoci, ya kasance yana bayyana tsarin aƙidun Musulunci daga mahangar Alƙur'ani, ta hanyar da take sa mutane su fara tunanin gina al'umma da tsarin zamantakewar Musulunci.[10] Bayan watanni kaɗan da kammala waɗannan zama ns laccoci, kuma sakamakon darussan da yake yi kan Sharhin Nahjul Balaga, sai gwamnatin Shah ta Iran ta kama shi ta kuma tsare shi.[11]

A cewar Ayatullah Khamna'i a cikin gabatarwar littafin, manufar waɗannan zama na laccoci ita ce nemo muhimman ginshiƙan tunanin Musulunci a cikin ayoyin Alƙur'ani. Sannan a bayyana su ta hanyar bayanin da yake koya wa masu sauraro hanyar yin tadabburi (zurfin tunani) a cikin Alƙur'ani. Haka kuma, a inda ya dace, ana amfani da ingantattun riwayoyi daga Annabi (S.A.W) da kuma Imaman Shi'a domin ƙarfafa da bayyana waɗannan ginshiƙai na tunani.[12]

Abubuwan Da Littafin Ya Ƙunsa

Littafin Tsarin Gaba ɗaya na Tunanin Musulunci a cikin Alƙur'ani ya ƙunshi manyan sassa huɗu: Imani, Tauhidi, Annabta (Nubuwwa), da Wilaya (Jagoranci). A ƙarƙashin kowane sashe kuma an kawo zaman laccoci da suka shafi[13] batun imani,marubucin yana bayyana cewa imani na gaskiya shi ne imani da mutum ya yi da sani, fahimta, da kuma ɗaukar alhakin abin da ya yi imani da shi. Wato imani ba kawai furuci ba ne, sai an haɗa shi da fahimta da kuma aiki. Tauhidi: A wannan sashe, bayan gabatar da ma'anar tauhidi, marubucin ya bayyana yadda tauhidi yake bayyana a rayuwar mutum mai imani da Allah. A cewarsa, mutum mai tauhidi ba ya miƙa wuya ga ikon ƙarya kamar su: Iblis, Ɗagutai (Azaluman shugabanni ko tsarin da ke yaƙi da Allah), da kuma sha'awoyin zuciya. Annabci: A wannan sashe, bayan bayyana ma'anar annabci da kuma makiyan annabawa, marubucin ya yi bayani kan nauyin da ke kan musulmi masu imani da annabci. Haka kuma ya nuna cewa ƙarshen tafiyar annabawa shi ne nasara tabbatacciya, duk da wahalhalun da suka fuskanta. Wilaya (Jagoranci): A sashe na ƙarshe, bayan bayanin ma'anar wilaya, an tattauna wasu muhimman fannoni na wannan ra'ayi, kamar: Haɗin kai na cikin gida a cikin al'ummar Musulunci, yadda al'ummar Musulmi za su yi hulɗa da al'ummomin da ba Musulmi ba, da kuma dangantaka tsakanin Imami (shugaba) da al'umma.[14]

Bahasosin wannan littafi ana la'akari da su matsayin tafisrul maudu'i.[15]

Siffofin Littafin

A cikin gabatarwar littafin, Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i ya bayyana manyan siffofi uku na muhawarar da littafin ya ƙunsa kamar haka:

  1. .Fitar da ilimin Musulunci daga kasancewa kawai a cikin tunani, tare da nuna cewa suna da alaƙa kai tsaye da ayyukan da ya kamata a aikata da kuma rayuwar zamantakewa.
  2. .Nazarin batutuwan tunanin Musulunci cikin tsari guda mai haɗin kai, wato a duba su a matsayin sassan wani tsari ɗaya, domin a iya fitar da cikakkiyar aƙida ko manhaja ta rayuwa (Ideology) wadda ta dace da rayuwar mutum mai fannoni da dama.
  3. .Fitar da muhimman ƙa'idojin Musulunci daga manyan tushe na addini, wato Kur'ani, tare da nisantar ra'ayoyin mutum ko son rai.[16]

Sauran siffofin littafin sun Kasance kamar Haka:

  • Gabatar da hangen tunanin Musulunci ga duniya baki ɗaya, ba ga Musulmi kaɗai ba.
  • Bayar da cikakken hangen tauhidi, tare da la'akari da fannoni daban-daban na rayuwar ɗan Adam.
  • Gabatar da sabon fahimta game da wasu muhimman ma'anonin addini, kamar wilaya (Shugabanci).
  • Daidaita batutuwan littafin da tarihin siyasa da gwagwarmayar Imaman Shi'a (A.S) wajen ƙoƙarin kafa gwamnatin Musulunci.
  • Mai da hankali kan babbar matsalar da al'ummomin duniya musamman al'ummar Musulmi ke fuskanta, wato raunin imani.
  • Koyar da masu karatu hanyar yin tadabburi da zurfin tunani a cikin Kur'ani.[17]

Daga cikin siffofin zahiri na wannan littafin shi ne cewa hotunan takardun polycopy (Kwafin takardun da aka yi amfani da su a lokacin laccocin) an saka su a ƙarshen kowane zama na lacca da ya shafe su.[18]

Maƙaloli Masu Alaƙa

Bayanin kula

  1. Khamna'i, Ɗarhe Kulli Andishe Islami Dar Kur'an, sashe ishara, sh 17
  2. Khamna'i, Ɗarhe Kulli Andishe Islami Dar Kur'an, sashe ishara, sh 20
  3. «ماجرای کتاب طرح کلی اندیشه اسلامی در قرآن»، Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyuka da Rubuce-rubucen Ayatullahi Khamna'i..
  4. «دوره تربیت مدرس طرح کلی اندیشه اسلامی در قرآن برگزار می‌شود»،‌ Kamfanin Dillancin Labarai na Hukuma na Hauza.
  5. «پایان فصل سوم دوره مطالعاتی بهار اندیشه در یزد»، Shafin yanar gizon Halqe-ye Vaṣl..
  6. «مسابقه مجازی کتابخوانی طرح کلی اندیشه اسلامی در ویژه طلاب قرآن برگزار شد»،Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim..
  7. «سلسله جلسات همخوانی کتاب طرح کلی اندیشه اسلامی در قرآن»،Shafin yanar gizon Halqe-ye Vaṣl.
  8. «کتب معارف اسلامی به ادبیات تحلیل و کارآمدی دین تغییر کند»،Kamfanin Dillancin Labarai na Hukuma na Hauza.
  9. Khamna'i, Ɗarhe Kulli Andishe Islami Dar Kur'an, sashe ishara, sh 11-15
  10. Khamna'i, Ɗarhe Kulli Andishe Islami Dar Kur'an, sashe ishara, sh 11-12
  11. Khamna'i, Ɗarhe Kulli Andishe Islami Dar Kur'an, sashe ishara, sh 13
  12. Khamna'i, Ɗarhe Kulli Andishe Islami Dar Kur'an, sashe ishara, sh 37
  13. Khamna'i, Ɗarhe Kulli Andishe Islami Dar Kur'an, sashe ishara, sh 22
  14. «طرح کلی اندیشه اسلامی در قرآن»،Shafin yanar gizon Sahba.
  15. «ماجرای کتاب طرح کلی اندیشه اسلامی در قرآن»، Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyuka da Rubuce-rubucen Ayatullahi Khamna'i..
  16. Khamna'i, Ɗarhe Kulli Andishe Islami Dar Kur'an, sashe ishara, sh 36-37
  17. Khamna'i, Ɗarhe Kulli Andishe Islami Dar Kur'an, sashe ishara, sh 16-20
  18. Khamna'i, Ɗarhe Kulli Andishe Islami Dar Kur'an, sashe ishara, sh 22-25

Nassoshi